Kuncin zuci
by @bintuuu
Da ta qaraso sai ta zauna a wani kujeran na nesa dashi, yana kallonta yayi patting gefensa yace "Babe ki dawo nan kinji" ta girgizai kai tana maqe kafada alamun A'a, sai ya kwantar da murya yace "Haka akeyin zancen kuma?" ta gyada kai tana murmushi cike da kunya, sai Ahmad ya rinqa kallonta ganin kyawun da tayi masa cikin atamfan jikinta sai kawai ya miqe a nutse ya qarasa gareta, madadin ya zauna kusa da ita sai ya tsugunna gabanta yana leqa fuskanta ganin ta sunkuyar dakai, dukansu sai murmushi suke Na'ima najin zuciyar ta mata wani irin sanyi, Ya Allah..son da takewa bawan Allahn nan yakai haka? wane irin so ne haka yakesa take rasa duk nutsuwarta kuma takejin kamar tayi melting in tana gabansa, dan sunkuyo dakai Ahmad yayi yana leqa fuskanta aikuwa suka hada ido da sauri ta damqe idanunta, ahankali tace "Ni dai ka koma gurinka" sai ya tsaya kallonta yana murmushi bece komai ba, ganin yayi shiru sai ta dago idonta ya fada cikin nasa suna kallon juna kowa da abunda yakeji a nasa zuciyar, kamar me rada Ahmad yace "I love everything about you Na'eemah" qasa tayi da kanta tana murmushi sai ya sake kwantar da murya yace "Ahaka zamuyi hiran yau Babe" ta gyada kai sai ya sake cewa "Rancan fa har cewa kikayi kina sona" sai Na'ima ta kai gyalen fuskanta tana dan ware ido dan bilhaqqi itama ranan batasan lokacin da ta fadi hakan ba ganin yanda ya birkice mata, yana kallon idonta da murmushin yace "Ki kace ni kike so, ni kadai fa" ta kauda kai tace "Ni yaushe nace haka" yana dan dariya ya miqe tareda zama a gefenta ya duqo kansa gareta kamshinsa na cika mata hanci, ahankali yace "Then say it now tunda ranan baki fada ba" har sannan bata juyo ba sai ya damqe hannunta yace "Toh ni Ina sonki kinji" kawai sai ta damqe hannunsa dake cikin natan ta juyo idanunta a qasa, kamar me rada tace "Nima haka" Ahmad ya rinqa kallon yanda lipbalm din yake ta sheqi akan smooth lips dinta dasauri ya kauda kai yace "You look beautiful dear" sai tace "Ban taba ganinka cikin fararen kaya ba" dan yawanci manyan kayan Ahmad baqaqe ne ko dark brown, sai ya dan kishingida jikin kujeran yana kallonta yace "I'm saving it for our wedding ne, amma na kasa hakuri" sai Na'ima ta danyi shiru tana kallonsa, ganin ya kwantar da kansa ajikin kujeran bai bar kallonta ba yasa ta dauke kai sai yayi murmushi dalilin tuna besan ranan da Na'ima zata fara jure kallon idanunsa na tsahon lokaci ba, sai sannan Na'ima tayi gyaran murya ganin yanda ya shagala da kallonta, cikin sanyin ta tace "Ina wuni" yace "Lafiya Na'eemah, how was your day?" ta amsa da "Alhamdulillah" da haka ta miqa hannun gurin table din ta fara zuba masa pineapple juice din da sukayin, da ta miqo masa a cup sai ya karba amma be sha ba ya ajiye tareda zuba wani a cup ya dauka duka biyu ya miqa mata daya, karba tayi tana fadin "Nakane fa" ya gyada kai yace "Musha tare toh" shiru sukayi suna sipping juice din jefi jefi zasu juya su hada ido sai Na'ima ta rigashi dauke kai, can yace "Babe nafara dawo da ayyukana nan like we planned" tace "Zaka bar can din gaba daya?" ya girgiza kai yace "Zan rinqa zuwa lokaci lokaci, but most of my work will be here" ta