Kuncin zuci
by @bintuuu
A dai dai lokacin da aka gama wannan sanarwan Ahmad dake zaune a masallacin yayi burying fuskansa a tafin hannunsa, aransa yana fadin "Alhamdulillah, Alhamdulillah" har wani rawa yaji jikinsa nayi, zuciyarsa na kadawa kan wannan al'amarin da bai taba kawowa aransa zai wanzu kwana kusa ba, lallai Allah yana ikonsa yanda yaso, So Na'ima is finally his wife... Him alone, wai yanzu Na'ima tazama tashi....Ya Allah.
Adam dake gefensa ya dafa bayansa yana murmushi yace "Congratulations Man" sai Ahmad ya dago kansa yana sakin wani yalwataccen murmushi, Faruk shima ya miqo masa hannu yana fadin "Congratulations Yaya Ahmad, Allah ya sanya alkhairy" miqa nashi hannun yayi fuskansu dauke da murmushi dukansu, nan kuma Ahmad ya hau gaisuwan da jama'an da suka halarcin daurin Auren, kowa sai fatan alkhairy yake masa yana amsawa, ji yake duniyar ta dawon masa sabuwa, wani nutsuwan da bai taba tsammani ba ce ta rinqa shigarsa kawai ya ciro wayansa daga aljihu ya danna kira.....Na'ima dake zaune har sannan cikin shock Mami ta matso tana shafa bayanta cikin fara'a tace "Ma sha Allah Habibti, Allah ya baku zaman lafiya da zuri'a dayyiba" ai nan Na'ima ta duqar da kanta kunya na cikata, Hajiya da ke miqe tun tuni, ta hau murmushi tana fadin "Kaii abu yayi kyau sosai, Na'ima Allah yasa gidanki" dasauri Mami tace "in sha Allah" shafa ma dake tsaye a falon tace "Yar nan, Allah ya baku zaman lafiya yakawo qazantar daki" sai Na'ima ta qara sunne kai duk bata amsa musu ba, wani irin abu takeji na taso mata tun daga kafarta har kanta..Aure aka daura mata da Ahmad, is this even real? Ahmad mijintaa? Itakam tayaya ma zata fara facing dinsa...Dasauri Nafisa ta dawo falon tana haki dan ta tafi har wajen leqo komai ne, aikuwa tagani kuma, cikin farin ciki tace "Mami wallahi andaura" Mami na dariya tace "Wai dama baki yarda ba" kawai ta kamo Na'iman tana jijjaga ta sai fadin "Amaryaaa" take, Na'ima na murmushi taqi dago kai har sannan, aikuwa sai ga kiran Husna a wayan Nafisan, tana dauka kawai suka fara ihun "Yeeeeeeyyyy" Mami na dariyansu tace "Zaku fasa mana kunne" Hajiya tace "Barsu..ai abun ayi farin ciki ne wannan abu, Allah ya sanya alkhairi" sai da su Nafisan suka gama ihun sannan Husna tace "Bari na kira video call ki nuna mana matar Boss, wayyoo Allah, kin ganni gidan Anty Fatima yanzu Mamma takira take fada mana" Nafisa tace "Kedai bari, ni wallahi na rasa inda zan sa kaina ma, the happiness is too much" cikin zakadi Husna ta kashe wayan atake ta sakeyin kiran, Nafisa na dauka Husna ta miqo hannu tace "Mu tafa tun daga screen" Nafisa har miqa hannu tayi alamun su kashe, sai ta juyo da wayan daidai Na'ima tana fadin "Ga Amarya" sai Anty Fatima ta sako kanta cikin wayan tana fadin "Anty Na'iman mu" Husna tace "Anty na Amarya" Hajiya dai sai raba idanu take tana kallon wannan soyayyar mutanen gurin Na'ima, qin juyowa Na'ima tayi sai ta kai fuskanta gefen kafadan Mami tana murmushi, sai Mami ta dafa ta tace "Kai kuna samin yarinya kunya" sai duk suka kwashe da dariya, sannan sukace "Allah ya sanya Alkhairi Antyn mu, Allah ya barki da Yaya har abadaa" kirane ya shigo wayan