Kuncin zuci
by @bintuuu
Ranan Saturday tunda sassafe Mami ta shigo dakin Na'ima dan ta dubata ko ta tashi, amma shiganta sai taga Na'iman zaune agado, sai ta qaraso tana kwantar da murya "Habibti nah barka da safiya" Na'ima tayi murmushin dole ta amsa da "Ina kwana Mami" sai Mami ta zauna gefenta tace "How was your night dear" tace "Alhamdulillah" dan kallonta Mami ta tsaya yi sai takai hannu tana shafa kanta tace "It's going to be alright Habibti" Na'ima ta gyada kai tana yin murmushin sai Mami tace "Toh tashi ku shirya kinji, it's a morning flight" Nafisa ce ta shigo dakin hannunta riqe da cups of coffee guda biyu ta qaraso ta miqawa Na'iman tace "Morning" karba Na'ima tayi ta amsa da "Kin tashi lafiya" sai Mami tace "Baby karku bata lokaci, kinsan Abbanku zeyi magana" tace "Yes Mami" da haka Mamin ta fice sai Nafisa ta dan tsaya kallon Na'ima, juyowa tayi tace "Meya faru" Nafisa tace "Nima sai yanzu na fara jin fargaban tafiyan sis" sai Na'ima tayi murmushi tareda kamo hannunta kawai dan itama fargaban ne fal a zuciyarta...
Karfe 8 jirginsu Na'ima ya tashi zuwa Kanon dabo, within hour daya suka isa, drivern gidan Abba dake kanon ne yazo shida wani yaron Abban cikin motoci guda biyu suka daukesu, Abba ne yace gidan Alhaji Abdullahi zasuje tukunna dan yayi waya da Baba shima zasu qarasa can ba da jimawa ba, Na'ima dai jinsu kawai take amma hankalinta duk baya jikinta, har wani rawa takejin jikin ta nayi, gashi zuciyarta sai tsananta gudu takeyi, Mami ce ta kamo hannunta ganin kamar rawa yakeyi, juyowa Na'ima tayi sai Mamin ta damqe hannun alamun bata reassurance, Nafisa ma sai kallon Na'ima take tanajin nata zuciyar na tsinkewa itama, dan duk wani alamomin tsoro sun bayyana akan fuskan Na'iman, tasani bawai bada ita su Mamin zasuyi ba tunda sun fada, Amma tana shakkan haduwa dasu Hajiya, karma azo ga kawunan ta na qauye in suka hadu da ita a agaba, cikin hour daya suka qarasa unguwar Alhajin suka faka a kofan babban gate din gidan Faruk ne yayi magana da maigadi akan ya musu sallama da maigidan bai dade ba yadawo yace dasu wai su qarasa yana ciki, basu kaiga shiga ba saiga motan su Baba ta shigo layin, Ahmad ne ya fara fitowa tareda budewa mahaifinsa back seat din da yake zaune ciki, sai su Faruk suka qarasa garesa ya fara takowa anutse Abba na isa garesa, musabaha sukayi sannan suka dunguma gaba daya, Na'ima ji take kamar ta shige jikin Mami Ahmad na lura da ita, a main falon gidan dake downstairs megadin ya musu iso, shigansu suka tadda Alhaji, Hajiya, Ayuba, Nasir, ga shafa tana ajiye ruwa agabansu Ayuba, duk miqewa sukayi Amma banda su Ayuba da ba wani shock sukaji ba, mamakinsu ma shine ganin Na'iman tareda manyan mutane attajirai haka, Hajiya tace "Innalillahi wa inna ilaihi rajiun, dama sune baqin, Na'ima... Na'imaaa" sai Na'ima ta buya a bayan Mami ta fashe da kuka, cikin bacin rai Mami tace "Ai de kya bari mu zauna ko" Abba yace "Fatima" tace "Toh sai ta bari mu zauna ai kafin ta gigita yarinya" Hajiya ta daga murya "A'a baza