Page-47
FASAHA WRITER'S ASSOCIATION*
(*F.W.A)*©✍️
⭐⭐⭐
Ƙungiya masu aiki cikin salon hikima da fasaha gurin juya tunanin al-umma, kaifin alƙalumansu ya zarta takobi ©✍
___________________________________________________
بسم الله الرحمن الرحيم.
اللهم صلي وسلم على نبينا محمد.
❁ 𝐒𝐀𝐍𝐀𝐃𝐈𝐍 Ƙ𝐀𝐃𝐃𝐀𝐑𝐀𝐓𝐀 ❁
Free book📓
By: _*🌹𝑍𝑎ℎ𝑟𝑎-𝑡𝑢𝑙-𝑄𝑎𝑙𝑎𝑚🖋️*_
Page4️⃣7️⃣
Asma'u zuwa ta yi ta zauna gefen Momy, sai dai ita Momyn ba ta sake mata fiska ba, "Momy akwai wani magana mai mahimmanci, da na ke son sanar da ke akan Nuriyyah", faɗin Asma'u, kallonta Momy ta yi, fiskarta ya bayyanar da mamaki, ka na ta ce, "akan Nuriyyah? To ina jinki".
Asma'u ta gyara zama, sannan ta buɗi baki ta ce, "Momy yanzu na riga da na san komai akanta, saboda na..." "assalamu alaikum" sallamata ya dakatar da ita, Momy da ke sauraronta jin sallamar da na yi, yasa ta miƙe ta nufoni tun kan na ƙarisa shigowa, ta ɗaura hannunta a fiskata tana faɗin.
"Lafiya ki ke Nur? Ba abun da ya sameki? Ina ki ka tsaya?" Ganin yadda Momy ke min tambayar cikin damuwa, sai na yi saurin sakar mata da murmushi, na kama hannunta da ke kan fiskata na sauke ƙasa, sannan na ja ta zuwa kan kujera.
"Momy ki kwantar da hankalinki lafiya ƙalau na ke fa, ba abun da ya sameni" ta sauke numfashi ta kuma cewa, "to ina ki ka tsaya har 'yan uwanki su ka dawo ba tare da ke ba?" "Sorry Momy forgive me, hakan ba zai sa ke faruwa ba, na saki cikin damuwa ko?"
Rungumeni Momy tai tana murmushin jin daɗi, kasancewar mun saba dawowa tare, ko tafiya wani guri mutum ɗaya a cikinmu baya tafiya shi kaɗai, shiyasa ta damu yau sosai. Ɗaga ido na yi ina kallon Asma'u da ta cika ta batse saboda haushi, yadda Momy ta fi ƙaunata akanta, amma a tunaninta, bare yanzu da ta gane wasu munanan abubuwa tare da ni.
Ayusha ma na tsaye can ta wani haɗe fiska, haushi duk ya cikata, saboda yadda ta ga Momy ta bani kulawa. Ɗagowa Momy ta yi ta ce da ni in je in watsa ruwa in fito inci abinci, da toh na amsa mata sannan na yi hanyar ɗakinmu, idona ya kai kan Ayusha sai ta sakar min da murmushin ya ƙe. Ni dai ban tsaya ba na wuce abina, ita ko ta kuma takowa har da zama gefen Asma'u.
"Ina jinki wani magana ki ke faɗa min?" Faɗin Momy wa Asma'u, ta cire idonta da kallon bayana da ta ke, sannan ta juyo gun Momy tana haɗiye wani miyau. "Eh faɗa mana 'yata" Momy ta kuma jefa mata tambayar, sauke ajiyar zuciya ta yi, yayin da zuciyarta ke cike da haushi, sannan ta ce, "Momy abun da na ke son cewa, yanzu na riga da na san komai akan Nuriyyah! Na gane ita mutum ce mai fahimta".
Zuciyar Ayusha ta buga saboda kalaman da Asma'u ta faɗi wanda ba haka su ka yi da ita ba, Momy kuwa murmushi ta yi ta ce, "dama wannan shine abun da ki ke son faɗa min? Ita Nur dama haka ta ke ai, sannan ki ƙara da sanin, ba ta damu da kanta kamar yadda ta damu da wani ba, da ta ganni cikin damuwa burinta ta kawar min".
