KUNCIN ZUCI

Kuncin zuci

by @bintuuu

Ahankali Ahmad ya dan yi baya bai saketan ba yana kallon fuskanta, cike da kunya Na'ima tayi kasa da kanta tana murmushi itama bata sakesan ba, sai ya duqo kansa yayi qasa da murya yace "Wife.. Na'eemah my wife" tana murmushi kawai ta dora kanta a qirjinsa tareda rufe ido, sake mannata yayi da jikinsa sai ya dora habarsa bisa kanta shima be bar murmushin ba yace "Alhamdulillah, Babe..it's a forever deal in sha Allah, kinji" sai Na'ima ta gyada kai har sannan bata dago kanta ba, shiru sukayi suna sauraron bugun zuciyarta junansu a tsayen, wani irin peacefulness suke ji dukansu a wannan moment din, sai aka sake kwankwasa kofan, ahankali Na'ima ta sakeshi sai shima yayi hakan amma sai ya kamo hannunta, kafin su nufi kofan aka dan bude kofan sai Nafisa ta sako kai tace "Yaya ga ruwa an aiko in kawo muku" sai ya gyada kai, da sauri Na'ima ta cire hannunta daga cikin nasa ta nufi Nafisan da ta shigo hannunta riqe da tray, sai ta nemi tayata amma taqi bata har saida ta ajiye drinks din kan glass table din sannan ta gaishe da Ahmad ya amsa mata da "Lafiya Nafisa" da haka ta juya ta fita daga falon, Ahmad ne ya sake kamo hannun Na'iman sai ta juyo ahankali tace "Ina wuni" bai amsa ba ya jata zuwa kujera suka zauna, yau ko gap din da yake bari beyi ba, Na'ima na murmushi tace "nidai ka matsa kadan" yana kallon idanunta ya kwantar da murya yace "toh bari in doraki a lap dina kawai" da sauri ta juya kanta bata bar murmushin ba tace "uhm uhm, nidai banaso" sai yayi shiru yana kallonta, Jin bai sake cewa komai ba yasa ta juyowa suka hada ido sai ta dauke nata idon ta danyi gyaran murya tace "stop please" kamar me rada yace "What?" bata kallesa tace "kallon" sai ya dan matso yace "kar na kalli matata?" sai bata amsa masa ya sake cewa "I feel like kissing you Na'eemah" da sauri takai tafin hannayenta ta rufe fuskanta ahankali tace "Ahmaad" yana murmushi yace "I'm serious wife" sai ya sake duqo da kansa daidai fuskarta ahankali yace "but next week isn't too far in sha Allah" ahankali ta sauqe hannayenta daga fuskanta tana kallonsa cikin ido, tsayawa kallon juna sukayi sai Ahmad yayi qasa da murya yace "A kiss that'll left us breathless" matsawa tayi daga kusa dashi tace "gaisawa kazo muyi fa, what's this Ahmad" sai ya fara dariya qasa qasa yace "banbancin da da yanzu nake nuna miki Babe" sai tayi murmushi ta girgiza kai, be sake matsawa garetan ba yayi relaxing bayansa da kujeran yace "Anty Amnah zata kiraki kuyi magana akan kayan da kike so" sai tace "kowanne ma, but please ka bar shi zuwa a month" yace "Me kenen? Tariyan?" Na'ima ta gyada kai ahankali tana kallonsa, dan dariya yayi qasa qasa irin maganan ta basa dariya ma, Na'ima na murmushi tace "Haba mana" sai yace "Babe dazu a falo da Abba yace sai anji ta baki na batun tariyan nan, kinsan wani abu?" ta girgiza tace "Don't say it please" sai ya miqe zai iso gareta yana murmushi tayi baya a kujeran tana cewa "Dan Allah kabariii" da ya qaraso gareta sai ya dan duqo daga tsayen tareda dora hannunsa agefen kanta, ahankali