KUNCIN ZUCI

Kuncin zuci

by @bintuuu

Washegari Monday 
Da asuba sai ga kiran Ahmad lokacin Na'ima na sallah ma, da ta idar da sake ganin wani kiran nasa, sauqinta ma ta saka wayan a silent shiyasa ta kifar da wayan bata kula ba, sai da ya jero missed calls guda hudu a jere bata dauki ko daya ba tana gani, ranta na takejin yana zafi akan tafiyan sa Abuja wai kuma dalilin Laila, gashi har sannan wani abune ya tokare mata wuya yaqi ma wuce wa balle ta samu sauqin abunda takeji din, zuwa Eleven na safen Al'ameen yakawo Mami gidan dalilin kiran da Abba ya mata dan ya koma Abuja shida Faruk sunacan gidan, yafada mata sunyi waya da Alhajin ba da dadewa ba akan Na'iman zata koma Abuja ana nemanta gurin aikinta, wanda hakan ba qaramin dadi yayi wa Mamin ba saboda tanason zaman Na'iman a kusada ita dan yanda Ahmad ya nemi matarsa ta tare da wuri dole tana buqatar tayi gyara me kyau a 'yarta itama, sai da suka gaisa da Hajiya ta kawo mata ruwa sannan Mami ta kawo maganan, su Na'ima da ke zaune falon babu wanda ya tankan acikinsu, Hajiya ce ta amsa da "Alhajin ya kirani ya fadamin, ai zata dawo nan din kafin lokacin tarewan nata ko" Mami na murmushi tace "Duk yanda kukace haka za'ayi Hajiya" sai tace "A'a ai ko acan din ne ma duk daya ne" sai ta qara da "Naima ku hado kayan naku, Dan Alhaji yace flight din yamma ko" Mami tace "Eh in sha Allah" miqewa su Na'ima sukayi suka bar Hajiyan nan zaune da Mamin a falo, shiru sukayi sai can kuma a nutse Mami tace "Har yanzu bakuji daga garesa ba?" asanyaye Hajiya tace "wallahi har yau dinnan mun gwada layinsa baya tafiya, gashi abokinsa da muke sa ran zamu ji labarinsa ta gurinsa ma tashi wayar bata shiga shima" ta qarasa maganan hawaye na kawowa idonta, jiki a sanyaye Mami tace "in sha Allah yana lafiya, zai dawo kwana kusa bi'iznillah" sai Hajiya ta share hawayen nata tace "Allah yasa" ta sake cewa "Maman Nafisa kuyi hakuri akan duk abunda ya faru dan Allah, nasani banyi daidai ba wallahi, tafiyan Na'ima nayi ta wishing kar ta dawo, amma sai yanzu na fahimci cewa ina ta fatan hakan ne zuciyata cike da tsoro da regret din abubuwan da suka faru, wallahi not a day goes by da bana tuna yarinyar nan araina, nasani nayi son zuciya kuma sai Allah ya saka mata, dan gashi nan yaron da nake ta wannan abubuwan akansa bai daukeni abakin komai ba a rayuwar nan, yau ace Ina mahaifiyarsa amma zai iya going by months bai nemeni ba" kawai ta fashe da kuka, Mami ta kwantar da murya tace "kiyi hakuri, Allah zai ganar da shi, kiyi ta addua kar ki gajiya, komai zai wuce" Hajiya ta gyada kai tana share idonta tace "Nagode, zan yi tayi" da haka suka sakeyin shirun, Husna ce ta fara sauqowa da nata akwatin sai Mami tace takai mota Al'ameen ya saka mata a booth dan yana wajen bai shigo bama, da su Na'ima suka tashi tafiya sai Hajiya ta rungumeta tana fadin "sai kin dawo Na'ima, munanan muna jiranki, Allah ya sanya alkhairy" Na'ima ta gyada kai tanajin embrace din na saka mata awkwardness at the same