KUNCIN ZUCI

Kuncin zuci

by @bintuuu

Lokacin da Ahmad ya kashe wayansa bayan ya gama fadin iya kacin kalmomin da yaga daman fada a Saddam din sai ya tsaya kawai yana staring into space, yasani Saddam yanason ganin bacin ran dake tafasa azuciyarsa a wannan lokacin, yasani Saddam yanason sanin ko Na'ima ce weakness dinsa, and that was it.. she was his biggest weakness in life, he just can't think straight when it comes to her, yasani son Na'ima wani iko ne na Allah da ke faruwa acikin rayuwarsa, domin a shekara biyu da suka wuce in an fada masa zai so mace har haka to zai iya yin shari'a da wanda ya fada din ma.

But it has come to this.

One look at her face and he was swept away like all the walls he built around his heart never existed, and he was greatful for it, and he will keep choosing her in this life and hereafter....
Yananan tsaye sai ga shigowan message din Mazzy, wasu numbers ne a jere sunkai biyar kuma kowanne special line, atake ya danna line na farko kuma cikin sa'a sai yashiga bugu daya aka dauka, wani budadden murya ce ta amsa daga daya bangaren, anutse Ahmad yace "It's me" Smoke yace "I know Boss, me za'a masa?" Ahmad yace "The Eos oil and gas dayake shirin budewa a Dubai, i want you to sabotage it, tempered all the papers, falsified all the documents, make him loose everything on his watch" smoke ya amsa da "Do i need to dragged his name too?" Ahmad yace "Zamuyi maganan wannan after this" dan yasani Saddam yafi son kudi akan martabarsa, so zeyi amfani da wannan shikuma, smoke ne ya sake cewa "Then it'll be done in two weeks" Ahmad yace "One last thing..ka hado min details na duk macen da yake hulda da ita" Smoke ya amsa da "Yes Boss" sai Ahmad ya cigaba "I'm sending all the expense bill right now, and name what you want after that" Smoke yayi murmushi yace "The Lambo at your garage dake gidanka na Toronto" Ahmad yace "Done..take it..it's yours..just make sure everything is done just the way i want it" Smoke ya amsa da "Done" sai Ahmad ya katse kiran yanajin nutsuwa na shigansa dan yasan dukiyar Saddam dake Dubai is as good as gone, guy din yasa shi yayi loosing billions last few months amma haka ya barshi bai taba masa tasa dukiyar ba yasa akan dan bubbuga masa shi kawai, And Now...Now the table has turned.

