HAWAYEN MARAICI

9

by @asmybaliyu

HAWAYEN MARAICI 9

By

Asmy b Aliyu

Juyawa yayi Yana kallonta da mamaki

Ruwa na shower na sauka akansa har lokacin,wani irin mayen kallo ta bisa dashi lokaci daya haka tana jin tsikar jikinta na tashi lokaci daya,wasu irin yawu ta hade babu shiri ganin kyakkyawar surar mijin nata,haka lokaci daya wata irin matsanaciyar shaawarsa ta binjiro masa,

Cikin bin umurnin zuciya da gangar jiki ta nufesa,cikin dakewa Abdulhakeem ya kalleta cikin ido yake fadin"please leave Jawaheer."Ware ido tayi tana kallonsa

Haka bata fasa kusantosa ba,lumshe ido yayi xuciyarsa na bugawa jin kamshin fitunannen turaren da tayi amfani dashi,cikin sakan din da baiyi goma ba,

Yaji gabobin jikinsa Sun mutu.hugging dinsa tayi ta baya gamida dora hannayensa akan fadeden kirjinsa mai dauke da yalwataccen gashi tana shafawa a hankali da wata irin murya fitina take fadin I need you!!!"sauran Runtse idonsa yayi Yana ambaton Allah a ransa, Jawaheer

This is the not right place please..........Kara manne masa tayi tana kwantar da kanta kan bayansa ruwa na dukansu sosai,

bata damu da yadda yake kokarin cireta a jikinsa ,takai hannunta daidai inda bazai iya bijirewa bukatarta ba,wani irin numfashi Abdulhakeem yaja.tana jin yadda ya shiga kokarin Kiran sunanta Sai dai yadda takai hannunta yasa ya firgice

Ya kasa furta sunan,ya wani irin fisgota ta gabansa tana ganin yadda idanunsa suka canja Kala,hade fuskarta yayi da tasa

Yana sauke mata numfashi mai dumi,

A haka ya lalubi bakinta ya fara yimata wani irin hot kiss,babu laifi Jawaheer ta basa hadin Kai acikin toilet suke sauke duk wani abu da sukeji,sunfi karfin awa daya a toilet Suna abu daya.duk da yadda Jawaheer Tasha wahala a hannunsa ko kadan bata nuna masa na,Dan Mami ta fadamata muddin tana masa korafi akan gadon aurensu tsanarta zai farayi daga nan Kuma tunaninsa zai tafi kan wata ya'a macce tunda ita baxata iya jure bukatarsa ba.lokacin da Mami ta fadamata haka,

Jin tayi zuciyarta tamkar Zata kama da wuta saboda turirin da takeyi,Zata iya jure komai Banda kishiya tana hango Ranar da Abdulhakeem Mai keke zai hadata da wata Sai dai kowa ya mutu.

####

Karfe Tara har da rabi na dare suna cin Abincin daren da Aunty salma ta girka Wanda bakajin komai sai karar cokulla suna cikin cin Abincin ne mukaji kararrawar (door bell)).

Mimi ce ta doshi kofar ta bude, Abdulhakeem ne hannunsa duka biyu cikin aljihun bakin wandon sa da kuma farar shirt mai guntun hannu wacce ta dan kamasa sai Mimi taga  yayi mata  kyau sosai acikin shigen duk da kuwa bai fiye son kananun kayan ba.

Yaaya  ina kashiga tun daxu? Cewar Mimi dake rike da hannunsa na dama sallama yayi a falon kafin yace Mimi kya bari na xauna ,ko matata bata damuba baranta na ke ya karasa mganar cike da xolaya nan take yanayinta ya canja A zuciya ta juya ta koma wajen cin Abincinta.

Auh fushi ma kikayi??

Sharesa tayi Aunty salma tayi daria ina ruwan Mimi kai kuma Abdul baka kyauta ba ta damu dakai shiyasa ta tambayeka tun daxu take Neman layinka " baya zuwa to Aunty bagani ynxu na dawo ba.

Jawaheer ta mike tsaye da murmushi a fuskarta take yiwa Aunty Sai da safe

yayinda Mimi tabita da harara .

"Angel.

Ya kirata cikin wani irin sauti ta turo baki batareda ta kalli inda yake ba,ayimin afuwa ina unguwar su Nura nan ma banxa tamasa Cikin sanyin jiki ya kalli Aunty salma Aunty kice tayi hakuri ta kulani mana.

