Chapter Two: (Anuwar & Ameerah)
Tana tafe a acikin sabuwar motar da Daddy ya bata, zuciyar ta cike da tunani kala kala, sautin karatun Alqur'ani da yake tashi a hankali ya taimaka mata wajen daidaita nutsuwar ta, gefen ta kuma Junior ne yake barci ga dukkan alamu yau ya gaji.
Wayar ta da take caji ce ta fara ringing, ganin sunan da yake kai ne ya saka ta wata sanyayyiyar ajiyar zuciya, a hankali ta ɗauka ta kara a kunnen ta tare da cewa:
"Assalamu alaikum!"
Ta ɗaya bangaren aka amsa sallamar cike da kulawa:
"Waalaikumussalam! Lafiya kuwa har yanzu baku dawo ba?"
Mai da hankalin ta tayi kan hanya sannan tace:
"Lafiya ƙalau AMEERAH na biya wajen Daddy na kai masa monthly report kuma kinga shekara tazo ƙarshe dole sai kunyi min haƙuri, amma ganinan ina hanya with big surprise."
Ta ƙarasa maganar tana murmushi.
Cike da ɗoki Ameerah tace:
"Wow! to sai kun ƙaraso, but na tabbata but sweet ɗi na yayi bacci saboda nasan bazai jure ba, lokacin baccin sa yayi."
Cikin murmushin jin daɗi Nuratu ta amsa da:
"Eh! Kamar kin sani "
"Nasani ai, Allah ya dawo daku lafiya."
"Ameen" Nuratu tace tare da kashe wayar.
Misalin ƙarfe 7:48 na dare ta juya kan motarta inda ta shiga jerin gidajen da suke unguwar Tudun Yola acikin birnin Kanon Dabo.
Sau ɗaya tayi horn mai gadin ya taso da sauri domin ya buɗe amma ganin bai san motar Ba ya saka ya ɗan dakata kaɗan, sai data sauke glass sannan ya buɗe mata get din.
A sannu ta shiga wannan katafaren gida tare da yi mata sannu da zuwa.
Gidan matsakaici ne tsarin Duplex mai hawa biyu, amma fa ko quarter na Daddy bai kai ba, amma fa shima ya tsaru sosai da kayan gini dana ƙawar na zamani.
Rumfar ajiye motocin ta nufa tare da yin parking, wata kyakkyawar budurwa ce ta fito wadda shekarunta basu wuce shekaru 22 ba ta nufo ta cike da farin ciki tana cewa:
"Wow! what a big surprise? gaskiya Ukhty mota tayi kyau kin zama big Hajiya Ubangiji Allah ya tsare."
"Ameen!"
Nuratu ta amsa tare da mai da hankalin ta ga bakin ƙofar shiga palour, in da ta hango wani kyakkyawan saurayi da shima bai wuce shekaru 26-27 ba a tsaye, dogo ne fari tas mai ɗan faɗin kirji ga suma da gemu fal a fuskar sa, sanye yake da riga suiter da wando baƙaƙe ya naɗe hannun sa yana kallon ta tare da ƙarewa motar kallo.
Haɗe ranta tayi da ganin sa musamman da taga kallon da yakewa motar kuma yana tsaye bai ƙaraso ba.
Mai da hankalinta tayi kan Ameerah da take ƙoƙarin daukar Junior tace:
"Yau bai je asibiti bane?"
A takaice Ameerah tace:
"Yanzu ya dawo."
Ta amsa mata tare da rungume junior a kafaɗar ta ta nufi ƙofar shiga palour.
A dai dai wannan lokacin wata dattijuwa mai matsakaicin jiki ta ƙaraso cike da far'ah tana faɗin:
"Sannu da zuwa Nuri."
Murmushi Nuratu tayi sannan tace:
"Yauwa Baba Rabi ya gidan?"
Ta faɗaɗa far'arta tace:
"Gida Alhamdulillah! ga kuma sabuwar mota Ubangiji Allah ya kaɗe fitina Allah ya tsare gaban ki da bayan ki kema Allah ya faranta miki rai kamar yadda kike faranta mana."