A wannan safiyar ranan Na'ima ta wayi gari almost physically alright amma zuciyarta har sannan yana mata nauyin tafiya kanon da Abba yace zasuyi, ji take kamar zazzabi ne ma yake neman rufeta, ganin yanayin Nafisa sai ta dauka itama tana taya ta tararradin haduwa da kawunnan ta ne, suna cikin yin breakfast sai ga Mami ta fito daga bangaren Abba ya qaraso gurinsu tace "In kun gama Abbanku yana nemanku" suka amsa da toh da haka Mami ta wuce kitchen sai Nafisa ta kalli Na'ima tace "Bobo kema kin kasa bacci ne jiya naji kina waya" sai Na'ima tace "Na farka ne" Nafisa tace "Nima na dade bacci bai ban wahala irin na jiya ba" Na'ima na kallonta tadanyi murmushi tace "Sannu" da haka suka yi shiru tareda qarasa cin abincin, da suka shiga falon Abban sai suka samu Faruk ma yana nan bai fita wajen aiki ba, gasu Al'ameen a gefe yana maganan komawansa makaranta da Abban kasancewan ya shiga final semester dinsa yanzu, Abba na sauraronsa yace "Zuwa yaushe ne tafiyan naka" Al'ameen ya amsa da "Ina tunanin next week ne Abba, amma zanjira in ga tafiyan Abu tukunna" Abba yace "Allah ya nuna mana, amma kasan tafiyar Abubakar zai dauki lokaci ba, so gwara kayi tafiyan ka so you won't missed a lot at school" Faruk ya qara da "Ai sai next month, kabari zan kiraka ka samemu acan din" sai Al'ameen ya amsa da toh sannan duk suka juya suna kallon Na'ima data zauna nan kusa da Nafisa aqasa kan carpet, gaishe da Abba su Na'iman sukayi ya amsa sannan suka gaisa da 'yan mazan gidan, sai Abba yace "Daughter zuwa jibi Saturday zamuje can Kano kinji" kanta a qasa ta amsa da "Toh" nan kuma zuciyarta ta hau bugu sai Abba ya dubi Faruk yace "Clear your schedules zamuje dakai, sannan mun sake magana da Baba jiya akan tare zamuje dashi da Ahmad" Faruk ya gyada kai tareda amsawa da "In sha Allah" Mami da shigowan ta kenan ta samu guri ta zauna itama, duk shiru  sukayi a falon kowa da abunda yake saqawa arai...
Har yamma Na'ima bata dawo normal ba, dan kwanciya tayi ma a daki ranan saboda yanda kanta ke mata ciwo ga Nafisa ta raka Mami gidan wata cousin sistern Mamin dake nan Abuja, kiran Ahmad ne ya shigo wayanta ta dauka tareda sallama ahankali, Jin muryanta yasa Ahmad cewa "Meya sameki?" ta miqe zaune akan gadon tace "Babu komai" yace "Tell me kinji" ta girgiza kai kaman yana kallonta sai ta sake cewa "I'm fine" calmly yace "Baba ya fadamin zamuje Kano zuwa jibi, karki sa damuwan hakan a ranki Babe" ahankali ta amsa da "Toh" sai ya sake cewa "Ko inzo anjima dear, you seems down today" ta amsa da "No, I'm fine kaina ke ciwo kadan kadan" yace "Then I'll come later to chat with you" sai tayi shiru bata amsa ba, Jin haka yasa Ahmad kwantar da murya yace "it's alright Na'eemah, i understand you need time to settle your mind about this journey, but don't think too much of it, everything is going to be alright kinji, I'll be there too" ahankali tace "Thank you Ahmad"  sai yayi shiru kafin yace "Na'eemah ki fadamin abunda yake damunki" ai nan hawaye ya fara zuwa mata idanu tace "Zuciyata tana bugawa da sauri, kamar lokacin da nake gidansa, i don't know how to face them Ahmad" sai kawai yace "Give me few minutes, I'll call you kinji" ta amsa da Toh sannan ta koma ta kwanta akan gadon tana Jin kuka na zuwa mata, tana na kwance shiru ba'a fi minti ashirin ba sai ga kiransa tana dagawa taji yace "Ina waje Babe" sai ta amsa da toh sannan ta miqe tareda daukan babban hijab ta fita daga dakin, falon Mami ta shiga bata sameta ba har dakinta sai ta sauqa qasa, nan ma bata samesu a kitchen din ba sai kuma sannan ta tuna sun ce mata zasu fita ashe, sai ta fita compound din ta fice wajen tana tafiya a hankali, tunda ta fito Ahmad yake kallonta ganin she looks so pale, kafin Na'ima ta qarasa sai ya miqa hannunsa daga seat din da yake zaunen ya bude front seat din , anutse ta shiga motan tanajin kamshinsa na cika motan gaba daya, sai ta juya ta kallesa , he was wearing white long sleeve ya cire necktie da suit din suna back seat, ahankali tace "Daga office kake" Ya dan gyada kai shima a nutse yace "Ina hanya muke wayan" sai tayi shiru batace komai, miqa hannu yayi ya kamo nata sai taji touch din nasa yau yana shiga jikinta kuma, his hand is so warm, bata ankara ba taga yakai hannun bakinsa yayi pecking sai ta juyo tana kallonsa, murmushi taga ya mata yana kallon idonta, sai ta samu kanta da maida masa murmushin, duqowa yayi gareta murya qasa qasa yace "Tell me how your heart is beating" ta girgiza kai tana duqar da idonta tace "Nadaina ji" sai yayi murmushi yace "Babe babu abunda zai faru kinji" ya damqe hannunta ahankali yace "I won't let anyone take you away" sai ta dago kanta tana kallonsa tace "It's not like that Ahmad" ahankali yace "Then what is it?" cikin sanyin murya tace "Guiltiness nakeji, like i've wronged them" yana kallonta yace "You haven't wrong anyone Na'eemah, they shud be the ones feeling that way but not you" sai ta gyada kai, again ya sake kai hannunta bakinsa yayi pecking sai ta fara qoqarin karbe hannun tana murmushi, ganin haka sai ya kamo dayan hannun yana murmushi yace "Toh ki kwacesu duka ingani ko zaki iya" turo cute lips dinta tayi tace "Riqon da zafi fa" sai ya dan fara dariya qasa qasa be bar kallonta ba, jin bece komai ba yasa ta kwabe fuska tana fadin "Da zafi fa, hannun ze min ciwo" sai ya sake hannun yana murmushi ya lakuci hancinta yace "Raguwa kawai" sai ta fara dariya batace komai ba, shiru suka sakeyi sai can Ahmad yace "Babe in muka dawo zan sake yin maganar aurenmu gurin Abba" sai tayi shiru alamun kunyan maganan takeji, ganin haka ya sa Ahmad duqowa ze mata rada a kunne tayi saurin bude motan ta fice tana murmushi, aikuwa nan yadan fara dariya shima yace "I just want to tell you something" tana tsaye a wajen motan ta girgiza kai sannan ta daga masa hannu alamun Bye bata bar murmushi ba, yana murmushi shima ya tada motarsa, sai yakai hannu backseat ya dauko wani babban leda mai cike da chocolates dasu biscuits masu tsadan gaske ya miqo mata, karba tayi tana godiya ahankali bai amsa mata ba da haka ta juya ta nufi gate din gidan, sai da ya jira shiganta gidan sannan yayi reverse yabar layin...

