“SANADIN ƘADDARATA”

Page-41

by @zahratulqalam51

*FASAHA WRITER'S ASSOCIATION*
     (*F.W.A)*©✍️
     ⭐⭐⭐

Ƙungiya masu aiki cikin salon hikima da fasaha gurin juya tunanin al-umma, kaifin alƙalumansu ya zarta takobi ©✍
___________________________________________________



بسم الله الرحمن الرحيم.
اللهم صلي وسلم على نبينا محمد. 




❁ 𝐒𝐀𝐍𝐀𝐃𝐈𝐍 Ƙ𝐀𝐃𝐃𝐀𝐑𝐀𝐓𝐀 ❁ 




Free book📓



By: _*🌹𝑍𝑎ℎ𝑟𝑎-𝑡𝑢𝑙-𝑄𝑎𝑙𝑎𝑚🖋️*_




Page4️⃣1️⃣






WASHE GARI. DA SAFE.

"Nuriyyah ya kamata mu je mu sanarwa su Momy komai, ayi gaggawar tsayar da wannan lamarin" faɗin Asma'u tana kallona cikin rauni, duk da na san cewa tana ƙoƙarin danne abun da ta ke ji a cikin zuciyarta. A hankali na ce da ita, "yanzu ne lokacin da ya dace, mu je mu samu Momy mu yi mata bayanin komai, kuma na san za ta fahimcemu sosa...".

"Me za ku sanarwa Momy? What's wrong?" Ayusha da ta shigo ɗakin yanzu ta katseni da faɗin haka, shiru mu ka yi daga ni har Asma'u ba wanda ya ce mata ƙala, kamar gaske ta iso gabanmu tana dubanmu ciki muryar natsuwa ta fara cewa.

"See, ni ban san akan me kunke magana ba, kuma ba na buƙatar sani, may be ko bai zama dole na na ji ba, amma ina son ku sani, ka da ku yi sanadiyyar abun da zai jefa iyayenmu cikin damuwa, suna sonku kuma suna farin cikin duk abun da ya sameku, don haka ina tunanin bai kamata ku je ku faɗi abun da zai zama dana sani a garesu ba, su iyaye a ko da yaushe burinsu kada 'ya'yansu su shiga matsala, to ya kamata ace muma mun kiyaye damuwarsu".

Kallonta kawai mu ke yi muna sauraron zantukanta, jin ta kammala ya sanya daga ni har Asma'u mu ka girgiza kai alamar gamsuwa da kalamanta domin kuwa ta yi shi cikin hikima, da haka ta fice amma ba ta wuce ba, ta laɓe a bakin kofa, "maganarta gaskiya ne, kuma na san idan na faɗawa Momy hankalinta zai gaza kwanciya" faɗin Asma'u.

Sai da na jinjina kai sannan na ce da Asma'u, "abun da na ke so da ke Asmee, ki kwantar da hankalinki, zan san yadda zan yi don ganin Momy ba ta shiga matsanancin damuwa ba, haka sauran ahali, amma bai kamata mu ɓoye wannam babban abu haka ba, Sunusi bai dace da zama garkuwarki ba".

Cikin zuciya Ayusha ta ja tsaki, saboda idan har na ce zan sanarwa Momy yanzu to abun da ta ke shiri ba zai haɗu ba, wucewa ta yi tana dialing number, "eh" ta furta sai kuma ta sauke wayar. 

Na daɗe ina rarrashin Asma'u don yanzu ma kukan ta kuma sawa, mun ɗau lokaci a haka, daga ƙarshe fitowa na yi cikin damuwa sosai. "Ash my head! Wayyo Allah!" Ayusha da ke zaune kan kujera ta yi wannan sauti, da sauri na ɗaga idona ina kallon inda ta ke, sai kuma na isa gareta cikin kulawa ina tambayarta me ya ke damunta?.

"Nuriyyah please help me, kaina ne ya ke matsanancin ciwo, jinsa na ke kamar zai tsage gida biyu!" Ta faɗi tana wani nukurƙusa akan kujera, wai kanta na ciwo, "sannu Ayusha, sannu, bari na... na je na ɗauko miki magani yanzu a ɗakinmu" na faɗi da ƙoƙarin komawa don ɗauko mata magani, domin na shiga damuwa da ganin yadda ta ke rirriƙe kanta.

Amma kafin na wuce Ayusha ta tsaidani da faɗin, "Nuriyyah ki tsaya, ba sai kin kawo min maganin ba, saboda idan kaina ya yi min irin wannan ciwon, maganin da na ke sha daban, ga shi nan a rubuce a nan, na ga akwai chemist à nan ba nisa, don Allah ki je ku siyo min à nan kin ji?". Ta faɗi tana miƙo min wani ƙaramin paper.