time kuma sanyi arai, murmushi kawai tayi sai Al'ameen ya qaraso ya karbi kayan nasu suka gaisa da Hajiya...A hanyarsu ta komawa gidan Abba dake kano Na'ima ta sake ganin wani kiran Ahmad din ya shigo wayarta amma sai ta saka wayan a side bag dinta ta juya ga window tana qara hade fuska sai kace tana gabansa, da suka isa gidan Abban ma abinci kawai sukaci sukayi sallah, sai Mami ta aiki su Nafisan su karbo mata wasu turarukan humra da tayi order daga maiduguri, an kawo saqon nata gidan kawarta, su Nafisa basu dade ba suka dawo nan suka hau shirin tafiya kuma dan qarfe hudu ne flight din nasu....
Da suka isa Abuja ma Na'ima na ganin kiran Ahmad da text dinsa bata kula ba har suka isa gida, dalili daya ne ya hanata kashe wayan gaba daya shine kuma jiran kiran Kamal da takeyi har sannan da yace zai hadata da salame saboda tana son ji daga gareta kuma har sannan shiru, ga layin Anty Amarya da take ta kira baya tafiya shima, Daren ranan tana daki a zaune bakin gado tana ware takardun ta da Abba yace zataje gurin aikin nata dasu sai ga Mami ta shigo dakin hannunta riqe da wani cup cike da wani hadin madara me kauri, zama tayi nan bakin gadon tareda miqa ma Na'iman tace "ungo Habibti, ki shanye kinji" Na'ima na sunne kai ta karba tareda gyada kai kawai, sai Mamin ta miqa hannu tana duban takardun tace "bari dai kiga, it's like baki gane wanne da wanne Abban naku yake nufi ba" da sauri Na'ima tace "I'm a little bit confuse ne Mami, kamar yace da wannan" ta qarasa magana tana miqo mata daya daga cikin takardun, Mami ta karba tana gani sai kawai ta jawo takardun ta fara ware mata su, tana cikin dubawan ta dago kai tana ganin yanda Na'iman ta riqe cup din a hannu har sannan sai tace "maza sha Habibti" ta amsa da toh tareda kai cup din baki, sai da Mami ta gama hada mata takardun sannan ta miqe ta fice daga dakin, can kuma sai ga Nafisa ta shigo dakin, itama zama tayi tana bin cup din hannun Na'iman da kallo tace "Bobo ya kamar milkshake" sai Na'ima ta gyada kai tareda miqa mata tace "shine ma" karba Nafisa tayi tareda kurba, ta sake kurba, again ta sake kurba itadai Na'ima hankalinta ta maida kan takardun ta da ta janyo tana dubawa ma, sai da Nafisa ta kusa  shanye hadin madaran nan Na'ima na kallonta jefi jefi suna hira, saida ya kusa qarewa sannan ta miqawa Na'iman aikuwa ta karba ta cigaba da sha,  Abu ne ya kwankwaso dakin sannan ya leqo kansa yace "Mami na kiranku" Na'ima ta amsa da "toh" da haka ya juya, a falon downstairs suka sameta tana ta buga list a takarda ita da lantana na qananun kayan girki da zasu buqata a bikin, dago kai Mami tayi tace "Habibti kin shanye kuwa" sai Na'ima tace "Eh" batareda ta kalli Nafisa da ta juyo tana kallonta ba, sai Mami ta sake cewa "na ajiye miki sauran a fridge din falona, Habibti banason sai nayi ta maimaita miki da'alla" Na'ima ama da "toh" tareda zama har sannan taqi kallon Nafisa that was deadly looking at her, maganan kayan da Na'iman zata saka suka hau yi nan zaune, Mami