kuzo har gida kawo mana 'yar bariki ba kuma kuce nayi shiru, Abdullahi kana jinsu dai ko" Alhaji yace "Jira muji me sukazo fada bayan boye yarinyar da sukayi" Ahmad kamar ya wankawa Hajiya mari haka yaji a lokacin sai ya danne ganin Mahaifinsa ya shanye komai fuska a sake, Ayuba ne ya miqe rai abace yace "Wannan ba mutunci bane Abdullahi, koma meye ne ai zamu jira muji meke tafe dasu, tafe suke da amanar da Yusuf ya bar mana muka kasa riqewa fa" bude baki Abdullahi yayi cikin tsawa yace "Ni zaka fadawa amana, gatanan" ya nuna Na'ima "Babu abunda bamu mata ba na gata, amma haka tasa qafa ta take sannan tayi choosing ta shiga duniya" rai abace Abba yace "Wallahi in ka sake magana makamancin wannan sai nayi shari'a dakai" Nasir yace "Dakyau" Hajiya tace "Ku bamu yarinyar mu, mungode da riqetan da kukayi" Na'ima ta sake fashewa da wani kukan sai kawai Ahmad ya juya ya fice daga falon, Baba yayi murmushi yafara takawa cikin falon
Ayuba ya qarasa garesu shida Nasir suka fara musu iso, Alhaji sai binsu da wani irin kallo yake, Ayuba ne sukayi leading din su Baban ga kujera Abba na gefensa, Mami da ranta yayi qololuwan baci itada Nafisa suka nemi guri sai Mami ta sake riqo hannun Na'iman tana hararan Hajiya dake tsaye, itadai bason azaunan take ba shiyasa ta tsaya a tsayen tanajin zuciyarta na dar dar, sai duk maganganun data shirya kitsawa domin zuwan rana kamar hakan duk suka watse daga kanta ma, Baba ne ya dubeta a tsanake yace "Mamana ki zauna, maganar fahimta ce tafe damu" batakai ga zama ba wayanta yayi qara akan table ta miqa hannu ta dauka bata duba ba ta zauna a gefen Alhaji, wani saqon ne ya sake shigowa wayanta ta dago tana dubawa, wani irin bugawa zuciyan Hajiya yayi sai da jinta ya dauke na wasu sakkani tana kallon wayan sai Baba yace "Ina Ahmad" yana duban falon, Adam yace "An dan kirasa a wayane" yace "Yayi hakuri da wayan nan tukunna" sai ya juya gurin Abdullahi yace "Bawan Allah magana ce ke tafe damu, amma zamuso ace danka yana dakin nan yanda komai zaifi zantuwa" Abdullahi yace "Yaro baya gari" Baba ya sake cewa "Duk bata baci ba, da farko dai menene alaqar ku da yarinyar dake zaunen can" Abdullahi ya kalli Na'ima data sunkuyar dakai har sannan jikinta na rawa, a nutse yace "Yata ce, yar dan'uwana ce" Ayuba yace "Kwarai kuwa, yarinya ciki daya muka fito da mahaifinta" sai Abba yace "Amma kuna da labarin rayuwar da tayi bayan ta baro gurinku?" Abdullahi ya riga amsawa da "Bangane maganar ku ba, Alhaji ya zaku zo har cikin gidana kunemi cimin zarafi ne wai" Abba yace "Mu bamu nemi cin zarafin ka ba, yarinyar da danka ya ciwa zarafi mukazo biwa haqqinta" Abdullahi zeyi magana sai Hajiya ta miqe da sauri jikin ta na rawa tace "Kuyi hakuri bayin Allah bari akawo muku ruwa" ta miqe da sauri, sai kuwa wayanta tafadi daga jikinta tayi sauri duqawa jikinta yana rawa ta dauka, dagowan da zatayi tayi ido hudu da Ahmad daya dawo cikin falon, gabanta ne yayi wani mummunar faduwa, Abba yace "Ki zauna ayi magana tukunna ke duk a rude kike ma" Ayuba