KAFAR HAGU

2

by @meenatyandoma

*'KAFAR HAGU*

©️Meenat A. 'Yandoma

MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION

🅿️age 2
... Ɗaya daga cikin mutanen da suka kawo Rauda ne ya fara magana a matukar fusace. "Allah wadaran wannan gida. A kawo diyarku magashiyan rai hannun Allah, amma ki saka ƙafa ki tafi neman goro. Shi iliyan yana ina, domin ni dai ba domin zuciya ta imani babu abin da zai tsayar da Ni a wurin nan" wani magidanci ne yayi karaf ya amshe maganar. "Yana da inda ya wuce wurin da ya fiye masa ko ina wato wurin cacarsa. Kunga bayin Allah ku shiga gidan nan ku aje yarinyar nan ai iyakar taimako kunyi mata. Ina jiye maku wannan mahaukacin Oga Gaga ya iske ku. Tsaf zai ce kune ku ka yi mata haka, don haka kuyi gaggawar kaita ku aje. Ni dai kunga tafiyata" Cikin gaggawa suka shiga da Rauda ciki tare da juyowa. Kiciɓis suka yi da Gwoggwo "bayin Allah ya haka? Daga ina kuke me ya shigo da ku gidan nan. Mutanen gida kuna ina?" Ganin zata tara masu mutane ya saka daya daga cikinsu ya yi mata bayani. "Ina wanda ya banketa ya ke? Ina kuma goron da aka yi ɓarinsa, ai Ni yau shar" Ba su yi mamakin jin abin da ta fada ba domin kaf ƙauyen kowa ya san halin mahaifiyar Iliya wato kakarsu Rauda. Don haka ba su bata amsa ba fa ce ficewa da suka yi a gida. 
"Ka ga lalatattun yara. Kai kira mini Iliya ta fadawa Shaho da shigowarsa kenan gidan." Kinga gwoggo ni ki daina sakani cikin harkar yarinyar nan. Domin bisa Gaga bama ga maciji da juna. Muddun kuma aka ce za a rika sakani cikin harkokinta to lahira ce zata yi bako. Don tsaf zan zama ajalinta" 
Rass! Gaban gwoggo ya yanke ya fadi.  "Amma kai dai anyi lalataccen. Yar uwar taka uba ɗaya zaka kashe? Ko da ya ke ba laifi ka bane laifin uwarka Atine ne. Nasan duk ita ke kitsa maka tsanar yar uwarta" "Sa'a dai gwoggo! Karki ƙara zagar muni uwa. La'anta kuma ki ci gaba, duk waye sanadin lalacewarmu ke da ɗanki ne" ya ƙara sa maganar yana tangaɗi. Gwoggo kuwa jin alamun shigowar Iliya ya saka ta fashe da kuka. "Na shiga uku na! Ni na haifi ubanku amma ban tsira ba daga zagi da cin mutumcin ts*nannun jikoki?" Ogan naku jin kukan gwoggo ya yi har cikin ransa da gudu ya karasa shigowa gidan. 
"To irin lalatattu! Haihuwar ku bata yi min rana ba. Share hawayenki Gwoggo wannan duk laifin Atine ne ita ke dorashi a hanyar da zai Rena muni uwa. Ki bari uwar tasa ta dawo zai gane Allah ɗaya ne" Shaho kuwa ganin In ya tsaya zai iya kaiwa Gwoggo sara ya saka shi ficewa ya bar gida.
Hankalin Malam iliya ne ya kai ga Rauda da ke kwance. Ya bude baki da niyyar magana sai ga Baraka ta shigo gidan kamar zararriyar mahaukaciya. "Ku bani ita sai ta biyani kudina. Malam Gwoggo duba ki ga yadda Rauda ta ja mini asara, an kwashe kudin goro kuma ya sha ƙasa. Yau Allah ne kadai me kwatarta a hannuna" 
"Ji mana Baraka. Kina nufin wanda ya banketa bai tsaya ba?" Iliya ya fada ya na gyara zaman taguwarsa. "Ina maganar an mini asara kana fadar wanda ya banketa. Ina zai tsaya dama"
"Baraka wahala ta dubeki. Kwandalata bazan saka ba sai ki san yadda za ki yi da ita ko kuma kije ki kira Gaga. Domin ina sane da in ya kawo kuɗi ba bani kike yi ba." Iliya ya karasa maganar tare da zama gefen Gwoggo. Caraf Gwoggo ta karɓe zancen. "Baraka ɗan bamu ko goron ne mu tauna tunda Allah ne ya aiko mana da ganima ai sai mu ɗan tauna."