gyada kai ahankali tace "Allah yayi jagora" shima Ahankali yace "Amin, ko kinaso mu zauna a Lagos din?" tana murmushi tace "Duk inda kaga yafi maka" sai yace "Duk inda kikeso dai Na'eemah, in ma California kike so sai mu koma can tunda mun bude branch acan" ta girgiza kai tace "Abuja is okay" ya ajiye cup din yana fadin "Shikenan princess" dan murmushi tayi tace "Ya Lamin yake?" yace "Yananan lafiya, shima zai dawo nan i think" Na'ima tace "Did he tell you about him and Nafisa?" yayi murmushi yace "Jira nake ya samoni da maganar sai in juyasa son raina" sai Na'ima ta danyi dariya tace "Habaaa" ya gyara zama yace "Bakisan halinsa bane, da bazakiji tausayinsa ba" tayi qasa dakai tace "Har da kai ai " Ahmad yayi shiru yana kallonta, Jin yayi shiru ta dago kai sai tayi murmushi ahankali tace "Kar kace komai please" sai ya hau murmushi tareda dan matsowa gareta, sai itama ta matsa baya kadan, yana dariya qasa qasa yace "Babe ba abunda zan miki" ta kauda kai tana murmushi tace "Nidai uhm uhm" sai yayi shiru yana ta kallonta admiringly while his heart keep beating so fast for her, In his heart, his thoughts kept whispering how badly he longed for that day to finally arrive, the day she would be his, He imagined the stolen smiles, the slow touches, the way he would pour out every unspoken feelings through love so deep it left her breathless, Those days he had replayed endlessly in his mind, the moments he had guarded in silence for so long, Days when he would finally show her what he truly meant by loving her...
Abincin da Ahmad beci ba kenan suka shiririce gurin hira shida Na'ima, dan daga baya matsawa tayi can nesa dashi sai ya qyaleta suka cigaba da hiran su ahaka har abincin yayi sanyi qalau a plate din da ta zuba masa, magana suke cikin raha yana bata labarin university days dinsa in Toronto, Na'ima sai kallonsa take admiringly ganin yanda ya taso cikin gata da arziqi wanda yafi na Bilal amma hakan bai chanja masa dabi'un sa zuwa ga munana ba, lallai Allah yana ikonsa yanda yaso akan mutum, and she was proud of this man sitting right in front of her...
Da Ahmad ya koma gida sai ya samu har sannan Abba bai tafi ba yana nan a part din Baba, sai kawai ya wuce part din Mamma, acan dakinta ya sameta tana zaune kan carpet din dakin me laushi tana ware wasu turarurrukan ouds masu qamshi acikin package dinsu, da sallama ciki ciki Ahmad ya qarasa dakin tareda da zama a resting chair dake gefe, Husna dake kwance kan gado ta miqe zaune tareda gaishesa ya amsa, dago kai Mamma tayi tana kallonsa, ganinsa cikin fararen kaya itama sai da ta dan tsaya kallonsa sai kuma tayi murmushi anutse tace "Baban mutum" ya dan shafa kansa yana murmushi sannan yace "Barka da dare Momma" ta amsa da "Ka wuni lafiya" yace "Alhamdulillah" da haka ya ciro wayarsa da yaji shigowan saqo yana dubawa, miqewa Husna tayi ta fice daga dakin sai Mamma dago kai tana kallonsa yana danna wayan, anutse tace "Nace zamuyi magana akan abunda ya faru ne daman" sai Ahmad ya ajiye wayan yace "Duk hotunan da aka kawo ba gaskiya bane Mamma" ta gyada kai tace "Nayi waya da Mamin tace gobe zatazo muyi magana" shiru Ahmad yayi sai ta cigaba "Zanso