Mami sai taga Mamma ke kiranta ta dauka sai da suka gaisa Mamma na fara'a tace "Oh Maman Faruk kinji wani ikon Allah kuma" Mami tace "wallahi fa..Ashe babu rabon sai an sake dawowa" Mamma tace "Abu yayi kyau sosai, Allah ya sanya Alkhairi, we are so happy gaskiya" Mami na fara'a tace "Amin Mamma, gaskiya abun farin ciki ne kam" Mamma tace "Gaskiya sosai, zaku dawo tare da itan ai ko" ta amsa da "Bamu sani ba tukunna, sai munji daga garesu in sun shigo" sai Mamma tace "Toh Madallah" da haka suka kashe wayan Mami ta kalli Hajiya tace "Maman angon ce" Hajiya tayi saurin cewa "Allah sarki, ai lamarin yayi kyau sosai gaskiya, Allah ya basu zaman lafiya" Mami ta amsa da Amin, Nafisa da ta gama wayan tace "Mami dan Allah mu tafi tare da ita, Abba yace zataje verification gurin aikinta fa ranan Monday" Hajiya tace "Ayya ta fara aikine?" Mami tace "Eh tasamu aiki a CBN, ai basu dade da dawowa tareda wannan din ba, sun qaro karatunsu acan England" Hajiya tadan sake baki sai kuma tayi saurin cewa "Allah dai ya biyaku da gidan Aljanna" Mami tayi murmushi kawai, Wayan Na'ima ce tayi ringing ta dauko daga gefenta, ganin numbern Ahmad sai da qirjinta taji ya bata wani sauti, maida wayan tayi gefe tanajin bazata iya facing dinsa yanzu ba, anya ma zata iya kallon idonsa...Abba ne ya kira Mami a waya ta miqe ta fita, Nafisa dake faman typing a waya ta tashi itama ta bi Mami falon akan zata tambayowa su Anty Fatima time din da zasu koma Abujan dan sunce zasuje can gidan su jirasu ne...Na'ima aka bari da Hajiya a falon dan shafa ta fice zuwa kitchen itama, sai sukayi shiru babu me magana cikinsu, cikin sanyin jiki Hajiya tace "Allah ya sanya Alkhairi Na'ima, nasan zakice bana daga cikin mutanen da zasu tayaki farin ciki a rayuwa, amma ba haka bane, inasonki kuma inason duk wani cigaban ki kinji" sai Na'ima ta gyada kai ahankali tace "A'a....Nagode" Mami ce tadawo falon tace "Tashi muje daughter ga sucan sun dawo falon" ta kalli Hajiya tace "Muje gasucan suna kiranmu" ta amsa da "Toh" suka miqe gabaya tareda komawa falon downstairs dalilin wani taron da Baba ya sake kira, kan Na'ima a duqe suka shiga falon sai boyewa take a bayan Mami, duk rukunin Jama'an falon kallonta suke cikin fara'a, gogan tun daga sauqowansu stairs idonsa ke kanta har suka qaraso falon, Adam ne ya dan mintsinesa yana murmushi sai Ahmad yayi saurin sauqe idonsa, anan gurin da suka zauna dazun suka sake zama, sai da aka nutsu Baba yayi gyaran murya ya fara bude taron da Addua, sai da aka dauki 5 minutes ana addu'a sannan yace "Alhamdulillah, kunga wani ikon Allah kuma, mu da muka zo sulhu sai Allah yayi exceeding tunanin mu yasako wani al'amarin me girma kuma" Abba da Alhaji suka amsa da "Alhamdulillah" sai Baba ya cigaba "Allah yasa albarka" duk aka amsa da Amin sai Alhaji yace "Tun da haka al'amarin ya kasance ina neman alfarman ku barmin Na'ima anan na wani dan lokaci kafin a miqata dakinta" Abba yace "Badamuwa Alhaji, hakan yayi, nayi magana da mamansu akan hakan dazu" Ahmad dai kansa na duqe har sannan, sai Mami tace "Zan zauna anan kanon nima, in yaso duk ranan da aka shirya kaita sai mu tafi tare" Alhajin sai farin