yace "Toh next week din kinji" da sauri Na'ima ta gyada kai tanajin kusancin su na sa mata wani iri a zuciyarta, kallonta ya tsaya yi ahakan, sai ya qurawa lips nata ido baya ko kiftawa, jin abubuwa na taso masa a zuciya yasashi miqewa yace "I need to go, muje ki rakani kinji" Na'ima ta gyada kai idonta a duqe ta miqe sai ya kamo hannunta suka fita daga falon cikin sanyin jiki, Fitansu compound din suka hango Adam tsaye a parking space din tareda Nafisa da Husna suna magana, Na'ima tace "shine ka barshi a parking space kuma" Ahmad ya juyo yace "sai mu jeru ni dashi muyi ta kallon ki kenan" dariya ma yabata sai tayi murmushi tace "Gaisawa fa zamuyi" sai Ahmad ya maqe kafada, ta sake cewa "ba dadi hakan fa, in yaji haushi fa" ya juyo gaba daya gareta yana murmushi yace "Haushi na kenan" tace "Har dani ma" sai ya qara damqe hannunta dake cikin nasa yace "Adam is not like that kinji Babe, ina kishinki shima ya sani" sai tayi murmushi tace "Har akan family kuma" yace "Akan kowa ma wife..akan ko wane namiji" dariya ta danyi tace "nima haka, i don't like seeing you with her" sanin wa take nufi yasa shi cewa "she's juts a sister to me, nothing else kinji" sai ta gyada kai kawai suka juya atare, gani sukayi Nafisa da Husna sun dauke wayarsu atare suka juya gurin Adam suna dan dariya, Na'ima dan ware Ido tayi tana murmushi sai Ahmad ya girgiza shima yana murmushin yace "Yaran nan" da haka suka qarasa gurinsu sai Husna tace "Yaya Ina wuni" yace "Yaushe kikazo" tana murmushi tace "Dazu... congratulations Yaya na, Allah ya sanya alkhairy" sai yayi murmushin shima yace "thank you" Na'ima ta kalli Adam a kunyace tace "Ina wuni Yaya" da fara'a yace "Amaryarmu" Ahmad yace "kingani ko" sai duk akayi dariya agurin, Nafisa tace "Yaya muma fa Amaryarmu ce" Ahmad yace "Tawa dai, zan ci taron duk wanda ya sake ce mata Amaryarsa" Husna na dariya har sannan bata daina daukan video a boye ba, Adam yace "lallai tarar da za'amin dayawa kenan" Naima dai har sannan kanta a qasa tana murmushi, cike da respect qannen sukayi hira da yayunsu anan parking space din, ranan Ahmad ya sake sukayi hiran dashi har yana amsawa akai akai Na'ima sai kallonsa take da mamaki, sai can suka fara shirin tafiya Adam yace "bari mu wuce Amarya, Allah ya sanya alkhairy" Na'ima tace "mungode" sai Ahmad ya zagaya dayan side din motan ya ciro leda babba ya miqawa Nafisa yace "ki riqe mata" ta amsa da "Toh Yaya, Allah ya saka" da haka ya shiga motan yana kallon Na'iman har Adam ya tada motan sukayi reverse, sai da suka bar gidan Nafisa ta leqa ledan hannunta sai ta turo baki tace "Ashe ma kudi ne" Husna tace "Duba mana dai ko da chocolates din a qasa, Yaya yasan masu dadi wallahi" Na'ima ta girgiza kai tana murmushi ta juya ta shige falon gidan, agadon dakin suka sake bararrajewa tareda ciro bunches na kudin suka ajiye a gefe aikuwa nan suka samu abunda suke son a qasan ledan, chocolates da cakes ne a sosai a ledan suka hau ci kowacce ta ciro wayarta suna duba hotunan da suka dauka, da dan mamaki Na'ima ke kallon uban kudin da Ahmad din ya kawo mata...
