PAGE 04
by @nanameera08
*WATA AL'UMMA🌹*.
Page 04.
Da mamaki Anna ke kallon tarin sojojin da suka yi wa garin su ƙawanya. Sudais ya kalli Ammar da ke tsugune yana murmushi ya ce“Allah ya yi zamu koma gida.” Tashi tsaye Ammar ya yi yana jinjina kai fuskarsa a sake. Anna ta juya ta kalle su ganin har sun samu damar miƙewa tsaye, Ta taɓe baki kana ta kalli hanyar da mutane suka dare. Tsaye ta hange shi, Wani dogon mutum mai jiki. Fari mai ɗan faɗin fuska, Kyakkyawane irin ajin farkon nan. Yana da tarin ƙasumba wadda take kwance luf akan farar fuskarsa, Idanunsa maƙale da glasses wanda zai hana ganin kalar idanun nasa. Sanye yake da wasu ƙananun kaya, T-shirt blue mai haske sai wando 3-quater na jeans wanda ya tsaya iya gwuiwarsa. Kansa sanye yake da wata pcap wadda ta ɗan rufe goshinsa. Hannayensa zube cikin aljihun wandon jikinsa. Sai da ta ƙare masa kallo daga sama har ƙasa sannan ta fara takawa a hankali har gabansa, Duk da tsayi irin na Anna sai ta zama ƙarama a gabansa. Cikin yaren fulatanci ya ji ta ce
“Su wane ne ku?”
Bai ko motsa ba, Ballantana ta saka ran ya ji abin da ta ce. Ita ma bata sake maganar ba, Dan duk tunanin ta baya jin yaren ne. Don haka ta juya tana kallon Sudais da Ammar waɗanda ke tawowa wajen. A gabansa suka tsaya, Cike da girmamawa suka ce
“Barka da yamma Yaya.”
Jinjina kansa kawai ya yi. Ya dinga kallon wajen ta cikin glasses ɗinsa, Ganin bai ga abin da ke nema ba ya sanya ya mai da idanunsa kan Sudais. Cikin wata sassanyar murya ya ce
“Ina yake?”
Da hannu Sudais ya nuna masa Anna kafin ya ce“Ita ce ta ɗauke shi.”
Kallonta ya yi. Kamar ba zai ce komai ba, Sai kuma ya sake taku ɗaya wanda ya bashi damar tsayawa a gabanta sosai, Ƙasa ya yi da glasses ɗin idanunsa. Nan take manyan idanun nasa suka bayyana.
“Ina yake?”
Ya tambayeta cikin harshen fulatanci. Bata bashi amsa ba, Sai kallon sa kawai da take. Ya ɗan yi jim kamar me tunani can kuma ya cafki maƙogwaronta cikin dakkakiyar murya ya ce
“Ina yake?”
Kokarin ture hannunsa ta fara yi, Sai dai sam ta gagara yin haka. Ya sake matse hannayensa kafin ya ce
“Idan na sake tambayar ki sai na kashe ki!”
Da hannu ta nuna masa hanyar cikin garin. Lokaci ɗaya ya yi wurgi da ita ta tafi ta faɗi ƙasa, Haki ta fara yi tana riƙe da wuyanta wanda take jin yana mata wani irin raɗaɗi. Ya kalleta ya ce“Tashi ki ɗauko shi!” Ya yi maganar yana gyara zaman glasses ɗinsa. Bata motsa ba, Bare ya saka ran zata yi abin da ya ce ɗin. Ya ɗan kalleta sai kuma ya mai da idanunsa kan Sudais ya ce
“Mene ya same shi?”
Kallon kallo aka shiga yi tsakanin sa da Ammar. Ganin haka ya sanya shi yin tsaki a harzuƙe ya ce“Ina magana da duwatsu ne?” Ammar ne ya yi saurin cewa
“A'a yallaɓai. Yana can. Yana cikin ƙoshin lafiya in sha Allah.”
