ƘWAI BIYU

Chapter Five

by @thehealerspen654

BAYAN SHEKARA UKU


Tsawon shekaru hudu kenan da auren Radiya har yanzu ko batan wata bata taba yi ba. Saboda gazawar da Uncle Sani yake dashi akan ta, sam ba tsarar auren sa bace yanayin halittar su ba daya bace shiyasa har yanzu ta gaza samun ciki.


Kasancewar a yanzu ta kammala karatun ta na Nursing a bangaren tana internship a babban asibitin koyarwa na Malam Aminu Kano da yake birnin Kano.


Idan ka ganta sam bazaka ce tana da aure ba, itama bata cika fada ba. Gashi ta zama cikakkiyar mace kyakkyawa ga diri sai dai babban abin sha'awar shine ko kusa Radiya bata bleaching tana nan da natural beauty din ta mai jan hankali wanda hakan ya saka take matuƙar birge mutane.


Radiya ta dada wayewa, ta goge sosai turanci ya zauna a bakin ta, musamman yadda ta hadu da kewaye wayayyu, sannan ga kuma zaman hostel da tayi, sannan tana da kaifin ƙwaƙwalwa da saurin rike abu. Kullum tas zaka ganta cikin fararen kayan ta saboda tsafta. Ga jan aji da yanga wannan ya saka ta ke jan ra'ayin maza da yawa. 


Amma kokusa bata kula kowa, saboda ita a duniya bata ga wani namiji da yake birge ta ba sama da Uncle Abbas,  duk da kasancewar ta yar gayu da iya wanka, amma tana kiyaye hakkin auren da yake kanta.


Yau ma kamar kullum bayan ta dawo daga asibiti ta  shigo gida ta fara ƙoƙarin ɗora girki. Take taji marar ta ta sake daure mata. Wannan ciwon nata in da sabo ta saba, hakan ya saka ta fito da sauri a daddafe ta koma daki ta dauko maganin da ta saba sha ta sha take bacci yayi awon gaba da ita.


Bayan Uncle Sani ya dawo ya tarar da ita a wannan yanayin ya fara kici kicin ɗora musu abinci saboda koda wasa baya nuna mata wani abu, hasalima yanzu lallaba ta yake yi, saboda ta dada wayewa sosai ya lura idan ya takura mata zata iya bijre masa gabaɗaya, kuma asirin sa zai tonu, hakan ya saka yake lallaɓa ta kamar kwai.


Bayan ta farka ta tarar ya gama abincin da sauri ta miƙe ta shiga toilet tayi wanka ta fito tayi sallah sannan ta fara cin abinci zuciyar ta sam babu dadi. Hankalin ta ya fara karkata akan samun haihuwa amma gudun kar Uncle Sani yaji wani abu a ransa ya saka bata taba furta masa. A tunanin ta tun da shima ya haƙura yake zaune da ita haka dole itama tayi hakuri. A hankali ta fara bincike akan mafita.


BAYAN SHEKARA GUDA 


Yana kwance akan gado ya kalli Radiya da take gugar fararen uniform din ta yace:


"Kin ga wani health organization suna bukatar ma'aikata kuma mata amma under 35 years zasu dauke su aiki ga portal nan na tura miki ta WhatsApp ki gwada ko Allah zai sa a dace."


Tsayawa tayi kasaƙe tana kallon sa tace:


"Wannan wanne organisation ne lallai sai mata kuma su kayyade shekaru?"


Miƙo mata wayar yayi ta karɓa ta kalla cike da mamakin tace: "Kuma imagine environment din very clean ya birgeni sosai amma ai a Abuja ne, sannan kuma sunce unmarried, kaga marasa aure suke nema kawai."


Murmushi yayi ya mike zaune ya kalle ta yace: "Radiya ƙasar nan fa ta rikice kawai ki cike, ke yanzu wa zai kalle ki yace kina da aure? Ai kawai ki cike kisa unmarried bamu san ta in da za'a dace ba."


