ƘWAI BIYU

Chapter One

by @thehealerspen654

KANO, NIGERIA

Unguwar Agadawsawa da take tsakiyar birnin Kano, daɗaɗɗiyar unguwa ce mai cike da ɗumbin tarihi. Mafi akasarin mazauna unguwar mahauta ne kuma wadanda suka gaji fawa tun iyaye da kakanni.

Acikin wani ƙaramin lungu mara ɓullewa akwai wani gidan bene,  da mai girman soraye har guda biyu zubin sa tsaf na ginin gargajiyar bahaushe. Sai dai kuma an zamanantar dashi da ginin bulon siminti tun daga farkon sa har karshen sa daidai gwargwado babu yabo babu fallasa.

Acikin tsakar gidan mai dauke da mayalwacin fili da bishiyar durumi da kuma ɗakuna a ƙalla guda biyar da kuma dakin dafa abinci na gargajiya,  bandaki  da kuma matattakalar bene da zata sadaka zuwa sama.

Wata dattijuwa da a ƙalla za ta kai shekaru 55-60 tana zaune a wata katuwar tabarma da take malale a tsakar gidan hannun ta riƙe da rariya  tana tankaden garin tuwo.

Tsakar gidan gwanin sha'awa kasancewar a malale yake da siminti ko ta ina, sannan gashi an share shi ya fita tas.

"Radiya ke nake jira fa, ki fito kije ki karɓo naman yamma tana yi,  har an fara Labaran biyar."

Dattijuwar ta faɗa tare da mayar da hankalin ta kan ɗaya daga cikin ɗakunan da suke tsakar gidan.

Wata matashiyar yarinya ce ta fito da bata wuce shekaru 12-13 ba, ranta a ɓace tana turo baki ta nufo in da take tana kokarin saka hijab ɗin ta.

Tana ƙarasowa ta kalli tankaɗen da take yi ta zaro ido tare da turo baki sannan tace:

"Wai tuwo zaki yi?"

"Eh tuwo zanyi sai me?"

"Wallahi bazan ci tuwo ba"

Ta furta tare da ficewa waje tana buga ƙafa tana maimaitawa. Bin bayan ta tayi da kallon takaici sannan tayi tsaki tace:

"Saboda ke wallahi bazan fasa yi ba, ina dalili rai na yana so, in kinga dama kar kici ki kwana da yunwa."

Dariya ta jiyo anayi ta saman benen tare da faɗin:

"Umma kema kin san ba zai barta ta kwana da yunwa ba."

Wata matashiya ce da bata wuce shekaru 22 ba ta faɗa tare da sakkowa a hankali daga benen, saboda tsohon cikin da yake jikin ta.

A hankali ta ƙaraso ta zauna kusa da ita ta karbi tankaɗen ta cigaba da yi.

To a hanya Radiya tana tafiya abun dai sai addu'a, ta tsaya acan ta tsokani wannan idan taga wata ta tsaya a gama kashe rigima ko gulma a haka dai har ta ƙarasa kasuwar.

Sai dab da ƙarasawar ta ainahin in da yake sayar da kilishi da dambun nama ta fara haɗe rai tare da ɓata fuska.

"Rady baby ya akayi ne kike ɓata rai? Sai yanzu ma zaki zo ki karɓi naman ko? Kin gama wasan ki a hanya ko?"

Wani matashi ne da bai wuce shekaru 27 ba yake yi mata maganar cikin salon tsokana.

"Yaya ba kace ta daina yin tuwo ba? To yau ma shi take yi, kuma wallahi bazan ci ba."

"Kwantar da hankalin ki Rady baby maza kije ki kai mata naman kizo muje mu siyo kayan dadi."

Aikuwa bata jira komai ba ta fizgi ledar naman ta ranta ana kare. Tana isa cikin gidan ko sallama batayi ba ta ajiye ta ƙara ficewa da gudu.

Umma tana "yaki...ba zaki zo ba" Amma ina kafin kace me tasha kwana. Juyowa tayi a hasale ta kalli wannan matashiyar tace:

"Ummie maza kirawo min Abbas naji me yake faruwa".

