Kuncin zuci
by @bintuuu
Mazzy na dauka rai abace Ahmad yace "Which one of your boys are in Lagos right now?" Mazzy ya amsa da "Smoke is there...you want something?" Ahmad ya miqe tsaye a falon cikin tashin murya ya fara magana "Someone mess with my woman and tagged me, I burn the account but still i want every single sharing post to go down this night, each one of it, i don't care how long it's gonna take, i don't even care how much you want, just put down every single account, and for the comments...DELETE every single word" da sauri Mazzy ya amsa da "And it's all going down right now Ahmad" sai Ahmad ya sake cewa "I'll send you the codes now" da haka ya kashe wayan yayi typing message, bayan ya gama sai ya sake daukan laptop din nasa ya zauna a kujera yacigaba da duban notifications nasa na Instagram ganin yada mutane ke ta dragging sunansa yanzu da babu post din, Adam ne ya sauqo falon da sauri wayansa a hannun yace "Ahmad what's going on, your name is going wild on insta right now" dan zuwa sannan Ahmad ya riga da ya goge post din sai dai maganganun mutane kuma dan ba sanin Na'ima akayi ba saboda ko account bata dashi a Instagram sai dai nashi da shima sama sama yake hawa saboda ayyukansa, har sannan ran Ahmad sai quna yake ganin irin hotunan da aka dora na Na'iman sai ya kasa amsawa Adam din ma yana kallonsa kawai, rai abace Adam yace "Ahmad ka amsa min" sai shima ya daga murya yace "Taya zan sani eh, how dah heck am i suppose to know? wani mahaukaci ya doramin Na'ima a internet with just Bra kuma kake tambayata me nasani akai...to hell with you too Adam" ya qarasa maganan tareda miqewa fuskansa tayi jaa, da sauri Adam ya dafa kafadansa yace "Be cool man, be cool...ni banga hotunan bama dan babu su, kawai wild comments dinne suka firgitani, we are going to find whoever is behind this, and we'll surely f*ck him up too" shi Ahmad ayanda yakejin zuciyarsa ma maganan nauyi take masa sai kawai ya dauki laptop dinsa ya nufi stairs, sai da ya koma dakinsa dake kusa da na Adam sannan ya sake kiran line din Nafisa, tana dauka tace "Thank you Yaya, the pictures are gone" sai yace "Karki bari ta sani Nafisa, banason ta sani" tace "In sha Allah Yaya, ai ka fadamin dazu ma" sai lokacin ya sake tunawa ashe ya kira Nafisan ma sai kawai ya kashe wayan, Nafisa na tsaye a dakinta taji wayan ya yanke sai tayi saurin fita ta nufi downstairs zataje part din su Faruk, aikuwa a bakin kofa suka kusa cin karo tayi baya sai Faruk yace "Hope baki fada mata ba, bata sani ba dai ko" Nafisa ta gyada kai da sauri tana fadin "Bata sani ba Yaya" da haka suka fita compound din tare, a kofar falon dake side din nasu ta hango su Abu da Al'ameen a tsaye suma , sai suka qarasa cikin falon tare, suna shiga Faruk yace "No one has to know about this kuna jina, the pictures are down, banason ko da wasa su Mami su sani, I'll handle everything" Nafisa ta gyada kai cikin sanyin jiki while Abu yace "Toh" rai abace Al'ameen yace "Wai who is this Bastard?" Faruk ya kallesa "Manners.. Al'ameen" ahankali yace "Sorry Yaya" sai kuma ya sake daga murya "But why her? Why do some people find joy in hurting her, she hasn't done anything bad" Abu ya qara da "She's innocent" sai Faruk ya sauqe numfashi tareda zama a kujera yace "Jarabawa ce, kuna mantawa Allah yana jarabtan bayinsa yanda yaso even if you're innocent, Na'ima might be strong on the outside regarding what happened to her in the past, but this could break the last