tace da Na'ima "Gobe sai ki wuce fitting wajen Meerah in kin gamo uzurin naki" Na'ima ta amsa da toh sannan tace "Mami..uh..akwai..yaturo mana da card dinsa shekaran jiya" Mami na murmushi tace "toh Habibti sai kuyi uzurirrikan ku dashi" dariya kawai Nafisa tayi Mami na kallonta tace "Baby bance kuyi almubazzaranci ba kuma" tana dan dariyan tace "A'a Mami, ni wata gown guda daya kawai zan siya ma" Mami ta dubi Na'ima tace "Ina card din" sai ta kalli Nafisa alamun yana wajenta, Mami ta maida dubanta kan Nafisa tace "kinsan Allah zan saba miki in kuka masa wasa da kudi" Nafisa tace "Mami shi fa yace ya bamu go ahead" tace "Banason siyan abunda bai dace ba, kina jina" sai ta amsa da "Yes Mami" Faruk ne ya shigo falon cikin qananan kaya, da fara'arsa yace "Finally....The house was like a silent forest these two days" Mami na murmushi tace "Mun dawo Yayansu" zama yayi a gefen Mami tareda gaisheta ta amsa, Na'ima na murmushi ta gaishesa yace "Matar yayanmu, ya Kano?" sai ta sinne kai tana murmushi, sai yace "Allah ya sanya alkhairy Na'ima" Nafisa dake zaune gefenta tace "Ina wuni Yaya" ya amsa sannan yace "Me kuka dafa a gidan" Mami tace "Egusi soup ne, Baby zubo masa" Nafisa ta miqe ta wuce kitchen, Bai dade da fara ci ba su Abu ma suka shigo tare, nan falon suka zauna sai Nafisa ta kawo musu abincin dukansu ma, sai kuma aka kama hira, cikin hiran Mami ke fadin "ai kuna sane dai a compound din gidan nan za'ayi event ko" Nafisa tace "Habaaa Maminmu, ni da Husna munata planning dinner fa" Mami ta dan harareta tace "Dazu nake maganan da Amnah, uban gayyan bayaso to" sai Faruk yace "Dama meye amfanin yin grand event din" Mami tace "haka Abbanku ya fada dazu ma" Abu nacin abinci yace "Either grand or not, we're still going rock this wedding" sai aka dara gaba daya, Na'ima dake jinsu tayi shiru sai murmushi take binsu dashi kawai, Nafisa ta talle qeyar Abu tace "you're ruining my pleads" Mami tace "ba'a gurina zakiyi pleading ba, kinsan gurin wa zakije ai" Nafisa ta kalli Na'ima tace "Bobo kiyi magana da'alla, munason yin dinner, har nace zanyi wa su Lauren ashoebe fa" Na'ima na murmushi tace "duk yanda Mami tace" dan dariya Mami tayi tace "duk yanda mijinki yace dai Habibti" sai Na'ima ta duqar da kai har sannan bata bar murmushin ba...Da Na'ima ta kwanta zatayi bacci sai Nafisa ta shigo dakin da waya a kare kunnenta da alamun waya take da Ahmad tana fadin "Toh Yaya" qarasowa tayi kan Na'ima dake kwance ta rufe idonta kamar wanda tayi baccin, sai ta tabata tace "Na'ima.. Na'ima" shiru Na'ima tayi taqi bude ido ma balle ta amsa, ganin haka Nafisa tace "tayi bacci Yaya" sai kuma ta juya ta fice daga dakin tareda rufo kofan, sai sannan Na'ima ta bude ido, ita kadai ta hau hararan dakin kamar shi ya bata mata rai, da haka ta sake juyi tana gyara blanket dinta ko bin ta kan wayanta batayi ba, amma kuma sai me, bacci yace bega guri ba a idanunta, haka tayi spending another 1 hour tana kwance sannan dakyar baccin ya dauketa...

