Page 5
by @abeedah343
ROMON BAKA
PAGE___ 5
Bismillahr Rahmanir Rahim.
Tun farar asubahi naji ana bugun ƙofar ɗakina kamar za'a cire, miƙewa nayi daga kan abin sallar da na idar, na buɗe ɗakin, Suwaiba na gani tsaye ɗaya daga cikin faccalolina, gaida ita na fara yi cike da girmamawa, amma sai ta wani mele baki kamar taga wani abin ƙyama tace, "To dangin ya hudu da nasara ai sai a tashi ayi sallah dan yanzu ba da bane an baro cikin marasa yin sallah, yanzu kuma an shigo cikinmu, ga kuma aikin gidan can yana jiran ki, idan da an saba da zaman kurum to yanzu akwai babbanci, dan kuwa yanzu aure kike kinga kuwa dole ki fito kiyi bautar aure kamar kowa, ba ki shige ɗaki ki naɗe ba kamar wani curin alkakiba, kina kwance ayi miki komai, dole ki fito kamar kowa na gidan nan kiyi aiki, dan ba shafaffiya da mai bace ke, uhmmm ni Suwaiba wama ya sani ko tuban mazuru a kayi, dan anga mai kuɗi, mukam dai ai mun gode Allah da muka kasance a musulunci".
Ta ƙarasa magana tana tsartar da yawuu.
Ni kuwa ina tsaye ne nayi kasaƙe ina fassara maganganun nata sala-sala, masu kama da gugar zana, duk da ba fahimtar abinda take cewa nayi ba, dan har yanzu bawai hausar ta gama bakina ba ne, sai dai ina fahimtar abubuwa da yawa, saɓanin daa da bana jin kozo na kashe ka a cikin yaren na hausa, amma yanzu sai dai nace, Alhamdulillah tunda har ina iya mai dawa, amma kamar waɗannan maganganun nata bam fahimci ko kalma ɗaya ba.
Cikin hausar tawa da ba wani fita take ba nace, "Anty Suwaiba nayi mana ko ba ita kike magana ba?". "Mtssss". Anty Suwaiba ɗin taja wani tsaki tana cewa, "Ke ban tambayeki ba, ko kinyi ko ba kiyi ba, tunda ko kinyi ɗin bai zama lallai a amsa ba, ki wuce kije kiyi sharar gida in ji Anaa".
Jin sunan Anaa da ta kira sai da ya saka gabana faɗuwa, saboda yadda uwar mijin nawa take nunamin tsana muraran babu ko sakayawa ba, hijabin dake jikina na cire na fara sharar makeken tsakar gidan wanda ko mutane uku aka bawa sharar shi a galabaice zasu gama saboda faɗin shi da kuma tsayin shi, amma ni kaɗai suka sakarwa sharar, haka na gama a galaɓaice duk jikina ta ko ina ciwo yake min, tsayawa nayi ina maida nunfashin gajiya, "Ungo". Naji an faɗa ana miƙo min abu, juyawa nayi dan ganin menene ake bani, bin abinda ta miƙo min ɗin nayi da kallon tambaya, "Wanke-wanke zakiyi, idan kuma ba zakiyi ba sai na koma na gayawa Anaa kin ce ba za kiyi ba". Murmushin dake fuskata ne ya sake yalwatuwa dan mawuyacin abu ne kaga fuskata babu wannan murmushin koda kuwa an ɓata min rai ne baya taɓa barin kan fuskata ya zamar min kamar jiki, na girgiza mata kai nace, "A'a zanyi". Jefo min omon tayi tana wucewarta, duƙawa nayi na ɗauki omon duk da uwar gajiyar dake nuƙurƙusata haka na nufi inda ake ajiye kayan wanke-wanken gidan waɗan da suke kiriga guda tsayawa nayi ina kallon shimilin wanke-wanken dake gabana, ganin ina ɓatawa kaina lokaci ne yasa na samu guri na zauna na fara wanke-wanken tun ina yin shi da daɗin rai har yazo ya isheni dan kaya ne ba kaɗan ba, saida na share sama da awa biyu ina abu ɗaya, sannan na gama, haɗe kayan nayi na ajiyesu a gurin da a ke ajiyewa.
