BLOOD CROWN (THE HEIRS APPARENT)
PAGE _______23 & 24
by @swrites22
Haka rayuwa ta cigaba da miqawa yau da dadi gobe babu, da buga buga suke cigaba da gungurawa Amma duk da haka sun rufawa kansu asiri, haka zalika ta bangaren Baba ilerika sosai yake mutunta su tare da nuna musu kulawa tun mutanen gidan na kuskus akan cewa saboda yaga yar budurwa kyakyawa ne har suka fito fili suna faɗin ai karuwar sa ce dama saisa ya fitar da ya'yansa ya basu ɗakunan.
Mu ɗan waiwaya baya abinda baku sani ba shi ne lokaci da Baba ilerika yace wa Hushaima akwai ɗakunan haya, ya'yan sa ne a ciki ya fitar dasu ya maida mazan ɗakin soron ƙofar gida, matan kuma ya ce su koma su raɓe ɗakin yan uwansu, a faɗin sa basu da amfani tunda basa kawo masa komai dan haka in sukayi wasa duk sai yayi waje dasu ya zuba yan haya a gidan dukda yanzu ma rabin ɗakunan yan haya ne a ciki.
Yau ta kasance lahadi su Hushaima basu da aiki, Shazeen kuma da Sahnish zai fita ya wuce ya kaita tahfeez da suke zuwa tun 10am sai 5pm a duk ranakun weekend. Zaman ɗakin ne ya isheta taji gwara ta fito ta sha iska duk da kuwa bata san zaman tsakar gidan, saboda har yanzu bata shiga sabgar kowa harkarta tsakanin ta da Baba ilerika ne sauran mutanan gidan kuwa saidai in ta kama, dan tunda ta karanci duk ba wanda ke kallon kan ɗan uwansa da gashi taja mutuncin ta.
Sanye take da ɗaya daga cikin rigunan da Amla ta kawo masu tsaraba, miqewa tayi tana neman Abinda zata rufe gashin kanta wanda na lura shi kaɗai Hushaima ta damu data suturta a duk inda take zakaga kanta a ɗaure da dankwali, ganin zata wahala yasa ta zari dankwalin atampa kawai ta kafa daurin ture sannan ta dau wayarta ta fita.
Kusan yau duk kowa na gida ga kuma alamar hadari dake haɗowa wanda yasa zafi ya yawaita, yawanci kowa na waje yana shan iska ƙarƙashin manyan bishiyun mangwaron dake cikin gidan, wanda suka yiwa kusan rabin filin tsakar gidan rumfa, kowa da abinda yakeyi wasu kuma zaune suke kawai suna gulmar junan su.
Fitowar Hushaima yasa ido ya dawo kanta aka fara kuskus ɗinta, bata kalli kowa ba ta Ƙarasa Kan wani table data gani an ɗaura qullin kayan wanki akai, ture kayan tayi gefe ta zauna tare da ɗaura kafa ɗaya Kan ɗaya, ta buɗe game a wayarta tanayi amma kusan duk hirar da suke tana ji , kunnen ta ne ya ɗauko Mata maganar da wata da Ake Kira da Sa'a super keyi da ƙawarta Wadda tafi tunanin ba a gidan take ba, saboda ita har yanzu tsabar yawan mutanan gidan baza ta iya ware su ba, faɗi take, "Kee kowa ya iya takunsa ustazi ne, amma wanna da kike ganinta akuya ce me fatar kura, karuwar Baba ilerika ce ai har kawalcinta yake yana haɗata da wasu manyan alhazawa a waje yaga yar kyakyawa, ke ai kinsan Baba ilerika baya zubin adashin da ya san ba ranar ɗauka ".