Babu ruwana wannan tsakanin Ku kunfi kusa kaga tafia ta anan Aunty salma ta fice...ya rage daga shi sai ita .

Ta kallesa ta wani hade rai na xubama Abincin?" Tunda naga matarka bata damu daka ci Abinci ba ko baka Ciba ,takarasa maganar tamkar xatayi kuka murmushi yayi ya dawo kusa ga kanwartasa hannunta na dama ya rike kina fushi dani Mimi taya xa'ayi naci Abinci."

Tun saukar ki kasar nan kike fushi dani gayamin meye laifina kiga yadda xan hukunta kaina." Jikin ta qlau yyi sanyi taji tausayin yayan nata ya kmata ,serving dinsa tafara yi   tashiga basa Abinci.

Sunfi minti goma a haka kafin yace mata ya koshi Anan ta dauko masa best drink dinsa wato maltina...

Kiyi hakuri Mimi ba laifina bane ,mum keson na Auri jawaheer hasalima ban taba jinta araina ba.

Da mamaki Mimi ta daga Kai tana kallon yayan nata.

Anan AY.ya bayyana mata komai to ita kuwa mum meyasa ta dage akan lallai lallai sai ka auri jawaheer?"shiru Abdulhakeem yayi Yana kallon rigimammiyyar kanwarsa,jin baice komai ba yasa tace.

Allah ya sa haka shiya fi xama Alkhairi."murmushi AY  Yayi ya dora da fadin Ameen Angel."  nan kuma suka canja hira xuwa na school dinsu anan ya biye mata da kallon pics din friends dinta A waya.

Sai kusan sha daya saura minti goma suka bar falon.

#####

Washegari suna gama karya kumallo sukayi shirin tafia Airport jirgin karfe goma xasubi xuwa Bauchi.

Mimi sai murna take ji take tamkar tayi tsuntsuwa ta ganta a Bauchi tare da mum dinta.

Wannan murna fa haka Angel?".. AY ya fada Yana kallon mimi  Yaaaya na kagara naje naga granny dasu mum  ,daria AY .yayi to Idan babu flight din safe fa,

Nan take yanayin ta ya canja sai ayi tafiar a mota nafiki son mu isa da wuri Angel ina da meeting karfe 3  a yau kuma motocin mu xasu iso ,woooowwwww kace xan xabi daya aciki.

" yaushe na canja maki mota da kike maganar canja wani??"...

Kai yayana shekara 2 fa yanxu ,Angel kina da rigima ne ,mexakiyi da mota keda ke karatu."

Ni dai Dan Allah  ,xan Dan jima shi yasa ba sai na barwa rukayya  nawa ba ." Angama my Angel idan aka kawo sai kowa ya xabi kalar da yakeso  keda jawaheer....hugging dinsa tayi.

Haka bakin Mimi yaki rufuwa saboda murna   Aunty sadiya,  yaaa saifullahi da kuma Rukaiyya ya'nyata  manya ,hardasu airport gurin tarbonta  ,granny mum tarasa da Wanda xataje ta fara runguma kai tsaye wurin granny tayi ta kankameta sosai tana  dariyar farin ciki itama hajja,daria tayi anan ta shiga gaisawa da mutanen gida gabadayan su su nufi gida  AY ya nufi office saifullahi ne ya  daukesu  A motarsa.

mum tarasa inda xata saka kanta da tsananin murnar ganin Mimin ta ,part din granny aka nufa duka har mum ,yayinda jawaheer ta wuce  part dinta Abunta.

Bata kara jin hayaniyar suba.sai bayan magrib da mum ta shigo ta duba lafiyarta

#####

Washegari

Suna gama break fast AY ..ya kira jawaheer a waya Dan tana dakinta ,shi kuma lokacin yana tareda Mimi a falonsa.

Cikin wata bingilar rigar body hook ta fito ,da kadan ta wuce gwiwoyinta  blue kallo daya yayi mata ya dauke kai ,jeki canxo kayanki kixo xamu fita Mimi baki iya gaisuwa bane?"

AY yace da kanwartasa

ina kwana.""

Ciki ciki  jawaheer ta kalleta kin tashi lafia??"