Ta ƙarasa maganar tana ɗaukar jakar Nuratu ta da nufi hanyar shiga cikin gidan.
Ita kuwa Nuratu "Ameen" kawai take amsawa a zuciyar tare da ƙarasawa ƙofar shiga palour.
Har yanzu yana tsaye, da gani isowarta yake jira, sai da ta ƙaraso dab dashi sannan ya kalleta yace:
"Congratulations!"
Fuskarsa cike da tambayoyi, kallon sa kawai tayi fuskar ta a ɗaure ta ɗauke kan ta ba tare da tace komai ba ta ratse ta gefen sa ta wuce.
Rintse idon sa yayi alamar yaji zafin abinda tayi masa, sannan ya ƙara mai da hankalin sa kan wannan sabuwar motar ta Nuratu yana nazarin wani abu a ransa, sannan yana fasalta tsadar motar, can ya ƙara harzuƙa yabi bayan ta cike da hasala yana ƙwala mata kira:
"Ukhty!"
Da ƙarfi.
Bai tarar da kowa a cikin palour ba haka ya ɗaga kansa ya hangota a sama tana hawa matattakala ko waiwayowa bata yi ba, ya sake harzuƙa yabi bayanta da sauri yana daɗa ƙwala mata kira, kafin ya ƙarasa inda take ta shige ɓangaren ta ta rufe ƙofa.
Hakan bai saka ya haƙura ba ya ƙarasa ya fara buga ƙofar da ƙarfin sa yana kiran ta.
Can ya jiyo muryar ta ta bayan ƙofa tana cewa:
"Ka tafi ka bani waje bani da lokacin ɓatawa akan ka, Please ANUWAR ka barni na sara".
Sannan ta cigaba da faɗin:
"Shikkenan bani da daraja a idon ka duk lokacin da kaso sai ka keta ni, yau da jarabar ka nayi breakfast, I'm always on my words baka isa baƙin cikin ka ya kashe ni ba, saboda haka ka tafi ka bani waje tun kafin rai na ya gama ɓaci akan ka..."
Juyawa yayi tare da yin wani mugun huci yayi ball da flower vase ɗin da yake wajen ya girgiza kan sa tare da yin ƙwafa ya nufi sashen sa.
Bisa ga al'adar wannan gidan kowa sai ya hallara sannan ake fara cin abincin dare, yau gaba ɗaya kowa yazo amma ban da Nuratu.
Gabaɗayan su sunyi shiru, dukan su ransu babu ɗaɗi ganin har yanzu bata sakko ba, banda Anuwar da hankalin sa na kan danna waya yana nuna kamar bai damu ba.
Ameera ta kalli agogon wayarta misalin 9:45 na dare, ta juya ta kalli Anuwar, harararsa tayi ba tare daya gani ba tasan duk laifin sa ne shiya ɓatawa Ukhty rai tun da safe sannan yanzu ma taji duk abinda sukayi, ta miƙe a sanyaye ta hau sama duk jikin ta ba ƙwari saboda a kullum Ukhty ce take bi bangaren kowa ta kirawo shi domin cin abinci wani lokacin har ta ƙwace wayoyinsu amma yau dai shiru ba alamar ta.
A hankali ta murɗa ƙofar shiga bedroom ɗin tare da yin sallama.
A zaune ta hangota akan makeken gadon ta, ga takardu birjik a gabanta, ta kara wayarta a kunnen ta tana danna laptop da ɗaya hannun, ga dukkan alamu da Daddy suke waya.
Ta ƙarasa a sanyaye ta tsaya sai da ta kammala wayar ta ɗago kai ta kalleta kaɗan ta ɗauke kai ta ci gaba da duba papers ɗin tace:
"Bibi na ya akayi? (sunan da junior ya saka wa Ameera tun kafin ya iya magana)"
Ameera ta daidaita tsayuwar ta sannan tace:
"Ukhty kowa fa yana jiran ki zamu ci abinci baki sakko ba."