ciki yake jin wannan soyayya da suke nunawa yarsa a fili, yace "Ai in kin tafi da itan ma ba laifi bane" Abba yace "Baza'ayi haka ba, zata zauna anan din na wasu kwanakin in yaso duk lokacin da shi mijin nata ya nemi ta tare sai su tafi taren" sai lokacin Ahmad yayi murmushi kansa a duqe har sannan, Na'ima dai tana duqe jikin Mami takasa ko dago kai balle ta kalli inda yake, amma ajikinta takejin presence dinsa a dakin....Maganan fahimta akayi sosai a falon suka tsaida magana akan in sun koma zasuyi waya da Alhajin don sanar masa lokacin tariyan, da haka duk suka miqe, su Ayuban suka rakasu waje har Alhajin, su Ahmad ne a bayansu sai ya zamto Adam yana bayansa, Ahmad na nufin juyawa sai Adam ya dan turasa yana masa radan "Muje for now, anjima dakaina zan kawoka" Faruk na dan dariya suka fice gaba daya...
Da aka bar su Mami a falon sai Hajiya tace "Ai anan zamu kai dare dai ko Hajiya" Mami ta amsa da "In sha Allah" sai Nafisa tace "Mami zan zauna anan please" Mami jitayi ranta ya dan kwanta dan tanata tunanin barin Na'iman tare da Hajiyan, amma sai ta maze tace "Ahh har dake" sai Hajiya tace "Ai kiyi zaman ki abinki, yanzu zansa a gyara muku dakin gefena" Mami tace "Ayi haka" Hajiya na murmushi tace "Ai an zama daya kuma, tayi zamanta wallahi" sai Mami tace "Mungode, ai sauran yaran nawa sunce zasu taho yanzu suma, zamu zauna acan gidan tare" Nafisa tace "Mami flight din zasu biyo" tace "A'a inaga da motansu zasu taho, Al'ameen zai karbi saqonsa a Kaduna" sai Nafisa tace "Bari na fadawa Husnan to, wai tunda bazamu koma ba zata taho itama" Mami tayi murmushi kawai, Hajiya dai nata ido da murmushi bini bini kuma sai ta dauko waya ta duba, sunanan zaune suna hira nan ma kiran Anty Amnah ya shigo sai Mami tasa a handsfree, aikuwa Anty ko sallama batayi ba tace "Mamiiiii, abun farin cikin da ya faru kenan" Mami na dariya tace "Kedai bari, muna namu Allah na nashi" Anty Amnah tace "Kaiii..I don't even know what to say, Alhamdulillah... Alhamdulillah" Nafisa tace "Antyyy" ta amsa da "Ah'an amare kikeji, dan kema babu kanki kuma" sai duk sukayi dariya tace "Ina daughter na, abani ita please" sai Mami ta miqa wayan gurin Na'ima da duk kunya ya rufeta, Anty Amnah tace "Daughter Allah ya sanya Alkhairi kinji, Allah ya baku zaman lafiya" Mami ta amsa da Amin, sai Anty Amnah ta sake cewa "Ai inanan tafe next week nima amma zanyi transit a Dubai dan Mamma tacemin sunyi magana da Ahmad kan siyan kayan lefen tun ba yau ba ashe, Fatima zata sameni acan ma, shima yamin text dazu wai ze kirani muyi magana" ta qarasa tana dan dariya, Mami tace "Ai se a gaisheda Ahmad, mudai ya bamu lokaci sosai gaskiya" Anty Amnah tace "Uhm, kema kin sanshi fa Mami" tana murmushi tace "Zai hadu dani kuwa, zan kirasa nima in na koma gida anjima" da haka sukayi sallama..Can sunanan zaune sai Na'ima ta sake ganin wani kiran Ahmad din, sauqinta ma ta saka wayan a silent, dauka tayi ta qura ido a sunan nasa kiran na tafiya daidai da bugun zuciyarta, katsewa yayi sai ga wani kiran ma, like seriously bata san taya zata fara magana dashi ba ga kuma su Mami a zaune falon, Kiran na katsewa sai ga Text dinsa kamar haka.
