BAKAR RANA

Introduction

by @alhunqawee

BAƘAR RANA

NA

FAISAL HARUNA HUNƘUYI ***

Haƙƙin Mallaka (M)Faisal Haruna Hunkuyi Shekarar bugu; 2025

GODIYA Yabo da godiya sun tabbata ga Allah maɗaukakin Sarki da ya bani iko da damar rubuta wannan labari. Tsira da aminci su ƙara tabbata ga fiyayyen halitta Annabi Muhammad S.A.W da Iyalan gidansa da Sahabbansa.

FAƊAKARWA Wannan littafi ƙirƙirarren labari ne, ba a yi domin cin zarafin wani ko wata ba. Idan yayi daidai da wani ko wata to arashi ne. GARGAƊI Ban yarda a juya min labari ko a karantashi a kafafen sadarwa ba tare da izini ba.

SHIMFIƊA Rayuwa kamar littafi take, kullum tana buɗewa ɗan adam sabon shafi ba tare da jiran shiryawarsa ba. Haka nan babu mahalukin da iya tserensa zai sa ya ɗauki tsere da ƙaddararsa matsayin wasa. Ita ƙaddara an raba an ba kowa ta shi. Tawa ƙaddarar na ke faman kokuwa da kunnuwana domin ƙaryata saƙon da su ke zuƙarsu daga wayar da ke kange a gefensu. Na manta cewa ƙaddara ta rigayi fata. Sannan, motar ƙaddara ba ta jin birki. "Ka cuce ni! Ka ci amanata! Kuma ka sani Allah ba zai barka ba, sai ya bi mini haƙƙina, mayaudari, maha'inci. Na yi nadamar saninka a rayuwata. Na rayu cikin walwala da nishaɗi kafin ka ƙwanƙwasa mini ƙofa a rayuwata, amma tun daga lokacin da na baka damar shigowa rayuwata na fara adabo da walwala, kalmar farinciki ta fara zama baƙuwar kalma a ruhina. Kaico! da tarayya da namiji irinka mai ƙoƙarin tsallake katangar da ba ta zama mallakinsa ba". Kuka ya ci ƙarfinta wanda ya haddasa maƙalewar raguwar maganar a maƙoshinta. Na fara kokuwar tattaro sauran natsuwar da ta yi mini saura da nufin tofa wani abu ko zan samu nasarar rage mata raɗaɗin da zuciyarta ke yi, sannan in fahimtar da ita yadda lamarin ya samo asali. To amma, kafin in gama saita tunanina da tattaro kalaman da zan furta, tuni ta danna madatsin da zai datse ji da saurarona daga kunnuwanta. Ƙwaƙwalwata ta hautsine. Wani azababben ciwon kai ya kawo min ziyara. Amsa kuwwar kalamanta ma su kamanceceniya da ɗiga ruwan dalma a zuciya suka cigaba da zarya a kunnuwana, lokaci guda na tsinci kaina a wani baƙon yanayi. Hajijiya ta fara watangaririya da ni da nufin sada ni da turɓaya, sai dai kafin faruwar hakan, tuni na nemawa kaina mafita ta hanyar jingina a jikin bangon ɗakin da na ke kallo yi wa kallon gara in kasance a gidan yari akan kasancewa a wannan ɗakin a halin da na ke ciki. 'Wace irin rayuwa ce na tsinci kaina a ciki irin haka? Ta ya ya mutane za su fahimceni in har wannan lamarin ya yi tambari? Mace ɗaya tilo da na gama tabbatar da samun yardarta bayan aminaina da suka yanke mini bahagon hukunci, ta hanyar amfani da bahagon lissafi har aka bi Yarima da su domin shan kiɗa. itama tana neman bin sahu'. Saƙar zucin da na ke ta faman yi ke nan. Alamun da kunnuwa suka ji ƙwaƙwalwa na bayar da gudummawa wajen ƙaryatawa, wani sashi na zuciyata na gasgata cewa Zainab ba zata juya min baya ba, balle har ta hukunta ni da laifin da ban aikata ba. Duk da sanin halin Zainab na saurin fushi da mayar da allura takobi, sannan ga mita, babu ruwanta da bincike ballantana uzuri akan duk abin da zai shiga kunnuwanta kuma yayi daidai da ra'ayinta. Amma, ko kaɗan ban kawo cewa akwai ranar da wannan halin nata zai yi tasiri a kaina ba, duba da yadda mu ke matuƙar ƙaunar junanmu. Hannu na kai ina shafa saman ƙirjina ta gefen zuciyata da ke suya tamkar ana zuba min garwashin wuta, cikin azama na ƙara danne wajen a lokaci guda kuma na runtse idanuwana. "Ba wani abu ke damunka ba illa damuwa, a turance ana kiran ciwon da suna DEPRESSION. Da dama akwai ɗimbin ababen da ke haifar da matsalar damuwa ga mutane, shiga damuwa dai matsala ce wacce take takura ɗan adam ta hanyar jefa shi cikin wani yanayi." Maganganun ɗan tsamurmurin likitan su ka fara karakaina da amsa kuwwa a fatun kunnuwana. "Tabbas ciwona a yanzu ya fi ƙarfin na damuwa, domin zuciyata ƙiris ta ke jira ta tashi daga aiki". Duk da maganar a saman laɓɓana ta tsaya, hakan ba zai hana a karanto abin da ke shimfiɗe a fuskana ba. Dogon nazari na tafi ina ƙoƙarin tuno yadda lamarin ya samo asali, wanda cikin abin da bai gaza daƙiƙu sittin ba har na tsinci talatata a laraba.