A fusace Baraka ta kalli Gwoggo. "Kada fa a kawoni iya wuya. Ɗiya da kake maganar in yi mata magani bayan asarar da tayi mini ai Malam sai dai ta mutu in sai na kaita Chemist." Jin abin da Baraka ta fada Iliya da mahaifiyarsa dariya suka kwashe da ita a tare. "To ke Baraka in baki kaita asibiti ba har ta mutu, wa yayi asara? Ni fa dama can ina kokonto a kan anya Rauda jini na ce? Domin ni kaf jinina in dai ni na haifeka to fa babu mutumin arziki. Ita kuma na ga har yau akwai sauran mutumci a tattare da ita." Luƙeƙiyar ashar Baraka ta watsawa Ilya. "Ban gane abin da kake faɗa ba. A tunaninka kowa irinka ne? Ina fa sane da biye-biyen matan da kayi don haka kada ka kaini wuya yanzu In feɗe maka aiki" ganin Baraka zata dama masa salalar tsiya sai ya koma rarrashinta, tsakaninsa da Baraka kar ta san kar ce. Hausawa suka ce Mugu shi ya san makwantar mugu. Motsin da suka ji ne tare da sallamar Zinatu ya saka su juyawa. Figigiyar matashiya wadda duk da duhun dare zaka iya hango hasken da Allah ya albarkace ta da shi, wanda In ka kula sosai zaka fahimci hada na Shago ta haɗa. Yanayin shigarta kuwa kana gani kasan ta raba hanya da nutsuwa ko kuma kamala. "Baba! yanZu a hanyata ta dawowa nake jin abinda ya faru da 'yar uwarta Rauda. Yanzu haka rayuwa ta ce kun sakata gaba baku kaita kemis ba bare asibiti" ta karasa maganar tare da rungumo Rauda da ke yashe saman tabarma. "Ke tunda kin je ki rarumo kudade sai ki fara sallamata kafin ki fita a gidan nan. 'yar nema nasan jikkarki cike take maƙil" Malam Iliya ya karasa maganar tare da miƙa mata hannu. "Ban gane ta sallame ka ba. Ai in Ka ga ta fita da ita a gidan nan to an biyani kudin gorona ne. Ina ba haka ba kuma to a bar mini 'ya ta ta mutu ai ni na haifi a bata, kilama ranar sadakar uku In mayar da kuɗina har da riba"  Dariya irin ta riƙaƙƙun ƙaruwai Zinatu ta tuntsure da ita. "Gidanmu gidan daɗi. Alelen giro bariki, inka iya ka haye in Baka iya ba ta kwaɓe maka. Yanzu kai Baba ungu wannan" ta miƙa masa dubu biyar. Ita kuma Inna Baraka ta miƙa mata dubu shida. Tsabar farin ciki guɗa Inna Baraka ta kwala"kunga haihuwa me albarka! Kai gobe ma a sake banketa wannan ai na mayar da kuɗina har da riba." Gwoggo kuwa ganin kudi ya sakata ta ruɗe. " 'Yar jikalle ni ba za a yagamin wani abu ba? " 
"Su Gwoggo iyayen son abin duniya. To ga wannan a sha sigari ko goro." Washe baki ta hau yi tare da karɓe Nera dubu.
Zuwaira da Atine a tare suka dawo gidan.
"Ban fa gane ba. Tun a soro na ji ɗiyata na rarrabe kudi kai ayi min bayani ban gane ba jama'a" Zuwaira ta karasa maganar tare da watsawa Zinatu kallon za ki yi min bayani. "Ke dai tunda kun dawo daga ɗan banza yawonku sai ki amsa rabonki." 
"A'a fa Gwoggo bana so ana shigarmin hanci da ƙudundune. Ki bari In yi da waccan mara mutumcin da ta gama mini gorin haihuwar ɗiya ɗaya kamar idon besfa."
"Ke kau Zuwaira mu ci arziki a ajiye masifar nan a gefe." Inna Baraka ta fada.
Zinatu kuwa Ganin zasu bata mata lokaci, juyawa ta yi da nufin daukar yar uwarta su je asibiti sai dai wayam! Babu Rauda babu dalilinsa. "Mun shiga uku! Ina Rauda ta gida? Yanzu fa take kwance nan wurin" Suka tsinkayo muryar Zinatu na fada. Kallon kallo aka fara cike da tashin hankalin wannan lamari na ɓatan Rauda. To ina ta je ita da ke kwance a sume? Gwoggo kuwa wasu yawo ta haɗin, ji kake ƙut! Kada dai a ce  tarihi ne zai maimaita kansa. Lokaci ɗaya gumi ya wanke mata jiki...

Meenat A. 'Yandoma

***