BAKAR RANA

4

by @alhunqawee

"Ɗan saurayi ka yi ganganci shiga gonar da tafi ƙarfin nomawarka, ka yi kuskuren zaɓo ni a matsayin abokiyar faɗarka a cikin ajin nan, don sai na zame maka hadarin gabas a cikin makarantar nan." Wani irin kallon sauna kira mini shashasha na bi ta da shi. "Ke kuma a su wa? Kare da gudun layyah! Ai ni giwa ce na fi ƙarfin sa'insa da kiyashi. Ni dai ina shawartarki da ki yi ƙoƙarin haddace allonki kafin ki nemi ruwan wankesa" Daga haka ban ƙara cewa komai ba na ci gaba da danna wayata dama akan dannawar ta zo ta sameni tare da rakiyar Hadiza wacce na ke tunanin ita kaɗaice ƙawarta a cikin ajinmu domin ko wajen zamansu ma tare su ke. "Watau tun shigowata cikin makarantar nan na lura kanka na fizga, sai dai idan kai wuta ce to ni ruwan kasheka ce, da sannu zaka fahimci Hannatu ba sa'ar yinka ba ce sai dai ina takaicin lokacin da zaka fahimci hakan tuni ka tsinci talatarka a laraba." Zaman gilashin da ke fuskarta ta gyara sannan ta juya da nufin tafiya. Hadiza da ta zame mata tamkar raƙumi da akala ta karaso ta daidai saitin fuskata ta rage murya tamkar Mai shirin isar da gulmar da take jin tsoron a jiyota. "Habib, don Allah ka daina sauraron Hannatu. Yarinyar tana taƙama da kuɗin mijinta, da ƙarfin family ɗinsa. Za ta iya cutar da kai domin mijinta babban mutum ne sosai. Ko da kaga ina bin ta darajar arziƙinta take ci amma ba wai domin ta cancanci a yi ƙawance da ita ba." "Allah ya raba bawa da kwaɗayi irin na ki Hadiza, kin san bata cancanta ba, amma ki ke tare da ita? To ga sako ki bata; Ta tabbatar ta martaba igiyar auren da ke sargafe a wuyanta ta hanyar fita safgar da bata shafeta ba, ko ba komai ita Uwa ce watarana. Ke kuma amfanin da za ki yi mata ki samu lada a duniya sannan ki gyara furarki bai wuce ki nuna mata darajar ɗan'adam ba, sannan ki kora mata da cewa nan jami'a ta shigo kuma jami'ar gwamnati inda kowa ke da 'yancin zuwa ya yi karatu". Daga haka ban ƙara cewa komai ba na tattara takarduna na bar Hadiza tsaye a gurin tana jinjina maganganuna.