Chapter O5
****Namiji Ƙanin Ajali****
>Page 05
A haka muka wuni anan tayi wanka ta tafi gida..
Ai ko kamar yadda na zata Bature yana dawowa ya sauke min kwandon bala'i akan meyesa zata zo mishi gida,maganganu dai marasa daɗi,tun ina kau da kai har ya kaini wuya,a hassale na ce,
"Bature wallahi baka isa ba, baka isa ka rabani da ƙawayena ba, dan kai naga baka san zuru ba,naga idan nayi wasa ƴan uwana da dangina su kansu saika rabani dasu,me baiwar Allahn nan tayi maka ka tsane ta haka?, saboda ƙin jini kawai,ba laifin tsaye ba na zaune"
Tun daga wannan maganar sai da muka kai ruwa rana,dan har ƙara ta sai da ya kai wurin malam mijin inna lami,kuma dama haka yake abu kaɗan sai kai ƙara,nidai har rana me kamar ta yau ban taɓa kai ƙararsa ko sau ɗaya ba wai yabon kai ba kuma ina da dalilin yin hakan, shi ya sasanta mu sannan yace mishi tunda yanzu tayi aure kuma dama yace saboda bata da aure ne ya rabamu to magana ta ƙare,na lura ba haka yaso ba amma ba yadda ya iya, haka muka koma bayan na bashi abincin shi, tsabar bashi da kunya sai yake tambayata na ajiye mishi ɗumame?, ko kulashi banyi ba,kuma na daɗe sanin Bature yana ganin nayi baƙi zai fara maganar ɗumame, in ajiye mishi ɗumame, kamar yana bada cefanen da zai kai har da ɗumamen ne,na daɗe sanin bashi da kyauta, kuma yana baƙin ciki yaga kayi kyauta,da haka maganar ta mutu muka cigaba da ƙawancenmu kamar Dahh.......
Maganar Lubna ce ta katse min tunani na ,ashe wai tana ta magana bana jin ta, ajiyar zuciya na sauƙe sannan na kalle ta na ce,
"Me kika ce?"
Ta kalle ni duba na natsuwa sannan ta ce,
"Meye matsalar?,dan na tabbata da ganin ki, kina cikin damuwa"
"To meye ne sabo lubna?,matsalar dai da kika sani itace,yanzu haka munkai kwana biyar baya bamu abinci,idan ni ya hana ni to yaran fa ,duk da cewa nima hakkinsa ya ciyar dani"
Lubna ta kalle ni sannan tace
"Hmmm,Halima wallahi bansan meyasa maza basu da imani ba, wallahi halima gidan Abdullahin ma bata canza zani ba, yanzu haka da kike gani yaji nayi ko Maman Jummai (wato mahaifiyar ta) batasan me ya faru ba, shine nace bari inzo na fara faɗa miki, wallahi auren nan kashe shi zanyi in huta, ba dan ɗan sana'ar da nake yi ba, da na tabbata sai buzu na a garin da ba dangin uwa ba na uba"
Da mamaki nake kallonta, mamakin da nikaina bansan na meye ba, to wai dama haka mazan suke mugaye,suyi rawar ƙafa akanki a waje kamar zasu miki sujada,sai kin shiga zaki gane Allah ɗaya ne ,to ashe dai kallon kitse mukewa rogo , na tuna irin yadda Abdullahi ya dinga bin Lubna Allah Annabi ta bashi dama shi zai wanke mata duk wani ƙunci daya yake damunta da takaicin ɗa namiji da ta ƙunsa a baya, ashe sabon karatu zai ɗora mata daga inda Sale ya tsaya....
"Halima!!!! wai tunanin me kikeyi haka" ta faɗi da ƙarfi bayanta jijjigani, hakan da tayi ya katsemin tunanin nake.