Washegari Tuesday 
Bayan Na'ima ta gama morning activities dinta sannan ta shirya cikin wani tsadadden lace dinta milk color ta dora babban mayafi akanta, tana cikin saka takardun a jakan Nafisa ta shigo cikin shirin kimono with inner fitted gown itama dan tare zasu fitan amma kowannensu da inda zai nufa, sai Nafisa tace "in kin gama sai mu hadu acan gurin meerah" Na'ima ta amsa da toh sannan suka fice zuwa gurin Mami dake falonta, a zaune suka sameta nan kan carpet tana video call da Anty Amnah, sai da suka jira ta gama maganan harda Anty Fatima da suke taren sannan suka sanar da ita fitan, Mami na kallon Na'iman tace "kin fada masa ai ko" dan stiff Na'ima tayi tukun dan bata kawo arai sai ta fadawa Ahmad fitan nata bama, ganin haka sai Mamin ta sake cewa "toh kirashi ko ki masa text yanzu banason shiririta Habibti" jiki a sanyaye Na'ima ta ciro wayanta ta shiga gurin messages ta tura masa

"Good Morning, zanje gurin verification din" 

Message din beyi second goma ba sai ga kiransa ya shigo, sauqinta har sannan wayan na silent shiyasa bata dauka ba har ya katse, sai kuma ga wani message din sa ya shigo

"Wait for me..I'll take you there"

Sai ta sake tura masa

"Tare da Abba zamuje ai"

Sai da message din ya dauki mintuna sannan ya turo

"Okay Wife...Allah ya taimaka, pick my calls please"

