BAKAR RANA

2

by @alhunqawee

Ina da tarin tambayoyin da nake tsananin kishirwar son jin amsoshinsu sai dai babu wata hanya da zan iya bi wajen kore wannan kishirwar tawa. 'Ka tattara ka bar garin nan kawai kafin wani mummunan al'amari ya faru da kai" Wata zuciya ta raɗa mini. "A'a, hakan fa ba zai zamo mafita ba, tun da mutanen nan suna tare da ni,ba zan iya guje musu ba, guje musu daidai yake da sauyawar ƙaddarata daga mai kyau zuwa mummuna. Da muguwar rawa kuwa gwamma ƙin tashi, sannan, faɗuwar gaba ai asaran namiji ne' Na ƙalubalancin shawarar da zuciyar tawa ta raɗa min. Haka zuciyata ta cigaba da karakaina wajen nemo mafita a wannan al'amarin... Firgigit! Na dawo hayyacina daga duniyar tunanin da na shilla sakamakon taɓani da aka yi ta bayana. "Haba Habib wani irin tunani kake yi haka kamar wanda ya fara soyayya a rashin sa'a?" "Abokina ka basar kawai ka taso mu je ana jiranmu." Kallon da na bi Naz da shi ne ya ba shi damar nemo natsuwa ya yi ma ta masauki a tare da shi, sannan ya zauna ya dafa kafaɗata cikin sigar lallashi kamar ƙaramin yaro. Fuskarsa na ayyana saƙon da yake karantowa a tawa fuskar. Wannan ɗabi'ar ta damuwa da damuwar ɗaya daga cikin abokanmu tuni ta daɗe da bin jijiyoyin jikinmu ta zama mana tamkar al'ada. "Aboki, yawan tunani ba shi daga cikin halayyarka, dole kana da damuwar da ba ka buƙatar sanar da mu, kuma ba shi daga cikin halayyar wani a cikinmu ɓoye damuwa, ko da bamu da maganin damuwarka za mu tayaka addu'a har zuwa lokacin da Allah zai yaye maka. Sai dai zan yi maka uzuri domin ciki ba don tuwo kaɗai aka haliccesa ba." Murmushin yaƙe na yi ƙoƙarin ƙirƙirowa domin bawa damuwar da nake ciki mafaka, sai dai abun ya zamo tamkar shafar mai a jikin danni. Hakan bai hanani tattaro natsuwa tare da ƴan tsirarun kalmomin da ke fatar bakina ba, wajen tabbatar da abin da ba shi ne haƙiƙanin abin da ke zama barazana ga zuciya da ruhi ba. "Naz! Babu abin da ke damuna a zahiri, idan ma akwai shi to tabbas na kasa gano ko mene ne, na san dai cikin kwanakin nan ina cikin wani irin yanayi da nake buƙatar addu'ar ka Naz" Shiru ya biyo baya, jim kaɗan na sauke numfashi mai haɗe da ajiyar zuciya, bayan na ba Naz amsar maganarsa. ***** Karaf! Idanuwanmu suka haɗu da na juna. Wani ƙasaitaccen murmushi ta jefeni da shi, irin murmushin da ke narkar min da zuciya. "Zainab matuƙar za ki dinga ƙawata kyakkyawar fuskarki da irin wannan ƙawataccen murmushin na ki to zahiri kin gama mamaye zuciyar Habib, inda ace kin san yadda ki ke komawa tauraruwa a cikin taurari a duk lokacin da kika ƙawata fuskarki da kalar wannan murmushin to za ki dawwama cikin yinsa, salon murmushinki dabanne da na sauran mata; hakan ya zama linzamin saita duk wani tunanina na damƙa a hannun sarauniyar kyawawa Zainabu." Dariya mai sauti ta yi "Habibina sautin kalamanka kullum su ke amo a zuciyata ba, don komai ba sai don baiwar da Allah ya yi maka na iya sarrafa harshe. In dai murmushina ne a ko da yaushe kaine zaka zama silar dawwamarsa a fuskata...." Sallamar da ta yi da siririyar muryarta da nake tsananin mararin sauraro, ita ta katse zuciyata daga tunanin yadda hirarmu ta kasance a wani yammaci a ƙofar gidansu. Duk yadda na kai da son ɓoye damuwata sai dai idan na mujiyar mu ba su haɗu ba, amma ina da tabbacin matuƙar suka gauraya Zainab zata karanto duk wani sirri da ke cikinsu. "Amaryar Habibi ke nan, watau ba za ki iya jira ba shi ne kika biyo sawun kayanki ko?" "Naz to kaga laifina? Ai kula da kaya yafi ban cigiya". Ta ƙarashe maganar tana kallona irin kallon da a ke yi wa laƙabi da kallon ƙurulla. Kamar yadda zuciyata ta kwana da sani, hakane ko ta faru. Kallon tuhuma Zainab ta bini da shi. "Habib bari in wuce zamu haɗu zuwa anjima sai mu ƙarasa maganar mu. Amarya a tashi lafiya." Naz ya tashi ya bar mu, duk da ina son kasancewa da Zainab a daidai wannan lokacin, amma ina shakkar abin da rashin sanar da ita damuwata zai haifar. Duk wanda ke cikin makarantar nan namu ya kwana da sanin irin tsananin ƙaunar da ke tsakanina da Zainab tun da