NI DA KANNENA

Chapter Eleven (Daidaito)

by @thehealerspen654

Washegari ranar lahadi da mota ta muka nufi inda sabon masaukin namu yake, daman ni na iya mota tun a gidan Hajiya, haka muka bi address ɗin da Al'ameen ya turo min muka isa.


Wato wani katafaren Estate ne mai ɗauke da ƙayatattun gidaje na zamani masu ban mamaki, ga isasshen tsaro sannan duk abinda mutum yake buƙata akwai aciki.


A gate ɗin shiga muka tsaya, sai da Al'ameen ya ƙara so sannan muka shiga ciki, abun gwanin birgewa da ban sha'awa, kuma abin da ya ƙara bani mamaki shine gaba ɗaya na ma'aikatan da suke aiki a ƙarƙashin Daddy ne, wannan Estate ɗin namu ne na manyan ma'aikata, akwai kuma na ƙananun ma'aikata daban.


Wani ƙayataccen gida muka isa, sabo fil gashi da bene mai matsakaicin girma, tsarin sa irin ginin turawa gaba ɗaya gidajen wajen hana suke, sannan ga komai da komai na buƙata aciki kama daga furnitures, elections, kitchen appliances da sauran su, abin da sai wanda ya gani.


Haka muka yi ta zagayawa acikin gidan, Al'ameen yana nuna mana waje waje gwanin sha'awa su Ameerah suna ta murna, amma ni cikin zuciyata mamakin dukiya irin ta Daddy nakeyi, ban sani ba ashe 'Wasa farin girki'.


Bayan mun gama ganin ko ina, Al'ameen ya miƙo mana mukulli tare da yi mana sallama, zama mukayi acikin mukayi sallah muka yi addu'o'i sannan muka nufi gidan mu domin fara haɗa kayan da zamu dawo sabon gidan mu dashi.


Acikin kwana uku muka gaba kai komai namu acikin mota ta, duk da ba wasu tarkace muka ɗi ba ba amma acikin kwana ukun kullum sai munje munyi karatun Alkur'ani acikin gidan sannan daga bisani muka tare, sauran kayan mu da suke wancan gida na rabarwa da mabuƙata sannan nace a samo wanda zai zauna a gidan haya.


Rayuwa tayi mana dadi sai dai muce 'Alhamdulillah' babu ƙunci, babu fatara babu talauci komai a wadace muke samu, da lokacin yin JAMB yazo Anuwar da Ameerah sukayi gaba ɗaya domin samun gurbi a jami'ah.


Babban abinda yake damuna shine yadda na kasa bankaɗo badaƙalar da ake tufkawa, hakan yana matuƙar damuna sosai kuma na kasa neman Al'ameen domin ya taimaka min akai, hasali ma na kasa tambayar sa akan ya faɗamin kalar badaƙalar da ake zargi, ganin na kasa ganowa da kaina ya saka na fara shirin tunkarar sa.


Wayarsa na kira nace masa ina so mu haɗu, yayimin umarni da mu haɗu a wani restaurant, bayan na isa na zauna a table ɗin da yace, take ɗaya daga cikin masu serving customers yazo ya kawo min tea, ina ɗaga cup ɗin zan sha naga wata karamar takarda an rubuta: "kar kice komai Al'ameen ne ki fito waje parking space akwai mota END OF DISCUSSION ki shiga."


Ba musu na miƙe na fita, ina shiga motar da mamaki na naga ba kowa ciki sai key ɗin motar ajiki, da na duba kujerun motar na hango wata takarda an rubuta: "ki tuƙa motar ki fita daga nan, sannan ki kashe wayar ki akwai waya acikin dashboard din motar ki ɗauka ki kunna."


Haka nabi duk abin da yace, bayan na kunna wayar naji an kirani ina ɗagawa naji muryar Al'ameen ce, yayi ta directing ɗi na har na iso wani gida acan bayan gari.


Duk tsoro na naji ya gushe, na samu parking space a harabar gidan nayi parking, banji komai ba, na buɗe motar na shiga ainahin cikin gidan.


Da mamaki na Daddy na gani a zaune tare da Al'ameen suna tattaunawa, aciki wani ƙayataccen palour madaidaici.