"Ya wardati🌹....My beloved Wife, please give this drowning man a chance to hear your voice...kinji"
Dan stiff Na'ima tayi tana jin saqon na shiganta, kowanne kalman na shiga lungu da saqon zuciyarta, samun kanta tayi da yin murmushi sai kuma wani text din ya sake shigowa kamar haka.
"I longed for you in silent prayers, I waited, I hoped, I trusted Allah, and today...He gave me you as a wife, you're mine in Halal Na'eemah..And every breath between us belongs together"
Na'ima ji tayi zuciyarta na melting, Ya Allah...what did she do to deserve Ahmad, me tayi Allah ya bata Ahmad ne?....
Agaainn sai ga wani text din.
"Zanzo anjima kinji"
Sai sannan tayi reply da "Allah ya kaimu" sai kuma ta hada da Emoji na love ❤️ guda daya tana murmushi...
Sai bayan magrib Mami ta fara shirin tafiya dan tana jiran su Al'ameen su iso ne sai su dauketa su nufi can gidan nasu tare, aikuwa basu dade ba sukaji megadi ya bude gate mota ta shigo, Nafisa ce ta fara tashi, sai Mami ta miqe tace "Toh Hajiya ni zan wuce, sai na kuma zuwa kuma" Hajiya ta miqe itama tace "Bazasu shigo bane" Mami tace "A'a barsu dare ne ai" miqewa Na'ima tayi itama sai Mami tace "Muje ku gaisa Habibti" ta amsa da "Toh" da haka duk suka fita compound din gidan, Husna ce ta fara fitowa sai Nafisa ta fara tafiya garesu da dan rawanta tana fadin "Oyoyooo.." sai sukayi group hug da Abu da Husna suna tsalle, Mami tace "Lower your voice ni" sai suka taho gurin Na'ima dake tsaye a baya tana ta murmushi, kwaqubeta sukayi dukansu har da Nafisan, sai Na'ima ta fashe da dariya itama, Hajiya da shafa sai bin ajebo kids din suke da kallo, dan duk kudinsu sai yanzu take ganin wanda suka damesu, ga wata uwar mota da taga sun zo da ita, bayan sun lafa sai Al'ameen ya qaraso yace da Hajiyan "Ina wuni" da sauri ta amsa da "Lafiya dan samari" sai lokaci su Husna da Abu suka lura da ita sannan suka gaisheta tareda shafan, sai Mami tace "Oya kuzo mu tafi hakanan" Husna tace "Nafee har da ke" sai ta girgiza kai, ai nan Husna tace bata ga gurin tafiya ba itama, Mami na murmushi ta kalli Hajiya tace "Qanwar angon ce" Hajiya tace "Allah sarki ai ga alama nan, kiyi zamanki kinji" Husna ta amsa da "Toh Mama mungode" Al'ameen ya qaraso gurin Na'iman suka gaisa yanata fara'a, Abu dake gefen ta shima yace "Anty zamu dawo gobe" tace "Allah ya kaimu Abu" dan sai lokacin kuma taji wani iri da Mamin zata tafi amma ta danne bata nuna ba, da haka su Mamin suka shiga mota, Al'ameen yayi reverse suka bar gidan...