piece of happiness she has found in her heart, so you guys shud zip ur mouth, banason ku fada musu komai, I'll tell them myself when the smoke has quite down..kuna jina?" Sai duk suka amsa da "Yes Yaya" Nafisa ta zauna a kujeran tana jin ranta na baci, Al'ameen yace "I went to hack it, amma mayen yayi encrypting account din strongly, i wonder ko Yaya Ahmad ne ya datse account din" sai Nafisa ta amsa ahankali "Shine" duk suka kalleta Abu yace "Ya sani?" ta gyada kai tace "Baku gani bane, he was tagged in it" Al'ameen yace "Nagani..That's why you don't mess with a computer freak, he'll definitely track it" Faruk yace "Zan samesa a gida gobe, kuje ku kwanta haka nan" da haka duk suka amsa tareda miqewa kowa ya koma makwancinsa, da Nafisa ta koma side dinsu sai ta wuce nata dakin ta zauna a kan gado, can aka bude dakin nata Na'ima ta shigo, cikin sanyin murya tace "Kin fasa kwana a gurin nawa ne Nafee" Nafisa na kallonta cike da tausayawa tace "A'a daukan abu nazo yi fa" sai Na'iman ta dan tsaya kallonta ganin taqi kallon idonta, dago kai Nafisan tayi itama sai ta mata murmushi tace "Meye kike kallona haka" Na'ima ta girgiza kai sannan ta juyo zata koma nata dakin, da ta hau gadon ta sai ta jawo wayanta tanason kiran Ahmad amma tuna cewan yace zai kirata sai ta maida wayan ma'ajiyansa tana gyara duvet din ta..Ranan Ahmad raba dare yayi yana zaune akan gadonsa sai goge goge yake su Mazzy na tayasa daga dayan bangaren suma, Adam sai leqosa yakeyi jefi jefi azuwansa na qarshe ne ya taho ta plate dauke da berries da bottle of yogurt, da ya miqo masa sai Ahmad din ya karba tareda muttering thanks kawai ya qara maida hankalinsa kan laptop din, nan Adam din ya zauna bakin gadon yana taya sa duban sauran posts din a wayansa yana fada masa shikuma yana bi yana gogewa, bashi ya nutsu ba sai kusan uku na dare, zuwa sannan Adam ya tafi nasa dakin sai ya tashi yayo alwala yayi sallah, bayan ya idar sai ya zauna kan sallayan yana azkhar, sai da ya idar da komai sannan ya jawo wayarsa dake gefensa yana qara duban lokaci, his heart is going to her at that moment, yana matuqar son jin muryanta ko zai samu sassaucin abunda yakeji har sannan, har ya danna kira kafin ya tafi sai ya kashe aikuwa sai ga kiranta nan take ashe kiran ya shiga kafin ya katse, dagawa yayi ahankali yayi mata sallama sai yaji muryanta babu alamun bacci sa'in da ta amsa, ya sake cewa "Na'eemah" daga dayan bangaren tana zaune akan gado itama bata dade da idar da sallah ba, cikin sanyin murya tace "Kaima ka farka ne" sai yace "Idona biyu Babe, i thought kinyi bacci shiyasa ban kiraba" tace "Farkawa nayi" sai yace "Kinyi sallah" tace "Uhm" ya sake kwantar da murya "Kin mana addu'a?" nan ma ta amsa da "Uhm, kaifa?" yana murmushi yace "Nayi mana Addu'a Na'eemah, nayi addu'an Allah ya mallakamin ke, nayi addu'an Allah ya bamu tsahon rai with full of blessings tare" sai tayi murmushi ahankali tace "Acikin addu'an nan nasamu qarin guda daya da banayi, zan fara sakawa dashi" sai Ahmad yayi qasa da murya yace "Na Allah ya mallaka miki ni?" cike da kunya ta fara dan dariya tace "Ni yaushe nace haka" shima yana dan dariyan yace "Ni inaga ma kin mallake nin ma" tana dariya tace "Uhm uhm nidai" sai sukayi shiru dukansu, can yace "Ki kwanta kar kanki yayi ciwo" sai tace "Kaima ka kwanta" ya amsa da Okay sannan sukayi sallama...Da asuba bayan Ahmad ya dawo daga sallah sai ga kiran Fatima qanwarsa, bayan ya dauka sun gaisa sai tayi shiru ta