Cikin bacin rai ta ɗago da Niyyar maida martani idanunta ya sauka cikin na wani kyakyawan matashin saurayi da ya fito daga wani ɗaki, yana sanye da t shirt me ƙaramin hannu sea blue da Ash wando, fari ne amma ba irin kau ɗin nan ba, fatar jikin sa a murje take kamar ta wani ɗan jariri, lips ɗin bakin sa pink dasu sunyi shar suna shining kamar ya shafa lipgloss suna zagaye da sirrin gashin Baki, hancin sa ɗan karami haka idanun sa irin Magnetic eyes ɗin nan ne masu kyawun kallo, baya tara gashi amma Wanda ke kansa a kwance yake baki siɗik ga laushi, kunnensa ɗaya maqale da earpiece. Kallonta yake shi ma kamar yaga wata sabuwar halitta, ganin ido na ƙoƙarin dawowa kansa ya sashi basarwa yana ɗan kashe idanun saboda ranar data hasko ƙofar ɗakin nasa, sai da yabi gabaɗaya mutanan dake tsakar gidan da kallo sannan ya Ƙarasa fitowa, A tsaye yake dan duk inda ake buqatar namiji wanna gayen ya Kai, ga six packs din sa da shatinsu ya fito dar ta cikin t shirt ɗin saboda fitting ɗin gymnastics body ɗinsa da tayi.
A bangaren Hushaima kuwa ganin ya dauke kansa yasa itama sauke nata ƙasa da mamakin wannan kyakyawar halittar data gani a yanzu a kuma cikin gidan da kwata kwata bai Mata kama da irin mutanan dake rayuwa a ciki ba, take ta manta da martanin da taso yiwa Sa'a super, jama'a duk fa wanna kyawun da Hushaima ta rude a Kai baikai rabin kyawun ta ba. " May I sit"........... Ta juyo wata murya, ɗagowar da zatayi kawai ta ganshi tsaye a kanta ba tare data san lokacin da ya ƙaraso ba, sai dai kuma ko da ta kalle shi bai mata kama da shi yayi maganar ba. "Stop looking at me before I poke your eyes out"............ Sai a lokacin ta tabbatar da eh lalle shi ɗin ne yayi magana, voice ɗin sa is so deep gata very clear sannan gata da low sound dan ko ita badan idanunta na kansa ba taga motsawar ɗan bakin nasa da baza tace shi yayi maganar ba, amma kuma duk wannan abun a banza tunda bata san me yace ba hakan yasa ta sake ɗauke kanta kawai.
"Ya jey zaka zauna ne ta tashi ko Kuma na kawo ma wani Abun zaman ?"............ Baheelah yarinyar kawu Adamu ta faɗa tana tasowa cikin salon dake nuna neman shiga take.
Ko kallon ta baiyi ba ya sanya farar ƙafarsa dake sanye cikin slippers ya ture kayan wankin dake gefen Hushaima qasa sannan ya zauna, matsawa Hushaima tayi can karshen bencin, har yasa hannu zai ɗauko wayar sa a aljihu ya tsaya ɗagowa yayi yana kallon space ɗin data bada a tsakanin su fuskarsa dauke da dimbin mamakin da ya gaza ɓoyuwa ya ce, "Are you in this house ? "............ Ya tambaya idonsa a kanta, kallon sa kawai ta tsaya yi kamar wata doluwa dan kwata kwata bata fuskanci abinda yake faɗa ba. " A gidan Nan kike?"........... Ya sake tambaya da wannan daddadar muryar tasa . "Eh". Hushaima ta amsa.
"Sabuwan zuwa?".............Ya sake tambaya, Kai kawai ta gyada masa alamar eh, still idon sa a kanta ya sake faɗin, " Bana son kallo".
"Ikon ALLAH, to Kai da wani idon kake kallona har kasan Ina kallon ka?"........... Tayi karfin halin faɗa duk da yadda takejin zuciyarta na rawa har lokacin. Ɗauke kansa yayi ya Ƙarasa zaro wayar tasa, taɓe baki Hushaima tayi tare da tashi da niyyar komawa ɗaki Baheelah ta ce, "Duk iya firirita dai da kissa irin ta kilaki saidai ta canza sheqa dan ba kowani tsuntsu bane me jan gashi yauw........." Ai bata karasa ba taji wani abu dummm akan fuskarta daga kan hancinta zuwa bakinta, da mamaki take kallon Hushaima dake binta da wani fusataccen kallon, dan duk gidan Baheelah na daga cikin tatattun marassa kunya gata da zubin garada wanda hakan yasa wasu daga ciki suke shakkar ta.
