AMRAH

AMRAH PART 18

by @hussainyusuf



AMRAH

<<PART 17>>

Amrah tana tsaye tana kallonsa, yana ta faman kyalkyala dariya kamar ba zai daina ba. Sai da ya yi mai isarsa sannan ya murtuke fuska, tamkar ba shi ya gama dariyar ba, ya kalli Amrah. Nan take idanunsa suka yi ja-jur kamar garwashi. Ya tashi sama kamar tsuntsu, amma ba fuka-fuki a jikinsa, kan tsaunin da Amrah take kai ya sauka daf da ita. Nan take Amrah ta gyara tsayuwarta ta fuskance shi.

Cikin wata irin murya mai ban tsoro ya fara yi mata magana, "Amrah, kin makara! Ki sani ƙungiya ta daɗe tana jiranki, ta ɗora duk fatanta da burikanta a kanki, amma yau ke ce ake amfani da ke ana kashe mana manyan 'yan ƙungiya masu ba mu kariya. Kin sani lokacin da kika kashe manyan bokayenmu guda biyu, Boka Rubbas da Boka Durwas, mun rabu da ke ne saboda muna kyautata zaton nan gaba za ki zama mallakin ƙungiya. Amma bayan wata doguwar halwa da shugaba ya shiga, ya tabbatar mana da cewa ba za ki taɓa zama mallakin ƙungiya ba. Saboda haka ya aiko ni na halaka ki, kafin ki halaka mutanen ƙauyen Kiyawa. In dai kika riga ni halaka mutanen ƙauyen Kiyawa, to ban isa na samu nasara a kanki ba. Sunana Boka Himras, ni ne sarkin bokayen aljanu da mutane na duniya, ni ne wanda ya koyawa bokayen da kika kashe ilimin tsafi. Saboda haka yau ƙarshenki ya zo, sai dai wata, amma ke ƙarshenki ya zo..."

Yana faɗin haka ya shammaci Amrah ya watso mata wata wuta mai ɗauke da tartsatsi. Cikin zafin nama Amrah ta sa hannunta guda ɗaya ta tare wutar. Wutar tana dukan hannunta ta juya da gudu zuwa kan Boka Himras, duk yadda ya so tare wutar sai da ta gagare shi. Gaba ɗaya ta zubo masa a jiki ta ƙona shi.

Cikin tsananin fushi ya kalli Amrah ya sake watso mata iskar bakinsa. Nan take wata guguwa mai ƙarfin gaske ta nufo Amrah, duk yadda ta so kaucewa guguwar sai da ta ɗaga ta sama, ta riƙa yawo da ita a cikin iska.

Mutanen ƙauyen Kiyawa suna tsaye suna kallon duk abin da yake faruwa, suna ganin an ɗage Amrah a cikin iska, sai suka hau murna saboda suna ganin yau Amrah ta haɗu da dai-dai ita.

Saboda ƙarfin iskar sai da ta sauko da Amrah daga kan dogon tsaunin nan, sannan ta sake ɗaga ta sama ta maka ta a jikin wata ƙatuwar bishiyar tsamiya. Amrah ta faɗo ƙasa a galabaice, hancinta da bakinta suna fitar da jini. Nan take ta sume.

Boka Himras yana ganin haka sai ya bushe da mahaukaciyar dariya, nan take mutanen ƙauyen Kiyawa suka hau taya shi dariyar. Sautin dariyar tasu ya cika kunnuwan Amrah, sai dai ba ta da ƙarfin da za ta iya buɗe ko idanunta saboda tsananin galabaitar da ta yi.

Bayan Boka Himras ya gama dariyarsa, sai ya haɗe fuska ya dubi mutanen ƙauyen Kiyawa ya ce, "Yanzun nan zan halaka muku wannan hatsabibiyar yarinyar, amma da sharaɗi."

Suka yi tsit suna sauraronsa. Ya ci gaba da cewa, "Sharaɗin shi ne za ku sadaukarwa ƙungiya jarirai sababbin haihuwa guda sittin. Saboda ƙungiya ta samu ƙarfin ba ku kariya daga mutane irin su hatsabibiya Amrah. Idan kun amince, yanzun nan zan halaka Amrah a gabanku, idan kuwa ba ku amince ba, zan tafi na bar ku da ita. Amma fa ku sani, idan har Amrah ta farfaɗo daga suman nan da ta yi, to za ta ƙara ƙarfi fiye da tunaninku, kuma babu wanda za ta bari da rai a cikinku. Hatta dabbobinku ba za ta bari ba, ballantana ƙananan yaranku. Cikin ɗan gajeren lokaci za ta mayar da wannan ƙauyen naku kufai, yadda ko a tarihi ba za a iya tunawa da ku ba. Saboda haka idan kun yarda da sharaɗinmu za ku ba mu jarirai sababbin haihuwa guda sittin, yanzun nan zan halaka muku Amrah."

Ba tare da wani dogon nazari ba, gaba ɗayansu suka amsa sun amince da sharaɗin.

Boka Himras yana jin haka, sai ya bushe da dariyar farin ciki irin tasu ta bokaye, sannan ya fuskanci Amrah ya dunƙule hannayensa ya runtse idanuwansa. Ya fara karanto waɗansu dalasiman tsafi marasa daɗin sauraro. Yana gama karantawa ya buɗe hannayensa ya nuna Amrah da su. Nan take wasu manyan kibiyoyi masu yawa suka fara fitowa daga cikin hannayensa suka nufi inda Amrah take kwance...

Hussain Yusuf✍️