MADUBI

Chapter 2: BABBAN GIDA

by @salmaahmadisah

*MADUBI...🪞 * ©Salma Ahmad isah PERSONA. Page | 2 •°{THE WHITE HOUSE: BABBAN GIDA!}°• A safiyar ranar juma'a, jama'ar garin Kano suka tashi da labarin rasuwar Alhaji Baba Musa. Babban ɗan kwangila, ɗan kasuwa sannan kuma Malamin da jama'a da dama suka sani, domin karamci, tausayi, kyatatawa da kuma adalici irin nasa. Alhaji Baba Musa shi ne asalin ginshiƙin kafuwar White House, wato Farin Gida, kamar yanda jama'a da dama ke indicating gidansa da yake rayuwa shi da iyalansa. Babban gida ne wanda ya samu ƙwararren gini a wurin masana abin, duk wani abu da ya kamata ace yana da kala a ginin gidan to ka tabbata fari ne, hakan tasa gidan nasa yake ɗaukar hankalin mutane a gaba ɗaya unguwar Rijiyar Zaki. Alhaji Baba ya rasu ya bar mata ɗaya, wadda ta kasance matarsa ta lalle, Hajiya Balaraba, a tsawon shekarun aurensu da ita, sun haifi yara biyar, mata uku maza biyu. Babban ɗansa shi ne Hashim Baba, wanda shi ne ya riƙe ragamar kasuwancin mahaifin nasa tun daga lokacin da ya fara jinya har zuwa lokacin da rai ya yi halinsa. Sai kuma Hannatu 'yarsa ta biyu, wadda Allah ya mata rasuwa shekaru da dama da suka wuce, ta rasu bayan ta yi aurenta na farko da mijinta wanda suka haifi ɗa ɗaya da shi wato Tahir. Hauwa ita ce 'yarsa ta uku wadda aka yi aurenta tare da Hannatu, ita ma tana da yara biyu, Khabir da Hassana. A ƙalla an kwashe shekaru sama da goma kenan, tana kwance tana jinya cikin halin da ba ta da maraba da mutuwa. Sai kuma Amina wadda take aure a garin Kaduna, Abubakar shi ne autansu, wanda yake zaune a garin Lagos tare da matarsa. Hashim da iyalansa na rayuwa tare da iyayensa a cikin Farin gida. A halin yanzu matansa huɗu, Hajiya Bilki ita ce uwar gida, yaranta bakwai a gidan Sadiya, Zainab, Maryam, Rabi, Mubarak, Jabeer da auta Halima. Sai kuma Hajiya Hamida wadda take da yara biyu a gidan Fa'ik da Nusaiba, Hajiya Badi'a ita ce matarsa ta uku wadda take da yaro ɗaya Idris, Aysha ita ce amarya sannan ita ce har yau Allah bai bata haihuwa ba. Wannan su ne iyalan Farin gida, wani babban gida mai ciki da abubuwa da dama. ----------------- ELEGANT BOUTIQUE. A hankali waƙar Boy With Luv ta BTS ke tashi a cikin kyakkyawan boutique ɗin, da yake maƙare da kaya, an jerasu cikin tsari mai ban sha'awa kamar a waje. Daga can jikin wani dogon mirror wata farar kyakkyawar matashiya ce tsaye tana ɗaukar hotunanta ta cikin mirrorn, yayin da take ta murmushi abinta, ba wai dalilin ɗaukar hoton ba, sai dan yanayin farin cikin da take ciki, musamman idan ta tuna cewa yanzu haka saura sati guda a ɗaura mata aure da saurayin da ta zaɓa. "Amarya kin sha ƙamshi!" Ta ji an faɗi daga bayanta, ba tare da ta juya ba ta kalli cikin madubin tana ƙara faɗaɗa murmushinta, ganin ƙawarta ce Rayyanatu. "Ƙawar amarya ma ta sha ƙamshi!" Ta faɗi ita ma tana juyawa. "Sabuwar order aka yi ne?" Cewar Rayyanatu tana kallon high-neck flutter sleeve maxi dress ɗin dake jikinta. Ta gyaɗa kai tana juyi a cikin kayan cike da nishaɗi. "Ya kika ga?" Rayyantu ta yi murmushi ba yabo ba fallasa. "Da ma ke akwai kayan da za ki saka ya kasa miki kyau ne?" Wannan karon dariya ta yi. "Za mu je ɗin ne?" "Ina ke nan?" Ta maida mata da tambaya cikin kokwanto, dan ba ta tuna ba. "Gidan naki mana" Kuma sai ta tuna, batun wayar Rayyana da ta manta a sabon gidan da za su tare da mijin da za ta aura nan da kwana kaɗan, lokacin da suka je kaiwa curtains. "Oh na manta! Amma kin san yadda za ayi? Bari na baki key ɗin kawai, sai ki je ki ɗauko da kanki, akwai baƙin da zan yi anjima, kuma yau juma'a ina so na je na duba tsoho! (Kakanta)" Da sauri Rayyanatu ta tari nunfashinta. "A'a! Dan Allah ki zo mu je tare! Bana son zuwa ni kaɗai!" Ta yi shiru tana nazari! Rayyanatu ta fi ƙarfin ta naimi alfarma a wurinta ta kasa mata. Ita tamkar 'yar uwarta take ta wuce ƙawa, ganin kamar ba za ta amince ba yasa cike da roƙo Rayyanatu tace. "Dan Allah Sanah!" Sanah