"Whl ki kiyayi ƙetara iyaka ta, bana tsallaka iyakar kowa a gidan nan, ba wai Kuma dan duk wani munafurcin da kukeyi baya dawowa kunne na bane, dan duk wata taqala da ake nemana da ita Ina sane da takun kowani kare da ƙarya kawai banga Sa'an yi na bane a cikin ku saisa, amma daga yanzu zan saukar da kai na daidai da matsayin naku inci kusun uwar duk shegiyar data sake shiga gonata. Banza jakar maza an gaya Miki kowa ire iren ku ne ballagazazzu" .
Ai take duk aka miqe saboda yadda Hushaima ta rikiɗe musu lokaci guda, yan surutai ne suka fara tashi wasu na bayan Baheelah wasu kuma na cewa Hushaima ta burgesu, harda masu cewa gaba da gabanta yau an samu wadda ta kwaɗe Baheelah, sai masu cewa dama bar raina mutum shuru shuru in aka ƙuresu basu da daɗi.
Duk wanna abun da ake yi Jey kamar baya wurin dan ko nuna yaji ma baiyi ba, tunda ya zaro wayar sa bai sake ɗaga ido ya kalli wani ba ballatana ya nuna yasan abinda ake yi.
A tunzure Baheelah ta ɗaga hannu da niyyar kaiwa Hushaima duka saidai kafin hannunta ya sauka a jikin Hushaima ta danqe shi tare da maida shi baya da ƙarfi har saida yayi Ƙara ta kuwa raka mata shi da wani wawan Mari ji kake tasss kamar tartsatsin wuta, da yawa yawan manyan da suke wurin sai da suka dafe kumatun su haɗe da saka sallallami amma babu wanda yayi ko da gigin tunkarar inda suke. "Whl kika sake yunkuri Kai hannu jiki na sai na illataki, shashasha Dabba kawai"............Ta faɗa a zuciye tana hankaɗata ta juya zata wuce ɗakinta, wani irin ihu Baheelah ta kurma ta fara dira tana sama da ƙasa, da sauri wata babbar mata ta fito daga bayi tana faɗin, "Na shiga uku meya samu Baheelah? ku Kira min Adamu".......... Ta ƙarashe tana nufar wurinta, da sauri wata budurwa ta riqeta tana faɗin, "A'a dakata umma Ina zaki? tana cikin wanna halin ai kawai a leqa waje a Kira su wulu suzo su ɗaure ta tukunna, mutanan ne suka tashi kuma kinsan hadarin dake tattare da aljanun Baheelah, ranar haka ta kusa Kai Fandi lahira".........kafin ta ida magana ma har samarin gidan sun shigo duduwa data kirasu tana biye dasu.
Igiyar shanya Jimbo ya figo tare da nufar inda Baheelah take tana faman bige bige, rirriketa sukayi suna kokarin zargayeta, wani ihu ta sake kurmawa tare da yin wata girgiza saiga su Jimbo sun watse kamar wasu fari, kuka umma ta fasa yayin da Baheelah ta tashi a guje zata nufi rijiya. "Ku rike min ita dan ALLAH, ku taimake ni, na shiga Uku".......... Tashi su Jimbo sukayi daƙyar suka sake riqota amma duka ɗaya ta sake musu suka sake bajewa, ai bagimba daga inda yake kwance ya fara rarrafe yana neman hanyar fita dan saida akayi wata Hajijiya dashi kafin ya samu isa kan ƙasa.
Runtse idanu Hushaima tayi take ko ina na jikinta ya ɗau ƙerma harta lips dinta, wani irin numfashi taja tare da dunƙule hannuwanta ta juyo a wani irin fisge ta nufi wurin Baheelahn, wasu irin gittattun Mari guda biyu ta sauke mata. A hankali Jey ya ɗago tare da sauke idanunsa a kansu saboda yadda yaji ƙaran saukan dukan kamar ba mutum aka daka ba, wani wawan wawura Baheelah ta kaiwa wuyan Hushaima tare da haɗata da bango ta makure. ihu wasunsu suka sa yayinda wasu suke dariya harda tsalle suna tafi. Su Umman ne sukayi waje da gudu dan zuwa neman masu kawo masu ɗauki Kar ayi kisan Kai. Shi kuwa Jey gyara zama yayi yana kallon su kamar ya samu cinema.