Ba tare da Nuratu ta ɗago ba tace:
"Na ƙoshi ne ai."
Ameera ta kwantar da muryarta sannan tace:
"Please Ukhty nasan yaya ya bata miki rai da safe don Allah kiyi haƙuri kizo mu ci abinci, kin san fa babu wanda zai iya ci in baki zo ba."
Murmushin takaici Nuratu tayi sannan ta ɗago ta kalleta tace:
"To in kunga dama sai ku kwana da yunwa."
Ameera zata ƙara magana Nuratu ta nuna mata hanyar fita tare da faɗin:
"Kar ki ɓata min rai please."
Ba yadda Ameerah zata yi haka ta fita ran ta a ɓace.
A sanyaye ta sakko ta nufi dinning ba wanda ta gani sai ta kalli plate ɗin Anuwar taga ko yaci abinci, sai ta lura da akwai abincin aciki amma fa ga dukkan alamu kaɗan yaci.
Sannan ta zauna ta ɗibi kaɗan taci ba don ranta na so ba sai don tayi maganin yunwa, ta kammala ta nufi ɓangaren ta tare da junior kasancewar tuntuni ya tashi yaci abincin sa har ya kuma yin bacci.
Misalin 12:48 na dare Nuratu ta kammala aikin nata, kasancewar ƙarshen wata ne kuma ƙarshen shekara za'a yi wa mutane albashi gashi bata so wata ya ƙare ba'a bawa kowa hakkin sa ba. Hakan ya saka ta takura kan ta don ganin komai ya daidaita.
Haka ta tattara komai ta miƙe ta nufi toilet, tayi alwala tazo tayi nafila tare da yin addu'o'inta da ta saba, ta miƙe da niyyar ta kwanta.
Wani ƙugin yunwa taji cikin ta yayi, sannan ta tuna ko breakfast ɗin kirki rikicin Anuwar bai barta tayi ba, kuma bata wani ci abincin kirki a gidan Daddy ba, ta tsaya ta auna taga ko zata iya kwanciya a hakan, can dai taga abun bazai yiwuba duk da bata son cin abinci after 9:00 na dare saboda gujewa ƙiba, amma ba yadda zatayi saboda yunwa zata iya hana ta bacci, bata da zaɓi dole ta nufi ƙofar fita domin ta nema wa kanta abinda zata ci.
Indomie ta fara ƙoƙarin sarrafawa, kasancewar dambun shinkafa suka yi, duk da tana son shi amma bazata iya ci ba a daren nan yayi nauyi da yawa.
Tea flask ɗin ta ta girgiza kasancewar always ba'a bar ma ta shi babu tea aciki, ta ɗakko ta ɗora a dining, ta kunna gas ta ɗora ruwa ta fasa ƙwai tana jiran indomie ta dahu ta soya.
Can ta tuna da wani saƙo da zata turawa Daddy hakan yasa ta nufi dinning inda ta ajiye wayar ta ta ɗauka ta nufin kujerun da ke palour ta nutsu ta tura masa ta zauna tuni tunanin rayuwa ya kufce mata ta manta da abinda ta ɗora, ba ta ankare ba bacci yai awon gaba da ita.
Can cikin baccin ta taji ana taɓa ƙafarta, firgit! ta farka.
Anuwar ta gani a tsaye hannun sa riƙe da plate da kuma tea cup, sai sannan tayi ajiyar zuciya tare da dafa kanta, can cikin ranta tana mamakin yadda akayi ta fara zama mai sakaci, tabbas abubuwa sun fara yi mata yawa, dole tana buƙatar hutu ko kuma mataimaki.
Ta ɗago kanta ta kalleshi dai dai lokacin da ya ɗakko ɗaya daga cikin coffee tables ɗin da suke palour, ya ɗora plate ɗin akai sannan ya ci gaba da juya tea ɗin da yake hannun sa.