Taɓe bakin ta kawai tayi tare da cewa: "tura min to, Allah yasa a dace."


Haka ya tura mata ta cike cike komai ta ajiye wayar ta fara sabgogin ta.


Washegari da safe ta shirya tsaf zata tafi private hospital din da take aiki, wayar ta ta fara kara,  sunan Anty Ummie ne ya bayyana akan screen din wayar, da sauri ta dauka cike da mamaki wannan kira haka na safe. 


Yanayin yadda taji muryar nata ya ɗaga mata hankali saboda ji tayi kamar tana kuka. Cikin sauri tace:


"Anty Ummie lafiya meya faru?"


Cikin shesshekar kuka ta amsa: "Abban Muhammad ne bashi da lafiya tun jiya da magariba aka shigo dashi wai faduwa yayi yana ta haki, cikin dare dole aka fito aka kai shi asibiti yanzu haka muna asibitin Malam Aminu Kano an saka masa oxygen."


Cikin matsanancin rudani Radiya ta fara ambaton "Innalillahi wa'ina ilaihi raji'iun! Tare da faɗin gani nan zuwa."


Hankalin ta a tashe ta sanar da Uncle Sani bata jira shi ba duk da yace ta tsaya ya kaita amma ta fice cikin sauri ta nufi waje tare da laluben number asibitin da take aiki ta basu uzurin ta.


Tana isa kasancewar da uniform din aikin ta ajikin ta sannan zaman sa tayi a asibitin ya saka ta san mutane sosai hakan ya saka ta shiga direct ɗakin da aka kwantar dashi.


Cikin matsanancin tashin hankali ta ƙarasa in da yake idon ta yana zubar da kwalla ta ƙarewa Abbas kallo sai kokawa yake yi da numfashi. Abun yayi matuƙar ɗaga mata hankali.


Haka ta fito ta nufi office ɗin likitan, da mamakin ta taga Dr. Nazir ne akan aiki ta san shi sosai sun saba. Haka ta shiga bayan sun gaisa ta tambaye shi abinda yake damun Abbas.


Take  ya fara yi mata bayanin da cewar damuwa ce tayi masa yawa shi ya saka jinin sa ya hau sosai ya fara taba masa zuciya amma inshaAllahu komai zai daidai ta da zarar jinin sa sauka kuma idan an bashi magunguna da allurai zai samu sauki.


A sanyaye ta fito sai sannan ta gaida Umma da Anty Ummie sannan ta kalle su tace:


"Ina takardar maganin?"


A sanyaye Umma tace:"Sadiq ya tafi siyowa."


Jinjina kan ta kawai tayi zuciyar ta cike da mamakin wannan wacce irin damuwa ce da har zata saka yaya ya shiga irin wannan yanayin.


Kimanin kamar mintuna goma sai ga Sadiq ya shigo da magunguna da allurai ya miƙo mata, ta karɓa ta koma wajen likitan, tare suka fito suka nufi dakin da Abbas yake suka fara kula dashi.


Bayan sun kammala Dr. Nazir ya kalle ta yace: "Ba zaki tafi wajen aikin ki ba? Ai jikin nasa da sauki."


Girgiza kan ta tayi sannan tace: "Bazan iya ba zan zauna nackula dashi kawai."


"OK hakan ma yayi. Allah ya bashi lafiya." Ya faɗa tare da ficewa. "Ameen" kawai ta amsa tare da kurawa Abbas ido da yake bacci hancin sa dauke da oxygen.


Sai yamma Abbas ya farka. Har yanzu Radiya tana zaune sai kai kawo take yi akan sa. Dadin ta ma tayi matuƙar kokari ta samar musu ameinity room suna zaune su kaɗai. Yana bude idon sa ya iske Radiya a kusa dashi ya saka hannun sa ya kamo nata tana yi masa sannu yana amsawa tare da kokarin karfafa jikin sa.