"To Umma". Abinda ta iya furta wa kenan sannan ta zaro wayar ta kirar visaphone ta fara laluben number sa.

Bugu ɗaya ya dauka tare da amsa sallamar da tayi. Sannan tace:

"Meyafaru ne Radiya ta shigo da gudu ta fita kuma?"

Murmushi yayi sannan yace:

"Ni nace zata rakani unguwa, kin san halin kanwar tawa sai a hankali...kin ganta ma har ta ƙaraso. Zamuje unguwa ki fadawa Umma sai mun dawo."

Murmushi tayi sannan tace:

"To Allah ya tsare hanya a taho mana da abun dadi."

Sannan ta kashe wayar tana kokarin yi wa Umma bayani.

Sai dab da magariba Radhiya da Abbas suka shigo gidan, hannun su niƙi niƙi da kaya. Suna shigowa aka fara kiran sallar magariba. Alwala kawai Abbas yayi ya nufi masallaci.

Bayan idar da sallar magariba suna zaune a tsakar gidan. Radhiya sai bude kayan take yi tana kokarin nunawa Umma abinda suka siyo.

"Umma kinga litattafai na yaya ya siyo min yace ranar Monday zai kai ni makarantar, ga sabon takalmi na ga jaka ta, kuma mun bada uniform din dinki."

Ta faɗa tana fito dasu daga ledar.

Kallon ta Umma tayi sannan tace:

"Naso boarding din aka kai ki mu huta da shirmen ki, amma wannan Yayan naki ya biye miki. Kinga da kin koyo hankali acan ai, mashiririciyar banza."

Zumɓuro bakin ta tayi sannan ta kalle shi yana ta kokarin haɗa musu shayi adaidai lokacin da yake zuba madara tace:

"Yaya kaji ko? Wai gwara na tafi?"

"A'a babu in da zaki je muna nan muna shirmen mu." Ya faɗa tare da yi mata alama da ta matso kusa dashi.

Dariya tayi tana kallon Umma. Sannan tace:

"Yaya shayin yayi min yawa wallahi bazan iya shanyewa ba."

Ta faɗa tana zaro ido.

"Sha ki rage min. Ga bread din, bari na gyara miki kifin ko?"

Cikin hasala Umma ta kalle shi tace:

"Kai kake lalata yarinyar nan wallahi, ace yarinya sai abinda take so zatayi? Haka ake rayuwa? Mace ce fa aure zatayi."

"InshaAllahu mutumin kirki ne zai aurar min kanwa, ba wanda zai wahalar da ita ba. Kuma daman ko waye sai na ja masa kunne akan ta. Zan fada masa na shagwaba kanwata zai aura a haka...?"

Dariya suka saka gabaɗaya. Sannan Ummie da take faman zira laumar tuwo ga katon cikin ta a gabanta ta kalle shi tace:

"Saboda kai da kaje neman naka auren haka akayi maka ko?"

Juyowa yayi ya kalle ta cike da tsokana yace:

"Laifin yayyanki ne basu fada min ba. Kuma tsakanin ki da Allah wacce kalar shagwaba ce bana yi miki?"

Sunkuyar da kanta tayi cike da kunya. Sannan tace:

"Alhamdulillah sai dai Allah ya saka maka da gidan aljannah."

"Ameen!" Suka masa banda Radiya da take ta faman zira laumar biredi Abbas yana saka mata soyayyen kifi a bakin ta.

Ummie ce ta kalle ta cike da tsokana tace:

"Rady baby babu tayi? Sammin kifin."

"Ke fa kika ce ba kyason ƙarnin kifi. Yaya kaji matarka ko?"

Ta ƙarasa maganar tana kallon sa.

"Rabu da ita ke dai ci abin ki kin ji."

Haka suka ta hira abun su, banda Umma da sauraron radio ya ɗauke mata hankali, kana daga bisani ta fara gyangyadi.

Haka suka cigaba da hira har zuwa lokacin kwanciya bacci sannan sukayi sallama kowa ya nufi makwancin sa.