" Ni zaka shaqe "............ Hushaima ta faɗa tana kallon cikin idon Baheelah da ya rikiɗe. Ai a ɗari suka watse kowa yaja baya, wasu na faɗin whl itama aljanun ne da ita wanna faɗan ba na mutane bane. Rufe idanu Hushaima tayi tare da sa hannu ɗaya a wuyanta sai gashi duk ƙarfin da Baheelah ta sa babu shi ta banɓare hannun daga wuyanta, ba tare data buɗe idanun ba ta haɗo yatsun Baheelah na hannu guda biyu manuna har saida sukayi Ƙara ji kake gugurus, mahaifiyar Baheelah in banda ihun kuka ba abinda takeyi gashi duk wanda ya shigo yaga abinda ke faruwa baya iya tunkarar su, ga gida ya cika maƙil da jama'a harda maƙota fadi ake a Kira malamai Kar su kashe kansu, buɗe idon da Hushaima zatayi gabaɗaya kwayar idanun sun koma blue ba fari ko kaɗan, yanke jiki Baheelah tayi ta faɗi ita Kuma Hushaima ta tsallake ta ta wuce dakinta ai da gudu aka dinga kaucewa ana bata wuri.
Tana shiga ta kullo ƙofar ta nemi wuri ta kwanta anan ƙasa kan siminti tana haki kamar wadda tayi tseren gudu.
A tare baba ilerika da kawu Adamu suka ƙaraso dan dama shi kawu garba yana bakin container sa kuma duk abinda ke faruwa yana da labari Kuma yana ganin shige da ficen da akeyi a gidan nasu, Amma yace ba abinda zai shigar dashi gidan nan haka kawai, maybe ma aljanun Baheelahn ne suka jefar da shi a banɗaki suka kawo masa shanyewar ɓarin jiki, dan haka bai ajje ɗa ba bai ajje jika ba a cikin gidan in sun ga dama su kashe kansu ma ba abinda ya sha mai kai.
Ganin har lokacin Baheelah bata farfaɗo ba yasa kawu Adamu miqewa yana faɗin, " Dole ma wanna Annobar su bar gidan nan, haka kawai za'a kashemin ƴa".
"Saboda Kai ka kawo su ? ko zaman ka suke? Ko kuma kana da gado a gidan"....... faɗin baba ilerika yanawa kawu Adamun wani matsiyacin kallo.
"Amma dai kasan da taimako na aka tashi ginin gidan nan ko, tunda ba kuɗinka kaɗai bane a ciki".
"To sai ka faɗamin in filin naka ne ?"........... Nan fa rikici ya balle tsakanin kawu Adamu da baba ilerika shi yana cewa saisu Hushaima sun bar gidan shi Kuma Yana cewa bai isa ba haka suka wuni abu ɗaya ranar.
Shi kuwa Jey zaman son sake ganin Hushaima yayi dan shi bai gama yadda ita ɗin ma ruwa ɗaya bace gabaɗaya, Amma har ya sha zamansa ya gaji bata sake fitowa ba, haka ya hakura ya tashi ya fita da tunanin ko aljanun sun ɗauke ta ne data shige datkin, Ni kuwa nace Jey ka raba kanka dan Hushaima dan whl in ta danqe ka mu dai bamu iya kwatoka hannunta yauwa .