yace "Dole zata rude ai tunda ita tayi riqon yarinyar har ta gudun" Hajiya ta saqqo qasan Carpet tace "Wallahi kome ya faru ba da son rai na bane, son zuciya ce ta jawomin komai, Na'ima ki yafemin" Abdullahi dake kallonta confusedly yace "Me kike cewa ne" Mami tace "Azaban da tasan sun ganawa yarinyar take neman yafiya akai, Alhaji ga yarinyar ka nan wadda matarka da danka suka kusa kaita lahira mun dawo maka da ita kaji komai daga bakinta, duk wani fada da tashin hankali ba naku bane dan wallahi nayi rantsuwa in kukace ba haka ba saidai mu hadu a kotu, yarinya kuma bazamu bada ita ba" Abdullahi yayi stiff yana bin baqin da kallo sai Abba yace "Alhaji Abdullahi kayi riqon Na'ima a lokacin da bata gata sai na Allah, Allah yaga zuciyar ka na son inganta rayuwarta amma kayi kuskure ko ince kunyi kuskure, ko da ba wani abu kukayiwa yarinyar nan ba, ko da ace laifinta ne na barin gidan da tayi to da naku laifin, da laifinku matuqa, ga tanan a gabanka tafada maka da bakinta abunda iyalinka suka mata, gatanan ta bude maka tafin hannunta kaga yankan da suka mata, ta bude maka har bayanta kaga irin izayar da suka gana mata, karfe ukun dare ta je gidana ranan da ta bar Kano cikin babbar motan kayan kamfani, a yanda yarinyar nan ta shigo min cikin gida karfin zuciyace tasa ban zubda hawaye ba, wane irin rayuwane wannan, ace yarinyar ka tana going through such extreme violence ahannun danka amma ace ko da sau daya baka taba maida hankali ka lura ba, baka taba maida hankali kaji damuwar yarinya ba, sai ranan da ta mutu kuma kazo kace kayi iya kokarinka akanta kenan, tunda kake sau nawa ka taba kiranta kaji matasalanta, sau nawa ka taka kaje gidanta domin dubo lafiyar amanar da ka dauko, sai da komai ya rikice bayan mun dawo da ita mu sanar dakai komai sai kace mun riqe maka yarinya..this is so shameful of you Abdullahi, so shameful" Baba ya girgiza kai yace "Baka kyauta ba Abdullahi" ya kalli su Ayuba "Har daku ma, amma bari muji ta bakin yarinya, bari ta sanar dakai duk abunda ya faru sai ku duba ku gani ku damu su waye masu kuskuren aciki" Ayuba ya fashe da kuka Nasir ma haka, yace "innalillahi wa inna ilaihi rajiun, 'yata Na'ima fada mana duk abunda ya faru kinji, ki fada mana komai dan Allah" Na'ima na kuka ta sauqar da kanta sai Abba yace "Daughter ki fada musu tun daga farkon zuwanki gidannan har zaman gidan aurenki, iyayenki ne karki ji nauyinsu, karki boye musu komai, kina da 'yancin fadan komai dakika riqe a zuciyarki" budar bakin Na'ima sai ta kalli Alhaji tace "Abba tun daga gidan nan yafara dukana, har dakina yake zuwa da daddare, da nace zanyi masa ihu ranan yafara dukana" kawai kuka yaci karfinta, Ahmad kansa na qasa yanajin zuciyarsa na karyewa, Nafisa ma sai hawaye, Hajiya tunda ta duqar da kanta jikinta ke rawa bata dago ba har sannan, Mamice ta riqo hannun Na'iman cikin lallashi tace "Sai me kuma Na'ima, fadi komai kinji" sai Na'ima ta sake duqar da kanta tafara basu labarin izayar da Bilal ya fara gana mata tun tana gidan, taqarasa