Murmushin dole Asma'u ta yi, yayin da ta ciki wani zafi ta ji, ta miƙe tana faɗin, "ina zuwa Momy" "ba ki ci abinci ba, ki bari ki ci sai ki wuce" cewar Momy, ta kuma cewa, "ba zan daɗe ba" sannan ta fice, Ayusha ta ya ƙe haƙora wa Momy itama ta bi bayan Asma'u, zuciyarta natafarfasa.
Kiranta ta ke yi amma Asma'u ta ƙi tsayawa bare ta amsa mata, sai da Ayusha ta janyota baya sannan ta juyo tana kallon Ayusha da mamaki, "Ayusha me haka?" "Ke dai zan tambayeki me haka? Akan me ki ka ƙi sanarwa Aunty Rahama komai? Bayan mun yi da ke za ki faɗa mata, kuma ni zan zame miki shaida? Ko tsoron Nuriyyahr ki ke ne?" Cewar Ayusha ta cika da baƙin ciki.
Asma'u ta ce, "akan me zan ji tsoronta?" Ayusha ba ta kuma cewa komai ba, ita ko Asma'u ta ba ta baya tana faɗin, "bayan duk abun da ya faru, amma zuciyata ta kasa tsayuwa guri ɗaya akan wannan lamarin. Tun haɗuwarmu da Nuriyyah, ba ta taɓa barin wani abu ya cutar da ni, ko a makaranta idan aka tsokaneta ko kuma nemanta da faɗa, kai koma me za'ayi mata tana jura, amma abun mamakin, da zarar ance miki wani ya taɓani to ba za ta taɓa haƙura akai ba, za ta iya zagewa indai akaina ne ta yi faɗa da kowa, to amma me yasa za ta aikata wannan abun, shin dama asali haka zuciyarta ya ke kawai ɓoyewa ta ke yi? Ko dai yanzu ne ta sauya? Ƙwaƙwalwata ya gaza tsayuwa cikin natsuwa".
Ayusha da ta cika da takaici har ta fara neman zuba, saboda ganin kamar wai fa Asma'u har yanzu ba ta gama yarda da shirin da su ka haɗa ba, ta ce, "Asma'u kada ki bari zuciyarki ta ja ki zuwa hanyar da ba daidai ba, taya bayan abubuwan da su ka faru, but again kina irin wannan tunanin?".
Asma'u juyowa ta yi tana kallonta itama ta ce, "kin manta kalaman da ki ka faɗa ranar? Iyayenmu suna son mu, bai kamata mu yi wani abun da zai jefasu cikin damuwa ba, haka ki ka ce. Momy ta yarda da Nuriyyah sosai, don haka ba zan iya sa zuciyarta ya karye ba, zan zauna a hakan ya zama tsakanina da ita kawai, ba tare da kowa ya ji ba, kuma kema da ki ka san komai ina son, don Allah ki barshi cikin zuciyarki".
"No Asma'u i don't do that! Idan ke ba za ki iya faɗa ba, ni zan je insanar da kowa abun da ya faru" cewar Ayusha tana juyawa, "idan ki ka je, ba na tare da ke, domin zan nuna ban san komai ba, rayuwata ce, ni abun ya shafa, don haka please ki cire kanki a ciki" faɗin Asma'u ta juya ta wuce. Waigowa Ayusha ta yi baƙin ciki na cinta, sai da ta buga ƙafarta ɗaya a ƙasa ta ja dogon tsaki.
Ba ta tsammata hakan daga gareta ba, "kina nufin komai da muka shirya ya tafi a banza ne? I will not allow that to happen! Sai na sa ki da kanki kin sanarwa kowa komai!" Ta faɗi idonta na bin hanyar da Asma'u ta bi, sannan ta ja ƙwafa.
A cikin kwana biyar mu ka kammala exam ɗinmu gaba ɗaya cikin ikon Allah, har yanzu komai na cikin raina, sannan har yanzu tsakanina da Asma'u bai canza ba, sai dai takan yi min magana ɗaiɗai idan ya zama dole. Ni da Abba kuma soyayya ba ta sauya ba, sai ma dai abun da ya ƙaru, amma ban sanar da shi komai ba, sai dai na fara neman hanyar da zan bi don fitar da gaskiya a idon kowa game da Subusi.
Domin kuwa ba zan taɓa barinsa ya ci banza ba, sannan ba zan taɓa zuba ido ya auri Asma'u ba, sai na yaye duk wani mayafin sharrin da ya yaɓa min a idon 'yar-uwata, sai na tona asirinsa! Daman bari na yi na kammala exam, saboda na fi maida hankali akansa, to yanzu kuma Allah ya nufa!.