abunda kakeso Babana, kuma nima a iya ganina da yarinyar da kuma irin nutsuwarta da na gani yasa raina bai yarda da gaskiyan abunda aka aiko din ba" Ahmad ya sake gyada kai yana kallon mahaifiyar tasa, tace "Amma ka taba magana da ita akan abunda yasa ta baro gidan?" sai da Ahmad yaji zuciyarsa na wani iri, shi bayason arinqa cewa ta gudu daga gidansu alhalin circumstance ne yasa tayi hakan, ahankali yace "Ta fadamin, amma tana da hujjan yin hakan shiyasa, they almost killed her" Mamma ta danyi stiff tana kallonsa sai yayi qasa da idonsa sukayi shiru, sai can tace "Gobe in Allah ya kaimu zanyi magana da Mamin, Allah ya rufa asiri" ya amsa da Amin tareda miqewa cikin sanyi ya nufi kofa tana kallonsa...Daren ranan Ahmad kusan raba dare yayi yana puzzling duk zargin da ke ransa na wanda ya turo saqon nan gurin mahaifinsa, he really wants to know, ganin har lokacin babu wanda ke zuwa kansa sai Bilal yasa bayan yayi sallah kawai ya kwanta, washegari kuwa da ya tashi tafiya office sai ya dauki hanyar barin gari dan ya dubo ajiyar da ya bawa Mazzy, aikuwa ya samu Mazzy na nan dayan bangaren gidan, anan falon suka zauna bayan sun gaisa sai Ahmad yace "Inason kayi duk yanda zakuyi su fada maka in sune suka aika saqo gurin mahaifina" Mazzy ya tabbatar masa zeyi hakan kuwa, da ya tashi tafiya har ya nufi gate zai tafi sai kuma ya juya tareda nufan side dinda su Bilal din suke, a zaune ya samesu adakin hannunsu duk nadin bandeji sanadin daurin da su Mazzy suka musu, da dan sauri Nasir ya fara rarrafowa yana fadin "Wallahi ban mata komai ba ranan, ko kayan jikinta ban cire mata ba ka yarda dani" Ahmad na tsaye yana kallonsu Nasir ya hau bashi hakuri while Bilal ya duqar da idonsa ya kasa cewa komai sai can kuma ya dago yana kallon Ahmad din dake kallonsa shima, kallon kallo suka tsayayi atake hawaye ya kawo idon Bilal yace "Kayi hakuri, ni babu komai tsakani na da ita yanzu, yafiyarta nake nema ranan da ka ganmu tare" juyawa kawai Ahmad yayi bai ce musu kala ba, Nasir nata kiran sunansa gardawan dakin suka handakasa tareda kai masa bugu, tafiya kawai Ahmad yakeyi yanajin ransa na laushi at the same time kuma yanajin haushinsu, har ya qarasa bakin motansa bai dena jin hakan ba amma taurin ransa ya hanasa yasa Mazzy ya sassauta musu, aransa yana fadin "He beats her, he torture her, he raped her" sai da ya zauna cikin motan sannan ya shafa fuskansa afili yace "They have to pay for it" da haka ya tada motan yana barin unguwan, sai da ya isa office bayan ya nutsu ya kira Na'ima lokacin tana ware kayan da zata wanke wa Mami adakinta, a nutse suka gaisa sai Ahmad yace "Babe jiya kinyi bacci da wuri" tana murmushi tace "ayi munyi hira shiyasa ban dauka zaka kira ba" yana duban wasu folders yace "Ni ban gaji ba" sai tayi murmushi bata amsa ba, ajiye wayan yayi kan table dinsa ya saka a handsfree sannan ya cigaba da aikin, shiru sukayi tana jinsa yana aikin sai can ya juya gurin wayan yace "Yau ma zanzo Babe" Na'ima tace "Ba kullum fa ake zuwa ba" dariya ma ta basa sai yayi murmushi kawai yace "Toh ai sai mu chanja namu salon ko" tace "Uhm uhm" yace "Bazan dade ba ai" ta sake cewa "Kabari gobe to, ni kunya nakeji" kawai