maganan da "Shi yace in zo na fada muku afasa auren in ba haka ba wai I'll be doom for life a gidansa, wallahi bana sonsa Abba nima bana sonsa, ranar da ya dawo gidan bayan wata ukun nan da mace yadawo gidan suke rayuwa a dakinsa" Abdullahi ji yayi kamar an kwara masa ruwan kankara ajiki ahankali yace "Na'ima mace fa kikace" sai ta gyada kai tace "Wallahi Abba, Hajiya ta sani, ranan danazo da safe gurinka a compound ba faduwa nayi abandaki ba kamar yanda tace, shi yamin duka, duka na yayi cikin dare bayan yadawo acikin yanayin da yake dawowa agidan nan" Baba sai kallonta yake ganin yanda jikinta yake rawa fuskanta tayi ja, Ayuba yace "innalillahi wa inna ilaihi rajiun" Nasir yace "Na'ima kiyi hakuri ki yafe mana, munyi kuskure da wofintar da rayuwarki" cikin sanyin murya Abdullahi yace "Hasbunallahu wa ni'imal wakil, Ladi fada min me yake tafiya a gidana kika boyemin" Sai Hajiya ta fashe da kuka tace "Kayi hakuri Alhaji, bani da bakin magana, wallahi kome ya faru nasani son zuciyata ne ya jawomin" sai Mami tace "Ai baka gama jin komai ba Abdullahi, ka jira kaji sauran ukuban da suka nuna wa Na'ima, kaga qannenka nan dake zaune, har gida taje ta fada musu, amma makirar matar ka taje har can ta dawo da yarinyar, Na'ima fada wa babanki komaiii" nan cikinsu Ayuba ya duri ruwa suma, Abdullahi na kallon Na'iman ya miqa hannu yace "Zo gurina Na'ima, zo ki fadamin kinji, Allah ya huci zuciyarki, na miki laifi, na miki laifi wallahi" sai Nafisa ta kamata suka miqe ta qarasar da ita gurin Alhajin su Ahmad na kallonsu, kamo hannunta yayi ya zaunar da ita kusa dashi yace "Ranar nace kuje asibiti da Bilal din, me ya miki bayan nan" kanta a duqe tace "Buga kaina ya rinqa yi a dining table yamin duka, Abba bana iya tafiya ranan, cewa yayi sai ya kasheni saboda nazo in fada maka dukan da yakemun" ta fashe da wani kukan Abdullahi ya damqo hannunta hawaye na kawowa idonsa yace "kiyi hakuri kinji daughter, fadamin yanda ya miki yankan hannun" nan Na'ima ta fara basa labarin rayuwanta da Bilal a gidan, da tazo inda Stella ta tura ta daga stairs sai da kowa na falon yaji zuciyarsa ta karye, Baba yace "Hasbunallah" Na'ima ta fadi yanda taje qauye kauye after that dakuma yanda sukayi da kawunan ta har Hajiya ta dawo da ita, Abdullahi yace "Ayuba kun ci amanar jini, wannan magana kunsani ba wai Ladi ce takeda ikon zartar da komai ba amma kukasa son zuciya aranku, wallahi sai Allah ya min hisabi daku" sukace "Ga tanan ta fada maka, maganar da ta fada mana acan ko kusa batayi kamanceceniya da ta bakin Na'ima ba" Hajiya tace "Wallahi nayi hakan ne dan kar ka raba auren nasu Alhaji, dan tunani na Bilal ze iya shiryuwa ta dalilinta" Kowa afalon sai da ya kalli Hajiya jin wannan furucin son zuciyar da ya fito daga bakinta, Ayuba yace "Aure kamar an rabashi ne ma" sai Abba yace "A gadon asibiti danku ya saketa tana cikin halin ha'ula'i" Abdullahi was shocked at that point sai ya dubi Hajiya a gigice yace "Me kikacemin lokacin" tana kuka tace "Wallahi nima sai da ya