daɗewa. "Habibi!" Ta kira sunana bayan ta ƙure ni da fararen idanuwanta masu kyalli. "Na'am Zee" Na amsa ina kallonta wanda sai a lokacin na samu damar ƙare mata kallo. Tabarakallah Maa shaa Allah! Watau duk inda ake neman kyakykyawar mace Zainab ta wuce wurin. Wani irin dandatsetsen materiyal ne ta caɓa ado da shi, duk da fuskarta babu wata kwalliya ta a zo a gani, amma tsananin kyawunta ya dusashe komai. Tsayayyen hancinta ya taimaka wajen kara ƙawata fuskarta da ke ɗauke da madaidaicin bakinta da yasha lip gloss. Fararen dara daran idanuwanta sun fi komai ɗaukar hankalina a duk lokacin da na kallesu. Takalmin ƙafarta ya taimaka wajen ƙara mata tsayi duk da tana da matsakaicin tsawo. "Habibi! Kwana biyu na kasa gane kanka, ban san yaushe ka fara ɓoye min damuwarka ba. Bana so zuciyata ta fara yi min saƙa da baƙin zare akan wannan baƙuwar halayyar da ka fara bijiro da ita a ɗan tsakanin nan." Shiru ta yi, sai dai har ta dasa aya bata ɗauke idanuwanta daga kallona ba tamkar mai son karanta wani abu a tare da ni. Murmushin yaƙe na sauke a allon fuskata, duk da yadda zuciyata ke rawa tana faman kai kawo da taraddadin yadda zan fahimtar da Zainab damuwata. 'Kada ka fara ka sanar da ita domin sanar da ita tamkar kururuwa ne ka daɓawa cikinka wuƙa, idan ba ka bi gargaɗin da a ke yi maka ba, to tabbas zaka saka rayuwar Zainab itama a cikin garari tamkar yadda naka ke ciki a halin yanzu. Amma kuma idan na ɓoye mata to waye zan sanarwa da damuwata in samu sauki? Wani irin kallo zata fara yi mini?., Irin waɗannan tunanin su ke faman yi mini karakaina a kokon kaina. Cikin alamun ƙosawa Zainab ta ƙara kiran sunana da wata baƙuwar murya mai cike da rauni tana girgiza. Ban ankara ba sai ganin hawaye na yi na ambaliya a saman fuskarta. Ba ƙaramin ruɗani da gigita na shiga ba da ganin ruwan hawaye na gudana daga ƙorama mafi ƙololuwar daraja daga ƙoramu a wajena, tabbas ina cikin wani bahagon yanayi mai wuyar warwarewa. "Zee, don girman Allah ki yi haƙuri ki share hawayenki, kin fi kowa sanin ba zan iya jurar kallon zubar ruwan hawaye a saman fuskar da tafi kowacce fuska daraja a wajena ba, fuskar da duk wani sirri na annurin zuciyata ke ɗauke a cikinta. In har ba kina son ki ƙara mini damuwa a cikin damuwa bane, Zee ki bar zubar hawayen nan". Cikin ƙarfin hali da ƙoƙarin kawar da damuwata na ke ƙoƙarin ganin dakatar da Zainab daga zubar hawaye. "Ta yaya kake tunanin hawaye za su daina zuba a fuskata alhalin kana a halin damuwa? Damuwar da har ni ɗin ka zaɓi ka ɓoye mini, tabbas na san ba ƙaramar damuwa ba ce wannan. Sai dai ka yi haƙuri ba zan takura zuciyar da na ke ƙauna wajen tursasata aiwatar da abin da bata ra'ayi ba; Yin hakan tamkar cin amanar zuciyata ne, amma dai ka sani, tsokar da ke maƙale a ƙirjina ba zata iya jurar cigaba da kallon damuwa a fuskarka ba." Cikin raunanniyar fuska take furta kalaman da fuskarta ke tabbatar da wanzuwarsu tun daga ƙasar zuciyarta. "Zee, na san kina so na, so kuma irin wanda ba kowanne namiji ke katarin samun irinsa ba. Ina so ki yarda da ni, ki yarda da irin son da na ke miki. Duk abin da zai zama barazana ga kwanciyar hankalinki ina yaƙi da shi. Wannan hawayen da ke zuba a doron fuskarki tamkar kina watsa mini narkakkiyar dalma a ƙahon zuciyata haka na ke jinsa. Ki taimaki zuciyar da ke kwana da begenki kar da ki hukuntata da laifin da gangar jiki da ruhi ba za su iya ɗauka ba." "Idan har kana so hawaye su daina sauka a fuskata to kaima sai ka yaye rigar da ka sanya a jikinka har kake ƙoƙarin ɓoyeta, duk da kasan hakan ba abu ne mai sauƙi ba, wannan rigar kwata-kwata bata da muhalli a tare da kai. Ba zan matsa ko in takura ka faɗa mini damuwarka ba, amma dai ka sani; komai tsanani maganinsa Allah. Kuma barin kashi a ciki baya maganin yunwa, zurfin ciki ba shi daga cikin ɗabi'arka kuma kada ka yi Ƙoƙarin farawa don ba zai yi maka kyau ba." Maganganun Zainab ba ƙaramin tsuma min zuciya suka yi ba, sai dai hakan bai sa na ji zan sanar da ita ainihin abin da ke faruwa don guje mata faɗawa irin halin da nake ciki.