Yau asabar, Hajiya Kaka ta nemi da kowa ya zo sashinta ayi breakfast, acewarta an daɗe ba'a ci abinci tare kuma anyi hira tare ba, kowa ya yi farin ciki da wannan batun na ta. Ni kuma a shirina, yau ce ranar da zan fara auwatar da aikina don tona Sunusi, zuwa anjima na ke son na samu damar fita daga gidan.
Suna zaune akan kujerun dining, yayin da aka jere abinci kala-kala na kari akan table ɗin, kowa ya hallara su Dady, Momy, Hajiya Kaka, Abba, Asma'u, Wasila, Hajja Mama, uncle Usman, Hanif, Nusaiba. Duka sune zaune a wannan wurin.
"Wai ina Nuriyyah ne?" Faɗin Hajiya Kaka da ta lura ba na ciki, Dady ma ya ce, "nima abun da na ke son tambaya kenan" taɓe baki Asma'u tai ganin duk iyayen na ta hankalinsu na kaina. Momy ta murmusa tana faɗin, "yau na tashi ba na jin ƙarfi a jikina, kamar zazzaɓi na son kamani, shine fa ta ce to sai ta yi min kunu ko zan ɗan ji daɗin bakina". Dukkansu murmushi su ka yi, ban da Mama, Asma'u, da kuma Nusaiba.
Ina can ina damawa Momy kununta, bayan na kammala ya zama a flask kawai ya rage na juye, kawai na ji ƙarar faɗuwan abu ta falo, hakan yasa na bar abun da na ke yi na fice don duba menene, domin à iya sanina su Momy duk sun tafi side ɗin Hajiya Kaka. Ko da na fito ban ga alamar wani abu ya faɗi a falon ba, da mamaki na juya zan koma ciki, sai dai zuciyata na bugawa a hankali, ba na jin wani abu a daidai, saboda ji na ke kamar akwai wani da ya laɓe a bakin ƙofa.
Takowa na fara yi ina ambatan, "waye a anan?" Amma shiru ba magana, ƙirjina na ba da fat fat, duk da cewa ba wai dare ba ne bare na razana, kaɗawar da labulen window ya yi ya sani da sauri idona ya kai gun, na haɗiyi nyawun fargaba ina cigaba da tafiya zuwa wurin, hannu na ɗaga a hankali bayan na isa, na janye labulen da ƙarfi, amma sai dai wayam na tadda shi ba kowa, sauke ajiyar numfashi na yi na dafe ƙirji.
Ganin kawai zuciyata ce ta ke raya min akwai abun da zai faru, yasa na juya zuwa kitchen, sannan na juye kunun a cikin flask, duk da cewa har yanzu zuciyata ba a kwance ta ke ba, na nufi ɓangaren Hajiya Kaka.......
Ayusha ce ta zo ta zauna a wurin Hajiya Kaka na tambayarta ina ta tsaya, ta ce, "ba komai Hajiya kiransu Mamyna na yi mu ka gaisa" "masha Allah suna lafiya dai ko?" Cewar Uncle Usman, ta amsa da eh, nan aka fara sanyawa kowa abinci, bayan an gama na shigo, kallona Ayusha ta yi, a ƙasan zuciyarta tai dariyar farin ciki, amma a fili ba ta nuna ba.
Idon Abba a kaina cikin jin daɗi har na ijje flask ɗin a gaban Momy, sannan na ja kofi na fara zuba mata a ciki, duk bai kawar da idonsa kaina ba, "thank you My daughter" faɗin Momy, murmushi na yi mata sannan na zauna a kujerar da ke gefen Asma'u, yayin da ita kuwa kawar da kai ta yi gefe da muka haɗa ido da ita.
Murmushi mai ciwo na yi ganin abun da Asma'un ta yi min, "a ah, amma ya na ga Momy kawai aka ba kunun? What about us?" Cewar Abba yana kallona da ɗaga min gira, ƙasa na yi da kaina kan abinci sannan na ce, "Momyna kaɗai na mawa", Dady ya yi dariya ya ce, "kun ga 'yar Momy kenan, wato har da Hajiya yau ba a ta na ta ko?". "Na ga alama ba ka ga kofi ɗaya ma takawo ba?" Faɗin Hajiya Kaka.