Sai da ya tabbatar da tea din ya saisaita sannan ya miƙa mata, ba musu ta saka hannu biyu ta karɓa ta fara sha kamar wata mai cutar yunwa.
Anuwar ya ƙura mata ido cike da tausayin ta saboda wannan yanayin nata ya tuna masa da rayuwar su ta baya.
Bayan ta kammala cin abincin ta miƙe ta nufi saman bene ya bi bayanta da wani irin kallo kasancewar babu wanda yace da ɗan uwan sa komai.
Maimakon ta nufi sashen ta, kama matattakalar benen ƙarshe tayi inda sashen Anuwar yake, kasancewar gidan hawa biyu ne, ƙasa ɗakunan baƙi ne da ɗakin da Baba Rabi take, sai ƙaton palour su da kuma wani ƙarami ta gefe sai haɗaɗɗen kitchen ɗin su shima babba.
Hawan farko kuma ɓangaren ta ne da yake kamar ciki da palour sai kuma ɓangaren Ameerah da junior shima kamar na Nuratu, kasancewar tare suke kwana, sai kuma wani ƙaton palour still, sannan wata matattakalar da zaka sake haurawa hawan ƙarshe inda ɓangaren Anuwar yake shi kadai, sai kuma wata baranda wadda aka ƙawatata da glass da grass carpet gwanin sha'awa wanda kana kallon ko ina daga nesa.
To wannan barandar Nuratu ta nufa domin tana buƙatar fresh air, nan take zuwa daman ta zauna idan tana buƙatar kaɗaici.
Duk da an ƙawata wajen da wasu kujeru guda biyu amma ta nemi waje ta zauna akan grass carpet ɗin, ta ɗaga kan ta tana kallon sararin samaniya, wadda take a washe ga farin wata ya haske ko ina, garin yayi shiru sai wata iska da take ƙaɗawa a hankali, wannan yanayin ya tuna mata da abubuwa da dama na rayuwarta ta baya.
A hankali taji wani zazzafan hawaye sun gangaro kumatun ta, ta buɗe idonunta ta kalli gefen ta saboda motsin da taji, Anuwar ta gani a tsaye yana kallonta, duk da babu isasshen haske a wajen amma ta gane yana cikin damuwa.
Fakar idon sa tayi ta goge hawayen da suka gangaro mata saboda duk rintsi bata taɓa bari Kannenta suga hawayen ta. Mai da hankalinta tayi kan sararin samaniya sannan ta buɗe dasasshiyar muryar ta tace:
"Anuwar!"
Juyowa yayi ya fuskanceta raunane, sannan ta ci gaba da magana ba tare da ta kalleshi ba:
"Meyesa kake zargina da zina?"
Ba ƙaramin razana shi maganar tayi ba, hakan yasa ya nemi duk wasu kalmomi nasa ya rasa, ya tsaya a dabalbalce kawai yana kallonta cikin tashin hankali, jin bai ce komai ba yasa ta juyo ta kalleshi, tashin hankalin da ta gani a fuskarsa ne ya ƙara bata ƙwarin gwiwar ci gaba da magana:
"Anuwar kafi kowa sanin wacece ni, kasan abinda zan iya yi kasan abinda ko da wasa ba zan iya aikatawa ba."
"Anuwar sanin kan ka ne mun shiga ƙunci da matsin rayuwa wanda koda nayi zina Ubangiji bazai kama ni da zunubi ba, amma kai ne kake zargina akan haifar junior ba aure? Ni shikkenan a waje ana zargina a gida ma haka?"
Ta ƙarasa maganar muryarta a sarƙe.
Durƙusawa yayi akan gwiwoyin sa sannan ya fara magana cikin kuka:
"Ukhty ba zargin ki nake ba, ki dai na faɗar wannan maganar tayi tsauri da yawa..."
Sannan kuka yaci ƙarfin sa.
Nuratu ta numfasa sannan ta kalli cikin idon sa tace: