Wasan Sarƙaƙiya

Chapter 2

by @aryaahriyad

Game of puzzle (Wasan sarƙaƙiya).

By Aryaah Riyad..

  Book one 1….

       Chapter 2…..

Kuwait, Bayan Palace……

masarautar kuwait).

Aiko hakan ne takasance dan tana shiga dining din ta ganshi a tsaye yajuya bayanshi yana magana da wani dabatama tsaya ganin wayeba tayi kashi tana dan ihu tareda tsalle tay hugging dinshi ta baya so tightly. 

Yin baya yayi kaman zai fadi dan yanda tayi kashi tay tsallen duk nauyinta ta sakinmai, hakan yasa tayi sauri ta sauka daga jikin shi dan ita tama manta bashida lafiya murnar ganinshi ya mantar da ita.

Daidai bayanshi ta tsaya still hannayenta na zagaye dashi, saidai shi bai juyo ba bai kuma nuna yasan da ita bah, dan cigaba da magananshi yayi da wanda ke gabanshi.

Sunkai wajen two minutes a haka sannan ta sake shi tareda zagayowa ta gabanshi dan taga me yahanashi ya juyo yayi mata magana, saidai bata karasa zagayowan ba suka hada ido da wanda ke gabanshi, a zaune yake a chair dake kusada na daddy a left side wanda hakan ya hana ta ganinshi tun shigowanta sai yanzu data juyo, saidai dukda a zaune yake bazai hanaka ganin cewa dogo ne sosai ba, full arab ne irin hadaddun UAE arab guys dinnan, eye color dinshi brown gashinshi kuma baki sidik yasha gyara daya gyarashi wasu sunyi baya wasu kuma sun zubo har gaban goshin shi, jikinshi is built da muscles dukda suit ne a jikinshi bazai hanaka gane hakan ba.

Dauke idonahi yayi daga kanta ya cigaba da magananshi dayakeyi da amrah dake gefenshi a chair din tadan rungumoshi ta side sun hade kujerun nasu guri daya, tana magana, shima brothernta ayaan dayake kusan kamanninsu daya da azlan saika zata yan biyu ne saidai shi ayaan gashin kashi wavy brown ne, tsaye yana dan ansa musu sama sama, gakuma mamah dake opposite dinsu itama tana dan tofa musu..

Danne abunda taji yazo mata zuciya tayi sannan tasa smile a face dinta ta kalli ayaan tace mishi “ welcome back big brother, an dawo lafiya? Ya hanya? Yazu anty?”. Ta fada voice dinta yadanyi kasa.

Juyowa yayi ya kalleta yadanyi mata smiling sannan yace mata lafiya kana yadanyi hugging dinta ta side for a split second kaman wanda kejin tsoron ta shafa mishi wani abu. Sannan ya koma side da mamah take ya zauna kusa da ita. 

Maida hawayen dataji suna kokarin zubowa tayi sannan ta juya kan azlan da yake gefen amrah tace mishi “ welcome back cousin”.  dago ido yayi ya kalleta tundaga sama har kasa sannan yadan gyada kanshi alaman amsawarshi, itama bata juya ta kalleshi ba bare ta jira ansar datasan bazata samu bah. 

Kusada mamah ta zauna saidai tabar sit daya tsakaninsu wanda ayaan yazo ya zauna anan din, sannan ta sauke kanta kasa tareda dauke hannayenta dake rawa ta daurasu a laps dinta dan bataso wani yaga halindatake ciki. 

Sunkai wajen 5minutes suna hira a junansu babu abunda kakeji sai kashin expensive turaren wuta dakuma garlic and paprika spices dake tashi sai dariya dasuke yi sunata hirarsu. Babu wanda ya tuna kokuma ya nuna yasan da yazrin a gurin.

Shigowan daddy ne ya fitar da ita daga tunanin datakeyi. Yana zuwa straight head of the table seat ya zauna batareda sun gaisa da su azlan ba, da alamun sun hadu kenan kafin su shigo nan.