Shiga ta ke da wuya suka mai da hankalin su kai na, na durƙusa na gaida da Daddy ya amsa min fuskar sa ba yabo ba fallasa, sannan yai min nuni da na zauna a ɗaya daga cikin kujerun palour na zauna tare da gaisawa da Al'ameen.


Bayan kamar mintuna biyar suna tattaunawa Daddy ya ɗago ya kalleni sannan ya fara magana:


"Wato Nuratu babu laifi na fara yabawa da ƙwazon ki shiyasa na amince har aka baki masauki a Company na hakan kuma ba yana nufin na gama tantance ki bane, a'a saboda na lura da inda kika dosa."


Ya sake numfasawa sannan yaci gaba:


"Wato abin da yake faruwa shine; yau wata takwas kenan da kungiyar yaƙi da sha da fataucin miyagun kwayoyi wato NDLEA ta aiko mana da takardar tuhuma saboda ana zargin shigo da miyagun kwayoyi ta motocin sufuri da containers na wannan company nawa, lokacin da na riski wannan al'amari nayi matuƙar baƙinciki sosai don ko bacci bana iyayi, saboda Allah ya sani, ina iya bakin ƙoƙarina domin kaucewa duk wani abu da ya karya dokar ƙasa data al'ada, amma sai da aka samu ɓata gari da suke ƙoƙarin gurɓatamin lasisin da nake dashi a ƙasar nan dama duk wata ƙasa da muke harkar kasuwanci da ita.


"To amma, da suka buƙaci zasu gudanar da bincike sunyi iya bincike basu kama komai ba, wato waɗanda suke yin wannan sabgar suna da matuƙar wayo, hakan ya saka suka haƙura tare da bani haƙuri akan hakan, amma duk da haka zuciyata bata aminta ba ina ta tunanin yadda zan ɓullowa al'amarin. Kwatsam wata shida da suka wuce Al'ameen ya samu wata makama da take tabbatar da cewar anayin abun nan kuma ba'a dai na ba, amma matsalar bai samu ƙwaƙwarar hujja ba, to babban abinda yake damuna shine; wannan company cike yake da ƴa ƴan ƴan uwana da abokan arziki ina jin nauyi na tunkari mutum kai tsaye ba tare da wata kwakkwarar hujja ba."


"Hakan ya saka na fara kai mutane office ɗin ko Allah zai saka a samu wanda ya iya gano wata alama duk ƙanƙantar ta amma abun yaci tira, nan fa na fara tunanin kawo mace mai rauni kenan, wadda ba'a sani ba kuma mai kaifin basira domin magance wannan matsalar kuma Alhamdulillah yanayin yunƙuri da kuma motsin da kikayi ya nuna za'a samu nasara ta ɓangaren ki wanda shine fatana."


Duk bayanin da Daddy yake yi kai na na ƙasa ina sauraron sa kuma inata ƙokarin faɗaɗa tunanina domin fahimtar sa yadda ya kamata.


Ya sake gyaran murya sannan ya kalleni yace:


"Shin Nuratu zaki iya wannan aikin kuwa?"


Na ɗago kai na cike da kwarin gwiwa sannan nace:


"Eh zan iya ranka ya daɗe."


Ya sake kallona fuskar sa da murumushi ga dukkan alamu ya gamsu da ƙwarin gwiwa ta ya sake cewa:


"Kin san haɗarin da waɗanda zaki tunkara suke dashi kuwa?"


Na girgiza masa kai alamar "a'a"


Ya dakko wata wayar Tab ya ɗanyi danne danne sannan ya juyo min da fuskar wayar domin na kalla.


Me zan gani...? Mota tace take ci da wuta a wannan restaurant ɗin da na baro yanzunnan.


Idanuna na zaro sosai cike da tsoro da firgici nace:


"Wannan kamar mota ta?"


Murmushi Daddy sukayi shi da Al'ameen sannan Daddy yace:


"Itace wannan shine kaɗan daga cikin makircin su, warning akai miki, zaki iya tunkarar su Nuratu ko bazaki iya ba?"