rasa ta Ina zata fara maganan ma, shiru yayi yana sauraronta sai can tace "Yaya are you alright?" ya amsa da "I'm fine, ya su hamra da megidan naki" tace "Lafiya kalau, Alhamdulillah" sai yace "ki gaishe dasu" tace "In Sha Allah" da haka sukayi sallama" bai kaiga tafiya dakinsa ba Husna ta shigo falon itama, anutse ta qaraso ta zauna dan nesa dashi tace "Ina kwana Yaya" da ya amsa mata da lafiya sai itama ta rasa me zata fada masa sanin ba shaquwar yawan magana bace a tsakaninsu, Dan Ahmad bai da mu'alama ta yawan hira a cikin gidan nasu kowa yasan haka, mutum ne da in kaga yana doguwar magana to da iyayen sa ne ko batun aikinsa, zama sukayi na dan wani lokaci Husna batace komai sai yace "Da wani abune Husna, akwai abunda kikeson fada min ne?" kamar zatayi kuka tace "Yaya dan Allah in ka kama wanda yayi abunnan ka hallakashi tukunna" sai yayi murmushi yace "Baki fadawa Momma ba dai ko" ta gyada kai tana fadin "They didn't know about it, har Baba da Anty" sai yace "Then keep it that way" kiran Faruk ne ya shigo wayan sa sai ya miqe yana fadin "Bari zamuyi magana zuwa anjima kinji" Husna ta amsa da toh sannan itama ta miqe ta nufi kofa while Ahmad ya nufi upstairs tareda daukan kiran...
Da Ahmad yaje office ba iya gane komai ya rinqa yi sosai ba saboda yanayinsa, haka ya zauna a meeting room absent-minded yana scrolling ipad dinsa bawai dan yana sauraron bayanin da head of HSE keyi a room din ba, da ya gama bayani sai ya nemi jin comment din Ahmad daya kasance head dinsu gaba daya, dan dago kai Ahmad yayi yana kallon projector screen din sai ya gyada kai kawai tareda fadin "Good work, let's end the meeting here everyone" sai duk mutan room din suka amsa da "Yes sir" wasu kuma "Thank you sir" suka hau rufe laptop dinsu suna shirin miqewa, Adam sai kallon Ahmad din yake wanda PA dinsa ya hau tattare masa takardun gabansa shikuma ya miqe hannunsa riqe da iphad ya fara fita daga meeting room din, Ahmad na zaune a office din yana duba mails dinda suke needing response dinsa sai ga kiran Mazzy ya shigo wayansa, nan take ya dauka yakai kunne sai Mazzy yace "Smoke tip me up..it's Saddam, that Bastard didn't learned his lesson yet" shiru Ahmad yayi yana jin ransa na harzuqa, so Saddam did this...anutse yace da Mazzy "Give me Smoke to work with" sai Mazzy yadanyi shiru saboda baya iya bada smoke a kowa kuma baya ganuwa, babu wanda yakeyin waya dashi sai dai text, yaronsa ne mai masa aiki a boye ta qarqashin qasa, but yanda Ahmad yake a gurinsa yasan bazai iya hanasa hulda da Smoke ba, sai ya sauqe numfashi yace "Ahmad i'm only giving you his details because it's you, kasan hakan ba" Ahmad ya gyada kai yace "And i appreciate that Man" sai Mazzy yace "Ni zan maka godiya for all you've done for me Boss, I'mma send you all his digits right now, you just have to keep trying each one of it to find him" Ahmad yace "Thank you" da haka ya kashe wayan atake ya danna kira a line din Saddam, sai da ta kusa katsewa sannan aka daga, daga daya bangaren anutse matashin dake ji da kansa yace "Took you long enough to call" shima Ahmad a nutsen yace "Bansan kana da tsaurin ido haka ba Saddam" sai Saddam yayi murmushi yace "So you're into girls like that, glad i know" ran Ahmad ne yaji ta fara baci sai ya danne yace "You drag my girl into this?" Saddam yace "It's all fair when it comes to win win situation Ahmad, kuma yanzu na fara" sai Ahmad ya miqe daga kan seat dinsa yana kallon glass wall din office din