----------------------√
Tunda Amjad ya sauka a Nifaz bai buɗe wayoyin sa ba tsawon kwana biyu saboda ƙoƙarin sa na daidaita abubuwan dake gabansa haka zalika ba wanda yasan ya dawo sai su Philip. Yau yake shirin tarkatawa ya koma can gida wurin su Anah, Misalin 6:30pm idar da sallar sa kenan ya jawo system ɗinsa da niyyar tura wani saqo, sanye yake da royal blue ɗin fitted jallabiya da tayi masifar karɓar sa, ji yayi an turo ƙofar falon nasa, sanin ba Mai shigo masa wannan falon nasa na ciki kai tsaye in ba Philip ba shi ma Kuma sai ya tsaya ya nemi izini ta hanyar Knocking, ɗagowa yayi da niyyar ganin waye idon sa ya sauka a kanta . "Nayrah!"........... Ya faɗa da mamaki saboda ko da wasa Bai taba kawo zuwan ta gidan sa ba a irin wannan lokacin, ya akayi tasan ya dawo? Waya fada mata ? Meya kawota? Wani irin faduwa gabansa yayi amma ya yi ta maza.
Tsaye take idanun ta yayi ja sosai alamun taci kuka har ta godewa ALLAH, Adire gown ce a jikinta duk tayi squeezing kamar wadda aka ƙwato daga bakin kura, wani Kukan ta sake fashewa dashi tare da tahowa da gudu, ganin haka yasa ya miqe tsaye tana zuwa ta faɗa jikinsa cikin muryar kuka ta shiga faɗin, "Na sha gaya ma kana ɗaukan Abun nan da wasa, to gobe za'a ɗauramin aure da farshad, Amjad in na rasaka Bansan in da zan sa kai na ba, bazan iya rayuwar aure da kowa ba in ba Kai ba. Naga gabaɗaya kai baka damu ba, tun kafin wanna abun ya faru nake faɗa ma ka tsaida ranar auren nan kaki sai sawa kake ana ƙara jan lokaci, wai ya kake so nayi da rai na ne ? Ina tabbatar ma da in aka ɗaura auren nan rayuwata tazo ƙarshe Amour"...........Ta ƙarashe tana fashewa da wani sabon kuka Mai taba zuciyar mai sauraro tare da sanya masa invitation card ɗin cikin hannunsa.
Zameta yayi daga jikinsa lokaci ɗaya idanunsa sa ya canza kala saboda ɓacin rai, ba tare da yabi ta kan invitation card ɗin dake hannun nasa ba, cikin wani kakkausan sauti da bata taɓa tunanin yana da irin sa ba ya ce, "Amma ban taba tunanin baki da hankali ba sai yau Ninie, kinsan abinda kikayi kuwa ? Kinsan me zuwan ki zai haifar min? Kinsan me zai biyo baya yanzu ? Innalillahi wa inna ilaihir rajuun".......... Dafe kansa yayi zuciyar sa na luguden duka, shi kadai yasan saqe saqen dake zuwa cikin kansa, cillar da katin yayi wanda har lokacin bai samu arziƙin kallo daga Amjad ɗin ba. " Tashi ki fita"..........ya faɗa a dake.
Ba shiri ta haɗiye kukanta tare da ɗagowa tana kallon sa cikin ɗinbin firgici, ta buɗe baki da niyyar magana ya tare ta, "kiyi maza ki bar gidan nan nace Miki ko bakyaji ne?".
Gyaɗa kanta tayi tare da faɗin. "Na sani dama, kai ɗin kanka kawai ka sani, zan tafi tunda ni nazo in da kake, amma karka ƙara nema na, Karka ƙara kusanto rayuwata nima na barka kamar yadda kake buqata ɗin, Zan karɓi ƙaddarar data zo m........." kasa ƙarasawa tayi ta juya a guje ta fice daga falon.
Jagwab ya koma ya zauna hannuwansa dafe da kansa, tunane tunane kawai yake can Kuma ya miqe da sauri kamar wanda ya tuna wani abu ya warci system ɗin ya wuce ɗaki yana me kasheta gabaɗaya ya ɗaura a kan gadon a lokacin da ya shiga dakin, sannan ya wuce ya ɗauki wayoyin sa ya kunna, kiran wata number da akayi saving da Nazbeer yayi, ana ɗagawa bai saurari gaisuwar da Nazbeer ɗin yake masa ba ya ce, " Kayi maza ka bi motar data fita daga gidan nan yanzu".