Da haka ta juya ta koma ciki yaaya bari naje na dauko hijab da handbag dina daga can xanje gidansu Aunty sadiya ohkey.....

Jawaheer da AY ne a gaban mota sai kuma Mimi dake baya ta damesa akan ina xasuje ??"

Mimi kin fiye gajen hakuri  bayan shudewar wasu mintuna ta gansu

A company mai keke   motor's  itama jawaheer takasa boye murnarta ,wowwww sweetheart karka cemin mota xan xaba?"

ya kalleta ko bakya sone?"

Batasan lokacin da ta rungumesa ba ,sai godia take xuba masa gabadaya ta rude Mimi ta dan ja tsaki aranta tace taga mota manyya gayyar mayu "duk ta wani gigice....

Motoci ne kala biyu baka da kuma Ruwan toka new model (2025) AY Ya kalli jawaheer yace ta fara xaba nan take jawaheer murnan ta ya karu a hankali ta fara xagayen motan tana duddubawa ,karshe ta dauki bakar car key yabata sannan ya mikawa Mimi dayan key din.

Angel ki dauki "Ash din nan ta amsa tana tsallen murna .....

Tom.kuxo mu tafi xuwa anjima sai akai maku su gida ko ,why not yanxu mu Dan Dana yaaaya..hohoho!

Angel kina dai bari ayi setting nata sa'annan kuma ayi mata full tank ...

Da haka ya juya dasu gida yana aje jawaheer Mimi ta axa rigima akan lallai sai ya kaita gidan Aunty sadiya .....haka ya juya kan motar suka nufi gidan Aunty sadiya.

Tare suka shiga gidan Aunty sadiya shigar su falo suka isko Rukaiyya na tikar rawa cikin Riga da Wando na English west.

Aunty Rukaiyya ga yaaa AY. Nan na kallonki cewar safeeya wacce itake biwa Rukaiyya cak! Ta tsaya haka takasa juyawa ,kunya gabadaya ta rufeta jin tayi anyi hugging dinta ta baya haka taji ihu a kunnenta Wanda tasan Mimi ce da gudu ta kwaci kanta ta gudu...

Safeeya tayi daria wacce shekarunta baxasu wuce sha ukku ba Ina wuni yaaya lafia qlau safeeyatu ya kk.?"

Tura baki tayi a hankali tana buga kafafunta a kasa ni Allah yaaya kai kawai ne  ke batamin suna ,Dan Allah ka daina karkasa Kamal yaje school ya fada.

Dariya AY.yayi gamida rike baki eyeeeh cikakken sunan ki fane ,ta tura baki cike da shagwaba ni bana son wannan sunan nafison,ka kirani da Safeeya na.

Ni baxan iya da surutun kiba,ina Mamy ?" Mami tafita olryt da haka ya Ciro waya ya dannawa Mimi  kira.

Tareda Rukaiyya suka fito ta xuba katon hijab kamar ba ita ce ke rawa ba.

"Ina wuni yaaaya

Harararta yayi yaushe kika xama haka Rak??" Shuru tayi takasa basa Amsa ,wannan katon hijab fa??"

Nan ma banxa tamasa ,dan ta gane yana Neman tsokana ne kurum.

"Olryt ..tunda baxaki Amasani ba kinga tafia ta sai da yakai kofa sannan ta daga murya pls yaaya  Kabar mana Mimi na kwana daya dan Allah."

" Nabarta Ku xauna kuyi ta gulmar mutane ,baxai yuyuba ki shirya xuwa anjima dake xanxo na tafi kiga amarya tunda na lura bakida kirki tunda nayi aure,baki taka gidana ba."

"Sabida haka ki shirya xuwa anjima tare xamu koma ,xan tura driver idan ban samu dawowa ba."

Naji xanje amma ni baxanje gurin matar ka ba,

Da gudu ta nufi upstairs ,yana kwala mata kira bata kulasa ba haka Mimi ta juya tabi bayanta.

####

BAYAN WANI LOKACI

Kamar yadda Abdulhakeem yayiwa Jawaheer Alkawari Sun tafi honeymoon kasashe guda ukku Wanda itace ta zaba,watansu biyu Suna shakatawa koshi Sai da jawaheer din tata korafin yayi kadan

Shikuma saboda aikinsa da companynsa

Dole suka tattaro suka dawo gida Nigeria

Gabadaya  Ahalin Yusuf mai keke  suka shirya xuwa umra cikin watan axumin Ramadan dama kuma haka sukeyi duk shekara ,satin su biyu suka dawo.....sukayi sati biyu a Nigeria akayi bikin sallah

Some months leap...

