HAWAYEN MARAICI

8

by @asmybaliyu

HAWAYEN MARAICI 8

By

Asmy b Aliyu

Haka aka cika gaban Mimi da cima kala-kala amma ta kasa taba komai gabadaya hankalinta na kan AY.

Yayanta yayi Aure bata sani ba, Wannan wane irin Aure ne??"

Jawaheer ce tayi saurin katse mata tunani meya faru Mimi ??" Ko bakiyi murnar ganin yayanki bane,gashi kin kasa taba komai cike da jawaheer,ta fara serving dinta babu yadda ta iya haka ta fara cin abincin sama -sama lallai tana bukatar ta kebe da yayanta.

Kadan taci ta fadawa  Aunty salma ta koshi murmushi Aunty salma tayi oya mu shiga ciki kiyi wanka. Yaaya  kaji rani naje nayi wanka akwai maganar da xamuyi, daga mata kai yayi dan yasan maganar dake yimata yawo acikin xuciyarta anan aka barsa shida jawaheer.

Babe!

Cewar jawaheer ido ya xuba mata ina son ka kaini gidan wata friend dina dake nan

Zoo road,

Kibari sai xuwa anjima, Nura nake jira fita xamuyi nan take Annurin fuskarta ya canja dan xaku fita da Nura shine baxaka kaini inda nakeso ba."

Sai kasa wani ya kaini idan fitar ne baka son yi dani ta karasa maganar fuska bbu walwala.tayaya zaayi su shaku dashi kullum Yana busy,bayada aiki sai zuwa office idan ya dawo kullum Yana tareda Ya'n uwansa.

  "Shawara ne kike bani ko kuma umurni??"ya fada Yana kallon cikin fuskarta,dauke kanta tayi akansa,

Tana jin zuciyarta tamkar Zata fashe,

Karar wayarsa ta katse sa Nura ne mai kiran yana dagawa ohkey gani nan fitowa ya kalli jawaheer,ki fadawa Aunty salma mun fita da Nura sai mun dawo,kin cewa komai tayi har ya fice daga falon.

Ta fito cikin Riga da wando na English west waya'ndda sukayi matukar yimata kyau ,kanta babu dankwali sai tudun gashinta dake tsakiyar kanta wandda ta kama da ribbon bata da cikar gashi sae uban tsawo da santsi.

Aunty jawaheer!!"

Dagawa Jawaheer tayi tana  kallon Mimi dake famar danna waya.Batareda ta kalleta ba take tambayar ta yaaya fa.

Kafin jawaheer tayi magana Aunty Salma ta fito,Ina Kuma  Abdul din ya tafi ??

Cewar Aunty salma,ya dan fitane  shida Nura nima yanxu xanje zoo road,kibari driver ya Kaiki,Aunty Salma ta fadawa jawaheer,itadai shiru jawaheer tayi batareda tace komai ba.

Yaaaya."

Where Are you??" Tayi maganar cike da  shagwaba,shine ka tafi baka jirani ba ko." Dif ta kashe wayar jin abunda yace hawaye suka xubo akan fuskarta  Aunty salma na mata magana bata ko kulata ba ta nufi  stairs da gudu kallon mamaki jawaheer tabita dashi ..

Murmushi Aunty tayi Mimi kenan ya'r rigimar Abdul ,bansan ya xakiyi idan kikayi Aure ba.

Nan aunty salma ta mai da kallonta kan Aliya " bara nasa driver ya kaiki in yaso daga baya shi Abdul din yaje ya dauko ki okey Aunty nagode."

#####

Misalin karfe shidda da rabi na yamma daidai lokacin da motar su AY. Ta shigo unguwar tarauni adaidai  lokacin  wata bakar motar ta shigo cikin rashin sa'a AY. Ya dan bugi motar.

Nan take yaja burki suna salati da sauri yaa fito daga motar,

Macce ce  matukiyar motar tana cikin shigar English wears riga da skirt, tayi rolling  kanta da bakin veil black  beauty ce haka kyakkyawar gaske tana da manyan idanu masu daukar hankali babu wata kwaliyya akan fuskarta amma akwai pink janbaki akan labban ta Wanda ya kara kawata fuskarta .

  Dogon hancin ta kuma tamkar Karas  ba'a sata a layin dogaye haka ma gajeru.

Fitilar motar taga ta fashe glass din idonta ta cire ta maidashi kan goshinta ,kai wane irin makahon mutum ne ?

Ta fada A tsiwance maganar da tayi shiya bani damar hango fararen hakoranta  wandda acikin Su Akwai hakorin  makka ajikin su wandda  bakaramin kyau yayi mata ba tana magana dimple na fita a fuskarta.

AY. Gabadaya ya rude daganin wannan matashiyar budurwa kasa cemata uffan yyi shikuma Nura yana a mota dama cewa yayi baxai fita ba.