Nan fa naji an raba min tunani, na fara ƙoƙarin daidaita nutsuwa ta, amma abinda ya dinga bani mamaki shine yadda a hankali zuciyata ta fara rinjaya ta akan na amince ko don saboda KANNENA su samu rayuwa mai kyau, duk da nasan mun shiga haɗarurruka da dama, kuma wannan bansan ta inda nasa kalubalen zai zo min ba, amma ina tunanin zan iya.


Ɗago kai na nayi na kallesu gaba ɗaya sun zubamin ido suna kallona nace:


"In dai za'a bani kariya zan iya."


Murmushin nasara Daddy yayi sannan yace:


"Zaki samu maximum protection awa ashirin da huɗu inshaAllahu. Sannan abu na gaba muna buƙatar sirri"


Jinjina kai na nayi alamar na gamsu sannan daga bisani muka yi sallama Daddy yace naje da wannan motar ta zama tawa.


Haka na tafi jikina a sanyaye na isa gida, ganin wannan sabuwar motar ya saka Anuwar fara tambayata inda na samo ta, nace masa waccan ce ke da matsala ya saka aka canjamin.


Wannan shine karo na farko dana fara yiwa KANNENA ƙarya, kuma na fara ɓoye musu abubuwa sannan karo na farko da Anuwar ya fara tuhumata akan al'amuran da suka shafeni.


Haka na cigaba da aiki a Company muna iya bakin ƙoƙarin mu ni da Al'ameen, saboda na lura da mu kaɗai Daddy ya amince, tun da na fara aiki ba'ayi wani general meeting ba Daddy ya dakatar, saboda haka ba kowa na sani acikin manyan ma'aikatan ba, wasu dai zan gansu a hanyar shigowa ko lokacin tashi, bana wani mu'amala dasu kamar yadda Daddy ya tsara kuma nima tsarin yayimin dai-dai.


Alamun rashin gaskiya suna ta bayyana a warehouse ɗin mu, duk ƙanƙantar motsi bana wasa dashi, kuma ina yin aiki da taka tsantsan kuma a sirrince, saboda idan nayi wasa na sani da rayuwata nayi wasa, haka naci gaba da kula har zuwa wata rana da na wayi gari da wani yanayi a jikina, gaba ɗaya tsorona ya gushe ji nake a shirye nake na tunkari kowa saboda a kullum cikin addu'a nake kuma ga dukkan alama Ubangiji ya karbi addu'a ta.


Miƙewa nayi cikin dare nayi sallar nafila sannan nayi addu'o'in samun nasara akan abinda na ƙudurce a zuciya ta zan aiwatar a yau.


Bayan na idar na miƙe ina sanɗa na fita daga bedroom ɗin mu, na leƙo Anuwar yana bacci, sannan na shiga storeroom na ɗakko wata school bag na fara fito da kayan cikin ta.


Riga da wando ne acikin da hular sanyi da na tanada tun rana na saka ajikina, sak namiji na koma, na ɗakko takalmi Canvas na saka na ɗaure maɗaurin, na zuge jakar akwai wayata ciki, ƙaramar touchlight da ruwan roba acikin sai biscuit guda ɗaya na rataya a bayana na na fice harabar gidan da muke, na ɗauki keken Abuwar na lallaɓa na fita ta ƙaramar ƙofar bayan Estate ɗin mu, da daman tun rana nayi dabarar samun key ɗin.


Haka naci gaba da tafiya misalin ƙarfe 2:15am na dare, da yake babu nisa da company mu na samu a hankali na ɓoye keken ta baya, sannan na lallaɓa na  haura katangar ɗin bayan jera bulo da nayi a wajen, sannan na shiga warehouse ɗin  kasancewar na saci mukullin gate tun da rana.


Haka naci gaba da zagayawa aciki cike da sanɗa ina haska touchlight har nazo daidai inda ake ajiye wannan tsohuwar motar babu ita babu dalilin ta.


Abun ya matuƙar ɗaure min kai, haka nayi ta zagawa, can najiyo motsi, ana shirin shigowa na nemi bayan wata mota na laɓe ina hango su daga nesa.


