FreeArewaPen original
NI DA KANNENA
- 1views
- 20chapters
- 0audios
- words
- 0likes
Share:
The story
Synopsis
No synopsis yet.
Sample · Chapter One: (Ashraf)
BIRNIN KANO (December-2023) A zaune take a cikin mota ta alfarma tana danna wayarta mai tsadar gaske cike da nishadi da wani yanayi mai ƙayatarwa. Ta ɗago a nutse ta kalli tagar motar, ta lura da yadda suke tafiya akan titın cike da nutsuwa acikin gudun mota matsakaici, a hankali ta maida hankalınta kan fuskar wayarta misalin karfe 12:58pm na rana ya nuna mata. Ta mai da hankalin ta kan driver motar tace: "Amir kadan kara sauri, kasan Daddy baya son jira." Cike da nutsuwa da ladabi yace: "To anty." Ba'a fı mintuna uku zuwa hudu da yin wannan maganar ba taji Amir yayi saurin taka birki, cakın sauri ta dago kanta ta kalli Amir dake zaune a mazaunın driver cike da tashin hankali tana ambaton "Innalillahi wa'inna ilahi raji'un" Cikin hanzari Amir ya mai da hankalin sa kan titin tare da leƙawa ta window motar yana faɗin: "Kaga irin ta nan, gashi nan sun kaɗe mutum, haba gudun ...
Contents
Table of contents
Preview every chapter, see what is free, and continue reading when you join ArewaPen.