Jinjina kansa ya yi yana taune jajayen laɓɓansa. Ya mai da idanunsa kanta ganin har sannan bata miƙe ba. Kwafa ya yi sannan ya kalli wani soja ya yi alama da ya zo, A gabansa ya tsaya ya ce
“Ina ji yallaɓai.”
“A je a tawo dashi”
Ya yi maganar a sanyaye. Gyaɗa masa kai sojan ya yi sannan suka nufi cikin garin, Anna ko tashi tsaye ta yi tana kallon ikon Allah. Sai da suka birkita garin kafin suka gano ɗakin da aka kwantar da Major, Cikin hanzari wani soja ya saɓo shi a kafaɗa suka fito. Tun daga nesa yake kallon su, Ya miƙe daga kan dutsen daya zauna, Hannunsa ya ɗora kan bayan Major ganin jini na zuba daga jikin sa ya sanya ya ɗan ware idanunsa. Lokaci ɗaya ya kalli Sudais kafin ya yi magana Sudais ya ce“Ita ce Yaya.”
Bai ce komai ba ya cewa sojan su kai shi mota. Sai da suka nufi hanyar fita daga garin sannan ya mai da idanunsa kan Anna wadda ke tsaye har sannan, Gabanta ya ƙarasa. Ya fizgi gashin kanta nan take ya warware daga ɗaurin da aka yi masa. Cikin kakkausar murya ya ce
“Ke wace da har zaki taɓa shi? Ƙazama!”
Ya ƙare maganar yana zabga mata harara a iska. Anna ta riƙe hannunsa saboda zafin da ta ji, Ya saketa yana kallon sojojin ya ce
“A tawo da ita”
Daga haka ya nufi hanyar fita daga garin ba tare da ya sake kallon kowa ba. Ajiyar zuciya Sudais ya sauke don har ya fara ayyana irin rashin mutuncin da zai mata. Wasu sojoji ne guda biyu suka ƙaraso gabanta suna mata umarni da ta je. Amma sam Anna ta ƙi tafiya, Don haka ɗaya daga ciki ya ɗauketa ya saɓa a kafaɗa suka fara tafiya. Sai a sannan su ma su Sudais suka fara tafiya, Kana sauran sojojin da suka rage. Sai a sannan mutanen garin suka saki ihu suna kiran sunan gimbiya Anna da kuma Abar bauta Kara. Nan take aka tafi aka faɗawa Golma, Jikinsa har rawa yake wajen tawowa ko keken nasa bai tsaya jira ba. Sai dai ko da ya zo bai tarar da kowa ba, Don sun jima da yin nisa. Ya saki wata irin razananniyar ƙara tamkar wanda ya zare. Cikin wata irin kakkausar murya ya ce
“A je a kira min Pore!”.
****
“Sudais! Sudais! Sudais!”
A hankali ya ɗan juya, Lokaci ɗaya kuma ya tashi zaune a firgice. Wata babbar mata ce tsaye a gaban gadon tana kallon sa, Idanunta maƙale da tabarau fari. Ta girgiza kanta cikin sanyin murya ta ce“Kana ta bacci har ƙarfe 10:00?” Langwabar da kai ya yi yana ƙoƙarin yaye bargon jikinsa ya ce
“Na gaji ne fa Mama. Kin san wahalar dana sha kuwa?” Taɓe baki ta yi ta ce“To ai sai ka yi ta bacci har gobe.” Ta juya tana shirin fita daga ɗakin ta ce“Na mance. Abokin ka Ammar ya zo neman ka” Tana gama faɗin hakan ta buɗe ƙofar ta fita. Ajiyar zuciya Sudais ya yi sannan ya sauka daga kan gadon, Bedroom slippers ɗin dake ƙasan gadon ya zura cikin ƙafafunsa sannan ya nufi hanyar banɗaki. Bayan mintuna kusan ashirin ya fito daga ɗakin sanye da wani yadi mara kauri, Hannunsa riƙe da wayarsa yana dannawa. Murmushi ya yi ganin Ammar zaune kan kujera yana kallon sa, Gaba ɗaya kamar ba su ba. Sun zama wasu yan gayun su kamar da, Ya zauna kan hannun kujerar yana ci gaba da kallon sa ya ce
“Baba an tashi lafiya?”
