HAWAYEN MARAICI

7

by @asmybaliyu

HAWAYEN MARAICI 7

By Asmy b ALIYU

Masu  aikine ke  kai da kawo haka  yayi mamakin da bai samu mum a falo ba daya daga cikin aikin masu aikin gidan ya tambaya.

Salame,

Na'am Alhaji, ta russuna ta kwashi gaisuwa matar da ya kira da salame shekarun ta xasu ba hamsin baya,

Da sauri AY.yace ta mike tsaye Mum fa?

Tana bedroom bata jin dadi ne,

nan take Ay.ya rude bata idar da fada masa ba ya nufi bedroom din nata da sassarfa jawaheer na a bayansa bakin ciki kamar zai fasa mata zuciya, ta shiga ukku haka Abdulkeem ke baiwa ya'n gidan nasu kulawa harda mum,wacce tasan mum makirar Macce ce,ita bata son kowa da kowa Yana rabarsu har mum din kuwa da tayi sanadin aurensu,

Dole ma ta kira maminta a waya,

da sauri Ay ,ya karasa gurin mum

Ta rufe jikinta da blanket da sauri ya karasa gaban gadon Yana Kiran sunanta

Mum!!"

Dakyar mum ta daga ido ta kallesa sabida tsananin zazzabin dake damunta.

Murya can ciki take fadin baka fita bane??"

Batare da ya bata amsa ba yake fadin mum meya sameki ?

Meyasa ba asanar dani ba ya fada fuskarsa cike da tausayin ta  ,murmushin karfin hali tayi gamida damke hannunsa karka damu dear zazzabi ne kawai,

Waye yaxo ya duba ki?" Dr.yaqub ne anan ya Ciro wayar sa yana Neman layin Dr.yakuq yayi sa'a kuma ya samesa fita waje yayi yana waya akan meke damun mum dinsa.

Anan yake masa bayani  ciwon sugan tane keson tashi amma idan ta kiyaye hakan baxai sake faruwa ba!

Ajiar zuciya ya sauke gami da huro iska mai xafi a bakin sa.

Mum ya jikin ?

Jawaheer tayi magana cikin kulawa da kissa, da murmushi mum ke fadin ai tasamu sauqi da haka jawaheer taja gefe ta xauna tana chart da wayarta.

Daidai kuma lokacin Ay ya shigo a dakin ya karaso wurin mum ,kallonsa mum tayi me Dr.ya fada maka??

Lumshe idonsa yyi a hankali kafin ya bude su akan mum ,mum meyasa kike yawan cin duk abunda baya baki lafia ga  ??" Na daina My son abincin ne namu bayamin dadi ne wata rana."

Olryt."

Ya kalli drip din da aka saka Mata wanda ko rabi baiyi ba mum break fast fa."

Murmushi tayi karka damu my son yanxun nan salame xata shigo dashi..."Kuma naci abinci kafin a sakamun drip,

Dai-dai nan salamen ta turo kofa ta russuna ta aje katon faranti ta kalli mum Hajia bara na taimaka maki kici Abincin...

Ay yayi saurin daga mata hannu no haka ma yayi mun gode."

Jawaheer

kallonsa  tayi

xoki taimakawa mum taci abinci mana." A zuciya jawaheer ta kallesa ranta idan yyi dubu to ya baci.

Ga ya'n aiki in banda rainin hankalin Abdulhakeem  Sai  itace xata ciyar da mum ." karo na biyu ya sake yin maganar,

Naji ta fada da wani yanayi a muryarta

Haka ta cigaba da kallon wayar hannunta,

Baki da hankali ne wai?

Yayi maganar cikin tsawa ,mum ta sassauta murya yimata a hankali  son  mum kinsan bana iya jure wannan abun tun farko keki ka kawo yarinyar nan yanxu gaya nan tun kafin aje koina ta fara rainaki.

A zuciya jawaheer,ta mike tsaye wani irin bakin ciki ya ziyarci zuciyar ta ,haka hawaye suka dinga sauka akan fuskar ta   idan Akwai abunda jawaheer tafi tsana a dunia shine ayi Mata fada ji yadda Abdulhakeem keyi mata fada agaban wannan tsohuwar matar a xuciya tabar dakin da gudu tana goge hawayen idonta.

Jikin mum qlau yayi sanyi ta maida hankalinta kan Ay.wanda yabi bayan jawaheer da wani irin kallo gami da yin dan karamin tsaki...

Abdulhakeem!!!

da Rinannun idonsa ya dago yana kallon ta bacin rai ne tsantsa acikin su ka dinga hakuri da jawaheer ,dan Allah har yanxu yarinya ce ,baice komai ba ya bar dakin baijima ba sai gaya tareda salame..

Anan yayi mata umurnin ta ta taimakawa mum taci Abinci ya kalli mum ,ni xan wuce office pls idan da matsala ki kirani mum ya fada yana kallon ta .