ta kalleta. "Shikenan bari na sauya kaya sai mu tafi!" Murmushi mai faɗi Rayyanatu ta yi, ganin ta amince. *** A gaban wani gida da kyakkyawan fentinsa yake bayyana sabuntarsa motar Sana ta yi parking. Kallon gate ɗin gidan ta yi tana faɗin. "Tun da ba zama za mu yi ba ai ba sai na shiga da motar ba ko?" Ta tambaya tana kallon Rayyanatu dake latsa wayarta, ganin kamar ba ta ji me take cewa ba yasa ta miƙa hannu ta taɓa kafaɗarta. "Rayyana!" Da sauri Rayyanatu ta damƙe wayarta ta kalleta a zabure. "Me kike cewa?" Ta faɗi cikin nuƙu-nuƙu. "Na ce tun da ba jima za mu yi ba ba sai na shiga da motar ba ko?" Ta maimaita tana nazartar yanayinta. "Eh! Eh ba sai mun shiga da ita ba, mu je kawai!" Ta yi wuff ta fice daga motar ta bar Sanah da baki a sake tana kallonta, ta lura yau Rayyana is acting weird! Ta kauda tunanin ta cire safety belt ta buɗe motar ta fita. Kallon gidan kaɗai murmushi ya haddasar a fuskarta, wai yanzu wannan shi ne gidan da za su zauna ita da Habib, kai abin is unbelievable. Haka ta takewa Rayyana da ta rigata faɗawa gidan baya, a farfajiyat gidan suka tsaya, ganin motar Habib a cikin gidan, mamaki ya kama Sanah, domin idan za ta iya tunawa yace da ita yau baya gari zai je Yobe yin wani aiki, to me yake a gidan? Ko dai motar ya kawo ya aje kawai? "Wannan ba motar Habib ba ce?" Rayyana ta tambaya, ba wai dan ba ta sani ba. "Motar Habib ce" Sanah ta amsa mata har yanzu ba ta gama fita daga kokwanto ba. "Amma me take a nan? Ko ya fasa tafiyar ne?" A duniyar nan, tun daga haihuwar Sanah zuwa yau, babu sirrin rayuwarta da Rayyana ba ta san shi ba, ta san komai a kanta, abu ɗaya ne ba ta taɓa gigin sanar da ita ba, kuma shi ma dan tana tunanin idan ta sani hakan zai iya taɓa alaƙarsu ne. Saboda irin yardar da ta yi da Rayyana ba ta taɓa ɓoye mata abu duk ƙanƙantarsa. Domin ba fa da Abokiyar shawara sai ita, sai kuma ɗan uwanta Jabeer. "Ban sani ba!" Ta amsa muryarta na rawa. "To mu shiga mu ga!" Da haka suka nufi entrance, a nan ne ta doka birki, domin ita ce kan gaba, ganin takalmin Habib a ƙofar entrance ɗin, ba wai takalminsa ne kaɗai ba, akwai wani a kusa da nasa, wanda ko ba a faɗa ba ta san cewa takalmin mace ne? Biyu-biyu ta fara gani yayin da zuciyarta ta yi skipping beat. "Mene ne wannan?" Cewar Rayyana kamar ba ta ga abi da Sanah ta gani ba. Kasa amsa mata ta yi, ta ɗaga kanta a hankali ta kalli ƙofar tana jin dariyar Habib a cikin falon, ƙwalla ce ta fara kokawar fita daga idonta, domin son tabbatar da abin da zuciya take raya mata ta ɗaga hannunta dake ɓari ta kama handle ɗin ƙofar sannan ta yi ƙarfin halin murɗawa ta tura ƙofar, idonta ta lumshe ta kawar da kanta gefe jin ƙofar a buɗe. Kafin ta juya kanta ta fuskanci ƙofar sai da ta furzar da numfashi kafin ta ɗaga curtain ɗin da yake ƙofar hakan ya bata damar ganin abin da yake wakana a falon, nunfashin da take son jabne ya maƙale mata, sannan hawayen da take ta son hanasu zuwa ne suka ƙwace, sannan suka zubo kan kuncinta, ƙofar da take riƙe da ita ta ƙara jimƙewa tana jin kanta na juyawa. Wace irin rayuwa ce wannan? Abin da ta tambayi kanta ke nan, kuma a dai-dai lokacin Habib da budurwar dake tare da shi suka hankalta da an buɗe ƙofar suka kalli ƙofar a tare sannan suka miƙe a zabure. Kallonsa take ciki da mamaki da kuma wani abu mai kama da ɓacin rai, yayin da yake kallonta da namadar da ta rufe shi nan take. Ba ta iya cewa komai ba, ta yi ƙarfin halin sakin ƙofar sannan ta juya da sauri. Sai a lokacin Rayyana dake bayanta ta samu damar ganin abin da yake faruwa, ta kama baki tana faɗin 'innalillahi wa inna ilaihi raji'un!' Sanah ba ta tsaya a ko ina ba sai cikin motarta, tashin hankali yasa ta manya cewa tare da Rayyana suka zo, burinta kawai ta bar unguwar, idan da hali ta bar garin, idan bai samu ba ƙasar ko ma ta bar duniyar, wata ƙila hakan zai fi. Kafin Rayyana ta fito har ta bar layin saboda gudun da take, hawaye ne ke zubo mata kamar ba gobe. Wai