Sannu da zuwa yazrin tayi mishi tanajin yanda kanshin turarenshi yanadan tadamata da zuciya, dukda yana mata dadi on normal days amma indai zata fara ciwo da shi take ganewa, dan koyaya kanshin turare yake indai bana incense ba irin na gida toh saiya fara tada mata da zuciya.

Sama sama ya ansa ta ba yabo ba fallasa sannan aka fara cin abinci. Yauma kamar kullun amrah ta tashi tayi serving kowa banda yazrin, yazrin ta tashi ta dauki falafel mai beef and cheese fillings da chicken salad ta zuba ta fara ci kwata kwata batada appetite dan har daci daci takejin abuncin na mata.

Hira suka fara tsakaninsu ayaan na basu labarin yanda ya gudu daga dubai yatafi russia batareda sarauniyar dubai ummin azlan ta sani ba, dan idan har kaje gidanta toh baka isa kabar kasan kaje wata kasar ba saidai idan ka dawo gidanku sunganka sannan ka juya ka tafi inda zaka, dan mugun tsoro ne da ita especially na tafiya, shiyasa hardly zakaga tabar dubai taje wata kasar.

So yana basu labarin yanda yatafi russian, mamah ce kuma ta tambayeshi gurin wayaje a russia,  bai bata amsa ba, daidai nan wayanshi tafara ringing. Amrah ce tai saurin daukan wayan nashi, tana juyoma kowa da screen din dan suga wake kira tana dariya kaman ba itaba. Face time ne ake kira video call an rubuta my fav cousin a jiki da heart and padlock dakuma ring emoji a gaba. 

Harara ya wurga mata sannan ya mika mata hannu alaman ta bashi wayan, ba musu ta mika mishi tana maida mai da hararan cikeda zolaya, lokacin har wayan ta tsinke. Dan typing yayi a wayan sannan ya mayar ya ajiye.

Daddy ne ya juyo inda yake sannan yadan gyara murya alaman zaiyi wata magana mai muhimmanci kenan. Yazrin da hankalinta kechan wani guri kaman bata cikinsu tayi saurin dago da idanunta ta kalleshi, hakan yasa dan kwallan dake gefen idonta tun dazu ya zubo. Sauri tayi tasa hannu ta goge batareda wani yaga halin datake cikiba dan kusan kowa ma ya manta da ita a cikin dakin. 

Daman idan har kaga yazrin tana cikinsu ana hira da nishadi to tsakanin amrah ko ayaan waninsu bayanan, indai ko duk sunanan gakuma azlan toh mantawa akeyi da ita, abun na mugun taba mata zuciya dan nuna mata sukeyi kaman ita ba cikinsu takeba.

Cikin no nonsense voice daddy yafara magana “ ayaan yaushe zaka fito da mata ne? Idan bason yarinyan nan adaab kakeyi ba kafito ka gaya mana sannan ka nemo wata ko mu nemo maka, kai ba yaro bane shekarunka 30 a duniya, sannan azlan nayi magana da abbanka nanda 1month zamuzo ayi engagement party naku kaida amrah, a ranan za’a daura aure saidai bazaku tareba harsai ta gama university nanda 6months kenan, ke kuma yazrin, na yanke shawara nida mamanki zamu hadaki da amrah, ridwan zaizo gobe yaganki, sannan kada nasakejin abu makamancin wanda yafaru tsakaninku yau, idanba hakaba zaki ansa hukunci kamar yanda tsarin masarauta ta tanadar”. 

Wani irin sarkewa nunfashinta yayi jin irin kalaman da daddy ya furta, she can’t believe it . Kodai kunninta kemata gizo? Dan bata taba tsammanin daddy zai iya mata hakaba. Meyasa zaiso ya hadata da mutumin daya kusan haifanta, mai yaya da mata duka duka shekaranta 17, dan ridwan na farko faryal shekaranshi 17 shima, infact class dinsu daya a school. Kodai daddy ya manta da alkawarin dayayi mata ne?, kokuma ya mata cewa matar sa cousin dinsu ne?.