Bata tura reply ba ta saka wayan a jakan sai taga Mami na kallonta, cikin sanyin murya tace "Nafada masa" sai Mami tace "Okay..Allah ya kare, sai ku biya gurin meerah" Nafisa tace "Eh can zamu hadu zuwa 11-12 haka" Mami ta gyada kai da haka suka miqe tareda fita daga dakin, atare suka fice daga gidan kowacce cikin motan ta...Ahanya Na'ima na tafiya Bilal ya fado mata arai dalilin tuna incident dinsu the last time da taje bankin, ita kadai ta girgiza kai tana tuqin...Da ta isa yau ma a premises din bankin ta waje ta ajiye motan ta sannan ta nufi ciki tareda nunawa securities din pass dinta, daman Abba ya fada mata gurin Adekunle zataje and hakan tayi, dan batafi 2 hours ba ta bar cikin bank din, sai da tayi waya da Nafisa ko da tana can gurin meerah sannan ta nufi motanta tayi reverse ta bar bank din, zuwa sha daya ta isa boutique din Meerah tayi parking a gefen motan Nafisa..Sai qarfe biyu na rana Meerah ta gama dasu sannan suka wuce gida, tun shigansu Na'ima taga motan Ahmad a fake, agefen motan tasa tayi parking sannan Nafisa ma tayi daga gefe suka fito a atare, Nafisa tace "Ni yasan mun dawo kuwa, naga bakuyi waya ba jiya" ahankali Na'ima tace "Bansani ba Nafee" sai Nafisa tadan tsaya kallonta tace "Meye faru ne sis" Na'ima tace "babu komai fa" sai Nafisa tadan yi murmushi tace "Nasanki fa..kinada gaskiya, gwara ki taka masa burki akan mahaukaciyar can tun yanzu, Laila can be cunning at times" cikin sanyi Na'ima tace "ko text fa baimun ba Nafee, and i've been calling" sai Nafisa tace "Bai kyauta ba duk da Laila qanwarsa ce shima, shiyasa nace ki taka masa burki, duk da ajikina nakeji yanada uzurin rashin call din amma dai karki hakura da wuri kinji, tun ranar da na fada miki tafiyarsa a Kano nagane ranki ya baci ai" Na'ima tace "Shine kika biyoni da waya jiya" Nafisa tayi murmushi tace "Yazanyi to ya nemi sasanci ta gurina" Na'ima bata amsa ba da haka suka nufi cikin gidan, aikuwa suna shiga suka samesa hakimce a falon shida Mami suna magana, duk yanda Na'ima kejin zuciyarta na dan sauqa bata kalli gefensa ba suka qarasa ga sofas din falon, a nutse ya dago kansa daga danna wayarsa da yakeyi ya kalleta, Na'ima da ba kallonsa take ba sai ta juya ga Mami dake tambayanta batun verification din, Nafisa ce ta fara gaishesa bayan ta miqawa Mami ledan saqonta, anutse yace "Lafiya Nafisa" sai tace "Yasu Husna?" yace "Lafiya" Na'ima ce ta juyo batareda ta kalli idonsa ba tace "Ina wuni" yana kallonta ya amsa da "Lafiya" sai tayi shiru bata sake cewa komai ba, beep din wayanta ta Jiyo, bata kula ba again ya sake tura mata wani, sai ta samu kanta da jawo jakanta ta zaro wayan, tun kafin ta bude wayan gaba daya ta hango notification na abunda yace "You went out like this?" sai ta dan bi kayan jikinta da kallo sannan ta dago suka hada ido yana kallonta cikin ido, da sauri ta dauke kanta tareda ajiye wayan har tana dan hade fuska kadan, miqewa yayi ahankali yace "Mami zan wuce" sai tace "toh Ahmad, thank you..I'll call you later then, in muka gama maganan da Amnah" ya amsa da "Okay" sannan ya juya, har ya fice daga falon Na'ima bata dago kai ba dan itama kanta tarasa me yasa ta kasa sauqowa gaba daya akan zuwan sa gurin Laila, itadai Allah yagani duk lokacin da abu yahado Ahmad da Laila aciki tanajin zafi a zuciyarta, toh dama haka ake kishin abunda akeso kodai itace me kishin dayawa, lallai toh bata taba son Bilal ko da na qwayar zarra ba tunda har yake rayuwa da wata macen a gidan aurensu...