duk duniya ita kaɗai ce irin wannan abin yake faruwa da ita? Ko kuwa duk wata 'ya mace mai shekarunta na fama da irin ƙaddararta? Shin laifinfa ne dan an haifota a mace? Shin laifi ne yin mafarkin samun rayuwar farin ciki tare da namijin da take so? Shin haka samun abin da rai ke so yake da wahala? Wai da ma haka zafin ƙaddara yake? Ko kuwa da ma yana ɗaya daga cikin ƙaddararta ne mutuwa ba tare da ta yi aure ba? Habib shi ne saurayinta na biyar da sai bayan maganar aure ta shiga tsakanin komai yake wargajewa. Da farko kanta take tuhuma, tun tana yin hakan har ta ta gane cewa hakan ƙaddararta ce... Kuka kawai take tana ambaton inna lillahi wa inna ilaihi raji'un. Sau uku wayarta tana ringing amma ba ta san tana yi ba ma, sai a na biyar ta lura da wayar dake cikin Centre console ɗin motar. Da ƙarfi ta taka birki a gefen hanya, ta ɗaga kanta sama tana share hawayenta, ta ja hanci, sannan ta sake kallon wayar dake ringing, hannunta ta miƙa ta ɗauki wayar sannan ta ɗaga ta kara a kunnenta. "Assalamu alaikum Baba mun wuni lafiya?" Ta faɗi cikin ƙarfin hali, domin ba ta so kawun nata ya gane halin da take ciki, alda ƙyar shi ma ya amsa mata. Kafin ya ƙara da. "Kina yanzu haka?" "Na ɗan fita ne? Ko ka zo shago ne?" "A'a ina gida, dan Allah ki yi ƙoƙarinki sanar da Khabir ke da shi ku zo gida!" Ƙirjinta ya ƙara bugawa da ƙarfi, har wani zazzaɓi na rufo mata. "To Baba, amma lafiya?" Tana iya jiyo ajiyar zuciyar da yayi, kafin yace. "Allah ya yi wa Malam Rasuwa!" Abin da za ta iya cewa ta ji ke nan, domin duk wasu bayanai da suka biyo bayan hakan ba ta ji su ba. Shin anya za ta taɓa samun dawwammamen farin ciki a rayuwa? Babu abin da za ta iya, sai kanta da ta kifa a kan sitiyarin motar ta co gaba da kukanta ita kaɗai, kamar yanda ta saba, domin ba ta da wanda za ta kaiwa kukanta bayan Jabeer, wanda ta san a yanzu haka shi ma yana can yana fama da tasa damuwar matsawar ya san da batun mutuwar kakan nasu. JABEER POV. Lokacin da Alƙali ya zauna bisa kujerarsa, duk wani abi mai numfashi a cikin kotun ya yi shiru domin saurarar karar da za a gabatar. Registrar ne ya tashi domin gabatar da jawabi a kan karar da za a gabatar. “Yau ashirin da uku ga watan Janairu, shekara ta dubu biyu da ashin da biyar, wanda ya yi dai-dai da 20 ga watan rajab 1446 hijirriyah, . Za mu ci gaba da sauraren shari’a tsakanin Abdul Ali da kuma Malam Laminu. Inda Malam Laminu ke karar Abdul Ali, bisa zargin kisan dansa Muktar!” Yana gaba karanto jawabin ya juya ya mikawa takardar zuwa ga tebirin alkali. Alkali ya daga kai ya kalli sashin wurin da lauyoyi suke zaune, bayan ya kammala duba takardar karar. “Lauyan masu kara, kotu ta baka dama domin ya gabatar da shedunsa!” Glasses dinsa ya dauka ya saka, sannan ya mike ya kalli alkali. “Ya mai girma mai shari’a, har yanzu shedarmu ba ta karaso ba!” Alkali ya kalli lauyan wanda yake kare wanda ake zargi. “Lauyan wanda yake kare wanda ake kara, kotu ta baka dama domin gabatar da shedunka!” Lauyan dake gefensa ne ya tashi, sannan ya fito daga seat dinsa, ya tsaya a gaban alkali. “Mun gabatar da duk hujjojin da suka nuna cewa wanda nake karewa bai aikata wannan laifin da ake zarginsa da shi ba, dan haka nake rokon wannan kotu mai alfarma, da ta wanke wanda nake karewa dan gane da bata masa suna da aka yi tare da hukunta wadan da bangaren da suke kara sakamakon batawa wannan kotu mai adalci lokaci da suak yi!...” Yayin da Habu Dan Ladi yake ta babatu. Wani dan sanda da ya shigo kotun, ya zo ya sunkuya a dai-dai kansa, yay masa rada. Da hannu ya sallami dan sandan, sannan ya gyara zama yana jiran Habu Dan Ladi ya gama maganganun da yake. Ya juya ya kalli wurin da iyayen Abdul suke, wadan da su ma shi suke kallo. Gaba daya alamun tashin hankali ya bayyana a kan fuskokinsu. Idonsa ya lumshe sannan ya buɗe yana musu alamun su kwantar da hankulansu. “Lauyan wanda yake kara! Shin shedunka sun kammala?” Cike da girmamawa ya mike, sannan