#####

Ranar wata lahadi mamin jawaheer  taxo Bauchi.

Inda suka kebe itada uwarta da kuma mum,Hajia Azumi bansan meke damun Jawaheer ba,gabadaya yanxu ta janye jikinta daga gareni ba dole ba jummai jawaheer tana son Abu baxaki iya tursasa Abdul yayi mata ba bayan ya daukeki kamar uwa.Azumi daga ke har yarki gaggawa ne daku bakusan wanene Abdulhakeem ba shigen kwaro ne

Hawa kansa bazai yuyu cikin sauki ba ni nafiku sanin wanene shi dole mubi komai a sannu idan muna son mu cimma duk wata nasara da Muke nema.

Nazo da shawara wadda a ganina itace mafita tunda yanxu sunyi 6 month da aure haka kuma babu Wanda xai gane dasa hannunmu acikin batar Abdul  ni naxo da mafita!_...mafitar kuwa shine anan ta bude Jakarta ta fito da wani kullin magani ta mikawa mum,jiki na rawa ta karba ,ki saurareni da kyau kiji jummai kuskure  daya xai rusa mana shirin mu...

Kece xakiyi wannan Aikin jummai  Haka bokana ya tabbatar min. Wannan garin maganin xaki xubawa Abdulhakeem cikin Abun shan sa ,ma'ana lemu ko wani abun,

muddin Abdul yasha bokana ya tabbatar min da xaibar gidan nan xaibar dukiyar sa   komai nasa ma'ana xaiyi nisa daku wandda baxai kara dawowa ba har sai idan  mu muka sa aka dawo dashi ...kinga xuwa lokacin mun xama shahararrun masu kudi dukiyarsa sai yadda mukayi dashi ,na tabbatar kuma bakin kowa xai rufe ba Wanda xai kara tambayarsa kowa xai cigaba da hidimarsa , jawaheer xata cigaba da juya companyn sa da dukiarsa gabaki daya" kowa xai dawo karkashinta." Akwai layar da boka yabani wadda yaman umurnin nayi rame mai xurfi nasaka ta aciki ,Wanda babu Wanda xai kara tamabayar Abdul "haka babu Wanda xai kawo mana matsala ,tun daga kan lauyoyinsa ,komai nasa da kika sani. Wannan aikin boka ya tabbatar min yana da hadarin gaske ...dolene a kiyaye."

mum ta sauke ajiyar xuciya kinyi tunani mai kyau  xan dauko Dan yayana ya taimakawa jawaheer.mami ta sassauta murya daga ni sai ke jummai ko jawaheer ban yadda taji wannan zancen ba kin San halinta batada hankali yanzu xatace tana son mijinta Zata iya lalata mana shiri,itama zanyi wani abu akanta bayan mungama wannan aikin..

wani irin gumi yaji ya hada   haka kuma yaji  lokaci daya wani irin xaxxabi ya rufesa mum!!!!Yana jin kalmar na masa wani irin daci a baki,

Ashe ya dade tun daxu A kofar shiga dakin mum ,dama yana so yabata wasu takardu ne daya daga cikin filayen daddy Wanda  daddyn ya mallaka mata guda biyu.kafin ya rasu,

Kai tsaye part din hajja ya nufa tana xaune A falo tana kallon tashar sunna TV..

Ganin Abdulhakeem a rikice yayi balain daga hankalinta tana tunanin meya daga masa hankali haka? "Haka tana tsoron tashin ciwonsa,  cikin karfin hali ta mike tsaye mamaki tsoro suka dirar mata ,ganin hawaye a idonsa wani nabin wani...jagwaf Ya fada kan kujera ya dafe kansa da hannunsa biyu.  Arude hajja  ta bude baki ta fara tambayar sa cike da tashin hankali....

#HAWAYEN MARAICI

#ABDULHAKEEM MAI KEKE

#JAWAHEER TARIQ

#HAUSA NOVEL

#LOVESTORY2026

#ASMY B ALIYU

#***