Da sauri na girgiza mata kai, sannan na ce bari na je na sanya mayafi, na faɗi ina komawa ɗakinmu da hanzari, ko da na shiga ɗaki na ɗauki hijab ɗina na sa, sannan na sanar da Asma'u cewa Ayusha ba ta da lafiya, zan je insayo mata magani, da haka na fice Ayusha har da min godiya. 

Ni dai bayan na fita direct wannan chemist ɗin na nufa, da sauri na ke tafiyar gudun kada na jinkirta ga yadda na bar Ayusha tana jin jiki sosai. Kwatsam na ga mutum a gabana ba tare da na lura ba, dakatawa na yi ina kallonsa da tsananin mamaki, a fili na furta, "Sunusi‽".

Ayusha tashi ta yi ta zauna daga kwancen da ta ke kan kujera, ta bi ƙofar da na fice da kallo, sannan ta saki murmushin gefen baka, ta miƙe ta nufi ɗakinmu, inda ta je ta samu Asma'u a kwance tana tunani.

"Wai me ya ke damunki ne? Ya kamata a matsayina na 'yar uwarki ki sanar da ni, may be ina da wani taimako da zan ba ki a ciki" faɗin Ayusha tana zuwa kusa da Asma'u, ita kuwa tashi ta yi tana kallon Ayusha jin wasu kalamai da ta ke fitarwa kamar ba ita ba, da ɗan mamaki ta ce, "babu buƙatar hakan, amma har kan na ki ya yi sauƙi ne Ayusha?" Kamar ba ta san me Asma'u ke nufi ba ta ce, "Ban gane ba, kai kuma?!".

"Eh mana Nuriyyah ta sanar da ni baki da lafiya, sannan ta je siyo miki magani" Ayusha ta ce, "ikon Allah, kuma ita Nuriyyahr ta ce ni? A ah ni ƙalau na ke, ba wani kaina da ya ke ciwo, amma me yasa Nuriyyah za ta yi min ƙarya?" Asma'u dai kauda kanta ta yi ba tare da ta cewa komai ba, ta koma ta kwanta.

Ayusha ta zauna kusa da Asma'u, tana cewa, "dama zuwa na yi ki ɗan rakani mu zagaya unguwarku, tun da na zo ban zaga ko ina ba, kuma idan mu ka yi haka kema damuwar da ke zuciyarki zai ɗan rage, ki sa mayafi mu je" ta faɗi tana son ɗaga Asma'u, "no Ayusha I'm sorry, amma ni ba na jin fita ko ina, ki jira Nuriyyah idan ta dawo ita ta rakaki,".

Da rashin daɗi Ayusha ta ce, "no karki min haka Asma'u, yanzu kina nufin ba za ki rakani ba? Abu ba wani guri mai nisa ba, haba please mu ɗan je mana ba daɗewa zamu yi ba" "ni ba inda za ni gaskiya, ba na wani jin daɗin fita yanzu" cewar Asma'u tana juyar da kanta alamar ta ƙare magana.

Da tsananin haushi Ayusha ta juya, shikenan shirin da su ka haɗa ya rushe, yanzu ya za ta yi kenan? Aikinta bai samu shiga ba?....

"Barkaaa kyakykyawa, ina fatan kina cikin ƙoshin lafiya?" Cewar Sunusi yana kafeni da idanuwsa, ni dai ban ce da shi komai ba, sai kallonsa da na ke kawai, ya sake cewa, "ba za ki amsa min ba? Ni fa surukinki ne" ya faɗi yana ƙoƙarin ɗaura hannunsa a jikina, da sauri na ja da baya numfashina na harbawa, sai kuma na yi gefe zan wuce, kuma shan gabana ya yi da faɗin, "tsaya tsaya mana, ya da sauri haka kyakykyawa Nuriyyah? So na ke mu yi hira da ke ko ba yawa?".

Cikin ɓacin rai da haushi na ɗaga idanuwana ina dubansa na ce, "Sunusi ka ba ni hanya in wuce! Na riga da na san ainahin ko kai waye, na riga da na san wani irin mutum ne kai! Girmanka ya gama faɗi a idona Sunusi, ka ba ni hanya in wuce!" Hannu ya sa ta inda na ke son wucewa, na kuma dubansa akaro na gaba ina jefa masa kallon takaici.

Sai dai shi murmusawa ya yi har yana gyara zaman kwalar rigarsa, "wow! Wow yarinya mai wayo, amma kin san me? Na yi farin ciki da ki ka san haka, ina tunanin akwai abun da ba ki gama sani ba, kina son in sanar da ke?" Ya ƙarashe yana girgiza min kai. Ƙasa na yivda kaina, domin ganinsa ma haushi ya ke sa ni, shi kuwa ya ɗaura da cewa.