Baki ta bude tanaso tayi magana amma ta kasa, kanta yayi mata wani irin nauyi, dakyar ta daga ido ta kalli mamah wanda ta sauke kanta tana yanka beef walington dake plate nata, babu wani reaction a fuskanta alamun tasan da maganan kenan. 

Wani sharp pain ne ya daki kirjinta daseda tayi kara, kowa a table din saida ya dago kallonta, tayi saurin dafe kirjinta tareda kokarin tashi ganin idon kowa na kanta. Dan layi tayi kaman zata fadi dan saurin mikewan datayi, saidai batai wata wataba ta nufi hanyan fita dakin tanajin dariyan amrah. 

Straight waje ta fice bata ko ganin inda take bi dakyau dan dishi dishi idonta keyi. Wajen palace din tayi tana tafiya a hankali tana dan tangal tangal kaman wanda tasha wani abun bugarwa. Takai wajen 1hr tana tafiya a haka batayi ko rabin fita daga fadan ba, wata mota blue ferrari ta tsaya gabanta. 

Glass din mazaunin driver dake side dinta aka bude, wani hadadden saurayi ne bazai wuce 17-18 years ba a ciki, face dinshi yayi kama dana amrah sosai hatta eye color dinsu da eye shape dinsu iri daya ne kaman twins. Cikin voice dinshi wanda dakaji kasan irin shagwababbun yaran nanne masuji da mulki, skin dinshi har wani glowing yakeyi kana ganinshi kaga dan hutu.

Cikin voice dinshi da kanaji kasan yana vaping a wani hankali yayi mata magana cikeda zolaya “ yazrin baby an koreki daga gida ne? Ko kina missing dina ne kika fito?”. 

Tsayawa chak yazrin tayi jin muryan bestfriend dinta kuma cousin dinta, da sauri ta juyo suka hada ido ya wani juya mata ido kamar mace, nan take kuma taji zuciyanta tadanyi sanyi. Zagayawa tayi passenger seat kafinma takai kofan ta bude authomatically, shiga tayi kofan ta rufe yaja motan tana sauke nunfashi da karfi da karfi.

Sunkai wajen 10minutes suna driving motan tayi tsit bakajin komai sai karan AC dakuma kanshin turarenshi saint lauren,  sannan suka fita daga masarautar. Sai a lokacin taji hankalinta yadan kwanta sannan kuma gajiya ta fara saukan mata. Dan reclining kujeran tayi tana gyara zaman ta, sannan ta daga kafafuwanta dasuke mata zugi ta daura akan saman kujeran tana rumgume gwiwoyinta.

Juyowa faryal yayi yana kallon yanda jikinta kedan rawa ta rungume kanta, mayafin abayan datasa ya sauko wuyanta gashinta datayi parking dinshi into a bun a waje. 

Gaban Wani katon high rise golden building suka tsaya an  rubuta  zeyz massage palour. Parking lot suka shiga yayi parking motan a vvip section sanna ya juyo ya kalleta. 

Idanunta ta a rufe tashiga tunani kaman mai bacci da alaman batamasan anyi parking motan ba. 

Hannu yasa ya ja kumatunta cikin zolaya, dasauri ta dago rinannun idanunta ta daura akanshi. Wani cool smile yayi mata yana fadin “ whats up babygurl, an daura aurenki da oldman dina ne?”. Yan fada yana kyalkyalewa da dariyan mugunta.