Da safe misalin karfe shida na safe Umma ta fito tana kokarin hura gawayi domin ta ɗora abun karin kumallo. Da mamakin ta ta jiyo Abbas yana kwala mata kira daga sama. Aikuwa da sauri ta nufi benenen.

Ummie ta gano a durkushe sai faman murkususu take yi ta jiƙe sharkaf da gumi. Banda ambaton ubangiji babu abinda take yi.

Da sauri Umma ta ƙarasa kusa da ita. Ta kama ta tana faɗin:

"Subhanallahi! Wannan ai nakuda take yi. Tun yaushe take a haka baku fada min ba?"

Sunkuyar da kansa Abbas yayi sannan yace:

"Tun wajen sha biyun daren jiya nace zan tashe ki ta hana ni, yanzu ma da ƙyar ta bari na kira ki."

"Haba Ummie haihuwa ai ba a bar wasa bace da zakiyi hakan. Banda abin ki tun jiyan ba sai mu tafi asibiti ba. Maza ka nemo abun hawa mu tafi asibiti."

Ta faɗa tana kallon sa. Cikin zafin nama ya miƙe ya nufi waje.

Tafiyar sa da kamar miniti goma sha biyar  ya shigo ya hau saman da sauri. Amma yana hawa me zai gani: jariri a kwance akan kujera an nannadeshi da zani. Umma tana ta kokarin gyara wajen ita kuma Ummie tana kwance akan wata katuwar katifa tana hutawa.

Da saurin sa ya ƙarasa cikin dakin cike da mamaki ya kalli Umma yace:

"Umma wai har ta haihu?"

Murmushi Umma tayi ta kalle shi tace:

"Ow har ne ma? Ai ni tuni nasan tana kan gaɓa,  shiyasa na koraka, kana fita ko soro baka je ba ta haihu. Gashinan an samu namiji."

Sunkuyar da kansa yayi cike da kunya. Sannan ya juyo ya kalli fuskar Ummie da kunya ta saka ta fara baccin karya. Amma duk da haka bai hana yaga murmushi a fuskar ta ba.

Shima kunyar ce ta kama shi. Hakan ya saka ya miƙe ya kalli Umma yace:

"Duk da hakan sai mu tafi asibitin ko?"

"Eh daman zuwa asibitin ai ya zama dole, duk da ta sauka lafiya, yana da kyau a bincika ta ita da jaririn. Bari mu gama kimtsawa sai mu tafi."

Umma ta faɗa tana ƙarasa goge wajen da jini ya zuba. A hankali ya nufi in da jaririn yake ya leka fuskar sa. Da mamakin sa ya kalli Umma yace:

"Umma wannan ai kamar su daya da Radiya ta.."

Murmushi tayi sannan tace:

"Wallahi munyi biyu da kai. Nima nace wannan ɗa da karanbani yake."

Dariya yayi sannan ya sake kallon jaririn yace:

"Wallahi yayi alkawari yadda Radiya take jiran zuwan sa. Aikuwa bari naje na taso ta."

Ya faɗa tare da miƙewa ya fice cikin sauri. Umma tabi bayan sa da kallo tana faɗin:

"Yanzu zai taso mana ita tazo ta hana mu sakat, ɗan baccin da zakiyi, ta hanaki."

Ta faɗa tana kallon Ummie. Ita kuwa murmushi kawai take yi.

A hankali ya ƙarasa cikin dakin. A kwance ya tarar da ita, tayi ɗaiɗai akan gado tana ta faman bacci. Ƙarasawa yayi ya fara dukan ƙafar ta.

"Ke Radiya ki tashi Anty Ummie ta haihu..."

Firgit! Ta miƙe tana turo baki. Sannan da ya sake maimaitawa ta zaro idon ta, ta murza su da hannun ta. Ba tare da tace komai ba ta duro daga kan gadon ta fita a guje yabi bayan ta yana kyakyala dariya.

Da gudun ta, ta kama matattakalar benen, saura ƙiris ta zamo. Umma tana juyo ta ta fara faɗin "Bismillahi ga masu hankali nan sun taho."

Ai kuwa da gudun ta ta ƙarasa cikin dakin ta dauki jaririn ta rungume tana ta faman murmushi ta rasa me zata ce saboda farin ciki. Can kuma ta kalli Ummie tace:

"Sannu Anty Ummie. Namiji ne ko mace?"

Murmushi tayi sannan ta kalli Umma a daidai lokacin da take fita daga ɗakin tana dariya sannan tace "namiji ne Radiya gashi nan kamar ku daya."

Murmushin jin dadi tayi sannan ta ajiye she ta fice da gudu. Umma tana kiran ta "Radiya zo kiyi alwala amma ina ta fice ta tafi fadawa makota."

Kafin karfe takwas gida ya cika da ƴan barka Radhiya ta gama haɗa jama'a. Daƙyar Umma ta kamota ta saka tayi alwala tayi sallar asuba.

                         **********************

Bayan kwana biyu da haihuwa suna zaune a tsakar gidan su. Wannan karon mai jego tana sama yayarta tazo. Abbas ya kalli Radhiya yace:

"Kin ce min zakiyi party suna ke da kawayen ki, nawa ne zai ishe ki?"

Murmushi tayi sannan ta kalle shi tace:

"Yaya ka kashe kudi da yawa, ka bar shi Anty Ummie da Yaya Hajjo zasu bani. Kai ka huta kaga maulidi ya kusa zaka kuma kashe wani kudin."

Murmushi yayi ya jawo ta kusa dashi sannan yace:

"Shiyasa nake son kanwata akwai tausayi to nagode kinji." Ɗaga masa kai tayi tana murmushi. Sannan daga bisani murmushin nata ya gushe a daidai lokacin da ta hango ƙofar shigowa. Da sauri ta ƙanƙame Abbas tana faɗin:

"Yaya kace kar ya dake ni don Allah."

Wani matashi saurayi ne da bai wuce shekaru ashirin ba ya shigo gidan. Fuskar sa a daure babu alamar wasa ya nufo in da suke ya dauki takalmi yayo kanta zai fara duka.

Abbas ne ya fara ƙoƙarin ƙwace takalmin yana ɓoye ta a jikin sa yana faɗin:

"Kai! meye haka? Me tayi maka zaka dake ta? Allah ka dake ta sai ranka ya baci..."

"Wai yaya kaji wani zagi da yarinyar nan tayi akan kunne na. Saboda an raba su faɗa. Ita bata da aiki daga gulma sai dambe. Wallahi zan kama ki ne Allah sai na dake ki tun da na rantse..."

Ya ƙarasa maganar tare da jefar da takalmin ya nufi dakin sa. Ita kuwa Umma tana daga zaune tace:

"Ai sai baya nan zaka zane ta, tun a bata jin magana mara kunya kawai."

Cikin kuka Radhiya ta kalli Abbas tace:

"Wallahi Yaya in baka nan duka na Yaya Sadiq yake yi Allah..."

Share mata hawaye yayi sannan yace:

"Allah ya dake ki sai na rama miki. Ki rabu dani dashi..."

Cikin sauri Umma ta katse shi da cewar:

"Wai kai me kake so ka mayar da ita ne? Gabaɗaya ka shagwaba yarinya bata jin maganar kowa in ba taka ba?"

Gyara zaman sa yayi sannan ya kalle ta yace:

"Umma kin sani yarinyar nan marainiya ce ba uwa ba uba, ai abun a tausaya mata ce.."

"Ba irin wannan tausayin ba" ta katse shi. "Wannan lalata ta kake so kayi malam." Ta ƙarasa maganar tare da miƙewa tana faman fada. Shi kuwa jin ta kawai yake yi ba don ya yarda ba.

"Yayana ai kai ne babana ko? Anty Ummie babata?" Ta katse shi. Cikin wani yanayin tausayawa ya kalle ta yace:

"Eh Radiya ta. Amma Meyasa kike zagi? bana hanaki ba?"

Sunkuyar da kanta tayi kasa. Cikin hikima ya fara yi mata fada wanda ga dukkan alamu fadan ya shige ta. Ɗagowa tayi tace masa: "Sai su dinga ce min Rady baby ni kuma nace musu kai kadai kake fada basa ji."