saketan sannan yazomin gidan nan, abokinsa Nasiru ne ya haike mata a dakinta ranan, Alhaji taya zan fara fadan wannan maganan" tasss Abdullahi ya dauke Hajiya da mari a falon, jikinsa har rawa yake yace "Yar tawaaaa....wani yaje har gidan aurenta zai keta mata haddi kice bakisan ta yadda zaki fadamin ba, Ladi dama ke mahaukaciya ce ban sani ba" Baba yace "Ka kai zuciya nesa, banda kai hannu kuma, ba muzo dan mu bata goma biyar bata gyaru ba" rai abace Abdullahi yace "Alhaji kanajin fa abunda take fadamin, ace duk wannan abubuwan sun faru amma kaf ta boyemin komai, tunanin me take kenan" Mami ta tabe baki dan jira take asake kai wani marin a Hajiya, matasan nan dai har lokacin suna zaune suna sauraren komai bakinsu duk a liqe ba mai magana sai ido, Abba yace "kadai yi hakuri, banda dukan..ba mutuncinka bane" Hajiya na kuka bilhaqqi takasa magana, sai Abdullahi ya kalli Na'ima dake kukan itama yace "Ya akayi har kukaje asibiti, sai Na'ima ta kasa magana tana kuka, ahankali Nafisa tace "Tun kafin wannan ma budurwarsa ta dauko wuqa zata kasheta, ranan nida Al'ameen ne muka kaita asibitin" ta kalli Mami tace "Washegari ma Mami taje dubata itama" cikin zaquwa Abdullahi na kallon Nafisa yace "Yarinya fadamin me ya faru kinji" nan Nafisa ta hau zubo nata sharhin, har gurinda Na'ima ta manta bata fada ba sai da ta fadosa kowa na sauraronta cikin sanyin jiki, har alluran nan saida ta fada amma batace sai sunzo mu'amala yakewa Na'iman ba kawai ta fada musu yana yiwa Na'ima allurai da suke sata bacci sosai....Sai da Abdullahi yagama sauraron komai sai ya sake kamo hannun Na'iman yace "Ki yafe min Na'ima, kiyi hakuri da duk abunda ya faru, munyi kuskure" Nasiru yace "Kiyi hakuri Na'ima" Abdullahi na kallon mutan falon yace "Nagode, Nagode sosai" ya dubi Abba yace "Nagode bawan Allah, wallahi bansan da wani kalman zan muku godiya ba, kun mana babban halacci da kuka kula da yarinyar mu, babu kalman da zamu iya gode muku da ita, shi yaro me hakuri daman a kullum shi akafi dannewa, yanzu da Na'ima yarinya me maganace da wani zancen mukeyi, Allah yaga hakurinki Na'ima shiyasa be bari kin salwanta ba da kika tafin, in sha Allah zamuyi iya qoqarin mu wajen gyara wannan kuskuren da mukayi, Allah ya yafe mana gaba daya" sai duk aka amsa da "Amin" Baba yace "Alhamdulillah, dama magana irin wannan zama take buqata dan a fahimci juna sannan a warware komai, sai dai muce Allah ya kiyaye na gaba, wannan yarinya kuma bawai mun kawo ta bane da nufin mun dawo muku da ita" sai Abdullahi yayi saurin cewa "Alhaji wallahi bani da bakin cewa ku bani Na'ima yanzu, kunada ikon riqe Na'ima" sai Ayuba yace "Babu abunda zamuce muku sai dai Allah ya biyaku da mafificin Alkhairi, duk mutumin da zai riqe maka naka da Amana batareda da ya sanka ba ai ya wuce komai" Abba yace "Yanzu Ina shi Bilal din yake" Abdullahi yace "Yau watanmu kusan biyar bamu sashi a ido ba, zuwa yanzu wayarsa ma bata shiga, Alhaji ina cikin jarabawa...ni kaina godiya nakewa ubangiji kawai aduk lokacin dana dubi halayen yaron nan" ya qarasa magana cikin rawan murya, Hajiya har da qara qarfin kukanta a falon, Baba ya girgiza kai tareda fadin "Hasbunallah, Allah ya shirya mana zuri'a" Abdullahi yace "Amin...Amin ya Allah, bazanyi musu ba akan duk abunda aka cemin Bilal yayi, mu muka rainesa akan turban da bata dace ba, shiyasa nake hamdala ga ubangiji ayanzu dan nasan hukuncin kuskuren mu muke karba" Hajiya kuka take bilhaqqi a falon dan ita kadai tasan kukan me takeyi, Baba yace "Tun da ka karbi jarabawan kuma ka godewa ubangijin, kagama komai kuma, insha Allahu komai ze wuce kamar ba'ayi ba, Allah ya shirya mana su da mu din gaba daya" duk aka amsa da Amin, nan suka jiyo kiran sallah zuhur a masallacin dake gefen gidan Alhajin, sai ya kalli Hajiya yace "Ki miqa matan sama, mu zamuje sallah" nan Hajiya ta miqe tana share hawaye sai Alhaji ya kalli Na'ima dake gefensa yace "Na'ima ku kaisu suyi sallah ko" ta amsa da Toh a hankali, itama ta miqe tareda su Mamin, Hajiya na gaba suka bi bayanta suka bar mazan na qoqarin miqewa, da Hajiya ta nemi su qarasa dakinta suyi sallan sai Mami tace zasuyi anan falon, nan ta gyada kai ta wuce dakin nata da saurin dan kawo musu darduma, Na'iman ce ta nuna musu bandakin dake nan falon Mami ta shiga sai Nafisa ta zauna a gefenta tace "Bobo in an tambayeki ko zaki zauna dan Allah kar kice "Eh" Na'ima na murmushi tace "Toh sis, zance musu kince nace musu A'a" Nafisa na murmushi tace "What?..kima zauna, kinsan su Al'ameen tsaf zasu biyoki ai, to wai tayaya ma zamu fara zaman hira babu ke a gidan" kafin Na'ima tayi magana sai ga Hajiya ta fito daga dakinta riqe da babban darduma me laushin gaske, miqewa Na'ima tayi zata karba sai tace "Kibarshi" Na'ima ta sake miqa hannu ta karba tareda shimfidawa, sai Nafisa tace "Hajiya zan sha ruwa" ta amsa da "Toh, bari na kawo muku" da haka ta fita daga dakin...Bayan su Na'ima sunyi sallah sai ga shafa ta shigo da abinci wanda Alhajin ne yasa Sufi siyowa a restaurant kasancewan ba'a samu lokacin yin girki ba, tana ajiye wa ta zauna kusa da Na'iman kamar zatayi kuka tace "Allah sarki Na'ima, da rabon zamu sake haduwa" Na'ima ta gyada kai idonta a qasa su Mami dake zaune gefe na kallonsu, sai shafa tace "Sufi yace in fada muku zai shigo ku gaisa" Na'ima tace "Toh" sai shafa tace "Sannu Na'ima, sannu yar nan, jiyan nan ma saida na gyara miki dakinki wallahi" wuf Nafisa tace "Ai ba zama zamuyi ba har itan" shafa ta juyo tace "Ayya tare zaku koma kenan" Nafisa tace "Eh mama" sai shafa tayi shiru ganin amsan Nafisan babu sakaya acikinsa, miqewa tayi ta fita sai ga Hajiya sun shigo da sufin, qarasowa yayi suka gaisa da Mamin sai Naiman suka gaishesa ya amsa tareda cewa "Naima how have you been?" kanta a duqe tace "I'm fine" yana kallonta cikin tausayawa yace "Welcome back home Na'ima" ta gyada kai kawai, Hajiya ce ta zauna kusa da Mami tace "Hajiya ga abinci kuci du Allah" Mami tace "Mungode" ganin fuskan Mamin ba'a sake ba sai ta miqe ta fita dan kaiwa mutan can falon nasu abincin.
