Chapter Seven
Laboratory din yayi shuru, sai sautin na'urar binciken kwayoyin halitta wato sequencing machine ne kaɗai yake tashi.
Dr. Kareem yana tsaye yana kallon fuskar monitor din da take gabansa, zuciyar sa sai bugawa take yi ya rasa dalilin da yasa yake jin hakan.
Amma kuma daga bisani ya alaƙanta al'amarin da tsoron rashin samun nasara da a kullum suke cin karo dashi yayin irin wannan gwajin.
A tsawon rayuwar aikin sa, yayi daruruwan bincike irin wannan, amma a kullum cikin faduwa suke domin rashin nasara akan ainahin nau'in ƙwayar halittar da suke nema.
Tsawon shekaru kullum faduwa suke sanarwa ba nasara ba, hakan ya sake ƙara gudun da zuciyar sa take yi saboda duk lokacin da zai fitar da sakamako irin wannan zuciyar sa tana bashi babu dadi amma wannan yanayin na yau yasha bambam dana kullum.
A hankali progress bar din ta fara sauyawa zuwa 42%... 43%...cike da mamaki Dr. Kareem ya matsa sosai jikin monitor din domin ya kara tabbatarwa da idon sa gaskiyar abinda ya gani.
"Wait..." Abinda ya faɗa kenan cike da mamaki.
Saboda ganin primary alignment panel din ya fara sauyawa automatically wanda hakan yana faruwa kadai idan na'urar ta karbi ƙwayar halittar da ta kasance ta musamman wadda samun irin ta sai a bincika acikin miliyoyi.
Take jikin sa ya fara rawa, hannun sa ya tsa cak! akan keyboard din computer, amma ya kasa danna komai, musamman lokacin da wata alamar gargadi ta bayyana a saman screen din computer.
Wannan karon ba jar alama bace ta nuna gargadi ko faduwa, a'a yaluwace da take nuna lallai ta samo wani abu da yake na daban wanda suka dauki shekaru masu yawa suna nema.
Numfashin sa ya tsaya cak! Rawar da jikin sa yake yi ya karu, haka bugun zuciyar sa ya kara karuwa. Cikin rawar murya yace: "that's not possible...ya Allah...!"
Haka na'urar ta cigaba da reading percentage din yana karuwa domin ta sake tabbatar da ta samu abinda ake nema.
Yana tsaye ya zubawa sarautar Allah ido, gani yake yi kamar a mafarki. Amma don ya sake tabbatar da abinda yake gani ya juya ya kwalawa abokiyar aikin sa kira: "Dr. Zainab...zo...ki..gani...."
Da saurin ta ta ƙaraso tana tambayar sa: "me ya faru ka samo wani abu ne...?"
Tana isa gaban monitor din ta kama bakin ta cike da mamaki, a daidai lokacin da yace mata: "look at the preliminary HLA alignment.."
"This is not real.... I can't believe this Doctor."
A hankali machine din ya tsaya da kansa, bayan ya kai adadin: 57%....58% adadin da suke tunanin kamar ba na gaske bane saboda matuƙar mamakin da ya lulluɓesu.
Durkushewa Dr. Kareem yayi akan gwiwoyin sa tare da kai goshin sa yayiwa Allah sujjada ya juyo ya kalli Dr. Zainab da take ta hawayen farin ciki yace:
"Abinda muke nema, muke yin aiki akan sa ba dare babu rana yau Allah ya cika mana burin mu acikin shekara goma yau dai mun samu abinda muke nema Alhamdulillah ya Rabbi...."
Ya ƙarasa maganar tare da ɗaga hannun sa sama yana dada jaddada godiyar sa ga Ubangiji. Ita kuwa Dr. Zainab sulale wa tayi ta zauna akan kujerar taci gaba da share hawayen farin ciki.
Su ma kenan da suka kasance ma'aikata....ina ga wanda ya saka su aikin....
Cikin zafin nama Dr. Kareem ya fara shirya sakamakon a jikin takardu jikin sa yana rawa, ya shirya file guda ya fito daga lab din da saurin sa ya nufi wani katon hall in da ma'aikata da yawa suke gwaje-gwaje mabanbanta.