Dariya mu ka yi Abba ya kuma cewa, "na san ma ba wani daɗi ya yi ba, shiyasa ta ke gudun mu sha mu ji test ɗinsa" "ba dai za ka sha shi ba, ni kaɗai 'yata ta yiwa" faɗin Momy tana kaiwa bakinta a karo na biyu, ta kuma cewa, "amma ya yi daɗi" faɗin Momy, uncle Usman ya ce, "to ki dai sha a hankali madam, don kada daɗinsa ya samu haɗiyar miyau mu ba mu sha ba" nan ma mu ka kuma darawa cikin nishaɗi.
Sannan mu ka fara cin abinci gaba ɗaya, Hajiya Kaka ta tsaya ta dubi Abba ta ce, "kai Abba ina Sayyid ne tun da safe ban ganshi ba..." kafin ta ƙare tambayar sai ga sallamar Sayyid a wurin. "Ɗan halak kenan, ina ka shige ne tun safe?" Zama Sayyid ya yi kusa da Abba yana murmushi kafin ya yi magana Abba ya ce, "Hajiya Kaka rabu da Sayyid, tun shekaran jiya fa yaso ya koma, sai da na dage a kansa sannan ya haƙura, amma duk da haka cewa ya yi wai ba zai daɗe ba, na kasa gane masa kamar cizonsa mu ke a garin nan".
Da mamaki dukkanmu mu ka zubawa Sayyid ido, sai dai shi ƙasa ya yi da kansa, ba zai iya cigaba da zama ba, ahakan ma ai ya daɗe, ya fi so ya koma idan yaso sai auren Abba ya zo, domin har i yanzu zuciyarsa cikin rauni ta ke akan Nuriyyah, yin nisa da ita ne kaɗai zai sa shi mantawa da komai, "me yasa ka ke son tafiya Sayyid ɗana? Ko dai nan ɗin ne bai yi maka ba? Ko kuma ana yi maka abun da ba son shi ka ke ba a gidan?" Dady ya yi masa tambayar.
Kansa da ke ƙasa ya ɗago haɗi da girgiza kai ya ce, "no Dady, ko ɗaya babu cikin wannan, ba wani abu da ku ke min sai mai kyau, kun zame min kamar 'yan uwa, kuna kulawa da ni, don haka kuwa ba abun rashin daɗi da za ku yi min, kawai dai I will return because of my family, sun nemi da na koma kusa da su, wannan shine dalilin".
Girgiza kai wasu su ka yi, uncle Usman ya ce, "haka ne, tun da iyayenka sun so ka zauna da su hakan yana da kyau" "to ko aure su ke son yi maka ne Sayyid?" Hajiya Kaka ta faɗi hakan, Sayyid ya murmusa haɗi da sosa ƙeya, ba tare da ya amsa ba, don shi kunya ma ta ba shi, Hajiya Kaka kuwa ta ƙara cewa, "au ba za ka yi magana ba?".
Abba ya ƙara faɗin, "Kakus ɗina rabu da shi, tun fa farkon zuwansa ya sanar da ni akwai yarinyar da ya ke so, kuma a cikin gidan nan, amma à ƙarshe yasar da maganar ya yi ya ƙi sanar da..." "a ah Hajiya Kaka, ni fa dama wasa na ke masa tun farko, domin ya addabeni akan sai na sanar da shi wacche na ke so" Sayyid ya tari numfashin Abba.
Dariya mu ka yi da yadda ya yayi maganarda sauri, da kuma niyyar kauce musu, kowa ya cigaba da cin abincinsa cikin natsuwa da salama.
"Momy da ta shanye kunun kofin da na sa mata ta kuma ƙara wani, domin ya yi mata daɗi sosai ko abincin ma ba ta fara ci ba, kwatsam ta fara jin wani yanayi a cikinta, da fari ba ta kawo komai ba, amma daga baya ta ji cikinta kuma ya fara wani irin sukanta kamar da kibiya ta ciki, anan kuma wuyanta ya fara amsa mata, ba ta san lokacin da ta ijje kofin kunun da ke hannunta da ƙarfi ba tare da sakin ƙara, wanda hakan ya dawo da gaba ki ɗaya hankalinmu gareta.