ya fito waje. “Kwarai ya mai girma mai shari’a, ina rokon kotu da ta bani dama, domin na gabatar da sheduna!” “Kotu ta baka dama!” Cewar Alkali. Jabeer ya juya ya kalli dan sanda ya zo ya masa magana dazu. “Kotu na da bukatar ganin Hassan Bala” Gaba daya hankalin jama’ar dake kotu ya koma kan saurayin da ya taso daga kujerun baya na kotun, wani irin dan iskan kallo Abdul yay masa yana dariya, domin bai hangowa kansa tunuwar asirinsa dalilin Hassan din ba. kansa a kasa hare ya karasa witnessbox, ya tsaya. Jabeer ya nufi witness box din, sannan ya tsaya a gaban Hassan. “Kotu tana so ta san sunanka” Yace yana dubansa. Kai a ƙasa ya furta. “Sunana Sunana Hassan Bala” “Malam Hassan, mece ce alakarka da Abdul?” Ya karashe yana nuni ga Abdul din dake zaune a tsakiyar wasu ‘yan sanda. “Abdul abokina!” “Kotu tana so ka mata alkawarin duk abin da za ka fada ya kasance gaskiya!” “Na yi alkawarin duk abin da zan fada zai kasance gaskiya, ba zan fadi wani abu da yake sabanin gaskiya ba!” “Malam Hassan! Me ka sani dangane da kisan Muktar!” “Muktar da Abdul duka abokaina ne! ranar da abin ya faru, mun shirya cewa za mu raka Muktar zance wurin budurwarsa, duk da kasancewar mun yi cewa mu uku za mu je, sai suka zagaye suka tafi su biyu ba tare da ni ba. lokacin da na je gidan su Muktar na tambaya yana ina? Kanwarsa ce ta sanar da ni sun Abdul da kansa ya zo ya dauki Muktar ya tafi! Duk da raina ya bai a lokaci na so na yi zuciya, amma sai na sha alwashin sai na bisu har gidan na nuna musu bacin raina! Hakan tasa na hau mashin na bi bayansa, yayin da nake kan mashin muna tafiya ina hange-hange a gefen hanya cikin bacin rai na hangi motar Abdul fake a gefen hanya, hakan yasa na yi saurin dakatar d ame mashin din, ya tsaya na sallame shi, sannan na taka da kafa na nufi wurin domin na je na hadasu su biyun na musu wankin babban bargo. Sai dai kafin na karasa wurin da motar take…” Ya dakata ya kalli Abdul da gabansa ya fara faduwa, domin sai yanzu ya fara ganin alamun tonuwar asirinsa. Kwalla kwance a idonsa ya furta. “A lokacin na ga sanda Abdul ya fito da Muktar daga cikin motarsa, sannan ya ci kwalarsa, ya daga kwajirin da baya rabuwa da ita a motarsa, ya kwada masa a ka!” Kasa karasawa ya yi, saboda kuka da yake son cin karfinsa. “Hakika ban san abin da ya hadasu fada ba, sai dai zan iya shaidar abu guda, cewa Abdul na da saurin fushi da mummunar zuciya! Hakan tasa ni ma na ji tsoron kada abin ya shafeni, na juya na bar wurin lokacin da nake kallon abokina a gargarar mutuwa!” Yana gama fadin hakan Bar. Habu Dan Ladi ya mike yana fadin. “Ina da korafi ya mai shari’a!” “Kotu ta baka dama!” “Idan har abin da sheda yake fada gaskiya ne, me yasa bai gabar da shaidarsa ba tun a zaman kotu na baya, sai yanzu da ake kan gabar rufe wannan shari’ar!” Habu Dan Ladi ya maida dubansa ga al’kali. “Ya mai girma mai shari’a ina rokon kotu da ta yi fatali da wannan shedar da suka bayar, domin suna so su yi wasa da hankalin kotu! Na gode me shari’a!” “Korafi ya karbu! Malam Hassan, mene ne dalilinka na rashin bayyana wanna sheda tun a zaman kotu na farko?” Hassan ya sauke kai yana hawaye. “Ban gabatar da wannan shaidar ba saboda tsoron abin da zai iya faruwa da ni, hakika Abdul abokinmu ne, amma halayensa da namu sun banbanta, sannan matsayinmu ya banbanta, domin shi iyayensa masu kudi ne, mu kuma dika iyayenmu masu karamin karfi ne, mu ganau ne ba jiyau ba, na yanda mahaifin Abdul yake kokari wurin ganin ya fitar da shi a ko wata matsala da zai fada, ko da hakan zai kai ga an dauki rai!” Alkali ya kalli lauyan wanda yake karewa. “Lauyen wanda ake kara, shin kana da ja?” Ya mike cikin girmamawa. “A’a ya mai shari’a!” Hakan ya bawa Jabeer damar cewa. “Ya mai girma mai shari’a! ina rokon kotu da ta bani dama domin na sake gayyato wanda ake kara!” “Kotu ta baka dama!” Jin hakan yasa Hassan ya fita daga witness box, shi kuma Abdul da alamun tsoro suka fara bayyana tattare