Yanayin fitowar da yayi yaja hankalin kowa na wajen cike da farin ciki ya kalle su yace: "we won"
Take hall din ya dauki sowa da murna mara misaltuwa. Sannan ya nufi wani katafaren office da yake saman bene ya fara ƙwanƙwasawa cikin zaƙuwa.
Da mamakin ta ta taso ta bude.
Wata mata ce da zata kai a ƙalla shekara 47 ta taso ta buɗe cike da mamaki. Cikin zaƙuwa ya kalle ta yace: "We found only one after our long journey Dr. Cara..."
Idanun ta ta zaro a daidai lokacin da ya ratse ta gefen ta ya shige cikin office ɗin cike da murna ya nemi waje ya zauna ya fara daddana laptop ɗin da take hannun sa yana kokarin tura mata complete report din ta email.
A hankali ta ƙaraso jikin ta duk yayi sanyi saboda da mamaki, ta kalle shi acikin gurbatacciyar hausar ta tace: "Kana so kace min Sultan ya kusa samun yaro...?"
Cike da zaƙuwa ya amsa mata da: "very soon"
Jagwab! ta zauna akan kujerar ta, ta dafe kanta da taji alamar yana sara mata, sannan da sauri ta ɗakko wayar ta ta fara laluben wata number waya. Tayi ringing a ƙalla sau biyar tana katse wa, sannan daga bisani aka dauka.
Yana kwance akan wani hadadden gadon sa, gefen sa kuma wata kyakkyawar matashiya ce daga gani matarsa ce saboda yadda suke rungume da juna.
Idon sa a rufe ya saka hannu ya ɗakko wayar tasa da take kan side drawer, sannan a hankali ya bude idon sa. Sunan Dr. Cara da ya gani ne ya saka ya bude idon sa sosai tare da saurin miƙewa zaune ya kara wayar a kunnen sa:
"Hello!" Ya furta acikin muryar bacci mai cike da mamaki.
Cikin zaƙuwa Dr. Cara tace: "you need to come to the lab ASAP we have the issue..."
Sakko da wayar tasa yayi daga kunnen sa ya kalli agogon wayar, yaga misalin karfe hudu da rabi na dare. A hankali ya sake mayar da wayar kunnen sa sannan yace:
"Have you checked the time before...?"
"We have an immediate issue Sauban you need to come to the lab NOW!"
Ta faɗa tare da kashe wayar. Cikin sauri ya miƙe tsaye cike da mamaki. Matar sa da take gefen sa da taji duk yadda sukayi ta kalle shi tace:
"Allah yasa an dace."
Jinjina kan sa yayi kawai yace: "hmm....Ameen to amma abun da kamar wuya..."
Ya fada a daidai lokacin da ya ke saka dogon wandon sa sannan daga bisani ya zira T-shirt ya sunkuyo yayi mata kiss a goshi ya dauko mukullin mota ya fice ta bishi da addu'ar samun kariya daga Ubangiji.
Da sauri ya isa office ɗin nata, tana tsaye sai kai kawo take yi a office ɗin ta kaza samun nutsuwa. Yana shiga ta nufo shi da sauri ta kamo hannun sa cike da farin ciki ta riƙe shi gam tana faɗin: "Congratulations Sauban we did it..."
Jagwab! ya zube akan kujerar da take office ɗin ya kama kansa, take wani kuka mai karfi ya ƙwace masa. Sai da yayi mai isar sa sannan ya ɗago ya kalle ta a daidai lokacin da itama take share kwallar da ta kwaranyo mata yace: "Who's the luckiest?"
Zama tayi akan kujerar ta, tare da juyo masa da screen din laptop din ta. Take hoton Radiya Hamza Gaya ya bayyana a screen din. Cike da mamaki ya ƙarewa hoton nata kallo. Sannan ya ɗago ya kalli Dr. Cara yace:
"She's too young...imagine.... Wannan itace shekara mafi sa'a ga rayuwar Sultan. Also..what's her health condition.?"
Murmushi tayi sannan ta cigaba da magana:
"She's extremely safe, genotype, blood group, family medical report and everything is under control."