sai ya bar abunda yakeyi din ya dan duqo kusa da wayan, ahankali yace "Kunyar su Mami bani ba ko" tana dan dariya tace "Da kai" kamar me rada yace "Karki damu, zan cire miki ita watarana kinji" diif yaji ta kashe wayan, dan girgiza kai yayi yafara dariya qasa qasa yana maida hankali kan aikinsa, ta bangaren Na'ima itama hakan ne ta faru,tana murmushi aranta tana fadin "This man" nan ta cigaba da ciro kayan sai ga Mamin ta shigo dakin tace "Habibti sannu" ta gyada kai tana murmushi kawai sai Mami ta zauna bakin gadon tana kallonta, shiru sukayi sai can Mami tace "Habibti" Na'ima ta amsa tareda barin abunda takeyi din ta juyo, Mami na kallonta da murmushi tace "Zo ki zauna nan muyi magana kinji" komawa tayi gefen nata ta zauna sai Mami ta dan kamo hannunta, anutse tace "Ahmad yazo mana da wata magana rannan, ya fada mana yana sonki kuma yana son auren ki" sai Na'ima ta duqar dakai, Mami ta cigaba "Amma Abba ya dan tsaidashi saboda yanason mu kaiki gurin kawunki Na'ima, munason 'yanuwanki susan inda kike bawai dan zamu maida musu ke ba, sai dan anzo gandun da muke neman consent dinsu akanki, sannan muna son abubuwan da ke tsakaninku su daidaita ko dan wani nauyi dake zuciyarki ya sauqa kema Habibti" ta qarasa maganan tana damqe hannun Na'iman, hawaye Na'ima taji yana zuwa idonta zuciyarta na karyewa sai tace "Duk yanda kukayi shine daidai Mami" sai Mami tace "Yauwa daughter, but mind you bazan iya basu ke ba ko da sun roqi hakan, dan nima inason daughter na a gurina" murmushi Na'ima tayi ta dago tana kallon Mamin sai taga itama murmushin take mata, sai ta gyada kai, Mamin tace "Amma yanzu ki fadamin, kinason Ahmad?" nan Na'ima ta sake duqar dakai tana murmushi sai Mamin ta sake cewa "Saboda kinga duk yanda ze kai da sonki sai da amincewar ki zamu bashi ke" sai Na'ima tayi shiru tana murmushi kawai, nan Mami ta fahimci komai sai ta dan rungumota tana fadin "Allah ya albarkaci rayuwanki Na'ima" ahankali tace Amin tanajin soyayyar Mami aranta sosai, dan a dan zamansu ta cike mata fiye da rabin gurbin rashin Mahaifiyarta da tayi a rayuwa, da haka Mami tace mata zata fita unguwa yanzun, Na'ima ta amsa mata sannan ta cigaba da aikin da takeyin...A daren ranan su Na'ima na falon Abba ana hira sai Faruk ya sako zancen ayyukan su Nafisan da Na'iman, yana kallon Nafisa yace "The work is speeding so fast kunje kun sake gani kuwa" Mami tace "Nagani dazu nima, Ma Sha Allah Baby na komai ya kusa kammaluwa" Nafisa na murmushi tace "Mami high luxury brands zan zuba" ta juya gurin Faruk tace "Yaya wane brand maza sukafi so these days, inata surveying har yanzu ban tsaida guda daya ba" Al'ameen yace "Mun banu ai" Abu ya juya suka fara dariya tare, sanin halinsu yasa Na'ima jijjaga kai, Nafisa kuwa ta danna musu harara dukansu, Abba ne yace "Allah ya taimaka, naduba business plan din naki jiya, yayi kyau sosai amma ki qara himma tukunna" Faruk ya gyada kai shima yace "Kinyi qoqari amma akwai gyara kadan, gobe da safe kafin na fita ki sameni mu gyara" Nafisa ta amsa da Amin sai Faruk ya kalli Na'ima dake kallon News a Tv yace "Na'ima kefa, yaushe zaki fara fita?" sai Abba yace "Nayi magana da Adekunle jiya