Haka su Umma suka ƙaraso suna yi masa sannu. Sannan zuwa dare da likitan ya dawo yayi musu umarnin da su tafi gida baya bukatar hayaniya Sadiq ya isa ya kula dashi.


Haka kuwa aka yi suka fito gabadaya har Radiya, duk da bata so hakan ba amma Abbas ya takura mata sai da ta tafi.


Washegari tun sassafe ta tashi tayi girki ta nufi asibiti. Wannan karon Uncle Sani ne ya kaita suka gaisa da Abbas ya wuce wajen aiki. Sai da ta tabbatar da Abbas ya karya sannan ta kalleshi tace:


"Yaya me yake faruwa? Me yake damun ka haka?"


Murmushi yayi sannan ya kalle ta yace: "Babu abinda yake damu na Radiya."


Shagwabar da fuskar ta tayi sannan ta sake kallon sa tace: "Yaya dole akwai abinda yake damun ka don Allah ka fada min wannan ciwon naka damuwa ce take kawo shi, ka fada min please."


Kare mata kallo yayi sannan yace: "Ni fa ban san me yake faruwa ba, kuma wannan yanayin na daɗe ina jin sa kawai dai bai kai yanzu karfi ba, sai kuma kwana biyun nan akwai ƴar matsala a kasuwa shine kawai. Amma banda haka ba zance miki ga abinda yake damu na ba, ki kwantar da hankalin ki.


Kin san kuma daɗindawa munyi gadon hawan jini shine silar mutuwar Baba kuma kin ga nima shekaru sun fara ja dole sai anyi hakuri."


Jinjina kan ta Radiya tayi alamar gamsuwa. Amma duk da haka sai da tayi masa nasiha tare da kwantar masa da hankali shi kansa yaji dadi sannan, daga bisani su Umma suka iso sun yi farin ciki sosai da ganin yadda Abbas ya samu lafiya.


Satin sa uku a asibitin sannan aka sallame shi. Sai da  aka tabbatar da ya samu lafiya sosai sannan aka sallame shi tare da bashi shawarwari. Duk da ya samu lafiya amma Radiya kullum a hanyar zuwa gida take tana kula dashi sai da ta tabbatar da yaji sauki har ya fara fita kasuwa sannan ta haƙura ta daina zuwa.


A wannan sintirin da ta dinga yi Umma da Anty Ummie suka matsa mata sosai akan batun haihuwa suna ce mata suje asibiti a gwada su.


Hakan ya saka dole tayi musu karya tace matsalar daga gare ta ne amma tana kan magani abun yayi sauki sosai. Wannan maganar tata ta saka sun tausaya mata matuka har kuka Umma tayi.


Ita kan ta abun yana damun ta amma babu yadda ta iya haka zata haƙura ta zauna har zuwa lokacin da ubangiji zai kawo mata mafita saboda gaskiya bata son abinda zai kawo mata matsala tsakanin ta da mijin ta.


Misalin karfe 12 na rana tana asibitin da take aiki wannan ciwon marar ya sake motsa mata. Da gudu ta nufi office ɗin Dr. Saleema kasancewar itace on duty. Bayan ta kammala yi mata allurai ta dubeta tace:


"Radiya kina daukar wannan case din naki da wasa ko? Is very serious issue Idan kika ci gaba a haka sai dole anyi miki aiki an zuƙe abinda yake taruwa a marar ki fa."


Lumshe idon ta tayi alamar ta gaji da fadan da take mata a kullum sannan tace:


"Maman twins ya zanyi a haka yanayi na yake ni kaina kin san bazan so na zauna a hakan ba, amma a haka zan haƙura har Allah ya kawo minafita..."


"Radiya mu fadawa kanmu gaskiya,  kin sani sarai laifin mijin ki ne ba daga ke bane. Kuma ma tun da yasan bazai iya gamsar dake ba ya haƙura ya daina jagwalgwalaki mana tun da abun ya zame miki larura." Ta faɗa ranta a bace.