Murmushi yayi sannan yayi mata umarnin da ta tura masa da komai ta email din sa sannan daga bisani ya miƙe ya nufi waje cike da farin ciki.
Haka ma'aikatan suka nufo shi suna yi masa murna ciki harda Dr. Kareem wanda Sauban ya jinjina masa matuka tare da yi masa murna yadda wannan sa'a ta faɗo daga gare shi.
Daga nan Sauban bai koma gida ba, office ɗin sa ya wuce bayan yayi sallar asuba ya dukufa sosai da bincike kala kala game da rayuwar Radiya sai misalin karfe tara na safe sannan ya gama tattara komai, kana ya nufi wani katafaren gida wanda akai masa gini irin na shararrun masarautu.
*************************************
Yana kwance a wani katafaren gym wanda yake dauke da kayan motsa jiki na zamani kala kala yana ɗaga karfe, gym instructor nasa da yake a tsaye a kan sa yana kirga masa adadin da yayi.
Da ganin jikin sa kasan an daɗe ana bashi kulawa ta motsa jiki, kasancewar yadda ya murɗe gabaɗaya. Idon sa a rufe sai gumi yake yi tare da nishi a duk lokacin da ya ɗaga karfen.
Wuf! yaji an ƙwace karfen a daidai lokacin da ya ɗaga shi sama kafin ya sauke.
Wani lallausan murmushi ya saki idon sa a rufe sannan cikin sigar dariya yace:
"You're here..."
Dariya suka saka gabaɗaya a daidai lokacin da yake miƙawa couch din nasa karfen ya ajiye shi a mahallin sa, sannan ya bar wajen. Saboda ya tabbata tun da yazo to an gama motsa jikin.
A hankali ya bude idon sa daga kwance ya kare masa kallo sannan ya sake cewa:
"Nasan duk duniya babu wanda yake kishi da workout ɗi na sai kai..."
Suka sake fashewa da dariya.
Miƙo masa hannu yayi ya kama ya miƙe tsaye sannan ya kalli ƙirjin sa da damtsen sa yace:
"Sultan na rasa me kake nema a jikin nan naka, 160kg fa kake lifiting. Idan six packs ne gasu nan ka samu. To idan baka rage ba tun jikin ka yana birge mutane zai fara tsorata su."
Sake fashewa da dariya yayi. Sannan ya kalle shi cike da tsokana yace:
"Ai bazan daina ba sai na fara lifting 180kg at once. Ko so kake na fara tumbi kamar ka, look out your belly like pragnent woman."
Ya faɗa yana naushin cikin sa a hankali a sigar wasa.
Dariya suka sake yi sannan ya miƙo masa robar ruwa yasha ya sheka a fuskar sa. Suka nemi kan wani benci a cikin gym din suka zauna.
A hankali numfashin sa ya fara daidai ta. Sannan damuwar da take a tare dashi ta fara bayyana karara. Saboda ya tabbatar da wannan zuwan na Sauban faduwa zai sake sanar dashi ba nasara ba.
Duk motsin da yake yi Sauban yana kallon sa. Zuciyar sa cike da farin ciki da ɗokin ta yaya zai isar masa da wannan saƙo mafi soyuwa a zuciyar duk wani masoyin su.
Kafaɗar sa ya saka ya zunguri tasa, a sigar wasa, murmushin yaƙe yayi ba tare da ya kalli Sauban ba, sannan ya wayance tare da sake kai robar ruwan bakin sa.
Gyaran murya Sauban yayi sannan ya kalle shi yace:
"Have you checked your mails?"
"No....not..yet..!"
Abinda Sultan ya furta kenan muryar sa tana rawa, sannan ya miƙe ya kamo hannun Sauban ya miƙe tsaye yana kawar da fuskar sa ga dukkan alamu baya son zancen.
"Muje muyi breakfast..."
Kasaƙe Sauban yayi yana kallon sa. Sannan daga bisani ya ce:
"You know bro...na ɗauki alwashin cika maka burin ka ko da hakan zai zama ajali na ko..."