ma, akwai sauran verifications da zata je yi, da sauran lokaci tukunna" Mami tace "Aikin gomnati sai qa'idoji daman, Allah ya sa afara a sa'a" sai duk suka Amin, Abba ya dan gyara zama yace "Na'ima kinyi magana da Mamin ku dazu ko" ta gyada kai ahankali tace "Eh Abba" sai yace "Inason muyi settling tsakaninki dasu daughter, in ma basu fahimci sulhun ba mu masu iya shige miki gaba har zuwa kotu ne Na'ima" sai tayi qasa da kanta tanajin hawaye na zuwa mata, Nafisa da basu fahimci zancen ba duk suka nutsu kowa yayi shiru, sai Abba ya cigaba "Kuma ba barinki zamuyi gurinsu ba ko sun nemi alfarman haka sai dai in ke kikace kinaso, shidin ma sai mun aminta da nadaman su kinji" Nafisa dai har sannan tanason ta tabbatar da ko abunda take zargi ne sai ta kasa hakuri a nutse tace "Abba komawa Kano zatayi?" sai Abba ya amsa da "Zamu je can kanon ne tareda ita har ke da Faruk" sai Nafisa ta danyi stiff tana kallon iyayen nata, Na'ima dake jin hawaye na qoqarin zubowa ta sake duqar da kanta, kawai Nafisa ta matsa kusa dasu Abban tana fadin "Abba dan Allah kar a maidata, wallahi har oxford ya bita ya daketa" su Abu da kejin wani iri duk sukayi zuru suna jira amsan Abba dan shi Faruk ya san da maganan, sauqe numfashi Abba yayi yana kallon iyalin nasa gashi Mami tayi shiru a gefensa tana jiran ya aiwatar da komai ranan, sai yace "Ba koma wa gaba daya zatayi ba Nafisa, in Sha Allah tare zamu dawo da ita, it's high time babanta yasan inda takeh, it's high time mu daidaita komai tsakaninta da 'yan'uwanta ko dan ta samu sauqi a ranta itama, munsan ko da batason komawa garesu akwai wani nauyi a ranta da in ba lamuran sun daidaitu ba bazata taba jin ya sauqa daga zuciyar ta ba" sai Na'ima ta fara kuka ahankali Mami ta miqa hannu ta kamota tareda zaunar da ita a gefenta tana dan bubbuga bayanta tace "Kiyi hakuri kinji daughter, komai ya zo qarshe bi'iznillah" Abba yace "Anyi ta nemamun yaron ba'a samesa ba, ko line dinsa da nasa ayi tracking ma baya tafiya, Amma in sha Allah in na samu ganin mahaifinsa yasan da komai zamu dau mataki, he won't go scot free daughter" Na'ima na kuka a jikin Mami sai Nafisa ta miqe ta koma kusada ita tana hawaye itama tace "Tare zamu dawo ai kace ko Abba" ya danyi murmushi yace "Tare zamu dawo, muma bazamu bada ita ba this time" Faruk yace "Munanan tare da Habibtin Mami" Abu yace "Abba zanje nima kar tace zata zauna" sai kowa ya fara murmushi, Al'ameen shima yace "Tana cewa zata zauna sai abamu daki muma mu zauna kawai Abu" nan kuma aka danyi dariya har Na'ima dake share hawaye tana murmushi, Nafisa tace "Dama a dakinta zan tare nikam" Abba na murmushi yace "Duk bazaayi haka bama" da haka suka cigaba da hira wanda Na'ima jinsu kawai take dan sai yanzu zancen ya fara dukanta, Hajiya....wane irin gamo zatayi da Hajiya..da wane idon zata kalli Alhaji...kar ma azo batun kawunan ta, ranan har aka gama hira Na'ima na zaune a falon ne kawai, sai da taje dakinta tana cikin saka night dress dinta Nafisa ta shigo hannunta riqe da pillow ta kwanta anan gadon Na'iman, murmushin dole Na'ima tayi tasan tazo consoling dinta ne, Nafisa na kallonta tace "Dagaske fa bazaki zauna ba Na'ima" sai da ta saka