A wannan daren Laila na kwance a dakinta tana waya da wani sugar daddynta kiran Salma ya shigo wayanta, bata dauka ba ta cigaba da making call din sai ga wani kiran ya sake shigowa, dakatawa tayi ta dauki kiran Salman, daga daya bangaren Salma tace "I thought ina daga cikin mutanen da zaki fara kira kiji batun auren ko gaskiya ne Laila, bakiga WhatsApp story na banzayen can bane?" dan stiff Laila tayi na rashin fahimtar maganan sai kuma tace "what do you mean?" Kai tsaye Salma tace "Auren Yaya Ahmad mana da sadaka yallan can" ai nan take Laila ta miqe daga kwancen da taken tace "wai me kike cewa ne Salma" sai Salma tace "wai kina nufin bakiji labarin ba bayan babu wanda bai sani ba a family? Toh yau su Baba sukaje Kano, 'yan'uwan yarinya dai a zilamance suka daurawa Ahmad auren 'yarsu atake" ai Laila batasan lokacin da wayan ya fadi daga kunnenta ba sai kuma ta duqa tayi saurin dauka tareda kashe kiran Salman ta hau WhatsApp nan take, kan status na Husna ta fara shiga, nan ta ci karo da hoton Ahmad riqe da hannun Na'iman fuskokinsu cike da fara'a, the next one sai da ya sa ta zauna a bakin gadonta dalilin ganin Ahmad ya duqo kamar me rada a Na'iman, qara sabule wayan tayi da ga hannunta sai ta miqe a birkice ta fita daga dakin, falon Mummy ta nufa nan ta sameta zaune tana waya kawai ta hau ihun fadin "Mummy yaushe Ahmad yayi aure" Mummy ta katse wayan ta kwantar da murya tace "Auta ki nutsu..waya fada miki?" jikin Laila har bari yake tace "Mummy aure fa, wallahi bazai yiwu ba, narantse sai ya rabu da ita, na shiga uku Mummy" kawai ta fashe da kuka sai mummy ta taso zata riqeta kawai sai taga numfashin Lailan yana fusganta, da azama ta riqota tana fadin "Laila..Laila...na shiga uku...ke Laila" sai ta kamata ta kwantar da ita a kujera har sannan numfashinta bai dawo daidai ba tana hawaye sai fadin "wallahi sai sun rabu" take, arikice mummy tace "Zasu rabu auta, zasu rabu kinji, innalillahi wa inna ilaihi rajiun" sai ta rarumo wayanta ta danna kira a Daddy dake qasar Cairo, aikuwa yana shiga Mummy ta daga murya "Wallahi ka baro duk abunda kake ka dawo qasar nan gashinan suna neman kashemin yarinya" cikin confusion Daddy yace "Me kike cewa ne haka?" Cike da masifa tace "Ina maganan zaku kashemin yarinya kana sake tambayata, wallahi duk wanda yace bayan 'yata zai gani sai nasa kafan wando daya dashi" da haka ta kashe wayan ta duqa gurin Laila da zuwa lokacin kawai kuka take kanta kife akan kujeran, shafa bayanta Mummy ta hau yi tace "kiyi hakuri Auta, kiyi hakuri kinji, babu inda auren zeji inanan dake" Laila na kuka sosai takasa magana ma,  wani kiran Daddy ne ya sake shigowa Mummy ko kulawa batayi ba sai da ya katse sannan ta dannawa Murja kira tareda Ummi...

Washegari da sassafe sai ga kiran Ahmad ya shigo wayan Na'ima da har sannan suna bacci, cikin baccin ta dauka sai tayi gyaran murya ahankali tace "Good morning" daga daya bangaren Ahmad yana kwance kan three seater na babban falon gidansa dake nan kanon, jallabiyace jikinsa alamun tun dawowansa daga sallan asuba yake kwance anan, yana murmushi shima ahankali yace "Wife" sai Na'ima tayi dariya kadan tace "katashi" yace "idona biyu ina jira ki tashi in kira, but i can't wait" sai ta gyara kwanciya tana kallon Husna dake gefenta ta hangame baki tana munshari,  ya sake cewa "kin tashi lafiya?" tace "Uhm Alhamdulillah, kaifa?" ya amsa da "Alhamdulillah, kwanan mu daya Babe" sanin me yake nufi yasa tayi murmushi tace "Har ka fara counting?" yana murmushi yace "And I'll keep counting" cikin annushuwan zuci suka yi shiru, sai can Na'ima tace "Kudin jiya fa? na menene?" Yace "Nima bansani ba, Anty Amnah tace ana baiwa Amarya kudi" Na'ima na dan dariya tace "But it's too much ai" Ahmad ya gyada kafada yace "I was thinking that bazai isheki ba fa, bansamu cash din sosai ba jiya, am sending you my card later" tace "No it's more than Okay..Nagode, Allah ya qara budi" Ahmad yayi murmushi hearing how addu'ar matarsa sounds different, ya amsa da "Amin wife, yi baccinki" ta gyada kai tareda cewa "Uhum" da haka sukayi sallama Ahmad ya kashe wayan sai ya gyara kwanciya akan kujeran ya cigaba da jan tasbahan dake hannunsa, yananan kwance shiru sai ga Adam ya fito daga wani daki dake cikin falon shima cikin jallabiya, qarasowa yayi ya zauna a kujeran dake facing Ahmad din yace "Man I'm flying back later, Daddy ya kirani yanzu" Ahmad ya dago kai anutse yace "Meya faru?" Adam yace "it's Laila, he said she's not Okay since yesterday, but likita ya dubata tun jiyan, zanje inga condition din nata" shiru Ahmad yayi da farko sai can yace "Then we're going together, have you booked the flight?" Adam ya girgiza kai sai ya ciro wayansa zeyi hakan, shiru sukayi bayan Adam ya duba musu available flight sai ya kishingida shima anan kan kujera tareda rufe idanunsa dan baccin bai ishesa ba shima...