Hannu ɗaya ta kai cikinta, ɗayan kuma wuyanta, saboda wani azababben ciwo da ya ke ziyartarta, dukkanmu miƙewa mu ka yi cikin tashin hankali mu ka yi kanta, muna tambayarta me ya sameta. Cikin wani murya da ta yi dauriyar fitar da shi da ƙyar ta ke faɗin, "wu...wu...wuyana. Ciki...na" maganar ya maƙale ta fara ƙoƙarin zamewa ƙasa.
Yanayinta ya ɗaga hankalin kowa sosai domin muryarta ma ya gagara fitowa, ganin abun ba na ƙare ba ne yasa Dady ya ce ya kamata su yi saurin kaita asibiti, dukkanmu mu ka yi waje su Dady riƙe da Momy, aka sa ta a mota, Hajiya Kaka na shirin shiga mota kanta ya sara mata, sakamakon yadda hankalinta ya ɗagu, da sauri na riƙeta cikin wani sabon ruɗewar.
Sannan na ce su je su kai Momy asibiti ni zan kula da Hajiya Kaka, sauran su ka shiga mota ban da su Mama da su Wasila, don suma har za su shiga sai Mama ta ce bai kamata su cika asibiti haka ba, su bari daga baya su ji me yafaru kafin su je.
Da hanzari su ka fice daga gidan ko wanne zuciyarsa ya ƙi natsuwa, su ka nufi asibitin Abba kasancewar ba wani nisa ya ke da shi ba. Ni kuma na kama Hajiya Kaka mu ka yi ciki da ita ina ta jera mata sannu.
Hankalin kowa ya tashi ƙololuwa, saboda yadda Momy ko motsi ta daina yi, da gaggawa Abba da Sayyid su ka shiga da ita emergency room, su ka ɗaura farar rigar likitoci a jikinsu, zuciyarsu ta kasa sukuni, wasu doctors su ka shiga da gaggawa, nan aka kama neman lafiyar Momy babu kama hannun yaro.
Su Dady na waje zuciyarsu cike da tsoro haɗi da fargabar jin sakamakon abun da ya faru da Momy, don a iya saninsu ba ta taɓa shiga wannan yanayin ba, ko suma ba ta taɓa yi ba.
BAYAN WASU AWANNI.
Su Abba su ka fito jiki babu ƙarfi, idon Abba har ya yi ja saboda tsananin ɗaguwar hankali, musamman da ya tabbatar da sanadin rashin lafiyar na ta, da hanzari su Dady su ka yo inda su ke, binsu da kallo Dady ya ke shi da Uncle Usman, Asma'u kam tun ɗazu kuka ta ke yi, sai Ayusha da ta ke rarrashinta kamar dole, "Abba me ya samu mahaifiyarka?" Faɗin Dady baki na rawa, ƙwallar da ya cika masa ido ya sauka, sannan ya share ya dubi Dady ya ce, "Dady!... bincike ya nuna, Momy ta shiga wannan yanayin ne ..." sai kuma ya dakata yana sauke numfashinsa da ke sarƙewa.
"Ina jinka Abba me ya samu matata?" Faɗin Dady tana shirin ruɗewa" sai da Abba ya matse idonsa cikin jin zafi ya ce, "Momy ta shiga wannan yanayin n.... sakamakon poison ta sha". Ba Dady kaɗai ba, hatta sauran sai da ƙirjinsu ya bada bugu mai ƙarfi, su ka zaro idanu, cikin tashin hankali Dady ya ce, "poison Abba?!".
Girgiza kai Sayyid ya yi ya ce, "ƙwarai kuwa Dady, guba ne kuma mai matuƙar hatsari, sannan duk da kasancewar mun kawota cikin lokaci, amma Momy na cikin babban matsala, wanda hakan yasa ta shiga cikin coma, yanzu haka numfashinta ba ya fita mai kyau, sannan kuma jinin jikinta yana neman daskarewa" faɗin Sayyid yana zubar da hawaye.
Last page
___________________________________________________
Kaii! Momy ta sha poison? Subhanallahi, a tunaninku a ina Momy ta samu guba? Cab! Hmmm.😳
To a baya Asma'u ta ƙi faɗin komai, amma a yanzu anya ba wata fitinar da ya fi wancan ba ne kuwa?. Wani hasashe ku ke da shi a kai? Mu haɗu a next😊
_*🌹𝑍𝑎ℎ𝑟𝑎-𝑡𝑢𝑙-𝑄𝑎𝑙𝑎𝑚🖋️*_