Ajiyar zuciya na sauke a karon da bansan adadin sa ba''mamakine ke shirin sani suman zaune,wai dama shima Abdullahi haka yake,ko da yake yaci ace na daina mamakin halin maza zuwa yanzu idan nayi duba da kaina"na furta
"Hmmm,Wallahi Halima Kada kibari takaicin namiji yasa kikashe kanki da tunani,ki gode Allah ma Bature baya neman matan banza,amma Abdullahi yau bashi gun waccen bazawarar, gobe yana gun waccan sakin wawan,jibi yana gun waccan budurwar, kuma babban abin baƙin cikin shine alaƙar banzace a tsakaninsu , duk abinda ya samu to a matan banza zai ƙare inda kika san bunsuru"
Dariya ma ta bani,wai yanda kika san bunsuru,
"Auuuww dariya ma na baki,hmmm wallahi halima na gaji da auren nan ɗah ɗaya ne a tsakaninmu Allah ya raya shi, idan ya girma zai neme ni a duk inda nake"
"A'a fah lubna tarbiyyar ɗa ai sai sai uwarshi,ba wadda zata miki tarbiyyar ɗan ki kamar ke, kuma ko an miki baza a miki yadda kike so ba,kuma gidan auren shine mutuncinki, mutane zaginki zasu dingayi, nima wallahi zaman su layla nakeyi a gidannan musamman idan nayi duba da cewar ƴaƴa mata ne ga kuma iyayena baza suji daɗi ba waɗannan dalilan su suke zaune dani a gidannan,idan ma nayi wani yunƙuri su umma ba bari na zasu yi ba, tunda kinga anyi na farko amma haka aka tirsasa ni komawa,da kuma maimaita min kalmar nan ta haƙuri,to tunda nasan haƙurin za a bani me yasa zanyi yunƙuri dan a bani haƙuri kawai, tunda nasan ba canzawa zai yi ba,su kuma ba fasa bani haƙuri zasu yi ba,shi yasa har yau ban taɓa kai ƙarar sa ba ko sau ɗaya sai dai shi ya kai,kalmar kuma ita ɗin ce dai ba canji"
"Hmmmm Halima kenan lallai da sauranki,wai ke dan kar mutane su zageki zaki zauna kiyi ta ƙunsar baƙin ciki, to lallai kina da aiki ja,jazur ma kuwa,ban ƙi dalilin su umma ba amma ni saboda ɗa bazan kashe rayuwata ba,balle ma shi Bature ba dangi yake dashi anan ba, ai dole ya barki dasu,su mutanen da kike gudun maganar tasu,a sanda ciwon zuciya zai kamaki waɗanda kike tunanin zasu zageki, ba mai baki gudunmawar ko daidai da ruwan da zaki haɗiye magani ne, kuma kisa a ranki indai mutane ne,ko kin zauna cewa zasuyi kin zauna kina shan wuya sai kace dole ne sai kin zauna da shi, indai mutane ne wallahi wallahi ba abinda zakiyi ki tserewa maganarsu,ki dai tsaya akan dalilinki na farko ƴaƴanki ƴaƴa mata ne kawai, kuma da kike batu iyaye babu iyayen da zasu aurar da ƴarsu suce suna so ta dawo sai dole,yanzu da zan lissafa bashin da ake bina a cikin sana'ar da nakeyi a can sai kin gigice , to halima so kike in zauna har sai ƙuda sun nuna kan ɗakina?, ko kuma sai an kaɗa min gangar bashi a garin mutane gsky bazaiyu ba, Abba da na barshi gashi yana zaune ba abinda ya sameshi shima Allah ya raya shi da imani zai nemeni idan ya girma, kuma zan dinga mai addu'a a duk inda nake, dan nasan Abdullahi bazai bani shi ba".
"Amma ai Abba yana da banbanci da Walid, Abba fa anan yake ga ƴan'uwa ga dangi ta ko ina kuma zaman da yakeyi a gurin maman Jummai yafi wanda yakeyi a gidan mahaifinsa,ina tabbatar miki gaba kaɗan nasan zai dawo gidan Maman Jummai gaba ɗaya, amma Walid fa ba kowa sai shi kaɗai, baki da dangi a can"
"Akwai dangin mahaifinsa da shi kanshi mahaifinsa nasa" ta katseni.
Hmmm kawai nace daga nan muka cigaba da tattauna matsalolinmu, haka muka bawa juna shawarar da ya dace,nidai da cigaba da haƙuri na bata, kuma muriƙa addu'a har Allah ya kawo mana mafita mafi Alkhairi, amma nace mata ta sake tunani akan barin auren da take shirin yi kada mutane su canfe akan duk inda taje sai tayi ɗa sannan tashi,koma ace taƙi zaman aure ,sannan na bata shawara akan yajin da da tace tayi dan hakan ba shine mafita ba, kar ma ta gaya kowa, dan nidai nace taje ta cigaba da haƙuri duk abinda Allah yayi mai kyau ne....
"Naji amma ki rabani da zancen mutane zasu ce ɗinnan danni basu bane a gaba na,dan a cikin masu cewar ba wanda yake zuwa muke raba wahalar da nake sha tare,sai gatan cewar kawai za'a dame Ni dashi".
Nayi dariya kawai, Haka muka wuni muyi hirar dariya muyi na takaici,har bayan magariba kafin ta tafi ta ajiye min dubu biyu nayi-nayi da ita ta ɗauki kuɗinta amma fir taƙi,tace kafin ta tafi zata dawo nima nace mata zanzo, muna tsaye sai ga Bature akan mashin ɗinshi ya tsaya suka gaisa,nan yace ta hau rage mata hanya,dama kuma idan yaso akwai wannan kirkin,amma idan shi yayi ra'ayi, amma wai dan kice Bature ɗan sauke awuri kaza sai yace yanzu ya dawo daga wurin gyara yana gwadawa ne yaga ko ta gyaru, saida suka ɓace min kafin na koma ciki......