AMRAH PART 21
AMRAH
©Hussain Yusuf✍️
<<PART 21>>
Alhaji Kabiru ya yi shiru, sannan ya dubi Hamrah, ya ce, "Daughter, yanzu ba lokacin wannan maganar ba ne. Ki je ki yi wanka ki huta, kin kwaso gajiya da yawa." Har ta buɗe baki za ta yi magana, sai Alhaji Kabiru ya yi saurin dakatar da ita ta hanyar ɗaga mata hannu. "Please Daughter ki je na ce ko."
Ba yadda Hamrah ta iya, tilas ta tafi. Amma zuciyarta cike take da tarin tambayoyin da suka ƙi barin ranta ya huta.
Hajiya Laila tana tsaye, tana kallon abin da yake faruwa. Bayan Hamrah ta tafi, ta dubi mijinta Alhaji Kabir, ta ce, "Alhaji sai nake ganin ya kamata ka sanar da yarinyar nan abin da yake faruwa. Shin ba ka ganin rashin sanar da ita ɗin zai iya jawo wata gagarumar matsalar?"
Alhaji Kabir ya ce, "Hajiya tun da ba ta san waye shi ba, to ba na so ta san shi. Saboda sanin nasa babu amfanin da zai yi mata, sai dai ma ya ƙara tayar mata da hankali."
Hajiya Laila ta ce, "Rashin sanin nasa ne ma zai fi ɗaga mata hankali."
Alhaji Kabiru ya ce, "Ki bar zancen kawai. In anjima za mu yi magana." Yana faɗin haka, ya fita daga ɗakin da sauri.
Hamrah tana zaune a gefen gado, ta zuba tagumi. Tunanin duniya duk ya ishe ta. Zuciyarta cike take da tambayoyin da take buƙatar amsarsu 'Wanne mutumi ne yake yi wa Daddina barazana a kaina, har yake son cuta da ni? Wanne laifi na yi masa?'
Kiran Jawad da ya shigo wayarta ne ya katse mata tunaninta. Ta ɗauki wayar ta kara a kunnenta. Muryar Jawad ta ji, cikin farin ciki yake yi mata magana, "Baby Hamrah! Albishirinki!"
Cike da zumuɗi, ta ce, "Goro!"
Jawad ya yi shiru, har Hamrah ta yi tunanin ko kiran ne ya katse, kafin ta ji muryarsa, yana cewa, "Zeenatu, matar Kamal, ta haihu lafiya! An samu ƴa mace."
Cikin farin ciki, Hamrah ta ce, "Ma sha Allah! Allah Ya raya ta!" Jawad ya amsa da amin.
Jawad ya ci gaba da cewa, "Yanzu haka ma muna asibitin. In anjima zan zo na kai ki, ki gano Baby ɗin."
Hamrah ta ce, "To, sai ka zo ɗin. Amma sai na sanar da Daddy, saboda ya ce na daina fita yawo anytime."
Cikin sigar kwantar da hankali Jawad ya ce, "Ba komai Baby, ai duk inda za ki shiga ina tare da ke."
Yayin da Amrah ta ɓace daga ƙauyen, ba ta bayyana a ko'ina ba, sai a bakin wani ƙaton kogi, wanda ruwa yake gudana a cikinsa. Kogin can nesa yake da ƙauyensu. Tana zaune a gefen kogin, ta zura ƙafafunta cikin ruwa, tana karkaɗa su. Iska tana kaɗawa a hankali, ta watso dogon gashinta ya zubo har gadon bayanta.
Samanta, tsuntsaye ne kala-kala suke ta shawagi a saman kogin, suna wani kuka mai daɗin sauti, wanda yake saukar mata da nutsuwa, yana rage mata damuwar da take ciki.
Jin zuciyarta take kamar za ta fashe saboda baƙin cikin rashin ɗaukar fansa a kan mutanen ƙauyen Kiyawa. Amma a can wani sashin na zuciyarta kuwa, tunanin baƙon mutumin nan ya hana ta sakat. Ko tuno shi ta yi, sai ta ji gabanta ya faɗi, amma duk da haka, sai ta ji zuciyarta tana mararin sake sanya shi a idanunta.
Kwanciya ta yi a kan ciyayin da suke gefen kogin, ta lumshe manyan idanunta masu matuƙar kwarjini.
Kamar daga sama, ta ji wata sassanyar murya tana yi mata magana.
Da sauri ta buɗe idanuwanta, ta kalli ɓangaren da ta jiyo sautin maganar. Shi ta gani a tsaye bisa kanta! Yana kallonta, fuskarsa ɗauke da ni'imtaccen murmushi mai narkar da zuciya.
Hussain Yusuf✍️