Ashe mutum uku ne suka shigo ciki har da mai gadin wajen, can najiyo ɗaya daga cikin su yana cewa:


"Yi sauri maza ka kirawo Ramadan suyi su dawo da motar nan saboda hankali na yau sam ba'a kwance yake ba ina tunanin ana bibiyar mu."


"Toshikkenan bari na kirawo shi."


Can naji ɗayan yana amsa waya bayan ya kammala ya kalli ɗayan yace:


"Yaya ai an kammala loda mata kayan sun taho suna hanya, suna ƙarasowa za'a aiki kayan."


"Ok kace masa suyi da jiki don Allah ina ji a jikina yau ba ranar sa'ar mu nace."


Haka suka yi ta zagaya wajen suna haskawa da fitilar waya, kafin su ƙaraso in da nake nayi saurin na shiga cikin wata container da take bayan wata babbar mota na samu wani ƙaton kwali na shiga ciki, ina jin motsin su suna dubawa Allah bai saka sun ganni ba suka mai da ƙofar suka rufe.


Nan fa zafi ya fara damu na, na fito da wayata na turawa da Al'ameen saƙo kamar haka:


"Just track my movement"


Sannan na saka wayar a Flight mode.


Haka nayi ta zama acikin wajen mintuna talatin babu wani motsi kuma a hankali na fito na fara haska ciki container, wasu irin kwalaye na gani an liƙe su, na zaro guda ɗaya na farke, hodar iblis ce a aciki danƙam, na saka wayata na ɗauki hoto na din ga Turawa ta WhatsApp ɗin kan computer ta da take gida saboda a halin da nake ciki a yanzu banyarda da kowa ba.


Haka na gama ina ta haɗa gumi, na sake jin motsi nayi sauri na koma cikin kwalin nan, ina hango su ta wata ƴar ƙofa suna fito da wasu kwalayen daga cikin body wannan tsohuwar motar ana sake jerawa acikin motar da nake ciki, a hankali na sai ta idon camara wayata na ɗauki video kuma nayi sa'a fuskar mutum biyu ta fito, bayan sun gama suka mayar da mukullin suka rufe sannan aka tada motar ta fara tafiya.


Bayan motar ta fara tafiya na tuna da inda na ajiye keke na a bayan company inata addu'ar Allah yasa kar su ganshi su binciko mu ko su biyo bayan mu.


Haka muka yi tafiya mai dogon Zango, na samu sauƙin zafi, amma fa sai sannan tsoro yazo min saboda na fara tunanin ta yadda zan fita kuma, ga evidence dai na samu na hotuna, videos da voice recording Amma kuma na tabbatar da na saka rayuwata a haɗari.


Sai da muka yi tafiyar kusan awa guda sannan dabara ta faɗomin na kunna wayata na saka ta a silent, saƙon daddy ne ya faɗo kamar haka:


"Ki kwantar da hankalin ki muna bin bayan ku da jami'an tsaro."


Wani irin sanyi naji a zuciyata, naci gaba da addu'a da ambaton Ubangiji acikin zuciyata har muka iso in da naji motar ta tsaya cak.


Can na fara jiyo jiniyar ƴan sanda da motar asibiti, zuwa wannan lokacin na galabaita, na fara fita daga hayyaci na saboda tun da motar ta tsaya nake jin wani irin zafi ga warin kayan mayen da yake ciki ya fara bugar dani, kafin kace me na rasa in da kai na yake.


Abin da zan iya tunawa shine naga Daddy a tsaye a kaina yana zuba min ruwa, a she a gefen titi muke jami'an tsaro ne suka tsai da motar saboda direct fitar da kayan za'a yi daga Kano, a hankali na buɗe ido na na hango Al'ameen yana kare fuskata saboda kar a gane ni sannan daga bisani aka saka ni a motar asibiti aka dawo cikin gari dani aka wuce asibiti kai tsaye.


Ni dai tun daga lokacin ban farka ba sai da safe, Al'ameen na gani still da Daddy sun ƙuramin ido, zumbur nayi na tashi zaune ina bin su da kallo.


Daddy ne ya numfasa muryar sa a kausashe ya hau yi min faɗa akan wannan babbar kasadar da na ɗauka da saida rai:


"Yanzu Nuratu da bama bibiyar al'amuran ki da ya kike tunani? Kin san a aikin banza zasu kashe ki, kin san adadin mutanen da suka kashe a wannan company kuwa kuma babu hujja ƙiriƙiri haka ake haƙura?"