da shi, ya fito jiki a sanyaye, ya shiga cikin witness box din jikinsa na rawa. Mahaifinsa ya kalla, wanda ya cika ham, alama ya masa da ya kwantar d ahankalinsa, shi kuma ya kalli lauyansa, shi ma ya mas alama da babu wata damuwa. “Malam Abdul! Ina so na maka wasu ‘yan tambayoyi!” Ya gyada kansa yana kallon Jabeer, sannan ya hadiyi miyau din tsoro. “Ka kwantar da hankalinka, ka amsa mini tambayar da zan maka!” Abdul dai kallonsa kawai yake. “Malam Abdul! Shin wasu tufafi ka fi sha’awar sanyawa?” “Pardon?” Ya fadi ido waje, domin bai tsammanin tambayar da zai masa ke nan ba, murmushi ya yi mai sauti yana gyara gilashin idonsa. “Wasu kalar tufafi kafi sakawa? Manyan kaya? Ko kanana?” Abdul ya kalli lauyansa, domin tambayar ta daure masa kai. Kallonsa da ya yi yasa ya mike tsaye da sauri. “Ina da ja ya mai shari’a!” “Kotu ta baka dama!” “Wannan tambayar da lauyan wanda ake kara yake, ba ta da hadi da wannan shari’a! yana yinta ne kawai saboda ya batawa kotu laokaci!” “Korafi bai karbu ba! lauyan wanda suke kara, kana da damar ci gaba da tambayoyinka!” Ya dan risina fuska ba yabo ba fallasa, sannan yace. “Na gode mai shari’a!” Bai juya ya kallo Abdul ba sai da ya yi wa Habu Dan Ladi wani kallo. Sannan ya kalli Abdul yana gyara gilashinsa. “Kotu tana saurarenka Malam Abdul!” Andul ya kalli Habu Dan Ladi da ya zauna a ɗarare, domin shi kansa yanzu abin ya fara fita aga ikonsa. “Ni… ni… bana saka… Manyan kaya… sam!” “Ba ka sakawa kwata-kwata? Ko ko dai akwai wasu lokuta da ba ka sakasu?” “Ba na sakawa sai da azumi, shi ma saboda mahaifiyata tana takura minu ne!” Ya shararo karyar hankali kwance, a lokaci guda hankalinsa ya kwanta, domin a ganinsa zai sha, wani murmushin ya sake yi yana gyara gilashin idonsa. “Amma shaidar gani da ido, wato Bilkisu kanwar Muktar! Ta tabbatar mana da ranar da abin ya faru, kana sanye da manyan kaya ne? me za ka ce a kan hakan?” Idonsa ya zare lokacin d aya rasa amsar bayarwa. Domin tsoro ya mantar da shi abin da zai iya alakanta case din da kuma shigarsa. “Na… na-na..na!” “Ka nutsu! Babu wanda zai tirsasaka a nan, ka kwnatar da hankalinka ka yi wa kotu bayani dalla-dalla!” Ya kasa amsawa, domin ya rasa abin da zai fada, lauyansa ya kalla wanda yake masa alama da ya yi shiru kawai. “Malam Abdul kai muke sauraro! Ka yi shiru bayan kotu kai take sauraro!” Ya yi shiru, banda gumi dake keto masa babu abin da yake. Jabeer ya juya ga alkali. “Ya mai girma mai shari’a ina rokon kotu da…” “Zan amsa! Zan amsa!” Ya fadi da sauri! Lauyansa sai alama yake masa da kada ya yi magana. Amma haka ya shareshi yace. “Muktar shi ne wanda ya takura mini kan sai na saka manyan kaya a wannan ranar, domin ba ya taba yarda mu je wurin budurwarsa sanye da kananan kaya!” Jabeer yay wani guntun murmushi. “Amma idan zan iya tunawa a zaman da ya gabata ka furta cewa kai ba ka hadu da Muktar a wannan ranar ba, ballanatana har ku fita zuwa wani wurin, haka ne?” Gabansa ya fadi, take ya rintse idonsa, gumi na ta keto masa, ban da ya shiga uku babu abin da yake nanatawa. “Ina da ja ya mai shari’a!...” “Korafi bai karbu ba!” Alkali ya yi saurin dakatar da shi run kafin ya kai ga furta korafinsa, haka ya koma ya zauna jiki a sanyaye, ko bai kalli mahaifin abdul ba ya san irin kallon da yake aika masa. “Malam Abdul! Zai fi maka sauki ka fito ka fadi gaskiyar abin da ya faru a waccan ranar, ka amsa laifinka, ko wannan kotu za ta dubeka ta saukaka maka wurin hukunci!” Idonsa ya bude yana jin kamar yay fiffike ya tashi sama, ya duba dama da hauni ya ga babu wani sarki sai Allah, dan haka babu abin da ya rage masa sama da fadin gaskiya. “Haka ne! tabbas ni ne wanda na kashe abokina Muktar! A waccan ranar mun fita tare ni da shi, yayin da muke hanyar zuwa gidansu budurwarsa na kasa riƙe abin da yake raina, saboda hirata da yake mini, fakaqa na yi a gefen hanya na dube shi lokacin da yake tambayata abin da ya faru, a lokacin nake sanar da shi cewar ni