Page-45
*FASAHA WRITER'S ASSOCIATION*
(*F.W.A)*©✍️
⭐⭐⭐
Ƙungiya masu aiki cikin salon hikima da fasaha gurin juya tunanin al-umma, kaifin alƙalumansu ya zarta takobi ©✍
___________________________________________________
بسم الله الرحمن الرحيم.
اللهم صلي وسلم على نبينا محمد.
❁ 𝐒𝐀𝐍𝐀𝐃𝐈𝐍 Ƙ𝐀𝐃𝐃𝐀𝐑𝐀𝐓𝐀 ❁
Free book📓
By: _*🌹𝑍𝑎ℎ𝑟𝑎-𝑡𝑢𝑙-𝑄𝑎𝑙𝑎𝑚🖋️*_
Page4️⃣5️⃣
Nusaiba na shirin shiga kenan ta ga Faruq ya yo ƙofar gida hannunsa riƙe da Sadiya, dimm diim! Ƙarar da ya shiga zuciyarta, ta saki ledar maganin da ta riƙo à hannu ya faɗi ƙasa, ta zare ido tana kallonsa har da sakin baki. Da sauri ta isa gareshi tun kan ya iso ƙofar, ta tsaida shi tana faɗin, "ina za ka je da wannan abar Faruq?".
Kafin ya ce mata komai sai ga su Baaba sun shigo, ganinsa riƙe da Sadiya a hannu yasa su ka nufo inda ya ke cikin tashin hankali suka kai hannu kan Sadiya suna tambayarsa me ya sameta? "Baaba asibiti!" Kawai ya furta sannan ya wuce har ya ture Nusaiba, suma su Baaba bayansa su ka bi su ka fice tare, a yayin fitar duk su ka tattake maganin da Nusaiba ta riƙo a hannunta.
Da gudu ta isa tana ambatar me haka ba kwa gani ne? Babu wanda ya saurareta sai gun motar da su ka yi, Faruq ya shigar da Sadiya su Baaba da Lantana ma su ka shige su ne riƙe da Sadiya, Baaba ta ce da sauran su je su sanarwa Malam. Faruq shiga mazaunin driver ya yi.
Sam ba a cikin hankalinsa ya ke ba, sai zubar hawaye masu Zafi ya ke yana jan motar da gudu, suma su Baaba sai ƙwallah su ke zubarwa, "ba abun da zai same ki, idan wani abu ya same ki ba zan taɓa yafewa kaina ba!" Cewar Faruq idanuwansa sun yi ja, zuciyarsa ba ta tsaya da bugun ba.......
Nusaiba hannu ta sa tana ɗaga maganin gashi duk sun ta ke mata shi, gaba ɗaya ya zube wasu sun fashe, ta dai yi asararsu, gashi Iya ta sanar da ita yana da mahimmanci sosai. Da tashin hankali ta miƙe tana tuna lokacin da ta ga Faruq riƙe da Sadiya.
Ga shi har da hawaye ta gani a idonsa kamar ƙaramin yaro, me hakan ya ke nufi kenan? Wai me ma ya dawo da shi bayan ta san ya tafi aiki? Ta yi tambayar da ba ta da amsarshi. Juyawa ta yi da hanzari tana ciro wayar da ke cikin ƙaramin jakarta, don kiran Iya Mairo......
Ko da isansu asibiti babu ɓata lokaci doctors su ka shiga da Sadiya ɗakin gaggawa, su Faruq su ka tsaya a waje, shi dai sai zirga-zirga ya ke ya kasa zama guri ɗaya, ransa cike da fargaba.
Ba a jima ba sai ga Malam ya iso, zuwa ya yi ya dafa Faruq saboda ganin yanayinsa, rungumesa Faruq ya yi ya fashewa da kuka, da ƙyar Malam ya rarrashesa su ka zauna. An shafe lokaci kaɗan, daga bisani Nurse ta fito. Da gudu Faruq ya isa gabanta, su Baaba ma haka don su ji me sakamakon?.
A daidai wannan lokacin itama Nusaiba ta hallara, domin Iya ta ce mata ta je ta ga komai a gabanta, tana tsaye itama tana jiran jin me Nurse za ta ce. "Please tell me what happened to my wife, Nurse? Ki sanar da ni" cewar Faruq zuciyarsa na bugawa kamar za ta faso ƙirji.
Nusaiba ce ta kuma shiga situation irin na ɗazu, kalmar my wife da Faruq ya furta akan Sadiya ta faɗo mata cikin kunne, "na shiga uku¡" ta furta tana dafe ƙirji. Nurse ta kasa magana, saboda yadda ta ga hankalinsu à tashe duka ta tausaya musu, sai dai ba ta da zaɓi sai na sanar da su abun da ya ke wakana, ganin za ta yi magana yasa su ka kuma maida hankalinsu sosai kanta, Norse ta fara cewa......
HALIMA.
Bayan ta hau mashin direct tasha ya ijjeta, sai da ta kwana saboda ba mota sai zuwa gobe, kasancewar lokaci ya ja, acikin kuɗin ta ɗan samu siyan abinci, mutane sai yi mata gani gani su ke, saboda yadda yanayinta ya ke, haka ranar ma ta kwana tana murƙususu, washe gari aka zo maganar biyan kuɗin mota, amma kuɗinta bai cika ba.
Wata mata mai suna Hajiya Luba ita ce ta cika mata, daga baya kuma wasu har cewa su ka yi ba za su shiga mota da ita ba, har da ce mata tana wari, taya masu mota za su amince da wannan da ƙila ma mahaukaciya ce. Hajiya Luba ce ta kuma jin tausayinta akaro na biyu, ganin sai kuka ta ke yi.
Ita da kanta ta taimaka wa Halima zuwa gurin wanka, sannan ta ba ta ɗaya daga cikin kayanta ta sa, sannan su ka dawo su ka shiga wata mota su ka kama hanya, godiya babu iyaka Halima ta rinƙa jerawa Hajiya Luba, a ƙarshe ta ke tambayar Halima menene ya sa ta hakan? Ba ta ɓoye mata komai ba, domin tana ganin rayuwarta ya ci mutane da dama su sani, don su ɗauki darasi a ciki.
Sai da matar ta share ƙwallah da jin wannan labarin, dama hausawa sun ce ramuwar gayya tafi ta gayya zafi, bare wannan da ubangiji da kansa ya nuna musu mu'ujiza.
Motar ta su ta yi gudu sosai, Halima ta sha wahala fiye da tunani, domin duk wani jijjiga da motar za ta yi to jinsa ta ke har ranta, don ko labarin da ƙyar ta iya ba Hajiya Luba, bayan magriba su ka isa garin Adamawa Jimeta.
Hajiya Luba mutumiyar kirki ce, don haka ta yi tunanin bai kamata ta bar Halima haka ba. Saboda gani ta ke ma da ƙyar ta iya isa gida da kanta, don haka ta kwashi kayanta ta tari napep aka sa a ciki, ta jawo Halima ta ce da ita, su je inyaso sai ta ijjeta a gidansu, sannan su su juya na su gidan.
Halima ta yi murna sosai da sosai, sai dai a zuciyarta tana fargabar ta fiskar da za ta tinkari Innarta, à sannu à hankali aka isa ƙofar gidan ta sauka, Hajiya Luba ta yi mata sallama sannan ta wuce. Tsayawa Halima ta yi tana bin ƙofar gidansu da kallo, take wasu hawaye su ka sauka mata, sai da ta ja numfashi sannan ta doshi gidan.
A hankali ta tura tana cusa kai kafin gangar jikinta, ba kowa atsakar gidan komai shiru kamar ba kowa ga duhu ko haske sosai babu, saboda fitulun gab su ke da mutuwa, taku ta ke yi ta fara shiga kamar mai tsoron taka ƙasa. A tsakar gidannta kuma tsayawa tana bin ko ina da kallo, kamar wacche ta shigo sabon gurin da ba ta taɓa ganinsa ba.
Inna Jummai da ta fito daga bayi hannu riƙe da buta, idonta ya dire kan wata da ba ta san wace ba ga shi ta ba ta baya, ta ce, "baiwar Allah daga ina?" Zuciyar Halima ya motsa da jin muryar Inna, ba ta juyo ba, Inna kuma ta fara takowa à hankali hannunta ɗaya dafe da baya domin kwanan nan yana yi mata ciwo, ɗayan kuma riƙe da butan, tana tahowa gun Halima.
Ko da ta iso gareta ta kuma maimaita tambayar ɗazu, idanuwan Halima da su ke tsiyayar da hawaye ta fara juyo da fiskanta ga Inna Jummai, kasancewar ba wani haske ba ne yasa Inna ba ta gane wace ba, "baiwar Allah lafiya kuwa? Ko kin yi ɓatan hanya ne?". Inna ta ƙara tambayar.
Cikin rawar murya ta amsa mata da faɗin, "Inna ni ce Halima 'yarki", butan ta saki ya faɗi ƙasa, Hannunta na kyarma ta ɗaga tana nuna Halima da yatsa, bakinta ya kasa furta komai.
Halima da ta lura da yadda Inna ta kiɗime, kawai sai ta yi ƙasa kan guiwarta ta fashe da matsanancin kuka, "Inna ki yafe min, Inna na roƙeki ki yafe min, Inna na ga sakamakona, wallahi na ga jarrabawata, babu abin da ya rage da ban gani ba izuwa yanzu, na yi nadama, na san na aikata miki kuskure babba, à matsayinki na wanda ta haifeni na wulaƙantaki, ki yafe min Inna na roƙeki!".
Ta kai ƙarshe da kuma fashewa da wani kukan, gaba ɗaya jikin Inna ya saki, ta durƙusa ƙasa gun 'yarta, ta rungumeta tana mai kukan itama, sun ɗau mintuna à haka, yayin da basu sani ba wata 'yar maƙwafciyarsu na ƙofa tana jin komai.
Sassauta kukan Halima ta samu damar yi sannan ta ɗago da idonta kan Inna, ta ce, "Inna na roƙeki ki yafe min kin ji? Na san na cutar da ke, gashi komai ya juye kaina, na jefa ki cikin halin talauci da takaici, gashi ni à yadda na ƙare".
Kallonta Inna ke yi yadda ta ga ta sauya gaba ɗaya, duk da kasancewar ba haske amma ta canji akanta Halima, ta rame sosai, ko da Innar ma ta rame amma na Halima ya fi yawa, ba ta ce komai ba sai hawayen da ke zuba. Halima kuma da ta ke ganin dama ce ta samu don sanar da Inna komai, da kuma sake neman yafiyarta akaro na babu adadi, ta kuma cewa.
"Tun ina ƙarama burina bai wuce na kasance a gida na alfarma ba wato na masu kuɗi, Inna, wannan dalili ne yasa na ke yawan yin abubuwan ƙarerayi don kawai na saje da 'ya'yan masu kuɗi, sannan na ke kutsawa duk inda na ga manyan yara ne a wurin, kuma na yi nasara don na samu ƙawaye kangararrun yaran masu hannu da shuni. Daga nan Inna, ko wani gurin party ina nan, ga shi ke kuma da na tambayeki kuɗi ki ke bani, wani lokaci har sace miki na ke yi, kuma kin sani amma sai ki yi shiru ki barni, yawancin dare na ke fita zuwa guraren baɗalà ba tare da saninki ba, ko kinga yanayina wani iri na buguwa ba kya tambayata, sanin halinki yasa mutane ko sun ganni a inda bai dace ba, ba sa zuwa su sanar miki, domin ke ba kya yarda da kuskurena, kuma ke a ganinki ba zan aikata hakan ba duk iskancina. A haka na haɗu da S man gurin shagalin wata ƙawata, akallo ɗaya na kamu da sonsa, duk da cewa na san shigansa ne ya fi jan hankalina, na yi ta bibiyarsa har ya yarda, shima ya nuna min duk duniya idan ba da ni ba ba zai iya rayuwa ba, ya sa ni a cikin wani kasuwancin kayan maye, ba tare da tunani ba na amince, na ke zuwa ina jan hankalinki da ƙarya don ki bani kuɗi. Daga ƙarshe na samu damar sace kuɗin da na gano kina ɓoyewa, a tunanina ke ba komai ba ce a gareni wannan lokacin, hanya ce a gurina da nima zan kasance cikin cikar muradina, na tafi na barki domin zuciyata ta bushe ba na kallon komai sai abun da na sa a gaba, samun abun duniya da kuma abokin rayuwa. Na zauna da S man kamar miji da mata, a ƙarshe dai na samu ciki".
Miƙewa Inna ta yi cikin rikicewar ƙwaƙwalwa tana jefawa Halima kallon tashin hankali idonta na zaryar ruwa, Halima kuka ta kuma sawa sosai, sannan ta dakata ta ɗaura da cewa, "alokacin da aka tabbatar min ina ɗauke da ciki na yi murna, a ganina zan aureshi sannan ga ɗanshi ina ɗauke da shi, amma ashe komai da S man ya ke yi min ƙarya ce, dama ce kawai ya samu don ya lalata min rayuwa, ya samu abun da ya ke so sannan kuma ya yasar da ni, a ƙarshe ma shayar da ni ya yi wani magani mai kama da guba don cikin na wa ya zube, ko kuma ya dawo yana illatani, sannan ya koreni daga gidan da ya min ƙaryar cewa ya siya min da dukiyata, na sha wahala Inna har kallon mara hankali ake min, ga maganin da yasa min sai azabtar da ni ya ke Inna".
Inna da kuka ya so kufce mata ta kuma durƙushewa, ta rungume Halima gaba ɗaya su ka cigaba da kuka mai ratsa zuciya, Inna ke cewa, "wani laifi mu ka yi da duk wannan abu ke faruwa da mu? Me yasa komai ya ƙare mana? Na sha wahala ya zama ko abincin da zan ci yanzu ba na samu, komai ya rikice min, me ne duk wannan lamarin?" Ta kai ƙarshen ta ɗaura da kuka.
"Haƙƙi!! Haƙƙi Inna" faɗin Halima idonta cikin na Inna, da rashin fahimta Inna ke dubanta, "kamar ya Halima? Wani haƙƙi ki ke magana akai?" Ƙoƙarin tashi Halima ta yi, ta fara takawa zuwa gaba da jan ƙafa, ta isa gun dogon ƙarfen dake haɗe da ginin, na dakalin ƙofar Inna. Ita kam Inna tana biye da ita ba tare da ta gane komai ba.
Halima ta kuma cewa, "Inna kina nufin kin manta komai? Kin manta Nuriyyah? Ba ki yi tunanin haƙƙinta zai iya bibiyarmu ba Inna?" Ta fito da idanu tana ganin Halima da ke juyowa. "Eh Inna, tabbas haƙƙin shekaru takwas ne ke bibiyarmu yanzu, komai da ya faru alhaki ne ba wani abu....".
Halima ta kasa ƙarasa maganar sai ƙara da ta saki ta durƙushe tana kama cikinta, hankali a ɗage Inna ta zo tana kamata, "ina so ki amince da maganata Inna, domin yadda mu ka kori Nuriyyah à wancan ranar haka S man ya koreni, Inna duk abun da ya samemu mara kyau to haƙƙinta n... aahhhh" ta ƙarashe da sakin ihu.
A wannan lokacin wannan matashiyar da ke maƙale tana sauraronsu ta wuce tana girgiza kai haɗi da jan ƙwafa. Ihu Halima ke yi saboda yadda cikinta ci juyawa kamar ana matse kayan wanki, Inna na kuka tana ta kiran sunanta, cikin sautin numfashi na wahala Halima ke faɗin, "na san maganin da S man ya bani ne, shine Inna, waiii zan mutu na shiga ukuna!".
Ciwon da ta ke ji a yanzu ya buge duk wanda ta taɓa ji a baya, da ƙyar Inna ta samu kaita waje, ta tari napep ta sanyata ciki su ka nufi asibiti, à wannan halin su ka isa government hospital da ke kusa, sai dai babban matsalar Inna ba ta da kuɗi, ko me mashin ɗin ma ganin halin da su ke ciki ne yasa shi tafiya ba tare da tambayar kuɗinsa ba.