"I've told you several times nafi son ka a kusa dani fiye da yadda nake so na haihu..." Ya katse shi.
"You know what? Don't ever talk about this sheet again...Karka kuma cewa zaka mutu akan wannan. I know it's my destiny and may be it's devine timing idan Allah ya kaddara I'll father a child, Idan bai kaddara ba I'll not.
Kuma ba don nayi masa laifi ba, no it's just a testament, also like I said millions of time don't ever talk about this again, I've closed the chapter."
Ya faɗa tare da fincikar hannun sa suka fita waje yana ta faman sirfa masa fada wai shi a dole babu abinda yake damun sa.
Haka Sauban ya dinga bin sa yana kallon sa yana mamakin irin wannan tawakkali na Sultan, bai yi aune ba yaji hawaye sun fara wanke masa fuska.
A kullum cikin tausayin sa yake. Gashi yana cikin damuwa kowa ya sani, amma baya taba bari a fahimta sai dai shi ya dinga rarrashin na kusa dashi yana nuna musu babu abinda yake damun sa.
Ɗif! Sultan yayi a daidai lokacin da ya juyo ya kalli fuskar Sauban yaga ta jike sharkaf da hawaye. Wannan shine karo na farko da yaga Sauban yana kuka akan wannan case din.
A kullum shi yake bashi ƙwarin gwiwa, baya taba nuna damuwar sa a gaban sa. Hakan ya saka ya kama kafadun Sauban guda biyu ya fara jijjigashi da karfi yana faɗin:
"What's going on....? Don't you tell me....?"
Cikin shesshekar kuka Sauban yace:
".....we...won...we...found....her.."
Numfashin sa ne ya ɗauke, kansa yayi wata muguwar sarawa. Sannan ya kara dakumar kafadun Sauban da mugun karfin da sai da yaji ajikin sa, sannan yace cikin sigar lallashi:
"You know bama yin irin wannan wasan a tsakanin mu...please don't play with my emotions...please Sauban..."
Shima ya fashe da kuka.
A hankali Sauban ya sauke hannun sa daga rikon da yayi masa, sannan ya rungume she ajikin sa. Sultan ya ɗago da sauri ya kalli fuskar Sauban yace:
"Don't tell me...na kusa samun yaro..."
Jinjina masa kai Sauban yayi alamar tabbacin maganar, sannan suka rungume juna suna kukan farin ciki.
Sai da suka yi mai isar su sannan cikin zafin nama da zaƙuwa suka fara tseren shiga gidan domin sanar da matar gidan.
Haka suka kafa tseren gudu, duk inda suka ratsa a gidan masu aikin sai su bi su da kallo. Waɗan da suka kasance baki ne a gidan abun yayi matuƙar basu mamaki saboda basu taba gani ba.
Amma wadanda suka daɗe a gidan suka san su tun suna yara abun yayi matuƙar basu mamaki saboda rabon Sultan da Sauban su shiga farin ciki irin wannan har sun manta.
Haka suka yi ta tsere har suka iso ɓangaren ta. Tana zaune a wani katafaren palour, daya daga cikin masu aikin ta tana shafa mata magani a ƙafar ta. Da mamakin ta, tun daga nesa ta jiyo muryar ƴaƴan ta suna ambaton: "Ammey.."
Zumbur! ta miƙe tsaye, fuskar ta cike da mamaki. A daidai lokacin da suka iso palour suka rarumeta suka ɗaga ta sama. Sannan Sultan ya kalle ta yace cike farin ciki yace: "Guess what?"
Mamaki ne ya kamata ta fara bin su daya bayan daya da kallo. Sannan suka sauke ta, a hankali ta lalubi waje a gefen kujera ta zauna ta kama kanta.
Ta sani sarai, duk duniya dalili daya ne zai dawo mata da farin cikin yaran ta. Shine ace Sultan ya samu mahaɗin rayuwar sa wadda zata iya haifa masa ɗa.
Take wani hawaye mai zafi ya fara zirya a kumatun ta, ta ɗago ta kalle su, suma sun fara zubar da kwallah ta rungume su gabaɗaya a jikin ta tana faɗin:
"Nasan ko menene..…