hulan baccin ta tareda cusa gashinta da ya leqo dayawa sannan ta qarasa kan gadon ta hau, a nutse tace "Nima banason zuwa dai Nafee, inajin zuciyata tana bugawa sosai" sai Nafisa tace "All will be fine in sha Allah, ba abunda matar can ta isa ta miki daga ita har dan nata, kuma ko giyan wake sukasha sun san aurenki da Bilal bazai maidu ba" Na'ima ta gyada kai ahankali tace "Bazan iya zama a gidan ba Nafisa, har gwara in koma qauyen yafi" Nafisa ta harareta tace "Kauye a Ina kuma? kinason kicemin har yanzu baki dauki nan a matsayin gidanku ba" Na'ima ta girgiza kai tace "Ba haka nake nufi ba Nafee, kinsan ko ban zauna agurinsu yanzu ba dole wataran in je hutu gurin su, shine bansan ta yanda zan fara zama a gidan ba after all that happened" Nafisa tace "Ba wani zuwa hutu, mutanen nan basu cancanci zuwanki hutu gurinsu ba" murmushi kawai Na'ima tayi dan tasan dole daman komin dadewa sai ta koma ga nata 'yan'uwan tunda har duniya ta nade bazata taba cewa su din 'yanuwanta na jini bane...bayan sun gama shirin kwanciya tana hira sama sama da Nafisa dake kwance gefenta tana danna waya sai ga kiran Ahmad ya shigo wayanta, bayan ta daga daga can bangaren Ahmad kafin yayi magana kiran Lamin ya shigo wayansa, bai dauka ba yace da Na'iman "Bakiyi bacci ba" ta amsa da "Uhm" gani tayi Nafisa tayi saurin tashi kamar wadda aka mintsina tayi saurin ficewa daga dakin, sai taji Ahmad yace "Bari na dauki kira I'll call back okay" ta gyada kai da haka Ahmad ya katse kiran tareda daukan kiran Lamin da ya sake shigowa, yana kaiwa kunne yaji shi agigice yace "Ahmad go to Insta noww" sai yace "What happened?" Lamin yace "One motherfucker tagged you, I try to hack it but it's coded strongly, they messed with your gurl Man..." Da sauri Ahmad ya jefar da wayan akan gado ya jawo laptop din dake gefensa akan gadon sai yaga ta aikin office dinsa ce, da sauri ya yaye duvet din jikin sa ya sauqa daga gadon ya nufi kofa ko takalmin gefen gadonsa bai saka ba, bibbiyu ya rinqa hada stairs ya isa falon da sauri ya dauki dayar laptop dinsa dake kan kujera ya bude, anan falon ya zauna qasan carpet yana duba post din da akayi tagging din sunansa just 5 minutes ago, sai da zuciyar Ahmad ta tsaya na wasu daqiqu ganin hotunan da aka aikawa maihaifinsa ne akayi posting anonymously da sunansa, hannunsa na rawa ya fara danna laptop din, nan ya fara bin hanyoyin da zeyi hacking account din, wani irin encrypted account ne da ya daukesa wasu mintuna goma kafin ya samu Access din shiga sannan ya goge komai har account din ya kulle gaba daya, kwantar da kansa yayi jikin kujeran dake bayansa yanajin ransa na tafasa a lokacin, like who dah hell is trying him this time, sake duba IP address na me account din yayi sai yaga ya nuna masa location Lagos ne, bottle water ya janyo daga kan table yasha idonsa na kan address din har sannan, sai ya dauko wayansa ya kira layin Nafisa, tana dauka tace "Yaya what is happening?, people are talking everywhere" yana shafa goshinsa in frustration yace "Don't let her know, karki bari tasan komai Nafisa, zanji da sauran masu sharing post din" da haka ya kashe wayan ya fara neman layin Mazzy ransa na qara tafasa...