An dai shigar da Halima ciki, bayan an bata kulawa da duk wani extermination aka fito, doctor ke cewa Inna ana da buƙatan yiwa Halima tiyata don a gaggauta cire jaririn da ke cikinta, sun gano akwai wani guba da ya shiga cikinta, don haka idan har ba a cireshi ba rayuwarta na cikin hatsari babba!.
"Likita to a cire mana, don Allah kada wani abu ya samu 'yata", cewar Inna hankali a tashe, doctor ya ce, "ki kwantar da hankalinki madam, zamu yi duk abun da ya kamata don ganin mun ba ta duk wani kulawa, amma kafin nan za ku biya 3 millions..." "ban fahimta ba likita".
"Ina nufin za ku biya miliyan uku kuɗin aikin da za'a yi mata zuwa gobe, kuma ya kamata ku hanzarta don abun ya yi tsanani a jikinta", yana kai wa ƙarshe ya wuce ya bar Inna da ta bushe tun da ta ji zancensa.
Miliyan uku? A ina za ta samu miliyan uku ita da ko dubu ɗaya a halin yanzu ba ta magani? Jingina ta yi da bangon kusa da ita tana faɗin, "inna lillahi wa'inna ilaihi raju'un!". Ba ta san ya za ta yi ba, ba ta da wani mafita ko kaɗan.
WASHE GARI.
Inna ce ke watsar da komai da ke cikin ɗakinta, sai bincike ta ke yi kamar wata zautacciya, wai neman kuɗi ta ke yi a ɗakin, tun jiya ta ke bilayin nema à ƙarshe wanda ta samu ko dubu goma ba su kai ba, a haka ma ta ci sa'a kenan, idanuwanta duk sun canza, tun da abubuwan nan su ka faru tunani ya zama ruwan shanta, ko barcin kirki ba ta samu, to jiya ko kaɗan ɗin ma ba ta yi ba.
Tunanin ka da lokaci ya ƙure gashi kuma likita ya ce a gaggauta, yasa ta bar gidan ta kuma nufan asibiti. "Haba madam, mu da mu ka ce miki three million naira, amma ki kawo mana seven thousand?" Cewar doctor bayan Inna ta kai masa kuɗin, Inna cikin magiya ta ce, "likita ai taimakawa za'a yi, iya abun da na samu kenan, wallahi bani da halin miliyan uku yanzu, wannan ɗin ma Allah ne kawai ya nufa bayin Allah za su taimakeni".
"I'm sorry madam, but I don't have the authority to help you in this situation, dole sai kin kawo kuɗin nan kafin a fara yiwa 'yarki aiki", tashi Inna ta yi tana tafiya kamar wacche ba ta da laka a jiki, a sanyaye hawaye cike da idanu ta isa ɗakin da Halima ta ke.
Ta zauna a gefenta ta ƙura mata ido, 'wai wannan duk mafarki ne? Yaushe za mu farka da cikinsa? Me ya s...", ba kai ƙarshen zancen zucin da ta ke ba, magan-ganun Halima na jiya ya fara dawo mata, 'Kin manta Nuriyyah? Ba ki yi tunanin haƙƙinta zai iya bibiyarmu ba Inna?... tabbas haƙƙin shekaru takwas ne ke bibiyarmu yanzu, a hankali Inna ta furta, "Nuriyyah!?".
"Ƙwarai Inna, Nuriyyah" muryar Halima na jinya, ta buɗe rarraunun idanuwanta masu nauyi.......
Last page.
____________________________________________
Me ku ke ganin Nurse za ta faɗawa su Faruq da har ta ke tunani?
Ga Halima dai abu ya motsa fiye da baya, kuna ganin za a samu kuɗin aikin? Inna Jummai za ta yarda da zancen Halima? Me zai faru gaba?
_*🌹𝑍𝑎ℎ𝑟𝑎-𝑡𝑢𝑙-𝑄𝑎𝑙𝑎𝑚🖋️*_