fa ina son budurwarsa, kuma sai na aureta ko da ba ya so... a lokacin shi ma Muktar ya kasa riƙe fushinsa, muka fara faɗa da shi, har ta kai ga na buga masa kwajiri a kansa... amma ban dake shi saboda ina so ya mutu ba, tsautsayi ne ya faru! Ina naiman afuwa!” Tsabar nauyin abin da ya aikata kasa tsayawa ya yi a kan kafafunsa, domin yanzu dai ya hangi zamansa a gidan yari gadan-gadan ya nufo shi. take kus-kus ya fara tashi a tsakanin ‘yan kallo, har sai da alkali ya tsawatar. “Lauyan wanda suka shigar da kara! Shin kana da wata tambayar?” “Babu ya mai girma mai shari’a!... Duba da irin gamsassun hujjoji da muka gabatar a gaban wannan kotu mai alfarma, ina rokon da ta yi duba na tsanaki, ta zartar da hukunci cikin adalici irin nata! Na gode!” Ya koma ya zauna. Alkali ya dubi lauyan wanda ake karewa. “Shin lauyan wanda ake karewa yana da ja?” Ya tashi jiki duk yay snayi. “Babu ya mai girma mai shari’a!” “Duba da sauraron wannan shar’a da muka yi, da kuma hujjoji da aka gabatar, wannan kotu mai alfarma ta gamsu cewa Abdul Ali shi ne ya kashe abokinsa Muktar Laminu, kuma ta yankewa hukuncin daurin rai-da-rai, wanda yake kunshe a sashi na 221 a kundin doka na penal code! Idan bai gamsu da wannan hukuncin ba, yana da damar daukaka kara daga yau zuwa ranar ashirin da tara ga watan Janairu” Kuma da haka shari’ar ta kare, shari’ar da aka farota cike da murda-murda da kulle-kullen da ake ganin kamar ba su warwaru ba, kuma dama ita shari’a sabanin hankali ce, ai ko yau ta sayar da jama’a da dama mamaki. Karewar zaman kotun ya bawa jama’a damar bajewa, yayin da wasu suka tsaya a farfajiyar kotun suna ta maida zance kan abin da ya wakana a kotun ta yau. Yayin da shi kuma Jabeer yake tare da mataimakinsa a jikin motarsa a farfajiyar kotun wasu takardu da ya kawo masa yake dubawa, fuskar nan ba yabo ba fallasa kamar kullum, domin shi dai kam duk kwakwaffin mutum ba zai iya gane inda ya dosa ba, yana da murddaden hali da kuma zurfin cikin da babu mai iya jin sirrinsa sai idan ya si, hatta mahaifiyarsa na kokawa da wannan halin nasa, shi sam ba ya son mutane ko shiga cikinsu, a ganinsa rayuwar kadaici ita ce komai, zai iya yin wata ba tare da ya yi magana da kowa ba, matsawar akwai littattafan da zai karanta, ko kuma wani case da zai yi research a kai. Ya fi gane rayuwa shi kadai fiye da rayuwa da wasu. Bam! Aka daki jikin motarsa da hannu, kansa kawai ya juya ya kalli wurin da ya ji an biga din, kallo daya ya yi wa barrister Habu Dan Ladi ya shekar ya ci gaba da abin da yake, mataimakinsa Ashiru ne ya gaisheda Habun, amma ko kallonsa bai yi ba ballantana ya amsa. “Jabeer Hashim!” Habu ya kira sunansa wani tukukin bakin ciki da takaici na taso masa. Ba wannan ne karo na farko da suka fara karawa a kotu ba, abin mamakin shi ne duk sanda za su kara Jabeer ne ke yi nasara, amma me yasa? “Karanto!” Jabeer ya fadi kai tsaye yana kallon takardun hannunsa, wannan kalma ta ‘Karanto!’ ta zame masa dabi’a, musamman idan an kira shi a wayar da ba ya bukatar dagata, domin duk wanda ya san shi ya sani cewar ba ya son kira, in ko ka kira shi a waya sai ya ga dama zai daga, kuma yana dauka kalma ta farko da za ta fito daga bakinsa ita ce ‘Karanto !’ wato ka fadi duk abin da kake tafe da shi, idan ya ga dama ya baka amsa, idan mizanin hankalins aya nun amasa cewar maganar ba ta da amfani take zai datse kiransa. Shi dama ba ka isa ka ce ya zo kana so ka yi magana da shi ba, sai dai kai ka zo ka same shi. ai ko Habu ya shaka, dan cikin danne fushinsa da ya cure wuri guda da hassada yace. “Wai kai a tunaninka ka fi kowa?” Sai da ya shafe sakkani kafin ya girgiza masa kai. “Not every one! Only you” Wani abu mai daci ya ci gaba da taruwa a wuyan Habu. “Na rantse maka da Allah sai na kada kai a shari’ar da za mu kara a gaba, sai na tabbatar da ka fadi shari’ar…” “Ashiru ka sameni a office idan ka gama, I’ll take my leave” Ya fadi yana kallon Ashiru, domin bai bawa existance