Na'ima bata bude wayarta ba har washegari Wednesday, da safe Mami tace su shirya suje salon, Na'ima na dakin Nafisa lokacin da Hajiya ta kirata, bayan sun gaisa tace "Muna tafe muda mutanen Adamawan ranar juma'a saboda sunce nan kano zasu kawo lefen ranan alhamis" cikin sanyin murya Na'ima tace "Allah ya kawoku lafiya" ta amsa da Amin sannan tace "ya aikin naki, amma zasu baki hutu ko" Na'ima tace "Ai ban fara zuwa ba" tace "Okay Ayya, Allah ya bada sa'a Na'ima, in kinada buqatar wani abun kimin magana kinji" Na'ima ta amsa da "Toh Hajiya Nagode" da haka sukayi sallama, Nafisa da ke gefenta tace "Sis ina Bilal ya shiga ne, kinji suma ko kiransu ba ya yi" Na'ima tace "Bansani ba nima Nafee, kuma bansan meyasa ba ko sanin banason yi" Nafisa tace "You're right Bobo, Allah ya kyauta..he better not be scheming something dan this time around, you're married to Yaya Ahmad gaba daya ma" Na'ima tayi murmushin batace komai ba, video call din Lauren ne ya shigo wayan Nafisa ta dauko tareda fadin "Hii Lau" Lauren tace "I'm coming tomorrow Babes" Naima ta sako kanta tana murmushi tace "Hi Lau" Lauren na fara'a tace "Baby the bride's energy is matching ur vibes" duk sukayi dariya sannan suka hau hira, sai da Al'ameen ya leqo ya musu tunin da Mami ta aiko yai musu sannan suka miqe Na'ima ta wuce nata dakin dan shiryawa, saida Nafisa ta kira Husna akan ta samesu acan beauty salon din sannan suka bar gidan cikin motan Nafisa, ranan Na'ima tasha gyara a shagon, dan gyaran gaske akayiwa gashinta sannan aka zana mata jan henna sama sama ba mai hayaniya ba, sai ya fito da kyauwun farin hannun tas, Nafisa da Husna sai santin lallen sukeyi ganin yanda ya fito da kyauwun hannun Na'iman...Ba su suka koma gida ba sai around 4 na yamma, aikuwa suna isa suka tarar da motoci gudu uku agidan wanda su Nafisa sun san su waye hakan, a babban falon gidan suka tararda Anty Amnah, Anty Fatima, Anty Murja, Anty Ummi sannan Salma da Ummi last born din Mamma, su Nafisa ne agaba sannan Na'ima dake bayansu sai kawai su Anty murja da Anty ummi suka taso da fara'a suna fadin "Anty Amaryarmu" Nafisa na kallonsu da mamaki suka qarasa ga Na'iman suka rungumeta, Mami dasu anty Amnah dake zaune suna fara'a Mami tace  "Ga Amarya nan, baku hadu ba ashe" Murja na murmushi tace "Ina kuwa Mami, ai mukace gwara muyi zuwa na musamman kar muji kunya, Mummy ma tace mu baki hakuri bata miki taya murna ba kunya takeji, sai kun hadu gobe zata baki hakuri" Mami tace "Laa ai bakomai, ba naji Laila bace ba lafiya" Anty Ummi tace "Eh..Fever ne but she's Okay now" Anty Amnah na kallonsu tace "toh ku bari Amaryar tamu ta qaraso mana mu gaisa" atare suka sake Na'iman suna dariya, har sannan Nafisa dai na kallonsu itada Husna, Anan falon suka zauna gaba dayansu, Na'ima ta samu gefen Mami nan qasan carpet ta zauna tana sunne kai, Ummi sai kallon Lallen hannunta suke itada Salma, Anty Fatima ce tace "Ma Sha Allah, Anty Na'ima lallen yayi kyau sosai" sannan suka juya suna kallon nasu Nafisa suna yabawa, Nafisa ko jinsu me kyau ma batayi idonta na kan yayun Laila dake zaune falon, nan aka hau gaisawa sannan Husna ta janyo flask din gaban su Anty Fatiman tafara musu serving abincin suma, gefen Na'iman suka matso akan suci abincin tare, kasa cin abincin Na'ima tayi tanata wasa da yatsunta sai Anty Amnah tace "Daughter kici abincin mana" sai tayi murmushi kawai...Hira Familyn suka hau yi anan falon, su Anty murja sai hiransu suke hankali kwance itada Anty ummi, basu suka tashi tafiya ba sai 6 na yamma, da suka tashi shiga mota ma nan duk sukayi hugging Na'iman da ke tsaye gefen Mami itada Nafisa, Anty murja harda fadin "Allah ya baku zaman lafiya Anty Na'ima" itadai idonta a qasa bata amsa ba da haka sukayi sallama da su Anty Anty Amnah da Fatiman tareda Salma, Husna ma binsu tayi suka shiga motan Anty Fatima itada Ummi da Salma dan Anty Amnah gidan ta ta nufa daganan, su Anty murja dama a mota daya suka zo su biyun....