Murmushi ya sake yi ya jawota jikin sa. Sannan yace: "my Rady baby." Suka yi dariya gabaɗayan su.

To ranar suna da ta zagayo an sha shagali. Abbas yayi kokari matuka wajen hidindimu kala kala sai dai Allah ya saka masa da alkhairi.

Su Radiya ansha shagali anyi party amma daga ƙarshe dole sai da akayi fada saboda ita sam bata daukar raini.

Abbas ne ya raba fadan da ƙyar. Da yazo jin ba'asi yaji wai daya daga cikin kawayen ce tayi gulma wai Abbas bashi bane ya haifi Radiya, aikuwa kokawa da Radiya kamar me, gata da karfi sai da tayi mata dukan tsiya. Da ƙyar Abbas ya raba faɗan ta hanyar shigo da ita cikin gida.

Sai da suka shigo gida sannan ta fashe da kuka. Radiya jaruma ce bata kuka agaban kawaye. A hankali Abbas ya jawota jikin sa ya hau share mata hawaye yana rarrashin ta. Sannan ya kalle ta yace:

"Ke ba marainiya bace nine baban ki, baki ga kamar ku daya da Muhammad ba?"

Cikin shagwaba ta kalle shi tace:

"To ai rannan naji kace min marainiya bani da iyaye."

Sake kwantar da ita yayi ajikin sa. Sannan yace:

"Kuskure nayi kuma bazan sake ba. Matuƙar ina raye babu ke babu maraici Radiya. Kinji ni ko?"

Daga masa kai tayi sannan. Yacigaba da shafa bayan ta har tayi bacci. A hankali ya juyo da fuskar ta ya ƙura mata idanu.

Bai san meyasa yake jin tausayin ta ba. Sam baya son abinda zai taba ta. Ya rasa dalili. Ko don yasan zafin maraici ne? Yasan wahalar suma da suka sha bayan mutuwar mahaifin su?

Ajiyar zuciya ya sake yi sannan ya sake jaddada aniyar sa a zuciyar sa. Matukukar yana raye bazata rasa komai ba. Duk abinda take bukata zai samar mata dashi. Duk wata hanya zai bi wajen inganta rayuwar ta.

Da haka ya miƙe ya kwantar da ita akan gadon sannan ya nufi waje.

Ƙafar benen ya kama ya nufi ɓangaren sa. A zaune ya tarar da Ummie tana canjawa jaririn kaya. Tayi wanka dakin an gyara shi sai kamshin turaren wuta ne yake tashi.

A nutse ya ƙarasa in da take, ya zauna a gefen gadon yana kallon fuskar jaririn. Sannan ya ɗago ya kalle ta tayi masa wani lallausan murmushi shima ya mayar mata. Sannan yace:

"A kullum kamannin yaron nan sake zama na Radiya yake yi na rasa me yasa?"

Murmushi ta sake yi sannan tace:

"Sharrin jini kenan. Ai duk in da yake sai ya nuna kansa. Kuma ai in dai da amana dole na na haifo mai kama da ƴar gaban goshin ka."

Murmushi ya sake yi alamar yaji daɗin maganar ta. Sannan ya miƙe ya shiga bandaki domin yayi wanka.

Sai da aka gama shagalin suna sannan Radhiya ta fara zuwa makarantar secondry school a karo na farko.

Abbas ne ya tsaya tsayin daka akan samar mata wata babbar unity school da take birnin Kano. Saboda da boarding school taci, amma fafur tace ba zata jeba shima daman baya so haka ya dage ya samar mata wata.

To kamar yadda al'adar kowacce makaranta take, haka Abbas ya shirya komai ya ɗauke ta a machine din sa kirar Lifan ya nufi makarantar da ita.

Bayan an kammala yi mata interview take aka tabbatar da Radhiya a matsayin daliban da zasu bakunci wannan makaranta.

Saboda ba iya iya rigima da rashin ji Radhiya ta iya ba, tana da matuƙar kaifin ƙwaƙwalwa.

Wannan shine karo na farko da ta saka ƙafar ta a wannan makaranta, wadda itace mafarin ƙaddarar ta...