Ɗakina na koma dan na huta gajiyar aikin da na sha yau, saboda yadda na kejin ƙasusuwan jikina suna amsawa tsabar gajiyar da nayi, amma dai me wai ance tsugunno bata ƙareba dan ina sanya haƙarƙarina a ƙasa dan na samu na hutawa raina, naji sallamar me kawo kayan abinci, "Hasbunallahu wani'imal wakil". Na faɗa ina dafe kaina da nake jin yana juyawa kamar zai rabe biyu tsabagen gajiyar dake jikina.
Amma na san ko mutuwa nake babu wanda zai ji ƙaina ya ɗora abincin nan, babu yadda na iya haka na miƙe na fito, duk da juyawar da kaina yake yi haka na daure na nufi madafa dan ɗora abincin ranar da ya zama dole a gurina kai bama iya na rana ba, dan kusan ko yaushe nice nake yin abincin gidan nan duk da yawa da jama'an gidan nan suke da shi, amma ni kaɗai ake sakarwa aikin abincin gidan, dan kuwa ba'a raba tukunya a gidan nan. haka na fara aikin cikin dauriyar azabar da kaina yake yi, har naci dunin aikin amma duk da halin da jama'ar gidan nan suka ganni a ciki hakan bai sa ɗayansu ya kama min wani abu ba.
Sai da na gama sannan su kuma suka raba, kowa ya ɗauki na shi nima nawa na ɗauka na nufi ɗakina da shi, zama nayi ina kallon abincin da aka zuba min, wasu hawaye ne masu gudun tsiya suka zubo min, hannu nasa ina sharewa amma ina sharewa ne wasu na sake zubowa a kan fuskata waɗanda nake jin zafin su har a kan fuskartawa.
Rayuwa ta shuɗa wanda zan iya cewa har yanzu babu wani sauyi a zamana da mutanen babban gida sai ma abinda yayi gaba, dan rayuwa nake kamar baiwa a gidan aurena, gidan da ya kamata na samu dukkan farin ciki a cikin shi amma hakan ya gagara, dan kuwa a ɓangaren Habibu ne kawai nake samu sauƙi da sassauci ga kuma shi ba mazauni ba, idan ya fita kasuwa tunda safe sai da maraice yake dawowa, hakan ne yasa duk abinda ke faruwa ba shi da masaniya, dan kowa daya dawo ya tambayeni ko akwai abinda ke damuna, sai dai nayi murmushi na girgiza mai kai, ya san kuma daga wannan girgiza kan bazan ƙara komai ba.
Ana cikin wannan halin ne Allah ya azurtani da samun juna biyu, nayi farin ciki mara musaltuwa, ganin nima zan ajiye nawa gudan jinin a duniya, hakama ga Habibu yayi farin cikin da ya zarta nawa, amma ga jama'an gidan nan kuwa wasu ma ƙiri-ƙiri suke nuna baƙin cikin su da hassada a kan cikin nawa duk da kuwa ko wacce tana da nata yaran dai-dai gwargwa, amma hakan bai hana su kasa ɓoye baƙin cikin su a kan nawa ba.
Na shiga rainon cikina inda nake samun tattali da kulawa daga gurin mijina dan kuwa ko a gaban waye baya hana shi nuna kulawarsa a kaina, wannan abu kuwa ya sake rura wutar ƙiyayyata a wajen jama'ar gidan mu, dan kuwa Anah cewa tayi bazata haɗa iri da dangin arnaba, ni kuwa na toshe kunnena daga maganganunsu, duk abinda zasu faɗa baya damuna.
BY
ABIDAH✍️