din Habu muhimmanci ba, tun bayan kallon farko d a ya masa bai sake ba, haushi yasa Habu ya kunshe sauran maganganunsa a cikinsa, domin ya san ko ya fadesu ba wani amfani za su yi ba, ko da sun yi tasiri a kansa ba nunawa zai yi ba, Jabeer ba irin mutanen da ake fusatawa da bakaken maganganu ba ne, shi sai ka rasa ma ta ina za ka oya handling dinsa, she’s very complicated person. “Idan ka gama i’ll excuse my self, Sir!” Yace yana kallon Habu dake tsaye jikin motarsa. Tsabar takaici kasa cewa komai ya yi, ya juya yana tafku da karfi sannan da sauri kamar zai dara kasa, ba tare da ya kara ko da minti daya ba ne a wurin ya shige motarsa yayin da Ashiri ke fadin a sauka lafiya, hannu kawai ya daga masa, yana kokarin saka safety belt. Kafin ya kai ga tada motar wayarsa ta soma ruri, tsaki ya ja a kasan numfashinsa jin wani zai addabi rayuwarsa, bai ma san ya aka yi wayar take ba a silent ba, domin wasu lokutan har sautin kiran dake kan wayar tasa yake mantawa ba, wayarsa ba ta rabo da silent. Da kamar ba zai daga ba, jin har kira uku na shigowa a jere yasa ya fahimci muhimmancin dalilin kiran, yana da tabbacin idan harw ansa ya san shi ne yake kiran babu yanda za ayi ya jera masa kira har uku, kiran da ake masa ba ya haura daya ko biyu. Yana duba wayar ya ga an rubuta "Sanguine" a matsayin sunan me kiran yasa ya gane cewa Halima kanwarsa ce, wayar ya daga ya kara a kunnensa da fadin ’Karanto’ ai ko ta karanto din, domin ita ce ta sanar da shi labarin rasuwar ginshikin gidansu, gatansu, farin cikin idaniyarsu da ta iyayensu, wato kakansu Malam Baba. *College of Nursing and Midwifery Hadejia, Jigawa State.” Sautin kiran wayar ya kara dokawa a karo na barkatai, haka karan ya ci gaba da tashi yana karade room 14 dake cikin hostel din mata. Karar da wayar take ya kai ace hatta makotan dakin yaci ace ta ishesu, amma budurwar dake kwance kan karfen gadon dake cikin dakin ko motsi ba ta yi ba, hatta net ba ta cire ba, sabanin sauran gadajen biyu dake dakin, wanda ko wanne a cikisu babu net, sannan an yi masa shimfida mai kyau da kyawawan zannuwan gadajensu, ko wani gado na dauke da pillow daya dake sanye da pillow case kalar na zanin gadon, duk da babu haske sosai a dakin kasancewar kofar dakin a rufe take za ka iya shaida cewar dakin ya sha shara yadda ya kamata, domin tiles din dakin har kyalli yake, komai tsaf-tsaf da shi a dakin nasu. Har sai da kiran wayar ya sake katsewa sannan aka bude kofar dakin ta waje, wasu ‘yammata biyu ne suka shigo sanye da fararen uniform din makarantar, ko wacce da pink stripe a jikin dogon hannun rigarta. “Ah-ah wai dama Nightingale ba ta je class ba?” Wadda ta fara shigowa dakin ta tambaya fuska cike da mamaki, dayar da ta samu ma zauni a bakin gadonta tana cire takalman kafarta ta bata amsa da. “Tashin duniya na mata sanda zan fita, amma ko motsi ba ta yi ba, kin san halin baccinta!” Ba tare da dayar ta karashe bayan da take ba, wadda ke tsaye har zuwa lokacin ta nufi gadon da take kai, ta yaye net din, sannan ta soma dukan kafarta tana kiran sunanta. “Nusaiba! Ke Nusaiba! Nusy! Nusaiba Hashim! Nightingale!” Duk wani suna d ata san suna kiranta da shi ba ta bari ba sai da ta ambata, amma ko a jikin Nusaiba wai an tsabiri kakkausa, bacci kawai take tana numfashi a sanyaye. “Ba fa za ta tashi ba sai kin saka mata ruwa!” Wadda ta kammala cire takalminta ta fadi. Ai ko hakan aka yi, bokitan da suke ajiyar ruwa ta nufa, ta daibo a kofi, sannan ta kara dawowa bakin gadon nata, ta watsa mata ruwan a fuska!. Sai a lokacin ta bude idonta, sannan ta tashi a firgice kamar wadda tra dakata a tsakiyar gasar gudu. Ko gani dai-dai ba ta yi saboda ruwan da ya jika mata fuska, numfashi kawai take tana dafe da kanta d aya sara nan take. “Wannan wani irin bacci kike haka Nusy? Ya kamata ace kin rage baccin nan ba wai ki kara ba, kin sani yanzu wata biyu ya rage mu zana School Final (Jarabawa ta karshe da daliban Nursing da