Bayan Ahmad yayi parking agefen motan Adam dake cikin babban parking space na gidan nasu sai ya fito hannunsa rataye da suit dinsa ko dauko briefcase din sa dake backseat beyi ba ya nufi side dinsu, a falon yasamu Adam zaune yanashan fura da nono me sanyin gaske, shima ya zauna kan sofa tareda duqawa yafara cire safan kafarsa, Adam yace "Mamma ta aiko Ummi ta duba ko ka dawo dazu, she was looking for you" ya gyada kai bayan ya gama cire safan sai ya kishingida ajikin kujeran yana jin gajiya na taso masa sosai, Ahankali ya dubi Adam yace "It was Saddam" sanin me yake nufi yasa Adam ajiye cup din nasa kan glass table yana dan ware Ido yace "That idiot?" Ahmad ya gyada kai sannan yace "Ban yarda shi kadai yayi ba, it takes two...in a situation like this" Adam yace "Abunda ya fara zuwa kaina nima, wannan karon ko me ka masa bazance komai ba saidai in tayaka, the guy is lunatic wallahi, tayaya ma zai fara tunanin wannan shirmen, wawa kawai" shiru sukayi sai Adam ya sake yin tsaki yace "Kaii guy dinnan wawa ne" sai Ahmad ya sauqe numfashi yace "The pictures are not my main problem, we're living in a world where Edits and Ai took lead on mostly everything, is the note I'm worried about, she didn't left home on her will, she was forced to left" Adam  yace "And she made the right choice, because in da ta zauna then it's either dan kwayan can ya kasheta ko kuma tayi suicide, the pain is too much Man" nan jikin Ahmad ya sakeyin wani sanyin yanajin duk kofofin zuciyarsa na qara buduwa da tausayinta, what if she stays, what if Bilal keep assaulting her, what if he keeps raping her...Ya Allah.