Taɓe baki Ammar ya yi kafin ya ce“Sai yanzu ka tashi?” Mayar da wayarsa ya yi aljihu sannan ya ce“To ya zan yi? Wallahi gajiya ce ta makeni.” Murmushi Ammar ya yi ya ce“To sannu. Ka tashi muje asibiti” Sudais ya ce“Bari na fara cin abinci mana.” Girgiza kai kawai Ammar ya yi ba tare da ya ce komai ba. Ya tashi ya shige kitchen...
****Misalin ƙarfe 12:20 na rana suka ƙaraso cikin asibitin, Kai tsaye kuma ICU suka nufa. Sai da suka nuna id card ɗin su sannan aka basu damar shiga ciki, Kwance suka same shi kan gado. Fuskarsa maƙale da na'urar oxygen sai ƙara take a hankali, Hannunsa maƙale da canolar jinin da aka saka masa. Ammar ya tsaya a gefensa na dama yana kallon sa, Sudais da ke ƙoƙarin zama gefen gadon ya ce“Bai farka ba har yanzu?” Ammar ya ce“E. Amma an ce zai tashi nan da yammaci” jinjina kai kawai Sudais ya yi, Sun jima a haka kafin Ammar ya ce“Ko tafiya zamu yi?” Girgiza kai Sudais ya yi sannan ya ce“A'a mu jira a zo daga gida mana. Ba anan Yaya ya kwana ba?” Ammar ya ce“E anan ya kwana mana. Da safe sanda na zo ya ce bari ya je gida, Don bai sanar da su mai martaba ba gudun kada hankalin su ya tashi” Sudais ya ce“Ai ko ya kyauta. To kawai mu zauna mu mana na san duk inda yake ya kusa dawowa” To kawai Ammar ya ce sannan ya jawo wata farar kujera ya zauna akai.
Ana idar da sallar la'asar ya shigo ɗakin. Tana tafe a bayansa hannunta riƙe da kwando irin na zamani, Tashi suka yi suka gaishe shi cike da girmamawa. Ya amsa sannan ya kalli Major,
”Bai farka ba?”
Ya tambaya ba tare da ya kalle su ba. Sudais ne ya ce“E. Ɗazu da azahar dai ya motsa hannunsa, To kuma tun daga sannan bai sake ƙoƙarin tashin ba.” Jinjina kai ya yi bai ce komai ba ya juya ya fice daga ɗakin, Sai a sannan ya kalleta. Fara ce tas mai kama da Major, Ta ɗan sunkuya ta gaishe su cike da girmamawa. Fuska a sake suka amsa, Sudais ya ce
“Fulani ai ban saka rai da ganin ki ba”
Ɗan tura baki ta yi sanin halin sa ta ce“Kai Yaya Sudais. Ni wallahi bana son wannan sunan” Waro idanunsa ya yi cike da zolaya ya ce“Dan na ce Fulani? Ba sunan ki ba ne?” Girgiza masa kai ta yi ba tare da ta ce komai ba. Ta ajiye kwandon hannunta sannan ta ja gefe ta tsaya, Ba'a fi mintina biyu ba ya dawo shi da wani likita. Sake duba Fa'ik ya yi sannan likitan ya kalle shi ya ce“He's out of danger. Ya tashi, In sha Allah nan da magriba zai buɗe idanunsa, Congratulations” ya ƙare maganar yana miƙa masa hannu. Murmushi kawai ya yi ba tare da ya miƙa masa na sa hannun ba ya ce
“Thank you doctor.”