Kafa mishi ido tayi tana kallonshi, tama rasa mezata fada, take hawayen dake bayan idonta suka zubo. Dariyan dayakeyi ya tsayar yana kallon yanda take kuka, saikuma cikin serious voice yace “ don’t worry, munada time ai, sai nanda 3months kafin nan we will figure out yanda zakiyi, bazan bari ki auri wanda bakya so ba, besides idan kika auri oldman dina dole nace miki anty, kuma kinsan hakan bazai taba yuwuwa ba, nagirmeki ko kinaso ko bakyaso, dan haka ki kwantar da hankalinki”. Yana fada yana shafa kanta kamar wata yar baby.

Hugging dinshi yazrin tayi tanajin kalaman daya fada, a bangare daya hankalinta yadan kwanta jin cewa sunada time kuma yana bayanta, saidai kuma tasani sarai cewa tunda akayi maganan nan tsakanin daddy dakuma ridwan to lallai yan fada sunsan da maganan, sannan sarki baya magana biyu so kotanaso kobata so dole ayi auren. 

Rumgume shi tayi koba komai atleast tasan akwai wanda kebin bayanta, shima hugging dinta back yayi. Cikin voice daya shake tadan dago kanta daga jikinshi “ kasan bazasu chanza magana ba, dan haka dolene auren nan, saidai idan guduwa zanyi”. Kallonta yayi sannan yace “ toh ki gudu kije ina, duk inda kikaje zasu nemoki, kinkuma san hakan ne zaisa a tsaurara miki, abu biyu zakiyi dazaisa daddy ya yarda ya barki kiyi making decisions dinki dakanki, na farko shine ki fara ciwo, ki bari ciwonki ya dawo sosai to the point bama za’a iya maganan yimiki wai abu banda magani ba, saidai kinsan hatsarin ciwonki, daga haka zaki iya rasa ranki, sannan kuma kina warkewa za’a sake tada maganan, dan oldman mugun sonki yakeyi bakuma zai hakura ba”. “

“ na biyu kuma shine kisamu wata masarautar suyi proposing aure, kinga dole sheikh zai yarda tunda idan bai yarda ba za’a samu rabuwan kai a tsakanin masarautun Middle East. Amma matsalan shine sai dole a cikin masarautun Middle East, sannan saikin samu prince da bashida aure sannan kuma zaki iya auren shi, amma wannan bashine mai wahalan ba, dan akwai su dayawa saikin zaba, mai wahalan shine yanda zamuyi mu samu attention dinsu, indai ba azlan zaki kwace ba, tunda dama chan ke kika fara cewa kina sonshi kafin amrah”. 

Ajiyan zuciya ta sauke tana sakinshi tareda komawa ta jinginada seat din, laushin kujeran na karamata nutsuwa tareda solutions dinda faryal yakawo. Kusan minti biyar tana tunanin meyakamata tayi, options dinta biyu ne kadai, saidai option nafarko bata tunanin zaiyi aiki “ faryal option na farko fah bazai yi ba, dan kasan idan har nabari nakara ciwo mai tsanani koda kadan ne zai kara sawa ana kallona kaman wanda bazata iya komai da rayuwanta ba sai abunda aka yanke mata, sannan daddy zai kwace position dina a library yaba amrah, idan hakan ta faru kuma babu wani abu dazan karayi a masarautar, dan haka nida banza daya nake, daddy da mamah sunfison amrah da ayaan, dan gani sukeyi banida amfani bakuma na kara komai a cikin masarautar, shiyasa ma suka bawa ridwan aure na, dan na tabbatar idan amrah ce bazasu taba yimata hakaba”. Tafada cikin kunan zuciya.

Dan sunnar da kanshi yayi bama yaso ya rarrasheta, dan baisan mezai fada mata ba, da yanada yanda zaiyi bazai taba bari yaganta a cikin wannan halinba, saidai rayuwa yanda tazo maka haka zaka bita.