Murmushi tayi masa tana yimasa Allah ya tsare hanya ya karesa a duk in da zai shiga,daga haka ya fice daga dakin ....

A office ma kasa zama yayi Sai waya kan waya yake yi akan ya jikin mum  yana cikin wannan yanayin kiran Mimi  ya shigo a wayarsa  A sanyaye ya daga wayar ..

Cikin sanyi murya yake fadin ..

"Angel!

Yayana baka nema na ko??

Takarasa maganar a shagwaban da  alamar ma bakayi missing dina ba ni kawai ke kewarka.

Nop!

Angel waye ya fada maki?"

Nayi kewar ki sosai Anan suka cigaba da hirar su..

Bayan dawowar sa office gaba daya wurin mum dinsa ya tare shike jinya duk da ta samu sauqi haka ma hajja taxo ta dubata , jawaheer kuma tun safe bata kara leko mum ba.

Sai kusan karfe goma Ay.ya dawo bangarensa   koda ya dawo bai nemi jawaheer ba dan har lokacin fushi yake yi daita...jin yayi xuwa wannan lokacin tamkar ya fasa tafiya daita.

,kwanciyar sa yayi batare da ya nemeta ba

Itama  bangaren jawaheer fushi ta hauyi dashi....duk da maminta ta bata hakuri ta fadamata kalamai masu dadi ,akan Sai ta rikayi tana danne komai ba lokaci daya Zata rika fito masa da halinta ba,

A wannan daren rufe kanta tayi a daki

Ta Bude bag dinta ta fiddo da expensive kayan mayenta tasha duk kalar da takeso bata Kara tuna wani Abdulhakeem mai keke ba da bacin ran da ya haddasa mata.

Washe gari

Karfe 8  na safe ya tura kofar dakin nata

dakyar ta samu ta tashi daga bacci tun jiya Sai da ta tashi ma taga miss calls din maminta ,dakyar ta daga yanayin muryarta Mami kawai taji hankalinta ya tashi

Ta tabbatar da Tasha wani abu,gashi jawaheer din ta gayamata zasuyi tafia a yau, jawaheer bakida hankali meyasa Zaki sha ??"mum bazaki gane bacin ran da naji a jiya ba ,nidai naji ki Sha abunda zai saukar dake yanzu daga wannan saman iska kin manta tafia zakuyi.sai lokacin ta tuna,dakyar ta samu ta shiga toilet tayi wanka.

tsaye take ajikin mirror dressing tana shirya kanta karar bude kofar da taji shi ya dawo da hankalinta jikin kofar ido biyu sukayi dashi yana cikin manyan kaya na captani ruwan kasa haka ya kafa hula kalan kayan ,ba karamin kyau yayi ba.zuciyarta taji ta wani irin nutse da sabon sonsa.

Saurin dauke kanta tayi akansa batareda ta kara kallon inda yake ba." Ki shirya da wuri jirgin  karfe 9 Xamu bi bai jira mai xata fada ba yyi ficewaer sa xuwa bangaren hajja,

Sallama yayi a babban falon karar T.V. yaji babu kowa a falon sai tashar sunan t.v. dake aiki kai tsaye bedroom dinta ya nufa nan ma bata nan mamaki ya cikasa to ina ta shiga ne??

Karar bude kofa yaji da sauri ya maida hankalinsa jikin kofa hajja ce murmushi tama sa harka shirya kenan?"

Ajiyar zuciya ya sauke

Daga ina haka hajja " ina kitchen muna ta kokarin hada Karin kumallo nida laraba.

Meya faru kuma?

Ya shagwabe fuska to ba keki ka tsorata ni ba,

Gyara xaman gilashin idonta tayi wanda ke karawa idon nata lafia oya muje kayi break fast nasan shiya kawo ka ban San yaushe wannan matar taka xata canja ba anan kuma hajja,ta shiga banbamin fada shidai Yana  biye daita batareda ya tankata ba.

Allah ya kawo maka wata matar kirkin wadda xata cikamin gida da ya'yanka."

murmushi mai kyau yayi amin my sweetheart mekika ta nadarmin ne?"

Yayi maganar gamida xaunawa akan kujerar dinning table ,koko ne da kosai

Ya tsine fuska yayi kai gaskiya ni baxan ci ba ya fada gamida harde hannayensa akan kirjinsa ya wani bata rai,

Oh Allah?"daga abun arziki,

Kuma da kake xuciya akan baxaka Ciba Yau shi nake sha'awar ci ga ruwan zafi kasha bakin tea sai ka hada da wainar kwai.

Suna breakfast yana mita hajja dai sai shan kokon take tana hadawa da kosai..

Yana gamaea yayiwa hajja

sallama akan idan sun isa xai kirata anan ta masa fatar Allah ya kiyaye ,hakama mum yau babu laifi taji sauqi tare suka shiga da jawaheer ta hade cikin wata Turkish abaya kalar maroon sai mayafin rigar da tayi rolling kanta dashi , yololon mayafi da ta aza wanda dashi da bbu duka daya."