Bayan Ahmad yayi sallahn maghrib tareda mahaifinsa sai suka bisa Falon sa shida Adam, nan suka gaisa yace dasu su shirya gobe Friday zasu rakasa wani taron daurin aure acan Kanon in yaso zuwa Saturday sai su qarasa can gidansu Na'iman da safe su samu su Abban, cikin ladabi suka amsa masa sannan suka hau hira jefi jefi while Baban yana kallon news, Ahmad ne ya fara miqewa zaije gurin Mamma, a falonta ya sameta tana zaune akan carpet as usual dan Mamma mutanen nan ne da basu cikason zaman kujera ba, nan qasa ya zauna a kusa da ita  suka gaisa, bayan ta amsa masa da "Lafiya Alhamdulillah" sai a anutse tace masa "Mahaifinka ya fadamin sunyi magana da Abbanka akan kana neman auren Na'ima" ahankali yace "Eh" sai ta gyada kai tace "Ma Sha Allah, abu ne mai kyau hakan, Allah yayi jagora, Mamin tazo nan munyi magana, ta fadamin komai game da yarinyar" Ahmad yayi shiru bai ce komai sai ta cigaba "Sun mata ba daidai ba, yarinyar na da hakuri" sai Ahmad ya gyada kai ahankali yace "Ya kusa raba ta rayuwanta ne Momma" tace "Duk ta fadamin komai, Allah kuma yana gani ai, hakurinta zai zame mata riba tun a duniya, sai kaima kayi mata riqon Amana, Ahmad ko da wasa karkayi amfani da hakurinta ka cutar da ita a rayuwa dan bazaka ga daidai ba, mutane irinta are rare to find in this period of time, ba kowacce mace ce zata dauki cin zarafin da ta dauka ba, sai ka dubi Allah ka riqeta da Amana, dan duk ranan da ka kuskura ka wulaqanta ta ni da kaina zan shige mata gaba gurin karban haqqinta, hakurin ta yayi representing kyawun halinta dan haka ban yarda watarana kaga hakan as an opportunity da zaka musguna mata ba" ya amsa da "In sha Allah Momma" tace "Allah yayi jagora, yanzu sai kun dawo dinne za'a koma neman auren kenan" sai yace "Eh da haka nake tunanin Abban yake nufi" ta gyada kai tace "Allah ya nuna mana" ta sake cewa "Kasha furan da na aika mukun ne" yace "Sai na koma zansha" ta gyada kai da haka suka kama wata hiran jefi jefi, sunanan zaune sai Adam ya shigo shima anan qasa ya zauna suka gaisa da Mamman, ba'a dau mintuna ba sai ga Laila ta shigo dakin cikin sallama, tasha babban hijabi har qasa, Mamma ta dubeta tana murmushi tace "Wata sabon gani Laila"
Laila na murmushi ta zauna a gefe tace "Ina wuni Mamma" ta amsa da "Lafiya, yasu mummyn naki" tace "Lafiyansu, tace in baki gaisuwa ma" "Ina amsawa" sai Laila ta juya gurin Yayun nata idonta akan Ahmad tace "Ina wuni Yaya" casual ya amsa mata da "Lafiya" sai Adam ne ya qara da "Lafiya, ya mutan gidan?" tace "Lafiya" sai Ahmad ya miqe tareda yi musu sallama ya fita, part dinsu ya tafi, anan falon ya zauna, sai can kuma ya miqe ya qarasa dining area din nasu ya debo fura me sanyi a cup, be kaiga sha ba yaji ana kwankwasa kofan falon ahankali, yasani biyosa tayi sai bai kula ba ya zauna a kujeran tareda daukan remote ya chanja tasha, bude kofan falon akayi Adam yashigo yana fadin "Meye kin tsaya a kofa kuma, haka kikeyi da can" tace "A'a Yaya naji kamar kofan a kulle ne fa" sai Adam ya gyada kai tareda wucewa upstairs, Ahmad na zaune a falon idonsa akan tv yana sipping furansa hankali kwance, sai Laila ta qaraso tareda zama a kujeran kusa dashi ahankali tace "Yaya kayi hakuri, kaga yau sai da na fara shiga cikin gidan ma" ta qarasa maganan tana kallonsa kamar ta koma kusa dashi takeji, har sannan be juyo ba idonsa na kan Tv sai kallonsa Laila take, aranta tana ayyana yanda Ahmad yayi daidai da tsarin rayuwanta, yayi daidai da burikanta, yayi daidai da irin halittan da takeso ga namiji, juyowa yayi suka hada Ido sai tayi saurin dauke kai, ajiye cup din yayi akan table yana kallonta yace "Sai dan ni zakije gaishe da iyayenki Laila?" ta juyo tace "A'a Yaya, ai wai in fada maka na gyara ne, kar kace banajin maganan ka" ganin bata gane maganan da ya matan ba yasa shi sassauta murya yace "Ke hankalinki bazai baki kije gaishe da iyayenki ba sai an fada miki, meyesa bakida tunani ne wani lokacin?" tace "Amma Yay.."  "Zan makeki" yafada kafin ta qarasa maganan nata, sai ya sake cewa "Get out" rai a bace tace "Wai meyasa kakemin haka ne Yaya Ahmad" yana kallonta bece komai ba ta marairaice "Kai duk qaunar da zan nuna maka baka gani dan Allah, komai nayi laifine a gurinka, Ina mace fa nake neman ka aureni Yaya meyasa bazaka ga hakan ba" anutse yace "Yaushe na zama sa'an wasanki" tayi shiru yasake cewa "Yaushe irin maganar nan ya taba shiga tsakanina dake?" kafin tayi magana yace "Tashi ki fita daga falon nan" tace "Amma Yaya kasan inason ka" yace "Fita ko in karyaki yanzun nan" ganin yanayinsa yasa ta miqewa jiki a sanyaye ta nufi fita daga falon, Ahmad ji yayi ransa na baci a wannan lokacin, duk shige da ficen ta a Abuja wanne ne ma bai sani ba, lallai zai taka mata burki tun wuri kafin maganan taje kunnen iyayen su...