"Shikenan tun da ba za ki amsa ba, amma zan sanar da ke" ya faɗi yana yin gefe, "ni fa dama tun asali kece wacche na gai kuma na ji ina so, ga ki da kyau ga komai ciff, sai dai matsalar shine, da na bincika na gane ke ba kowan kowa ba ce, ke ɗin mara gata ce, tsintacciya kuma wahalalliya! Ko yau a ka koraki daga wannan ahalin to fa ba ki da madafa" rintse idona na yi ƙirjina na ba ni sautin rashin daɗi sosai, kalaman Sunusi suna ratsani kamar tafasasshen ruwa.


Sai da ya dawo ya tsaya a gabana ya cigaba da cewa, "ba ki da wani abun mora ta fannin dukiya, kenan ba zan samu abun da na ke so daga gareki ba, to daga nan sai na yi tsalle izuwa ga Asma'u, wacche na san idan har na bi komai cikin tsari to tabbas zan mallaki kuɗaɗen da na ke so, amma kuma duk da haka dole sai na aureta, shiyasa na haɗa komai ba tare da kowa daga cikin ahalin sun gane ba, sai ke yanzu da ki ka san gaskiya, me yasa ba ki yi shiru da bakinki ba ki ka labartawa Asma'un? Bayan kin san tana sona sosai, da kin faɗa min kin ga sai mu tsara komai tare da ke kema ki samu rabonki a ciki ko?".

Sai à sannan na buɗe idona ina kallonsa cike da tsana matuƙa, na buɗi baki ba tare da jin tsoro ba na ce, "na gode da ka sake bani haske, sai dai ina son kasan wani abu, ni Nuriyyah ba zan taɓa zuba ido ka cutar da wata ba, bare Asma'u wacche take 'yar uwata, kasa a ranka burinka da ka ke da shi akan wannan ahalin ya rushe!".

Kafin ya amsa min wayarsa ya yi ƙarar shigowar massage, ba tare da ya ɗaga wayar ba ya fara yin magana cikin wani muryar da ko kusa ban fahimci me nufinsa ba, "à ah Nuriyyah ka da ki yi min haka, à baya ban taɓa tunanin za ki yi mana haka ba, sai ga shi yanzu kina son aikata min babban abun da zai iya jefa ni cikin matsala, kin san cewa ni da Asma'u muna matukar son junanmu, ba mu da wani fata sai na mu rayu a tare, me yasa za ki so raba wannan soyayyar?".

Yayi maganar kamar zai yi kuka, ya share hawayen idonsa ya ɗaura da, "saboda kin yi ta bina akan mummunar mu'amalar da ki ke son mu aiakata, ni kuma na ƙi amincewa, na ce ba na sonki, ni Asma'u ce wacche na ke so, amma ki ka ce ba za ki barni haka ba, kin ce sai kin rabani da ita, ga shi yanzu kuma kin yi nasara, ko na kira Asma'u ba ta ɗagawa, ban san me ki ka ce mata ba. Kiran da ki ka min yanzu na ɗauka kin haƙura da ƙudurinki ne, ashe duk ke ba haka ba ne, kin kirani ne don ki kuma gasgata min cewa sai kin rabani da masoyiyata, Nuriyyah menene ribarki a ciki?".

Ni dai sakin baki kawai na yi ina sauraron Sunusi, wani irin magana ya ke faɗi ko fasali babu? Na kasa fahimtar dalilinsa na yin wannan kalamai, me yasa ya ke yin hakan? Yana shirin sake wata maganar na dakatar da shi da hannu ina faɗin, "ya isa Sunusi! A tunaninka wa'yan nan kalaman da ka ke yi, zai sa na canza abun da na ce akanka?".

Sunusi ya ce, "ai dama na san ba za ki karaya ba, saboda yadda mutane ke tunaninki kin wuce haka, shikenan kin yi nasara akaina, kin riga da kin yi min tsakani da farin cikina, don haka zan tafi sai dai na san wanda ya ke tare da Allah ba zai taɓa faɗi a banza ba" ya faɗi sannan ya juya yana shirin barin wurin.

"Babu inda za ka je!!" Muryar Asma'u ya ratsa kunnuwana, wani irin bugu zuciyata ya yi jin yadda ta furta maganar. Shi kuwa Sunusi ya washe baki yana ɗan zaro idonsa kaɗan na makirci....


Last page
___________________________________________________

Hmmmm! Me tunaninku akan wannan lamari? Mu haɗu da ku a kashi na gaba idan Allah ya kaimu🙏🏻




_*🌹𝑍𝑎ℎ𝑟𝑎-𝑡𝑢𝑙-𝑄𝑎𝑙𝑎𝑚🖋️*_