nasa har sannan bece komai ba, Saddam ya cigaba "Kazata zaka tabani ka zauna lafiya ne? Mark my words Ahmad, asannu zan kaika qasa kana gani" sai sannan Ahmad yayi murmushi ahankali yace "We'll see then, we'll see who's going down" da haka ya kashe wayan, ta bangaren Saddam ji yayi ransa ya baci bayan kiran ya katse, yazata zaiji Ahmad din ya hayayyaqo masa kamar yanda yake burin ji sai kuma baiji hakan ba, wato har yanzu shidai bega mutum irin Ahmad ba, at that moment sai ya rasa me zeyi ma sai kawai ya sake daukan wayan ya danna kira....Laila na zaune tareda Mummynta a falon suna magana, itadai sauraron Mummyn nata kawai take amma abunda ke cin zuciyarta yafi qarfin fadi, kira ne ya shigo wayan nata adan gigice ta miqe sai kuma ta waske ganin irin kallon da mummyn ke bin ta dashi, tace "Mummy zan dauko abu a daki" Mummy tace "Dama tambayata kike in zaki dauko abu?" sai ta dan turo baki tace "Mummy dai, ai naga muna hira ne" da haka ta nufi stairs da dan saurinta ta shige dakinta, zuwa sannan kiran ya katse sai wani ya sake shigowa ta daga, daga daya bangaren Saddam yace "You're right, he finds out" adan firgice Laila tace "Sai da na fada maka ai, he's into coding.. kana gani jiya ko minti ashirin bai bari pictures din sunyi a media ba, Saddam ka bar Lagos ayau dan wallahi sai ya nemoka" Saddam yace "Babu inda zanje until i see him fall" da sauri tace "Ba haka mukayi dakai ba Saddam, you're dragging him too much, comments din zasuyi tarnishing dinsa" yace "Laila kar muje nan, it's a win win situation tsakaninmu, you want his girl gone and i want him dragged in the mud, why are you complaining?" Laila ta girgiza kai tace "Not like this gaskiya, ni tsoro nakeji yanzu, nasan after this baza'a bari ya auretan ba amma kasan inyayi dogon bincike zai ganoni, Saddam banason yaqi aurena akan wannan" rai abace Saddam yace "Laila karki sa in fada masa abunda ke tsakanina dake" da sauri tace "Kar muyi haka dakai" yace "Then stop telling me all this, ai ba shi kadai yasan yadda ake bala'i ba, wallahi sai nayi dragging dinsa har qarshensa" kamar Laila zatayi kuka tace "But I love him" a harzuqe yace "F*ck you Laila, kizo Lagos yau ko gobe, and you'll repeat those words on my bed, you hear me?" ahankali tace "Naji" da haka ya kashe wayan, tsayawa tayi ta rasa ma me zatayi a wannan lokacin sai ta fara duban numbern Luba kawai ta Jiyo muryan Mummy a bayanta rai abace tana fadin "Laila yaushe zakiyi hankali ne, ke bazaki taba hankali ba kenan arayuwanki, ban hanaki yin abubuwa gaban kanki ba" cike da tsiwa Laila ta juyo tace "Toh Mummy ya kukeso inyi ne, ya zanyi Dan Allah?, kina gani fa ko me zamu barbada masa yaci baya masa komai, duk abunda zan shafa dan ya shaqan baya amfani" ta fashe da kuka ta cigaba "Na rantse ko Ahmad zai ajiyeni a matsayin hoto a gidansa sai ya aureni, Mummy ni bana buqatar soyayyarsa ma ni kawai ya aurenin nakeso ko in kashe kaina wallahi" afirgice Mummy ta iso gareta batayi wata wata ba ta dauketa da mari tana huce tace "Bakida hankali ne Laila, hauka kika fara akan namiji, anya sonsa kikeyi kuwa" Laila na kuka sosai dafe da kuncin ta batace komai ba sai jikin Mummy yayi sanyi ta rungumota, cikin kwantar da murya tace "Kiyi shiru Auta, zaki aure san, ai ba lallai sai shi kadai abun ze ci ba, ba lallai sai shi kadai zamu qulle ba, sai mu chanja sheqa tunda taqi cinsa shidin" Laila ta gyada kai tana sake kwantawa a jikin mahaifiyartata har sannan bata bar kuka ba....