Anan main falon gidan bayan mazan sun dawo daga masallaci sai Hajiya suka fara fito da abincin itada shafa suna jerawa anan tsakar falon, dan hira manyan suke kamar ba yau suka fara haduwa da Alhajin ba, sai da suka ci abincin wanda sama sama kowa ya taba nan ma aka cigaba da magana, cikin hiran Alhaji yace "Ma Sha Allah, so she has completed her Masters now" Abba yace "Yes, tareda yar gurina sukayi a Oxford university" Alhaji yadan ware ido in amazement, sai Abba ya cigaba "Takardan aikinta ta fito a CBN yanzu haka, amma verifications dinta ne bai kammalu ba, zuwa Monday dinnan zata je suna nemanta" Ayuba yace "Alhamdulillahii, shi CDM din acan Habujan ne kenan" Faruk yana murmushi yace "Eh, babban bankin Nigeria ne gaba daya" Nasiru yace "Allahu Akhbar" Ahmad dai har sannan bece komai shida Adam dake zaune gefensa, Ayuba yayi ta zubo addu'o'i asu Abba kamar bakinsa zai yanke suna amsa masa, sai da Aka nutsu Abba yayi gyaran murya yace "Alhaji Abdullahi tafe nake da wata maganan bayan wadda muka gama dazu" Alhaji na murmushi yace "Muna jinka" sai ya dan gyara zama yace "Idan babu damuwa, Ina neman hannun yarku Na'ima ga dana Ahmad gashinan zaune" duk suka juya suna kallon samarin cikin fara'a Alhaji yace "Ma sha Allah wanne daga cikinsu, dan duk suna yanayi ma" Ayuba har hannunsa na qaiqayin kamar zai nuna Ahmad yace "Wanda yafi hasken" sai yayi shiru dai yana ta fara'a, Abba ya nuna musu Ahmad dakansa ke duqe yace "Wannan ne" sai ya kalli su Abdullahin yace "Ina wakiltarsa gurin neman auren Na'ima a wajenku" Baba na murmushi sai sannan yayi magana "Kai dai da shirinka kuka hado baki da dan naka kenan" Abba yana murmushi yace "A'a faduwa ce ta zo daidai da zama, haka Allah ya tsara" Ayuba da Nasiru suka hau fadin "Masha Allahu, ai mu ba abunda zamuce, dattakon ku kadai ya wakilci halin dannan naku, wallahi Na'ima dai mun baku ita ko yanzu kuka shirya da sadakinku zamu baku aurenta" Abba ya jinjina kai yace "Alhamdulillah" ya juya yana kallon Ahmad daya duqar dakai zuciyarsa na tsananta bugu, Sai Abba ya sake juyawa gurin Alhaji yace "Ba muji ta bakinka ba Alhaji" sai yace "Wallahi kunya naji, ni nabaku ikon yin duk abunda kuga ya dace akan Na'ima, kuma iyayenta ne" sai Baba yace "Ai har abada kai Uba ne a gareta, duk iyaye kuke gurinta babu abunda zai chanja hakan" Alhaji yace "Mun baku auren Na'ima, ko yanzu kukeso a daura sai adaura a masallacin tunda la'asar ta gabato" sai duk mutan falon suka amsa da "Alhamdulillah" Ayuba da Nasiru bakinnan har kunne, Adam na murmushi ya juya yana kallon Ahmad da har sannan kansa aduqe yanajin wani sanyi na taso masa tun daga qasan zuciyarsa, Abba ne ya tambayesu nawa suka yanke sadakin, sai sukace kawai su kimanta yanda zasu iya biya, Abba yaciro wayansa ya karbi details din Alhaji Abdullahi atake yayi musu transfer na 2 million as sadakin Na'ima, daga nan kuma masallaci suka dunguma gaba daya sukayi sallah, sai da aka idar da sallah sai liman yayi sanarwa ga mutanen cikin masallacin akan akwai daurin Auren da za'ayi yanzu....Abangaren su Na'ima kuma, bayan Mami ta gama sauraron maganar da Abba ya mata a waya sai ta ajiye wayan tana murmushi ta juya tana kallon Na'ima dake magana da Nafisa, wani irin farin ciki takejin na lullube ta, Hajiya na zauna gefenta zugum da ita itama tana kallon yanda Na'iman da tasani ada ta chanja mata ta kowanne fanni, dan dakatawa da maganan su Na'ima sukayi dalilin jiyo maganganun da ake a speaker na masallacin, sai zuciyar Na'ima ta tsananta bugu jin ana sanarwan aure, Nafisa ma ta ware Ido da mamaki takamo hannun Na'iman, sai da Na'ima ta daskare alokacin da taji ance "Ma Sha Allah jama'a ku shaida Aure ya dauru tsakanin Ahmad Umar Wadzani da Na'ima Yusuf Dabo akan sadaki miliyan biyu"....
Don't forget to share your thoughts on the readers lounge, follow my account, and share this book with others😊🤍
Bintu Musa ✍️ 📚