Amrah tayi sa’a, tanada kyau, ga ilimi da hankali, takuma iya harka da mutane kamar hawainiya haka take. Dan haka tun tana karama kowace masarauta da manyan yaran shugabannin kasashe da iyayensu kowa burinshi ace danshi ya auri princess amrah, gashi Allah ya bata farinjini, daddy da mamah kuma sunmata training mai kyau, sannan duk wani abu na masarauta musamman a harkar bincike da history tasani, sannan taci manya manyan competitions na duniya ba saudaya ba basaubiyu bah, dan haka duniya tasanta, gashi batada tsoro tanada courage sosai dake burge mutane, duk abunda tasa kanta yi saitayishi, har fan pages gareta tanada millions of followers a instagram, da fan accounts dake posting dinta, da irin fashion din datakeyi, da tafiyanta, mutun dayane tafita fans da abubuwa itace princess of Qatar princess Alina bin malik.

a dayen bangaren kuwa yazrin tunda aka haifeta bata tabayin lafiya ba, cutar field disease aka haifeta dashi wanda itace mutun na uku a duniya daya taba yin cutar, cuta ce mai kashe garkuwar mutun a hankali harsai ta kashe shi, sanna kwanansu kadan ne a duniya, basa dadewa, wani lokacin har brain dinsu take tabawa. Dan haka tunda aka haifeta babu wanda yasanta a duniya, a kasar ma kowa dai yasan matar sarkin kuwait ta haifi ya amma babu wanda ya ganta, sannan tsananin rashin lafiya saida tayi shekara bakwai bata mike tayi tafiya kokuma magana ba, infact saida tayi shekara goma sannan ciwon ya lafa tasamu aka fara koya mata karatu a gida, yau lafiya gobe babu, a haka har tayi 15years , dan Allah yayi tanada brain sosai dan haka bama zaka taba gane bataje school ba, saidai mu’amalan ta da mutane zaka gane bata saba da mutane ba, dan da bama ta iya dogon magana da mutun, saida tayi 16 years harta kusa 17 shine daddy ya yarda ta shiga university, shima saida ya hadata da faryal dakuma securities dan bai yarda tana mu’amala da mutane ba, indai ba faryal ba da wasu cousins din, a cewar shi zasu iya mata wayau tafada musu sirrin masarauta.

Sannan baya bari tana shiga harkar masarauta, shiyasa babu wanda yataba zuwa dacewan yana sonta kokuma masarautar dasuka nuna sha’awan sunaso dansu ya aure ta, dan koda aka santa bayan ta fara zuwa school, media sun dauki hotunanta tayi trending sosai harta samu title din most beautiful girl and princess in the world, mutane na fadin cewa tafi amrah kyau dakomai, saidai banda kyau babu abunda zata nunama amrah, dan amrah tafita komai, sannan masarautu basa auren kyau, auren jafi sukeyi, yanda zasu amfana da juna, shiyasa babu mai maganan yazrin dan a ganinsu bazata kara musu komai ba, dan wayanda suke zuwa domin neman auren amrah idan aka fada musu cewa an riga an bawa azlan aurenta saidai yazrin basa kara dawowa.

Yazrin ma kawai tunanin yanda rayuwanta zai kasanse takeyi, ringing din wayan faryal wanda muryan yazrin ne tana fadin ‘faryal why are you not answering my phone tun jiya? Zan biyoka gidanku fah’. Kanaji kasan AI generated ne, juya idonta tayi jin yauma ya chanza ringing tone din nashi, bashida aikinyi sai amfani da voice chat dinta yana sawa a ringing tone, yau yasa wannan gobe yasa wanchan. 

Wayan ya ciro daga cikin pocket dinshi yana kallon mai kiran, an rubuta “prince ayaan”. Juyawa yazrin wayan yayi ta kalli mai kiran sannan ta juya kanta gefe tana kallon waje, shikuma ya dauki wayan yasa a speaker. Gaisawa sukayi da ayaan sannan ayaan ya tambayeshi ina yazrin, a take yace mishi gatanan, ya tambayeshi a ina suke yace mishi suna zeyz massage palour, “ ok ku juyo ka kawo yazrin gida nanda 40minutes ina jiranku”. 