Na'ima ta riga su Nafisa tashi, Dan bayan tagama waya da Ahmad din Anty Amnah ta kirata suka yi dogon magana game da batun abubuwan da ya shafi kayayyakin auren, bayan wannan ma Mami ta kirata akan ko da abunda suke buqata sai su Abu su taho musu dashi zuwa anjima, sai da suka gama tayi wanka sannan ta shirya cikin kaya mara nauyi daga cikin wanda Husna ta taho musu dashi, tana tsaye a bakin mirror ta tattaro gashinta ta qulleshi guri daya da ribbon sannan ta yafa veil ta fita, gidan shiru alamun su Alhaji basu tashi ba suma, downstairs ta sauqa sai ta jiyo shafa na ta fama a kitchen dan tsayawa tayi anan falon tana bin ko ina da kallo ganin abubuwa da dama sunanan kamar yanda tabar gidan a baya, dakinta na da ta nufa ta tura kofan tana bin ko ina da kallo memories suna dawo mata kai, sai ta bude wardrobe, murmushi tayi ganin babu komai ciki, like what was she thinking..it's been five years already, juyawa tayi ta fice ta tafi kitchen bayan sun gaisa da shafa suka cigaba da aikin tare suna hira jefi jefi, tare suka gama komai sai Na'ima ta dauko wasu flasks da plates din suka nufi falon sama, Hajiya suka samu ta fito itama tana zaune kan sofa, sai tace "yanzu fa nace bari na leqa in taso ku Na'ima" sai tayi murmushi tace "na tashi ai, ina kwana" Hajiya ta amsa da "lafiya, to ki tado yan'uwan naki suzo suyi breakfast" ta amsa da toh tareda wuce dakin Hajiya na kallonta, samun su Nafisan tayi sun tashi suma amma duk pj's ne ajikinsu, sai suka sako hijabai suka biyo ta falon, Alhaji da fitowansa shima yana zaune a kujerar dake kusada na Hajiya yana cin abinci da tayi masa serving akan glass table, da fara'a ya amsa gaisuwan da suka masa sai yace "Madallah mun samu qarin baquwa kenan" Husna tayi murmushi sai Nafisa tace "qanwar sa ce" sai Alhaji yace "ai ga kamanni nan, ma sha Allah.. sannunku" Hajiya tace "Na'ima maza yi muku serving" sai Nafisa ta fara taya Na'iman tareda zuba tea din a cups bayan Na'iman tayi serving dinsu sai ta miqa mata cup daya tace "Bobo ungo" karba Na'ima tayi sannan Nafisa ta miqawa Husna dayan cup din duk su Alhajin na kallonsu, murmushi Alhaji yayi yace "me kuka karanta ne Nafisa" ta amsa da  "Ni Business Analytics ne Abba, ita kuma Data science" ya gyada kai yace "Ma Sha Allah kefa" ya qarasa maganan yana kallon Husna, tace "Ban gama ba Abba, ni Economics ne under Nile University" yace "Allah yayi jagora" duk suka amsa da Amin, suna nan zaune a falon suka jiyo noise din shigowan mota gidan, basu jima ba sai ga shafa ta shigo tace "Hajiya qannensu ne suka zo" sai tace "kice su qaraso nan ba komai" ta amsa da toh sannan ta juya, bata jima suka dawo tareda da Abu da Al'ameen sun riqo akwatin kayan su Nafisa da Na'iman niqi niqi a hannu, anan falon suka ajiye tareda zama a carpet suka gaisheda su Alhajin, da fara'a suka amsa Alhaji yace "kune 'ya'yan gurin Alhaji Abubakar ko" Al'ameen ya amsa da "Eh Baba" yace "Ma Sha Allah" kafin Hajiya tayi magana Na'ima tace musu "Ga breakfast" sai Abu yace "Hadamin tea din Anty" Husna tace "baka sha bane a gidan" Al'ameen yace "He had a long sleep, Mami kuma ta damu wai bakuda kayan sawa sai be tsaya yayi breakfast ba" Nafisa tace "Maganin sa ai" Abu yace "Am going back with ur box" Na'ima na murmushi ta miqa masa cup tace "kayi hakuri" Hajiya ma tace "Ayi hakuri babana kasha shayinka tukunna" Abu na murmushi yakai cup din bakinsa...Gidan da ya kasance kaman kufayi don shiru sai ranan ya zamo lively dalilin zuwan Na'ima da iyalan wadzani da suka zo dalilin ta, Alhaji na zaune yana kallon yanda yaran suke mu'amalantar juna sai fara'a yake, daga yanayin bond din tsakaninsu da kuma sunan Mami da Abba dake fita a bakinsu duk magana daya zuwa biyu ya gane cewa shaquwar su da iyayen daban ne, sai yaji baya regretting haduwarsu da Na'iman, abunda Allah ya tsara kenan cikin rayuwanta daman.