Jinjina kai kawai likitan ya yi sai kuma ya ce“Aikina ne” daga haka ya juya ya fice daga ɗakin ba tare da ya damu da yanda ya ƙi bashi hannun ba. Yarinyar da ke tsaye jikin bango ta dinga kallon sa, Sam bata ji daɗin abin da ya yi ba. Sai dai sanin hakan ba wani sabon abu ba ne a wajen sa ya sanya ta kawar da tunanin. Agogon hannunsa ya kalla, ƙarfe 4:10 na yamma. Ya kalli Sudais ya ce “Sudais ku ɗan zauna anan zan je na dawo.” Sudais ya ce“Tom a dawo lafiya." Jinjina kansa kawai ya yi sannan ya juya ya fice daga ɗakin cikin tafiyar ta isa. Sai da ya fita sannan Sudais ya ce
“Ameema ki zauna mana.” jiki a sanyaye ta ce “To Yaya” daga haka ta ƙarasa kan kujerar da ke can gefen ɗakin ta zauna ta yi shiru tana tunani. Suna nan zaune har lokacin sallar magriba ya yi, Suka tashi don zuwa masallaci. Ita ma ta tashi ta shige banɗakin da ke ɗakin ta ɗauro alwala, Bayan ta fito ta shimfida dankwalin kanta akan carpet ɗin dake ɗakin sannan ta gabatar da sallah. Ko da ta idar zama ta ci gaba da ta yi a wajen tana addu'o'inta. Motsin da ta ji ya sanyata kallon inda gadon yake, Motsi ta ga hannunsa na yi. Ta yi saurin tashi daga wajen ta ƙarasa gabansa ta riƙe hannunsa ta ce
“Yaya Fa'ik.”
****Wajejen bayan sallar isha'i ne. Ya ƙaraso wajen yana kallon sojojin da ke tsaye. Da idanu ya kalleta, Tana sanye da kayanta na jiya, Sai rarraba idanu take. Ya taɓe baki sai kuma ya kalli ɗaya daga cikin sojojin ya ce
“Ku saketa ta tafi.”
Cike da girmamawa ya amsa. Ya juya yana shirin barin wajen ya ji ta ce
“Ina kuma za ka sake tafiya?”
Ta yi maganar cikin harshen fulatanci dan ta fuskanci yana jin yaren sosai. Juyowa ya yi, Ya ganta tsaye a gabansa ta kafe shi da ido. Kamar ba zai magana sai kuma ya ce
“Kina da wata alaƙa da ni ne?”
Anna ta ɗan juya manyan idanunta kafin ta ce“Ba ni da wata alaƙa da kai. Kuma bana fatan samunta, Amma dole na tambayi in da zaka je tun da ka kawo ni nan.”
Ta ƙare maganar tana taɓe baki cike da rashin kunya. Gyaɗa kai ya fara yi, A hankali ya tako har gabanta. Hannunsa na hagu ta sanya ya damƙi gashin kanta, Cikin dakkakiyar muryarsa ya fara cewa “kin ci sa'a babu abin da ya samu ƙanina. Don haka kina iya tafiya yanzu, Sannan duk lokacin da ki ka sake gigin taɓa shi to ba iya ke ba. Sai na saka an ɗaure gaba ɗaya garin naku!” Ya saketa ta yi baya kamar za ta faɗi. Kallon sojan da ke kusa da ita ya yi ya ce “A mai da ita gida!” Ya ƙare maganar yana ƙoƙarin juyawa. A fusace Anna ta ce
“Ina zan tafi ɗin?” Ta yi tambayar tana matsowa inda yake. Juyowa ya yi, Ya ɗan kalleta fuskarsa a haɗe ya ce“Magana ki ke?” Shiru ta yi tana kallon sa, Ya ɗan kalli agogon hannunsa kafin ya ce“Idan bata so ba sai kun rakata ba. Ta tafi da kanta!”
Ya juya da niyyar sake tafiya ya ji ta riƙe masa riga, Runtse idanunsa ya yi. A ransa yana jinjina ƙarfin halin irin na yarinyar, Ya juyo a fusace yana kallonta da idanun sa wanda suka fara sauya launi. Kafin ya yi magana ta yi saurin cewa
“Ai ba ka isa ba. Yanda ka je har garinmu ka satoni haka zaka ɗaukeni ka mai da ni!”
***
Nanameera.