Karo na biyu ta karaso a gabansa a fusace malam bakaji ina magana,

Nan ma shuru yayi mata yadda take maganar ma Abin burgewa ne.

Karar wayar ta taji dama tana hannunta duba wayar taya taga mai kiran nan take ta rude tashin hnkali ya bayyana akan fuskarta.

Hannu ta aza akai Sai kace baitace mai tsiwar nan ba

Nashiga ukku !!

Yaa Anas na kirana a waya kasheni xaiyi a fusace take kallon AY da yake kallonta har lokacin tamkar Wanda ya samu Tv

kaga hasarar da kajamin kayi shuru baka cemin komai ba kuma ka tsaya kana kallona da manyyun idonka!"

daidai lokacin Nura ya karaso gurin ganin Nura yana kallonta ya zabga mata harara itama harararsa tayi taja tsaki dama nasan xa'a Arina kace min da wannan mugun mutumen kake  murguda masa baki tayi kafin ta maida kallonta kan AY

Baxan yafe maka ba!!jin kalmar yayi har tsakkiyar kansa.

Yanxu ma kaci sa'a ina sauri da wallahi  Allah sai na Tara maka jama'a Allah ya hada mu dakai WATA RANA! "Sai ka biyani

Murmushi dauke a fuskarsa

Ya wani ware mata ido Yana fadin"har nawa zan biya miss drama Queen, takara murtuke fuska jin abunda yace

kadaina murmushi kyawun ka baxai gigita niba."

Afusace Nura ya daga hannu xai zabga mata mari a xuciya AY yayi saurin rike masa hannu da kabarsa ya mareni da ya tattaro ma Kansa masifa da bala,i  Takarasa xancen tana binsa da mugun kallo ta murguda masa baki gamida Jan dogon tsuka ta shige motar ta  tada  tabar gurin da wani irin speed ..AY Yabita da kallon SO" Aransa yake fadin (DRAMA QUEEN) sunan da xuciyarsa ta bata kenan. Maganar Nura ta dawo dashi hankalinsa.

"Meyasa baka barni na mata shegen duka anan ba? Nura yayi maganar sounding so fed up ,wlhi albasa batayi halin ruwa ba. A haka AY. Ya lallashi Nura xuwa mota Sai masifa yakeyi...

#####

Ana bude mata get din gidan nasu  ta hango motar Yaa  Anas da dayan motan daddy,da alamar ya dawo

Xuciyarta Sai da ta kusayin bindiga Dan tsoron  jiki sanyaye tayi parking motar,cikin sanyin jiki tayi sallama babban falo  ido biyu sukayi da daddy,

Da kuma yaa Anas dake binta da mugun kallo gwiwowinta ta xube A kasa daidai nan ummi  ta shigo falon.

Wani mugun kallo daddy yayi yimata.

Wanda yasa hankalinta ya Kara  tashi "Ashe ke babbar ya'r iska ce ban sani ba?" Iskancin naki har yakai ki dauki motar da nake hawa ki fita dashi .............cikin rawar murya ta fara magana kayi hakuri daddy wlhi ba laifina bane ,shikenan nagode bani key din motar.

Jiki na bari ta mika masa ..Anas ka kaita a store ka rufe kar Wanda ya bata Abinci a yau har Sae ta fada min daga ina take.

Hawaye suka xubo a idonta Dan Allah daddy kayi hakuri daga gidan kitso  nake....gidan kitson ubanki!!

Daddy yayi maganar A fusace kai Anas ko bakaji abunda nace bane?

Gadan-gadan  Anas yayi gurinta da sauri ta rarrafa gaban daddy ta rirrike kafafunsa Dan soyayyarka da manxon Allah kayi hakuri daddy!

Na tuba

Daddy nabi Allah ."baki tuba ba Asma'u har Sae na aurar dake ,haba mana daddy nice fa Asma'u mai sunan yayarka!

Fisgota yaaa Anas yayi tana ihu ya nufi hanyar store daita ,Sai famar ba yayan nata hakuri take haka tana kwalawa ummi kira...

#######

"Nura dama kasanta ne  yama abokin nasa tambayar  batareda ya kallesa ba dan hankalin sa duka yana kan driving ,A kufule Nura ya kallesa unguwar mu daya. "Dan murmushi AY.yayi haba mana Abokina Dan Allah ka sauko haka  kasan mata ya'ntattali ne Kuma Kaga karamar yarinyya ce tsarar su mimi ,banda wannan shaidaniyar yarinyar Nura yayi magana a zuciya.

Har cikin ransa AY yaji Kalmar ta shedanci da Nura ya kirama drama queen dinsa.

Kadaina kiranta shaidaniyya mana! Da mamaki Nura ya kalli abokinsa ya bata rai sabida baka so aga laifinta."