Daren ranan bayan Abba ya dawo daga sallan isha sai su Na'ima suka je gaishesa, Mami da Al'ameen suka samu a falon nasa suna magana, sai da suka gaishesa sannan yace "Na'ima bamuyi maganan aikin nan naki ba ko" ta amsa da "Eh Abba" yace "jiyan uzurirrika na dayawa, ya kukayi dashi Adekunlen" nan Na'ima ta fara masa bayanin a nutse yana sauraronta, sai da ta gama Mamin tace da Abban "ya kamata kuyi maganan hutun nata dasu" Abba yace "We've already settled that, Ahmad has already met with Adekunle ai" Mami ta gyada kai cike da gamsuwa, sunanan zaune Na'ima na kallon news sai ga Abu ya shigo dakin, yana kallonta yace "Na'ima kije Yaya Ahmad na kiranki, yana guestroom" dan stiff Na'ima tayi a lokacin, sai ta kasa juyawa ta kalli su Abba dake zaune yana magana da Mami hankali kwance,  ji tayi kunya ta lullebta, like how can he sends for her agabansu Abba, sai kuma ta maze ta cigaba da kallon news din, can Mami tace "Habibti" ta juyo da sauri tace "Na'am" sai Mami tayi murmushi tace "tashi kije kar ki sashi jira" ahankali ta gyada kai ta miqe cikin sanyin jiki ta fice daga falon Nafisa na kallonta tana danne dariya, anutse ta isa bakin falon sai ta tsaya bata tura ba tanajin wani iri, sai ta kai hannu a hankali ta turo qofan tareda shiga idonta a qasa, Ahmad na tsaye a falon yana kallonta, madadin ta qaraso straight sai ta bi dayan gefen falon ta nufi kujeran dake nesa dashi duk yana kallonta, zama tayi sai shikuma ya taka a nutse ya nufi kofan falon, hannu yakai ya murda key din tareda rufe qofan, da dan sauri Na'ima ta dago kai Jin qarar key sai ta miqe ganin ya juyo yana kallonta, da dan rawan murya tace "Ya ka rufe kofan kuma, please ka bude" sai ya fara takowa gareta ta fara baya tana fadin "Dan Allah ka bari" ganin ya kusa cimmata tace "Ahmad stop please" yana isowa batayi aune ba ya kamota tareda hade bakinsa da nata guri daya, daskarewa Na'ima tayi a wannan lokacin jin wani abu daya tsarga mata a zuciya, ahankali Ahmad ya fara kissing dinta, a deep steamy one wanda ko numfashi ma a rarrabe sukeyi, sake rungumota yayi bai sake bakinta ba, idon Na'ima a rufe har sannan sai ta samu kanta da kai hannu ta riqe gefen rigansa tana sake damqe idonta, sai da Ahmad ya tabbatar da yayi kissing dinta to his content sannan ya barta tareda hade goshinsu guri daya dukansu idanunsu rufe, Na'ima har sannan ji take komai nata yayi sanyi sai taji sa a hankali yace "Don't ever do this to me again please" sai ta samu kanta da gyada masa kai alamun "toh" ya bude idonsa yana kallonta ganin har sannan idonta a rufe sai ya sake rungumota tareda dora kanta a qirjinsa cikin kwantar da murya yace "Don't make me loose my sanity like this again, please wife" Na'ima na kwance a qirjinsa ta sake gyada kai ahankali dan bilhaqqi taji bacin ran da tashigo dashi yana watsewa da daddaya kuma, sai da suka dauki almost 2 minutes ahaka sannan Ahmad ya sake kwantar da murya yace "I'm sorry wife" sai ta dan ja baya ahankali batareda ta kallesa ba ta gyada kai, riqota yayi duk da haka taqi kallonsa dan wani nauyinsa ya saka mata arai kuma, sai yadanyi murmushi yace "Bazaki kalleni ba" kawai sai ta juya masa baya, ahankali ya rungumota daga bayan ya daura kansa a kafadarta, ahankali ya rada mata "kiyi hakuri kinji matata" sai sannan ta danyi murmushi tana kallon wall din falon, cikin sanyin murya tace "Meyasa wayarka yaqi shiga ranan?" anutse yace "Ta fadi a airport ranan, and the reason why i didn't you call is that, the flight was too early, Adam ne ya siya ticket din and it was 7 o'clock, we had to leave home at 6:30, dayan wayana kuma na manta da ita a kano" sai Na'ima ta cewa "How was she?" shiru yayi da farko sai can yace "Tana bacci time da mukaje, and by Allah ban sake haduwa da ita ba har yau...I had to go because she was my sister too Na'eemah, but nothing else after that" sai Na'ima ta gyada kai ahankali tanajin jikinta na yin sanyi kuma....a kunyace ta fara raba jikinta da nashi, sai ya sake riqota ya dawo da ita jikinsa, tana murmushi tace "Kabari please" sai ya kai bakinsa kunnenta ya rada mata "Naqi, i want my wife close to me" bata bar murmushin ba tace "Dan Allah kabari Ahmad" sai ya fara dariya qasa qasa, da haka ta kwace jikinta tace "zan tafi" yana kallonta while hannunsa riqe da nata yace "pick my calls please" sai ta gyada kai batareda ta kalli idonsa ba ta zare hannunta sannan ta nufi kofan fita daga falon Ahmad na bin ta da kallo.....

Bintu Musa ce ✍️ 📚 

Follow my account please and let me know what you think about the chapter at comments section ❤️