Da ok ya ansa sannan ya katse wayan yana tada mota, basu kara magana ba har saida sukayi kusa rabin tafiyan sannan yazrin ta juyo takalleshi “ lets go with the second option, ka bincika mun princes din ka kawo mu zaba, zanyi tunanin abunda zanyi”. Gyada mata kai yayi. 

A daidai gate na shiga part dinsu suka tsaya akayi security checks sannan aka bude musu, goge face dinta tayi sannan ta gyara mayafinta, yana parking motan ta sauka, batako juyoba harta kai kofar shiga, sannan still batare data juyoba ta daga mishi hannu sannan ta shiga ciki. 

Direct dining ta nufa dan tasan nan tabar wayanta, saidai koda ta shiga babu wayan a inda ta zauna, babu kuma kowa a dining din. Tasan waye zai daukan mata waya, ayaan ne ba kowaba, dan haka fitowa kawai tayi ta nufa room dinta. 

Tana shiga straight toilet tayi ta watsa ruwa a jikinta sannan ta wanke face dinta ta fito daure da white soft towel a jikinta, ayaan ta gani kwance kan bed dinta yana daddanna wayarta, jin an bude kifan toilet ya dago ya kalleta, da sauri ta dauke kai ta shige walkin closet sannan tasa pj white a jikinta. 

Koda ta fito kallo daya yayi mata yacigaba da abunda yakeyi, itama batabi ta kanshi ba saima kara hada rai takeyi, danma yasan ranta a bace yake. Gaban mirror ta tsaya ta shafa moisturizers a jikinta sannan ta kunna AC a dakin jin yayi zafi dayawa, dan bata cika son AC bah. 

Bed ta nufo ta dayen side din da yake tahau ta kwanta tareda juyamai baya, ta dago silk bed wrap ta rufe jikinta tana karanto addu’an bacci. Muryan ayaan ne ya katse mata adduan datakeyi “ yazrin yau bazaa mun magana bane? Nima nazama amrah ne? Toh ga wayarki tunda bacci zakiyi, gobe da daddare zan fita dake outing mu zaga gari saimuyi hira koh? Saiki fadamun menayi miki ake share big brother”. Hannu ta mika mishi yasa mata wayan sannan ya sauko ya zagayo inda take ya manna mata kiss a goshi yana fadin good night baby sis. 

Cikin yar karaman voice kaman wanda bata iya magana ba tace “ good night to you too”. Sannan ta daura bargon har a kanta. Jin an kashe fitilan dakin tareda bude kofa da rufewa yasa tayi saurin ciro kanta daga wrap din dan harya fara sarke mata nunfashi, bata iya shiga kanta cikin bargo saboda nunfashi, da gangar taki mishi magana dan ya bata mata rai, takasa gane wani irin wasa da hankali suke mata daga shi har mamah da daddy, yau su nuna suna sonta kaman duniya ta tashi, gobe kuma su shareta suyi mata abunda sukaga dama, abun yana mugun damunta sosai, da kullun hakanta faru saita zauna tana kuka, amma yanzu yabi jikinta.

Notifications akayi mata a wayanta ta dauka danta gani, daga instagram ne an rubuta princess Aryaa, budewa tayi ta shiga, page ne na princess din Qatar, kyakyawan yarinyace ajin farko bazata wuce shekara 18bah, tafi kowace princess ko prince followers a duniya, tanada wajen 300m followers a instagram kadai, sannan itace akaba title na most beautiful princess infact woman in the world sannan amrah. 

Post tayi na invitation zuwa ga anniversary celebration na yarjejeniyar zaman lafiya da akayi a tsakanin Iran da Qatar, na wajen shekara dari kenan. 

Fita yazrin tayi jin bacci nadan fizgarta. Ta ajiye wayan tareda rufe idanunta bacci yay awon gaba da ita.