Da rana suna zaune a falon qasa sai ga kiran number ya shigo wayan Na'ima, tana dagawa taji muryan kawunta Ayuba yana fadin "Na'ima" sai ta miqe ta fita daga falon tana amsawa da "Ina wuni Baba" yace "lafiya Na'ima maigidanki ne ya turamin layinki ai" tana murmushi tace "yasu Umma da Anty" yace "Ga umman taki, Abida taje garinsu" da haka ya bawa Umma, tana karba tace "Allahu Akhbar 'yata Na'ima" tace "Ina wuni Umma" "lafiya Na'ima, ashe abubuwan da suka faru kenan, kiyi hakuri kinji yar nan" tace "babu komai umma, yasu salame" umma tace "tana gidanta itama dai mijin qarayar arziqi ce ta samesa, abincin bakinsu ma sai an harhado, jiya tace zata kiraki ma ai" sai Na'ima tace "toh umma abata layin nawa sai mu gaisa, in Kamal na nan ya kirani sai in tura masa wani abu akai mata" Umma tace "mungode.. mungode sosai Na'ima, ai munce zamuyi anko ma in zamu taho bikin" Na'ima na murmushi tace "toh umma duk zan turawa Kamal kudin komai sai kuyi hidiman dashi" tace "toh toh, yaje kasuwa yanzu haka, yana dawowa anjima zai kiraki, Allah dai yayi albarka" Na'ima ta amsa da Amin sannan umma ta miqa wayan ga Ayuba, yana karba Na'ima tace "Baba ka turamin account numbern ka zan tura maka na wasu hidiman, harda na motan zuwan naku" da sauri Ayuba yace "toh Na'ima, Nagode Allah yayi albarka" ta amsa da Amin, da haka sukayi sallama sannan ta koma ciki..
Da yamma sai ga driver yazo har gidan yakawo ma Na'ima card din Ahmad da kuma key na motan sa da driver'n yazo dashi akan ya bar musu ko zasuyi amfani da ita, bayan Na'ima ta karba tayi godiya sai ta kira line din Ahmad din taji baya tafiya, again ta sake kira taji baya tafiya nan ma, sai tayi tunanin ko yana wani uzurin ne Amma har dare bai kirata ba kuma line nashi baya tafiya, sai da sukazo kwanciya Nafisa tagama waya da Lamin sannan ta kallesu tace "Kai wai ashe Laila babu lafiya, dalilin komawan su Yaya Ahmad Abuja yau kenan" sai da zuciyar Na'ima ta dan buga ta tsaya tana kallon Nafisa, ita bata ma san ya koma Abuja ba tukunna, and again tun asuban nan bai sake kiranta ba kuma line nashi baya tafiya, Husna tace "shegiya ce, likimo tayi ban yarda bata da lafiya ba wallahi" Nafisa ta tabe baki tace "Matsalarta ce wannan" ta qarasa magana tana kallon Na'ima da ta juya tana lullubuwa da blanket, sai tace "Bobo" Na'ima bata juyo ba tace "na'am" dan tsayawa kallonta Nafisan tayi sai kuma ta fara gyara kwanciyanta itama, Na'ima na kwance ne kawai amma batayi bacci ba har gurin 12 na dare ranan, can kuma ahankali ta miqe ta nufi bandaki zatayi Alwala sai taji hawaye na zuwa mata kawai ta kai hannu ta share aranta tanajin zafi, a wannan lokacin ba Laila bama har Ahmad din haushin sa take ji matuqa arai...