Murmushin takaici Radiya tayi sannan ta kalle ta tace:


"Ya daina kulani Anty? To ya kula wa kuma?"


Itama murmushi tayi sannan tace: "Ga kuma kishin ki na tsiya ba kyaso a taɓa mijin ki. Amma seriously Radiya ku nemi mafita abun naki is getting worst sannan ga matsalar rashin haihuwa duk tafi damuna."


Murmushi ta sake yi sannan tace: "Yana kan magani har yanzu haihuwa kuma lokaci ne idan lokacin yazo za'a samu."


"Allah ya kyauta" Dr. Saleema kawai ta iya fadi tana mamakin wannan irin soyayya ta Radiya.


Bayan ta dawo gida tana zaune wayar ta tayi ringing bakuwar number ta gani, sai da tayi kamar bazata ɗaga ba sai kuma daga bisani ta dauka tare da sallama. Bayan an amsa aka fara yi mata bayani kamar haka;


"Good afternoon. Am I speaking with Radiya Hamza Gaya?"


Cikin nutsuwa tace: "Yes, this is Radiya speaking."


Ta daya ɓangaren akace:"Good afternoon, Radiya. My name is Daniel. I'm calling from Concordia Institute. You filled an online application form with our organization some weeks ago."


Radiya ta ɗan kama kanta alamar mantuwa, sai daga bisani ta tuna da link ɗin da Uncle Sani ya tura mata sannan tace: "Oh... yes, I did. Please go on."


Ta daya ɓangaren aka ci gaba da magana: "We're calling to confirm if you are still interested in the position you applied for."


Ta sake cewa:"Yes, I'm still interested."


"That's good to hear. May I ask, are you currently available for work?"


"Yes, I am available."


"Alright. The next stage of our recruitment process is a physical interview, and it will be held in Abuja."


Radiya ta danyi jim sannan tace: "Okay..."


"The interview is scheduled to take place within the next three days. Will you be able to attend if shortlisted?"


Duk da ɓata san wanne irin aiki bane kuma ta san da wuya ta iya zuwa har Abuja amma bata san lokacin da ta tsinci kan ta da amsa musu ba: "Yes, I can attend."


"Excellent. We will send you the interview details, flight ticket, venue, and date via SMS and email before the end of today."


Cikin sauri tace:"Alright, thank you very much."


Sannan shima ya amsa da: "You're welcome, Radiya. If you have any questions, feel free to reply to the message we'll send."


"Okay. Thank you for calling."


Ta iya fada tare da kashe wayar cike da mamakin wannan wanne irin aiki ne haka harda turo da ticket din jirgi? Ko dai Allah ya amshi addu'ar ta zata samu aiki mai kyau domin ta kula da ƴan uwanta musamman ma yayan ta Abbas da yake matuƙar bata tausayi. Sai dai kuma aiki a Abuja tana ganin kamar da wuya gurguwa da auren nesa.


A ƴan mintuna komai suka sauka akan text message din ta da email dinta, ciki har da flight ticket. Abun ya matuƙar bata mamaki. 


Abbas yana dawowa ta sanar masa. Aikuwa ya hau murna. Ita abun nasa ma har mamaki ya bata hakan ya saka ta kalle shi a ƙufule tace:


"Wai kai ko kishi na ma baka yi, in tafi har Abuja ko a jikin ka?"


Murmushi yayi sannan yace:" Na yarda da matata duk in da taje Allah zai tsare min ita. Kin ga idan aikin nan ya tabbata ai kakar mu ta yanke saka sai mu koma Abuja da zama kinga kin zama Hajiya ko? ni kuma mijin Hajiya."


Murmushi tayi saboda ya koɗa ta. Haka yacigaba da zigata a haka har ya samu ya shawo kanta ta haƙura ta fara shirin tafiya Abuja amma ba tare da sun fadawa kowa ba, saboda ta tabbatar da a gidan su baza'a barta ba.