Bayan Isha sai ga kiran Ahmad kuwa, dan tsayawa Na'ima tayi tana tunanin ta Ina zata fara cewa Hajiya tayi baqo ne ma, baqon ma wai mijinta da aka musu aure yau, sai ta juya tana kallon su Nafisa da Husna dake bararraje akan gado sunashan ice cream dinda su Husnan suka taho dashi, hira suke sunasha hankali kwance kamar basu bane baqi a gidan, nan ma wani nauyi ne ya kama Na'iman ganin ga Husna zaune bazata iya fadawa Nafisan ba, qarasawa tayi ta zauna bakin gadon sai Husna ta miqo mata roba daya na ice cream din, karba tayi sai kuma ga kira ya shigo wayan Nafisa, dauka tayi tareda tattaro duk nutsuwarta ta amsa da "Salamu alaikum, Ina wuni Yaya" sai tayi shiru tana sauraronsa while Na'ima ta juya kanta gefe, can Nafisa tace "Toh Yaya, yanzu ma" da haka ya kashe kiran, Nafisa na kallon Na'iman tace "Tab ai tsaf zan kaiki ma baruwana da wata Hajiya" da haka ta miqe Na'ima tace "Allah ya shiryeki Nafee" tana dariya ta fice daga dakin, afalon Nafisa ta samu Hajiya da Alhajin sai Alhaji yayi saurin masking bacin ran fuskansa yana kallon Nafisan, Hajiya kuma ta duqar dakai batason aga hawayen nata, sai Nafisa tace "Abba daman Yayun mu ne sukazo" yace "Okay har yanzu Na'iman bataje ba, ai suna guestroom" Nafisa tace "Toh" da haka ta koma dakin tace da Na'iman ta tashi suje, cikin sanyin jiki Na'ima ta miqe sai Husna ta bude box dinda ta taho dashi dansu basu taho da kayaba daman, aciki ta dauko wani milk abaya ta miqawa Na'ima akan ta saka, bayan ta saka sai Nafisa ma ta dauko turare a jakanta ta hau fesa mata suna tsokalanta tana sunne kai, sai da Na'ima ta kintsa sannan ta biyo bayan Nafisan amma basu samu su Alhajin a falon ba dan sun tafi daki, sai da suka isa falon qasa cikin sanyin murya Na'ima tace "Ayya Nafee kunya nakeji wallahi" Nafisa tayi dariya tace "You're not doing this with me, ke da mijinki" kawai sai ta kamo hannun Na'iman suka fita waje, a parking space suka hango Adam a front seat na motansu ya sakalo kafansa daya waje amma kansa duqe yana danna waya, sai Nafisa ta kalli Na'ima tace inane gurin, Na'ima tayi pointing wata kofa anan gefen falon suka qarasa, dan tura kofan Nafisa tayi sai ta kamo Na'iman ta turata ciki tareda leqo kai tana murmushi tace "Yaya gatanan na kawota" Ahmad na tsaye a mini falon cikin black jamfa sai tashin qamshi yake, sai yayi murmushi yace "Toh Nafisa" da haka ta rufe kofan tabar Na'iman tsaye gurin shikuma yana tsaye a tsakar falon yana kallonta, murmushi ya sakar mata sai ya fara takawa a hankali ya isa gareta, duqar da kai Na'ima tayi tanajin kamar numfashinta ze bar qirjinta, batayi aune ba taji ya rungumeta a qirjinsa, sai yayi burying fuskansa a wuyanta kamar me rada yace "My Other Half" binne kanta tayi a qirjinsa itama zuciyarsu na bugawa a tare, ahankali Ahmad ya qara manna ta da qirjinsa har sannan bai dago fuskansa ba idonsa a rufe ya sake rada mata "Next week....Next week kinji wife" ahankali Na'ima takai hannayenta tayi wrapping dinsu a bayansa tanajin wani irin shauqin da bata tabaji akansa ba, sun kai minti 3 nan tsaye zuciyoyinsu ne kadai suke martani ga juna babu magana..