AY yaushe ka  canja??"...ba haka bane Nura ba laifin ta bane nawa ne ,ohkey ! Nan Nura ya shiga nodding din kansa. Daga lokacin Nura yaja bakin sa yyi shuru Dan ya lura Abokinnasa akwai sakar da yake yi aransa.

Yana son yaji Karin bayanin Asalin drama queen dinsa".

Yana gudun kar Nura ya tuhume sa ,Dan haka yaja bakin sa yyi shuru amma ya dau Alkawari ko yaushe ne  Sai ya nemota .

Daidai lokacin da sukayi parking ,adaidai lokacin kuma jawaheer ta fito daga cikin wata mota (406) nan take yanayin AY Ya canja ya dai hango macce da namiji a gaban motar wanda namijin shine  matukin motar  sai front seat macce ce

Sai jawaheer bayan motar.

Wa nake gani kamar jawaheer AY

Bai kulasa ba ya shiga dannawa mai gadi horn ,haka jawaheer ta hango motar tasu  Amma ko ajikinta sai ma bin motar da tayi da harara.

Ya ina tambayar ka kayimin shuru ??" Cewar Nura car key dinsa yabasa ,da dare xan shigo unguwar Ku da haka AY Yayi gaba yayinda Nura ya saki baki  yana kallon abokin nasa.

A falo ya tarar da Aunty salma da maigidanta da kuma  Autan ta sameer wandda  da fara'a Mijin Aunty salma ya tari AY har ka dawo kenan??"

Nan sukayi musabaha daidai kuma lokacin jawaheer ta shigo Anan ta gaida maigidan Aunty salma." Dama tareda madam kake kenan??

Ehhhhh uncle tare muka zo jawaheer ta nufi up stairs  AY. Ya cigaba da hirarsa Da uncle jabir  da kuma Aunty salma.

Aunty wae ina Angel ta shiga ne??"..

Tana barci  agogon dake sakale A hannunsa ya duba barci haka yamma yayi fa sosai hop tayi sallar la'asar ta kwanta.

Murmushi AY.yyi nasan laifina aunty uncle jafar  yyi dariasu   ta manyya ina ruwan mimi har yau ganin kanta take yarinya uncle bara naje na watsa ruwa naga magrib yana gabatowa " Anan ya haura sama ya samu jawaheer da ya'r bingilar Riga ta shan iska xuwa lokacin har tayi wanka tana xaune ne akan soofa tayi crossing leg's  dinta waya takeyi kasa-kasa tana jin karar bude kofar ,tayi saurin fadawa mamin Xasuyi magana xuwa anjima ,bai kulata ba ya rage kayan jikinsa ya nufi bathroom saurin shan gabansa tayi ,yana daure da brown  towel a kugunsa. sumar jikinsa baka wuluk ..

ta kwanta luf daita gwanin Sha'awa.

Lfia ??"

Ya fada yana kallonta "Am sorry  xan hada maka ruwan wanka ."

 Sai aka fadamaki bana da hannuwan hadasu , please mana.ta fada cike da shagwaba,matsamun jawaheer dan Allah."

Yayi maganar babu wasa a fuskarsa daure fuska tayi gamida yin folding din hannunta akan kirjinta ,baxan matsa ba !

Tayi maganar cikin fushi tunda muka sauka garin nan kake wulakanta ni wai menayi maka ne??

Hawaye suka xubo akan idonta ,nan take jikin AY.yayi sanyi ta gefenta yabi ya wuce abinsa  ,wani irin kuka taji yaxo mata da gudu taje ta fada kan bed ,baxata iyaba ba wlhi baxata iya jure wannan wulakanci  nasa ba.

Maganar mamin tace ta fado mata Arai jawaheer shifa namiji dan tattali ne dole ki aje duk wani girman kai naki ki tarairaye sa tamkar yaron goye dole kiyi hakuri da wani wulakancinsa   na dan  lokaci ne ba lokaci daya maganin zaiyi aiki akansa ba basa Dan lokaci ne "kafin mu dawo kansa dolene kiso duk abunda yakeso.

da haka ta dinga tuna maganganun maminta motsin ruwa taji alamar ya fara wanka Kai tsaye ta nufi kofa ta saka key,

Jakar kayanta ta nufa ,wata ya'r karamar kwalbar ta fitarta Sai da ta cire rigar jikinta tabi lungu da sako ta shafe jikinta da turaren nan take kamshin turaren ya cika dakin a haka ta nufi kofar toilet tana sakin wani kayatattacen murmushi.

#HAWAYEN MARAICI

#AY MAI KEKE

#JAWAHEER

#MIMI

#ASMY B ALIYU

#***

#FOlLOW ME IN AREWAPEN @asmy b Aliyu.