4hours later….

Jin baccin na sakinta ne yasata bude ido tareda daga hannunta dan tayi mika tareda bude bakinta domin karanto adduan tashi daga bacci, saidai banda bude idanunta babu abunda ya yuwu a ciki, nandanan kuma dakin ya dauki wani duhu dayasa taji gabanta yawani fadi ras dan tasan meke shirin faruwa.

Sanyi dakin yafara dauka tareda fara haske dan saida hasken yafara yima idonta yawa saidai takasa koda ta rintse idon ne, wasu irin halittu ne suka fara forming masu ban tsoro, bazakace ga suffan suba dan basuda ita, saidai duk wanda yay arba da koda dayansu ne mawuyaci ne hankalinshi bai gusheba, dan bawai hallitar ne abun tsoratarwar ba gaba daya, abunda sukeyi da mutun ne abun tsoratarwa.

Matsowa kusada ita suka farayi su uku ne amma sun cika dakin gabadaya, ga tsananin hasken da dakin yayi yasa kake ganinsu tartar gasu bakake wul.

Daidai bakin gadonta suka tsaya, nandanan kuma dakin gabadaya yakoma kaman irin manya manyan hotel dinnan ta baya gurin swimming area, ga swimming pool nan mantarere kaman kasa mutane dari a ciki, gakuma zagaye dashi mutane ne maza da mata suna zazzune akan beach chairs babu runfa dayake indoor pool be so ba rana.

Kaman daga sama taji an dagata dukda bawani hannu kokuma alaman wani abune ya dagata, sannan aka wurgata cikin swimming pool din, razanannen ihu tasaka tareda kokarin dago jikinta dan tuni ta nitse, saiki taji jikinta yasaki tadawo tana iya motsa jikinta.

Saidai kash, bata iya swimming ba, cikin kadewa tafara ihu a cikin ruwan saidai ba fitowa yakeyi ba tunda cikin ruwa take, dakyar ta dago da kanta tana kalle kalle da yunkurin komawa gefe danta fito, babu alaman dakinta ma dan gurin yakoma complete swimming area ne, mutanen gurin ne sukahau mata dariya suna chemata ta nitse, wasu na jifanta da coconut beach drink dinsu dayasa ta kara nitsewa, dakyar shima ta kara yowa sama da kanta tana ihun a taimake ta, saidai babu wanda yabi takanta.

Tana cikin haka kuma taga face din Nara daga cikin mutanen tana mata dariya tareda motsa bakinta dukda bakajin sautin amma tagane metake fada ‘ki mutu yazrin kowa ya huta, bakida amfani a duniya’.

Wani irin abu ne ya tokare mata a makwogwara ganin amrah, tuni kuma ta kara lumewa cikin ruwan, saidai a wannan karon bata iya tayo sama ba, tun tana iya rike nunfashinta tana kokarin yin sama harta kasa tuni ta shaki ruwa, wani irin ƙuna ne dayafara tun daga hancinta har zuwa makwogwaronta, kirjinta kuma kaman an daura mata dutsen dayafi kowanne girma da nauyi a duniya, idonta yafara sauyawa tanaganin duhu duhu, azaba ta cikata ta koina, kafin a hankali taji rai nafita daga jikinta.

Dogon nunfashi ta sauke tareda mikewa zunbur, saidai jikinta dayayi mata nauyi yasata komawa ta kwanta babu shiri, jin wannan ƙunan a makwogwaronta da nauyin dake kirjinta tareda taste din ruwa me chemical yasata tuna abundayafaru, dasauri kuma ta fara bin dakin da kallo, ajiyan zuciya ta saki tareda sakin wani marayan kukan murna tasaki ganinta a dakinta kuma kan gadonta. Saidai murnar komawa ciki tayi jin an bude kofar…..


for more information ga wattsapp number na *** @Aryaah Riyad.