Sai wasu uban hill dake a kafarta kalar handbag din hannunta bbu laifi tayi kyau ,nan tayiwa mum ya jiki anan Ay.ya kara fadawa ya'n aiki akan su kula da mum.

Idan akwai matsala su nemesa da haka yayiwa mum sallama drivernsa ya jasu xuwa airport da sauran tawagar masu tsaron lafiyarsa watau security.

A mota sai kiran sageer yake baya shiga ,har lokacin da jirginsu ya daga xuwa kano.

####

Sosai Aunty salma tayi farin ciki ganinsu sai nan nan take dasu itakam Jawaheer duk a takure take ,Suna xaune gabadaya a Falon aunty salma wanda baifi awa daya ba jirgin su Mimi ya sauka.

Wai aunty ina Nana ne?

Murmushi Aunty salma tayi ,tadan harare sa a wasance sai yanxu kasan daita sorry aunty na sha'afa ne aikin San ya'r gidana ce."

Tana gidan kanwar Abban su kwanan ta biyu yau acan, saleem kuma yana Abuja Kasan mahaifin nasu da tsastauran ra'ayi akan boko mussaman A boarding school

Haka yana da kyau Aunty uncle jafar yayi tunani mai kyau.

Uffan dai jawaheer bata cemasu ba sai hirar su sukeyi a tsakanin su ana saura minti talatin jirgin su ya sauka gabadaya suka nufi airport.

A wannan lokacin AY sai duba agogon hannunsa yake ,ya kagara yaga ya'r tilon kanwar tasa rabonsa daita shekara daya kenan har karfe biyu dai dai na rana ya buge babu alamar saukar jirginsu abun da ya saka AY.cikin matsanaciyar damuwa da wasi-wasi kenan biyu da mintuna goma sha biyar jirgin su ya sauka.

Murna kamar meye a wajen AY Gabadaya ya rasa natsuwar sa burinsa kawai yayi tozali da ya'r kanwarsa .jawaheer na lura dashi sai dai ta kallesa ta tabe baki gamida dauke kai.

Matashiyar budurwar ce ke saukowa daga matattakalar jirgin Atamfar ce ajikinta kalar xubin brown da ratsin light pink ajikin ta dinki doguwar rigar fitted dinkin zamani,tayi kyau acikin kayan,

Medical glass ne A idonta haka din kyakkyawa ce ajin farko tana da manyan idanu masu daukar hankali kallo daya xakayi mata kaga tsantsar kamar da sukeyi da AY. Ta koina kanwartasa shi ta debo.

Sae dan karamin veil brown wanda ta sakalo sa tun daga bisa kai ta sakalo sa a wuyan ta babbar trolley ce take jaye daita....

Matashiyar budurwa mai kimanin shekara goma sha takwas a dunia.

Tafia kawai ta rasa inda xata hango ya'n gidansu nan take yanayin fuskarta ya sauya tamkar tayi kuka wato ma Yaa Abdul din baixo ba, Babu hajja, bbu mum babu Aunty's dinta.

Tunanin ta ya katse dai dai lokacin da taji saukar hannunsa akan Fuskarta. Haka taji kamshin jikinsa wanda tasan wannan tabbas yayan tane.

Ihun murna tayi ya janye hannunsa akan fuskar ta tayi arfa dashi ihu  tasa fasa A karo na biyu,   tayi hugging dinsa sosai tamkar xata koma ajikinsa.

Wayyoni yayana!!"

"Ashe zaka xo??

Murmushi dauke A fuskarta ta subbaci goshinsa ,tareda fadin "I miss you yayana!

Murmushi ya sakar mata ,tareda fadin I love you my Angel muryar Aunty salma taji a bayansu Sai lokacin ta kula daita tsabar murnar ganin yayanki kin manta dani cikin sangarta take fadin sorry my Aunt nan tayi hugging dinta tana murna ,Anan ta maida hankalinta kan  jawaheer,wadda bata Santa ba gabaaya dan babu wanda ya fada mata Yayan nata yayi aure.

Karasowa tayi gurinta murmushi dauke a fuskarta ,dan Mimi harga Allah ta dauka jawaheer ya'r uwar mijin Aunty salma ce hannunta ta bata nadama a ya'ngace jawaheer ta mike mata hannunta sukayi shaking hands.

Lailah Yusuf mai keke!!"

Nyc name"

Thank you .

Cewar Mimi still bata saki hannun jawaheer ba .haka tana jiran taji sunan ta .

Jawaheer tagano nufinta  murmushi tayi mata"Jawaheer Abdulhakeem mai keke !

Nyc 2 meet you ,cikin rashin fahimta Mimi ta saki hannunta da sauri kallon yayan nata tayi lokaci daya cike da mamaki..

#HAWAYEN MARAICI

#AY MAI KEKE

#JAWAHEER TARIQ

#LAILA MAI KEKE

#LOVE/ROMAMCE

#ASMY B ALIYU

#***