BAYAN KWANA BIYU 


Isar ta garin Abuja ke da wuya wata lafiyayyiyar mota tazo ta ɗauke ta a Airport direct aka wuce da ita Fraser Suites hotel da yake a 294 Leventis Close, Central Business District, Abuja.


Wannan hotel yayi matuƙar kayatuwa. Radiya tasha kallo ta rasa me zatayi a zuciyar ta, farin ciki, kokuwa tsoro zata ji. Haka ta danne zuciyar ta ta nufi masaukin ta, ta kira Uncle Sani video call suka sha hira tare da nuna masa wani bangare na hotel din.


To Washegari misalin karfe goma na safe ta shirya tsaf cikin wata bakar Abaya tayi mata kyau sosai. Taji an Ƙwanƙwasa ƙofar ɗakin, daman tuntuni ta sani hakan ya saka ta dauko jakar ta da wayar ta ta nufi waje. 


A tsaye ta tarar da driver da ya ɗakko ta daga Airport jiya, bayan sun gaisa sannan ya shige gaba tabi bayan sa suka isa parkin space ta shiga motar zuciyar ta tana ta bugawa amma ta daure tare da ambaton sunan Ubangiji har suka isa wata katafariyar ma'aikata wadda kyawun ta da tsaruwar ta sai wanda ya gani.


A wani kayataccen hall aka kaita in da ta tarar da kujeru a ƙalla guda 50. Ga computers na zamani a akan kowanne table. A ƙalla akwai mutum 30 a zaune,  kuma babban abinda ya bata mamaki duk musulmai ƴammata kuma kusan shekarun su daya. Ƙwaƙwalwar ta ta fara raya mata wani abu. Amma haka ta haƙura ta zauna. 


Bayan kamar mintuna 30 hall din ya cika aka fara basu sanarwar cewa zasu gabatar da digital test akwai tambayoyi guda hamsin ana bukatar kowacce ta cike su ba tare da tayi karya ba, sannan duk wadda ta kammala ta shiga lab za'a dauki sample na jinin ta. Mai sanarwar tayi nuni da wata ƙofar glass da take nesa da hall din.


Cikim rashin fahimta Radiya ta ɗaga hannun ta da niyyar tambaya, amma suka katse ta da cewar babu tambaya a yanzu sai bayan test. Haka ta haƙura ta fara amsa tambayoyin da suke acikin computer.


Babban abinda ya bawa Radiya mamaki shine; gaba daya tambayoyin sun karkata ne akan family medical history, sai kuma gynotype,  blood group da sauran su. 


Ko sau daya ba'a tambayi qualification  ba matsayin karatu kenan, abun ya bata mamaki sosai amma haka ta haƙura ta amsa tambayoyin ta miƙe ta nufi lab din aka dauki jinin ta sannan ta fito ta tsaya a parking space din tana jiran driver.


Wani abun da ya kara bata mamaki shine; yadda kusan kowacce mace da taje wajen driver da zai dauke ta a mota daban, wannan al'amarin yayi matuƙar saka shakku a zuciyar Radiya gashi ance sai ta zauna na tsawon sati guda a Abuja kafin ta koma gida.


Hakan ya saka data dawo masaukin ya ta zayyawa Uncle Sani komai. Shi sam bai damu ba sai bata ƙwarin gwiwa ma da yayi yana dada ce mata "yawancin health organizations haka suke bankuna ma suna yin hakan saboda suna son su dauki samari masu jini a jiƙa."


Ita kam har yanzu sam hankalin ta bai gama kwanciya da wannan aikin ba. Ta amsa ne kawai ba don komai ba don taga iya gudun ruwan su.


Amma matuƙar sati gudan nan ta cika suka zo mata da rainin hankali, ko abinda bata gamsu fashi ba, to kuwa babu abinda zai hana ta daukar hanyar Kano cikin gaggawa......