"Boss ai ta ɗan jima da fita, kuma a yadda ta fita ɗin nan kamar fa ta qure gudun motar ne ".
Cikin ɗaga muryar da bai saba ba ya ce, "Ka bita nace, Kuma ka hanzarta, titin sea Stone zakabi har zuwa mrovo rock, yanzu yanzu karka ɓata lokaci".
"Okay boss"............ Ya faɗa tare da kashewa ya kira wata number ana ɗagawa ya ce, "Jack ya ake ciki kun same shi ne?".
"No boss, an samu matsala domin yanzu nan muka baro ƙofar gidan an kawo gawar yaron ".
"Whattttt!"...........Ya fada da ƙarfi Wanda har hakan yasa jijiyoyin kansa Sarawa kasancewar hayaniya ba dabi'ar sa bace yafi gane abu simple.
"Yes boss ance wai kashe shi akayi Amma ba'a san dame ba saboda ba yanka bane ko harbi sannan ba accident bane kuma ance ɗazun ya fita da yamma, yanzu Kuma aka kirasu an tsinci gawarsa a gefen titi tare da motarsa ".
"Innalillahi wa........." Bai ƙarasa ba kiran Nazbeer ya shigo hakan ya sashi katse wayar Jack ya ɗaga ta Nazbeer ɗin. "Boss motar data fita yanzu fa gata nan akan mararrabar mrovo rock tayi accident, ɗaya motar da sukayi accident ɗin ma ta tashi da wuta, yanzu haka an Kira Ambulance".
Wani irin rugugi yaji a cikin kansa ba shiri ya laluba bakin gado ya zauna yana karanto duk addu'ar da tazo bakinsa ganin komai yana neman ƙwace masa, daƙyar ya iya daidaita kansa sannan ya samu faɗin, " Ka bisu ka san hospital ɗin da zasu, sannan ka sanar dani zanzo yanzu ".
"Boss........"....... Saurin Tarar sa yayi, "I must come Nazbeer, dole naje koma me zai faru"..........Ya ƙarashe yana me kashe wayar, wani siririn gumi ne ke zirarowa ta gefen goshin sa na dama daƙyar ya samu ya miqe, key ɗin mota ya ɗauka ya fita .
Kamal na ganin sa ya taso, tsaidashi yayi ta hanyar ɗaga masa hannu ya wuce wurin motar ya shiga ya tada ya fita dan already securities sun buɗe masa gate ɗin.
Mathew ɗaya daga cikin body guard ɗin sa ne cikin gurbatacciyar hausar sa ya ce, "Kamal bai kamata mu barta ta tafi ita kade ba, yanayin sa akwai damuwa".
"Yes Mathew, inaga mu bishi a baya ".
"Lets be fast, Aram let's follow the boss "..........Ya faɗa Yana yafito Aram ɗin suka shiga motar da Kamal ɗin ya fito da ita daga parking space suka bar gidan.
A hanya Nazbeer ya kirashi tare da shaida masa hospital ɗin da aka Kaita, bai tsaya jin ƙarashen zancen ba ya kashe tare da Ƙara gudun motar. Kusan a tare suka ƙarasa hospital ɗin dasu kamal dukda gudun da yayi dan suma ba ƙaramin taka mota sukayi ba, tare suka shige amma shi bai lura dasu ba saboda tashin hankalin da yake ciki, duk inda ya wuce sai an bishi da kallo harda masu nuna shi saboda yau ba zance sanya p cap ko nose mask ya ma manta dasu, A kofar emergency ya tarar da Nazbeer ɗin. "Ina take?".
"Sun shige ciki da ita" ............Wayar sa ce ta fara ringing, kallon screen ɗin yayi dake wayar na hannun sa ne, da mamaki ya dago Yana kallon Nazbeer, "kace motar data fita tayi accident?".
"Eh boss yanzu haka suna ciki tare da yarinyar ".
"You are a big liar Nazbeer, sure I will fire you".........Jikin Nazbeer ɗin ne ya fara rawa ya shiga rantse rantse kan maganar daya faɗa gsky ce, Bai saurare shi ba yai picking call ɗin yana faɗin, "Hello My ninie...............