"Kar ki kuma yin wannan kasadar kinji ko?"


Jinjina masa kai kawai nayi sannan nace ina son zan yi magana dashi in private.


Murmushi kawai yayi sannan yace:


"Ki kwantar da hankalin ki na yarda da Al'ameen."


Sai sannan na samu kwarin gwiwa sannan nace a bani wayata, Daddy ya miƙo min na nuna musu duk wasu shaidu da nake dasu.


Daddy yayi matukar jin daɗi sannan ya karɓi wayar tawa tare da tabbatar min da samun tsaro, sannan ya yaba da shigar mazan da nayi kuma hakan zai taimaka sosai wajen ɓoye identity na.


Sannan daga bisani ya umarci da a sallame ni daga asibiti, haka na miƙe muka fita a sirrince, bayan mun shiga mota Al'ameen ya miƙo min wata jaka yace na koma baya na canja kayan jikina Kasancewar daga ni sai shi a motar haka na koma na canja kayan.


Kayan motsa jiki ne aciki, gashi anyi sa'a weekend ne, haka ya kawo Ni dan da Estate ɗin mu sannan ya sauke ni, na fito da kayan motsa jiki, idan ka ganni zaka rantse daga motsa jiki na dawo.


Haka na shiga gida na tarar Anuwar bai tashi ba ita kuwa Ameera tana kitchen tana haɗa breakfast, ta kalleni tace:


"Ai gwara ki fara motsawa ki rage wannan ƙibar Ukhty "


Wata sanyayyiyar ajiyar zuciya nayi tare da yi mata dariyar yaƙe na hau sama bedroom ɗi na da ƙyar saboda gaba ɗaya jikina babu ƙwari.


Haka na daure na din ga zuwa office a sirrince likita yana kula da lafiyarta har ma samu na warware.


Duk yadda akayi da direbobin motar nan sunƙi su faɗi da waɗanda suke yin aikin, ƙarshe dai da hujjojin hotunan da na ɗauka da videos da audio ne ya toni asirin su daga bisani suka amsa laifukan su tare da bayyana duk waɗan da suke da hannu acikin wannan baɗaƙalar.


Abin da zai baku mamaki shine ƴaƴan ƴan uwan Daddy ne da ƙannen Mummy, Daddy yayi iya bakin ƙoƙarin sa wajen hukunta masu manyan laifuka, waɗan da ba'a kulle su ba kuma ya sallame su tare da duk wani wanda yake da alaƙa dashi a Company tare da basu jari mai ƙarfi domin kowa ya dogara da kansa. Kunji adalin mutum.


Ni kuma tun daga lokacin na zage damtse nake aiki tuƙuru tare da tarwatsa duk wata badaƙala, Daddy ya saki jiki dani sosai kuma ya jani jikin sa sosai har zuwa wani lokaci da wata babbar matsala ta afku dani a Company.


Ta ɓangaren ƴan uwana mun samu kwanciyar hankali, komai yana tafiya dai dai, watarana ina bincike online naci karo da wata ƙungiya da zata tallafawa  matasa da yin karatu a ƙasashen ƙetare, haka na saka Anuwar ya cike wannan application ɗin domin mu samu yayi karatu mai kyau saboda a zahirin gaskiya ya nutsu sosai.


Watanni na shida sun cika a wannan company, Daddy ya ƙaramin matsayi zuwa Accountant Manager, haka na zage na nuna ƙwarewata da ilimi na sosai a wannan ɓangaren.


Watarana mun kai ziyarar aiki company sarrafa shinkafa da Daddy muna zagayawa, da muka zo ɓangaren da ake dafa shinkafa kwatsam naga Baba Rabi tana aiki a wannan waje duk ta rame ta lalace, da gudu na tafi wajen ta, sam ita bata gane ni ba sai da na yi mata bayani sannan ta fashe da kuka nima sai da ta sakani kuka.


Haka muka nemi waje muka zauna na tambaye ta bayan saduwa ta fara bani labari: