Chapter 3
by @aryaahriyad
Game of puzzle (Wasan sarƙaƙiya).
By Aryaah Riyad..
Book one 1….
Chapter 2…..
Kuwait, Bayan Palace……
( masarautar kuwait).
Da wani azababben sauri ta juyarda kanta zuwa ga kofan harsaida wuyanta yay kara, saidai ba wannan ne gabanta ba, dan dishi dishi take gani amma hakan bai hanata ganin sarai waye a kofan ba, mamah ce ta bude ta shigo tana sanye da nightgown alaman yanzu ta tashi.
Da sauri yazrin ta juyar da kanta, sotake tayi kaman tayi bacci amma tasan mamah ta ganta, dan haka sai kawai ta juyar da kanta tareda gyara kwanciyanta. Hasken dakin mamah ta kara dan wanchan babu wani haske sosai irindai na barci ne.
Gabanta tazo ta tsaya tana kallon face dinta dayayi ja sosai gashi yayi chaba chaba da hawaye, rintse idanunta yazrin tayi jin kallon kurilla da mamah ke mata, addua kawai takeyi a zuciyanta kada mamah tagane cewa mafarkin nan takoma yi, dan babu abunda ke wuce idanun mamah kamar macijiya.
Gefen ta mamah ta zauna sannan ta daura hannunta a face na yazrin tareda share mata hawayen fuskanta, kwace face dinta yazrin tayi tana bude jajayen idanunta akan mamah, batasan meyasa ba kawai ranta baci yayi ganin mamah yanzu, inatake jiya datake nemanta? Take neman wanda zai tsaya mata koya rarrasheta? Sai yau ne zatazo tawani nuna mata kulawa.
Mamaki ne ya kama mamah ganin yazrin ta kwace face dinta, saidai tasan da dalili akan hakan, shiyasa ma batace komai ta ta mike tashiga toilet. Ruwan wanka ta hada mata mai zafi sannan ta fito harzata shiga closet kuma ta fasa ta juyo, dan yazrin bataso ana bata kayan da zatasa tun tana karama, sai wanda ta zaba.
Kara dawowa inda yazrin din take tayi “ yazrin baby tashi ki shiga toilet kiyi brush kiy wanka saikizo kisha maganinki, naga jiya kwata kwata baki shaba gashi kindawo kina mafarke mafarken nan”. Wani yawu yazrin ta hadiye sannan cikin murya irinta safiya dakuma rashin son magana tace “ mabah niba mafarke mafarke nakeyi ba, abunda kuke shirin yi mun shiyasani a damuwa, dan banma samu nayi barci ba bare nayi wani mafarki, magani kuma kin manta yakare?”. Tafada ranta babu dadi kuma zaka gane hakan a yanayin magananta.
Daga haka ta mike dakyar tanajin kasusuwanta na gogan juna, ga kirjinta da haryanzu nauyi yake mata dan dakyar ta iya mikewa straight. Toilet din ta nufa tana tafiya dadan sauri dan bataso mamah tagama karance ta, the last thing datakeso wani a gidan nan yasani shine batada lafiya ko tana mafarke mafarke, dan yanzu yanzu zasu hanata zuwa school dakuma library, wanda sukadai ne abubuwa datake yi a duniya tajita kamar cikakkiyar mutun yanzu.
Toilet din ta shiga ta rufo kofa tareda sakin ajiyar zuciya, batareda ta cire kayan jikinta ba dan batada kargin yin hakan ta shige jacuzzin. Yanda ruwan zafin ke ratsa jikinta yake bata wani niima mai dadi. Jikinta nanan amma kunninta naga kofa, sotake taji ko mamah ta fice daga dakin, saidai babu sound ko daya, nanne ta tuna kuma cewa dakin soundproof ne, so bazataji komai ba.
Tsaki taja aranta tana fadin who cares? Inma tananan inma tafita bata damu ba. Saida taji jikinta yamata dadi sannan ta mike ta cire pj din jikinta ta fito a jaccuzi din tareda draining ruwan ciki. Shower ta nufa ta kunna ruwan dumi sannan ta wanke jikinta ta fito daure da towel a jikinta daya kuma ta daure gashinta dashi, bata nuna tasan da zaman mamah dake zaune kan bed dinta bah.
Gaban Mirror tazo ta zauna tayi yan shafe shafenta sannan ta saki gashinta. Har tsakiyan baya ya zubo mata tasa towel din tana gogeshi a hankali, mayukan gashinta na Augustinus bader & sisley, one of the most expensive haircare brand in the world, ta shashafa products din wajen guda 8, sannan ta taje shi.
Scrunchie ta dauko ta daureshi a baya kaman donut sannan ta shiga toilet ta wanko hannayenta tareda dauro alwala ta fito ta tada sallah. Bayan ta idar ta mike ta nufi. Walk in closet ta dauko wata ocean green abaya mara kwalliya very plain, sanna ta dauki wata dark green alkyabba da akayi decorating dinshi ta gefe da gefe da rhinestones dakuma royal embroidery shima maroon and black color.
White mayafi ta dauka irin na abaya da akayi mishi similar embroidery da alkyabbar a gefe da gefenshi ta yafa a kanta, yazamana kawai daura shi tayi batareda ta linkashi gefe da gefe ba, kawai ta sakeshi a gaban alkyabbar dan gaban gashinta dayake a cike a kuma kwance yasha gyara a waje yau bata rufe shiba. Sannan ta dauki ocean green loubotin heels ta saka tareda daukan black shades na dior ta sa a idonta, takuma dauki wrist watch dan siriri dazaka zata band ne, saidai watch ne tasa a hanun damanta.
Fitowa tayi ta tsaya a mirror tana kallon kanta. Tayi wani fitinannen kyau kamar wata hurul ayn, idanka ganta saika ratse ba mutun bace, ga lips dinta da batasa ko janbaki ba banda lip gloss sai kyalli yakeyi yayi ja kaman tasa lipstick.
Saida ta tabbatar tayi ma kanta kyau yanda takeso sannan ta koma ta dauko birkin bag dinta, a jere suke a side daya wajen guda 30 different colors, su a side daya kawai suke ga wasu sides din kuma wasu different designer bags dinne sunfi 50 a kirge, green birkin din ta dauko yahadu da kayanta sosai sannan ta fice.
A tsakiyan dakin ta tsaya sannan ta juyo ta kalli mamah, “ mamah am off to school, idan na dawo nayi monthly check up din, ayi prescribing maganin na wannan month din”. Tana gama fadin haka kuma ta juya zata fice, jin mamah na magana yasa ta tsaya “ gobe ayi check up din, yau by 4pm ridwan zaizo, so ki dawo daga school da wuri”.
Ti tayi kamar batasan me mamah tafada bah, ta juyo ta lalleta sau daya sannan ta bude kofa ta fice.
Girgiza kai mamah tayi sannan ta mike ta fice itama daga dakin ta koma nata.
Yazrin na saukowa suka hade da amrah, itama tayi gayu sanye da green alkyabba she’s dressed to the nines, saida yazrin tayi kasa da kanta sannan ta kalleta, dan dama tafita tsawo gashi kuma tasa heels, abun saikagani, wasu kuyangu ne su hudu mata a bayanta kowanne rike da tray yazrin na gani tasan azlan zataje kaima abinci.
Rashin dadin yanda yazrin ke kallonta ta sama amrah taji, sam bambancin tsayinsu na kona mata zuciya, dan gani takeyi kaman yazrin din ta raina tane, gakuma wani irin kyau datakeyi koba kwalliya a face dinta, ta tsani taga wani yafita kyau ko Aura, ga ko yanda yazrin ke tsaye kaman wata high end model. Dason kular da yazrin din kuma saitayi murmushi tana fadin “ little sis, congrats fah, zaki auri daddyn bestie dinki, kinga shikenan keda faryal kunzama mom and son, zaku kara shakuwa kenan fiye da yanzu koh”. Tana gama fadin hakan kuma tabi ta saide din yazrin ta wuce, kuyanjin bayanta ma sukabi ta gefenta suka dan sunnar dakai alaman gaisuwa suka wuce biyeda amrah a baya.
Yazrin bata bari face dinta ya chanza ba ta kura ma amrah ido, saidai amrah nagama fada ta wuce hakan yasa itama tayi wucewanta ta nufa dining. Babu kowa a dining din sai abunci kawai da aka jera. Usual tea dinta ta zuba ta dauki garlic bread da salted butter ta shafa a jiki ta fara ci ahankali. Saida tagama cin bread din sannan ta dauki tea din ta kurbe tana duba agogon hannunta, gani tayi still its 6:50am 7 am batayiba yasa ta fito main palour dayake makeke, set uku ne na kujeru a ciki kowanne a nashi side dib saiyayi kaman palour uku ne a cikin daya. Center set din ta nufa ta zauna akan leaning 3seater seat din white color tadan kwantar da kanta akan hannun chair din dan ta jira 7 tayi sannan ta tafi.
Dan rufe ido tayi tanaso tadan maida bacci, saidai tana rufewa face din ridwan take gani, kokarin ture tunanin shi takeyi daga zuciyanta saidai hakan yaki yuwuwa, gashi yau dole zata ganshi, kawai hango ta takeyi wai ita za’a aurama wannan mutumin? No ina bazai yuwu bah wlh, ga matarshi maman faryal matan nan mugun kishi ne da ita, ga masifa da rashin tausayi dan kuyangu a part dinta guduwa sukeyi tsabar balain ta, sannan bata daukan masu kyau, dan a cewarta zasu kwace mata miji, shine su mamah sukeson chusata su hadata da mahaukaciyar matannan.
Jin takasa cire tunanin daga zuciyanta gakuma ciwo da kanta keson farawa dan jiya batayi bacci da wuri bah gakuma mafarkin nan datayi duk sun hade mata ga tunani, kawai ta dauko wayarta ta shiga instagram. Page din amrah ta shiga tanada wajen 200m followers, following list ta shiga wanda amrah ke following, basufi mutun 20 take following back bah, tukkan su princesses ne da princes na Middle East, dan scrolling tayi zuwa inda princes din suke. Mutun daya zuwa biyu zata iya cewa zata aura, daya shine prince na UAE Abu Dhabi , na biyu kuma prince na bahrain.
Sukadai ne idan har suka bukaci aurenta daddy zai fasa da ridwan, dan idan har bai basu bah za’a samu problem tsakanin su, tunda neman aure a gurinsu kaman yaki yake, idan kace yes toh shikenan za’a samu zaman lafiya, no kuma rabuwan kai dan zasuga kaman an rainasu ne.
Saidai ita yanzu batasan yanda zatayi masarautar abu dhabi ko bahrain suyi proposing bah.
Ringing wayanta yafara yi faryal ne ke kiranta. Dauka tayi tareda yin sallama. “ babygurl fito gani nazo daukanki, yau tare zamuje school inji oldman dina, yabani amanar ki”. Katse wayar tayi jin abunda ya fada. Wato shi ridwan harya fara shiga mata harkoki kenan? Zata gyara mishi zama ne bayaga daddy na bin bayanshi bah. Tsaki tayi sannan ta mike, waje ta fita a parking lot ta ganshi.
Ferarri yauma ya taho da ita amma ba irin model din jiya bah, Ferrari 12Cilindri (Coupe & Spider) ce ya zoda ita white color, zagayawa tayi ta shiga ta rife yaja motan suka fice.
Wajen 45minute drive ne daga palace din zuwa university dinsu, gashi da mugun gudu yake tafiya kaman bayason ranshi.
Itadai yazrin adduoi take ta jerowa dan bata kaunar gudu, gashi tasan kotace yadena ba bari zaiyi ba, tasan halinshi sarai shiyasa bata binshi school dukdan course dinsu daya.
Gaban university of kuwait(KU) suka tsaya, akyi security check sannan aka bude mishi gate ya shiga. Hadaddiyar university ce number 1 a kasar, tanada girma sosai dakuma students wanda duk top students ne a secondary schools, dansai marks dinka da grades sunkai wani level kafin ka samu admission a cikinta, bawai kawai dan kanada A’s ba, no sai kanada 90% a kowanni subject sannan.
Gaban faculty of engineering suka tsaya yayi parking motarshi a parking space na staffs dan students basa shiga da motocin su cikin gurin faculties, saidai shi dayake babu wanda ya isaya hanashi shiga.
Bude mata kofa yayi sannan ya sauka, ta dauki bag dinta da phone dinta ta fito. Students dayawa a gaban faculty din ana tsaitsaye kaman ana jiran wani, yawanci duk yan mata ne. Yazrin bata kalli kowaba tasa kanta gaba ta fara tafiya zuwa gurin entrance din, faryal nabinta a baya. Tasan taruwan menene, dan inda sabo ta saba indai tazo tareda faryal toh yan mata nanan na jiranshi kaman masu bara, kowa so yake yakalleta, saidai shima biye musu yakeyi yayitayi ya maidasu mahaukata.
A hankali take tafiyan tanajin idanuwan yan matan akanta, babu dai cikinsu wacce tayi mata kallon banza ko wani abu dan sunsan sauran, saidai suyita binta da kallo, wasu idonau cikeda hassada wasu kuma cikeda admiration, dan indai zatazo guri toh idon kowa dole yadawo kanta, ko waye kuwa.
Matsa mata sukayi ta shiga, faryal na bayanta yana ma ya matan smiling suna kiran sunanshi. Ta daidai bakin kofan ya rungume wata yar gajeriyar yarinya ce kana ganinta kaga America girl, siririyace irin sosai tasha uban fake lashes da red lipstick, tanada kyau ba laifi, tana mishi magana dawani fake voice kamar yar tsana.
Second floor ta nufa inda department of Aerophysics and engineering yake, course din datake studying kenan su biyu ne kwata kwata a course din, daga ita sai faryal, danba kowa ke iya karatun shi ba.
Exam room 1 suka shiga wanda yana chan ciki ne a floor din, already lecturer dinsu dake musu robotics na jiransu a ciki, yau test zasuyi. A gaba yace faryal yazauna sannan yazrin a chan baya, dan yasama faryal ido dakyau. A computer sukayi test din 2hrs, babu wanda yayi ma wani magana a lokacin har suka gama.
Finalizing sukayi sannan sukai submitting, sannan suka fita. Mota suka shiga yaja su suka fice daga school din. Halfway through suna dan hiran test din tace ya tsaya a Burger king tasai chicken nuggets. Kin tsayawa yayi a cewarshi babu tsafta cin abuncin waje, rokonshi tafarayi akan dan allah ya tsaya, saidai baimabi ta kanta ba, yanda batada lafiyan nan koyaya taci wani abu daba tabbatar da tsafta dakuma ingancin abubuwanda aka sa a ciki ba, sai a samu matsala.
Ganin dagaske bazai tsaya bane yasa tadan ciza lips dinta, aranta tana ayyana wlh saita rama, zaizo tamai wani abu shima. Yana kallonta yasan metake tunani saidai murmushi kawai yayi.
A dan gaba yay parking motan sannan ya ciro laptop dinshi daga bayan motan ya kunna. Kallonshi tayi tanaso taga meyake son yi tadan matsa dan taga menene. Hoton wani arab guy ne hadadde dogo handsome guy, prince na Abu Dhabi ne UAE, sannan uncle din azlan ne.
Faryal ya juyo yakalleta sannan yafara fadin “ ga target dinki, wannan file dinshi ne, zan turo miki file din, duk wani abu akanshi yana ciki classified information ne wannan nakashe kudade kan a samomin wannan abun. Within this 3months dole ne musamu yayi proposing, saidai fah ba karamin mutun bane dakike ganinshi, duk wani tactic dazamubi zai iya ganewa, dan haka dole ayi planning abunnan, kije kiyi studying file din sannan ki fada mun abunda kike ganin za’ayi, nima kuma zan fada miki”.
Dan ajiyan zuciya ta sauke sannan ta kalleshi, “ faryal kaga ni hankalina yafi kwanciya da prince na bahrain, shifa wannan ya girmeni sosai wajen shekaranshi 30 fah, sannan ba taba ganinshi ba bansan halinshi ba, sannan naji azlan na fadama daddy cewa bashida mutunci kwata kwata, gaskiya banaso”.
Tsaki faryal yayi a kufule yake fadin “ ke yazrin ina ruwanki da wannan? Shekaranshi 30 toh oldman shekaranshi 49, prince na Bahrain umar shekaranshi 26 amma an hada aurenshi da princess na qatar Alina, ba’a fada ba amma nasamu labari danayi bincike akanshi, sannan bazai iya rike kiba, bashida karfin zuciya sai abunda iyayenshi suka fada mishi. Shikuma prince Azaan dakika ji ance bashida mutunci kawai don yanabin ra’ayin shine, babu wanda yaisa yafada mai yayi inbaiga dama ba, kowaye kuwa, shine irin wanda yakamata ki aura. Sannan daddy bazai taba cemishi no bah so baki da wani option sai shi”.
for more information ga wattsapp number na *** @ Aryaah Riyad.