Midwifery ke zanawa a makaranta) Sannan ga Councill (Jarabawar karshe da Nursing And Midwifery Council ke shiryawa daliban da suka kammala training na shekara uku a college…) Dan Allah Nusy ki yi wa kanki fada!” Ba ta ce komai ba sai idonta da ta lumshe tana murza goshinta, domin wani irin azababben ciwo kanta ke mata. “Na ji!” Ta iya furtawa da kyar domin gojewa fadan roomate din nata, dan ta san idan ba ta yi addmitting ba, Aisha Musa za ta iya kwana tana mata fada a kan gaskiya. “Kada Allah yasa ki ji” Cewar Aisha a kufule, domin wani abin idan Nusyn ta yi cikata yake da takaicim kwakwalwa bakin ya tata, kokari bakin ya nata, amma sam ba ta da hali ya uwar akuya a kasuwa. ba ta son kowa ya rabeta, ba ta abota da kowa, ba za ka taba ji ta zauna tana hira da wani ba, hatta ganin murmushinta wuyar gani yake. Ta fi minti ashirin still tana zaune a tsakiyar gadon tana dafe da kanta, gashin kanta mai tsayi duk ya barbaje ya hautsine, idanuwanta a bushe haka ma bakinta, ruwa kawai take bukata amma ta kasa tashi saboda ciwon kai. “Karbi ki sha” Ta ji an ce a saman kanta, da kyar ta iya daga kanta cikin layi ta kalli Maryam dake tsaye a kanta tana mika mata ruwa a bottele. Ta mika hannu ta karba. “Na gode!” Ta ce, sannan ta bude ruwan ta fara sha. Sai da ta shanye tass, sannan ta fara samun kanta. Cikin karfin hali ta sauko daga kan gadon. “Wayata! Ina wayata?” Tace cikin yanayin da ba za a kira da maye ba. Maryam da har yanzu take hankalce da ita ce ta yi kokari ta cire wayar a caji ta mika mata, ta karba sannan ta kunna, ganin missied call 10 daga lambar D.P.O yasa ta zaro ido tana dafe goshinta. “Na shiga uku!” “Me ya faru?” Cewar Maryam da Aisha lokaci guda. “Yau za mu koma kotu!” “Kuma kike zaune a nan?” Cewar Maryam, dan yatsanta ta ciza cikin rashin sanin abin yi, domin ba ta sna ya za ta yi ba. “Ki tashi ki shirya ki tafi.. yau na yi magana da SUG presdent, insha Allah komai zai wuce, za su shiga maganar dan Allah kar ki daga hankalinki” Kai kawai ta daga, sannan ciki juriya ta tashi ta nufi bayi. Sai dai kafin ta karasa wayarta dake hannunta ta sake kara. Ta yi sauri ta duba zatonta D.P.O ne, amma sai ta ga ‘Ya Jabeer’. Ta san ba ya kiran banza, lallai ma akwai abin da ya faru a gida, jingina ta yi da bango domin ba z ata iya tsayuwa kan kafafunta ba. “Ina kwana ya Jabeer!” Ta yi saurin fadi cikin sanyin murya, shi ma a sanyayen ya amsa mata. “Na kira student affairs office na school dinku, na sanar da su cewar za ki dawo gida, ki yi kokari ki rubuta letter ki basu, idan suka baki exit sai ki bawa kawanyenki…” “Me ya faru?” Ta katse shi jin ya dauko wani dogon zance mara kan gado, domin ta san shi ma kamarv ita yake, ba shi da surutu. “Nusaiba!” “Na’am Ya Jabeer!” “Allah ya yi wa Malam rasuwa!” Dimm! Ya ji faduwar abu kasa, ya san za a rina, dan haka ya yi saurin kashe wayarsa. Ba suma ta yi ba, gravity ne ya jata zuwa kasa, a cikin hayyacinta take, domin takan iya tuna yanda komai ya wakana tsakaninsu a wancan daren, tana iya tuna sautin muryarta dake roko cikin kuka da fitar hayyaci, ta tuna sanda ta rike kafafu cike da magiya kan a bata abin da idan ba ta sha ba za ta iya rasa ranta, ta tuna sharadin da ya biyo baya, ta tuna sanda ta shiga dakin Yasmin (Kakarsu) ta sato key din dakin Malam. Ta tuna komai ciki har da sand ata sallama key din ita kuma aka bata madogarar rayuwarta. ‘Ni ce silar mutuwarsa! Ni na kashe Malam!’ Haka tunaninta yace mata a lokacin da Maryam da Aisha ke aikin jijjigata suna kiran sunanta, kuma tana ji, amma nauyin damuwar da ya fi karfin rayuwarta shi ne yake naiman kaita ga mutuwarta. ````````````````````` To fa! Yanzu muka soma tafiyar, yanzu za a soma labarin, kun dai ji kalar salon da ya zo da shi, to da fatan za a gyara zama domin sauraron wannan kayataccen labari, wanda yake cike da ilmantarwa da kuma nishadantarwa! Sannan kada a manta paid book ne a kan 700 #SalmaAhmadIsah #Madubi #Candy #Bahadejia