BAKAR RANA

7

by @alhunqawee

TSAUTSAYIN TAUNA Kaiwa da komowa na ke ta yi a tsakiyar ɗan tsududun makwancina wanda ba wani tarkace ne ma su yawa a ciki ba idan aka cire katifata da ke shimfiɗe a ƙasa sai teburin karatuna da jakar da na ke adana suturuna. Wayata ta ce ta yi kuwwa. Da hanzari na nufi inda take ajiye bisa teburin karatuna na kai mata agaji. Abdullahi abokin karatuna shi ke sanar da ni cewa ya tura min sunayen mutanen group ɗina na jinga ɗin da Malam Musa ya bayar. Ban yi ƙasa a gwiwa ba wajen kunna data domin in duba jerin mutanen da zan jagoranta a wannan karon. Sai dai kuma list ɗin da ya tura min baya ɗauke da sunaye sai lambar rajista haɗi da lambobin waya. Kai tsaye bangon yamma na kai idanuna domin sanin haƙiƙanin lokaci, ganin yanzu ne ƙarfe takwas da rabi na dare ta yi hakan ya bani ƙarfin gwiwar buɗe sabon zaure a dandalin whatsapp da nufin nan zai zama mana wajen tattauna yadda za mu gudanar da jinga ɗin cikin sauƙi. Bayan na gama saka lambobin a group ɗin ne na lura akwai lamba guda ɗaya wacce ba a yi rajista a manhajar whatsapp da ita ba. Ba tare da fargabar komai ba zuciyata ta bani umarni kuma na bi umarnin cikin gaggawa. Madannin kira na danna sai dai har ta gama kuwwarta ba a samu mai taimakonta wajen dakushe mata murya daga neman agajin da ta ke yi ba, cikin ƙarfin gwiwa na ci gaba da kira har zuwa lokacin da aka yanke mata wahala ta hanyar ɗaukar kiran da aka yi. Ban jira an gama amsa sallamata ba balle in saurari abin da zai biyo baya na isar da saƙon da na ke ɗauke da shi, sai dai sautin amon muryar da kunnena ya ɗauko min ƙiris ya rage ban kifa daga tsayuwar da na ke yi ba. Yawun bakina ya nemi ɗaukewa yayin da kwakwalwata ta tafi hutun wucin gadi. Wannan muryar ba ta zama baƙuwa a kunnena ba, sai dai kuma bana fatan da gaske ni ne na kira mamallakin muryar. Magana ya ci gaba da yi wanda alamu ya nuna tabbas bai fahimci da wane ya ke magana ba, sakamakon layin da na yi kiran da shi bai kasance gama-gari ba. Ban ankara ba har zuwa lokacin da ya kashe wayar, musabbabin da ya saukar min da ciwon kai ke nan a wannan daren. *** "Aliyu, ina buƙatar sanin mai wannan lambar a cikin ajinmu kuma a cikin rukunin (group) ɗin da na ke jagoranta" Aliyu da ya yi wa kansa mazauni a bisa tebur ya diro yana gyara zaman wandonsa. "Habib, watau kaima akwai ka da wauta kamar ɗan fari wani lokacin!" Kallonsa na yi fuskata ɗauke da alamar tambaya da son fashin baƙi a maganarsa. "Ina nufin a matsayinka na wanda ke jagorantar group ɗin ai kai yakamata a samu bayanan duk wanda ke group ɗinka a wajenka. Ka sha kuruminka kana zaune koma wane ne zai zo ya sameka." "Maganarka haka take amma a matsayina na shugaba yana da kyau in yi tuntuɓa ko don duba da rashin lokacin da mu ke fuskanta." "I, maganarka gaskiya ne, sai dai ka kira lambar wayar da ke maƙale a jikin jadawalin sunayen mana." Maganarsa ta yi min famin inda yake yi min ƙaiƙayi sai dai gargaɗin da zuciyata ke yi min ya dakushe manufata ta bayyanawa Aliyu muryar da na ji bayan na kira lambar. Ko da na faɗa masa ma bai zama dole ya fahimci abin da na ke nufi ba. Ɗagowa ta da nufin ba shi amsa ya yi daidai da ƙarasowar Hannatu da ƙawarta wajenmu wanda ba mu lura da zuwansu ba sai da sallamarsu ta ankarar da mu. "Habib!" Yanayin salon da ta bi wajen kiran sunana yasa na bita da kallo kwakwalwata na ƙoƙarin hasko wani abu da na gagara fahimta. "Na samu labarin kaine shugaban group ɗin mu na aikin da Malam Musa ya bayar?" Ta rufe maganarta da sigar tambaya, sai dai ba ta jira na amsa ba ta ci gaba magana. "Ka yi haƙuri fa, ba na cikin ajin lokacin da ya rabamu shi ya sa aka samu kuskure Hadiza ba ta saka lambar whatsapp ɗina a jadawalin da ya fitar ba." Ta yi min susa a inda ya ke yi min ƙaiƙayi hakan ya ba ni damar jifarta da tambayar da na ke matuƙar buƙatar amsarta ko don in rabu da wasi-wasin da zuciyata ke yi min tare da ƙoƙarin saƙa zaren zargin Hannatu da ya fara ƙulluwa yanzu. "Lambar wanene ta saka a matsayin na ki?" "Karka damu da sanin ko lambar wane ne inda zaka maida hankali mu yi abin da ya haɗa mu da hakan zai fi mana." Duk da rashin jin daɗin maganganunta da zuciyata ba ta yi ba sai dai kuma nasan hannunka mai sanda ta ke yi min da sharaɗin da na gindaya mata a wasu sa'o'i da suka shuɗe. "Babu buƙatar sai na samu lambarki tun da kin nemo inda na ke ina ganin kin sauƙaƙa min wajen isar da saƙon da ban san ta yadda zan tura ya riskeki ba. A taƙaice gobe da ƙarfe huɗu na yamma za mu zauna gabaɗayanmu domin tattara yadda za mu ɓullowa aikin." Na gama maganar ne a lokacin da na ke shirin jan ƙafafuwana da ke neman yi min turjiya wajen tafiyar da na ke da niyyar yi. Aliyu kuwa da tun zuwansu wajen ya fara amsa waya ya kashe wayar ya dawo fuskarsa cike da annuri. "Abokina, za mu iya fita daga makarantar nan yanzu ko?" "Ko ba ku shirya fita ba ni na shirya ka nemo Naz ku sameni a shagon Patrick zan karɓi canji." Daga haka ban sake cewa komai ba na raɓa ta gefen da Hannatu ke tsaye na wuce zuciya cike da zarginta. Mene ne alaƙar Hannatu da wancan mutumin? Wane ne shi ma tukuna? Waɗannan tambayoyi ne da na ke jifan kaina da shi waɗanda kuma nasan ba zan samu amsarsu ba har sai idan Hannatu ta bani haɗin kai. Kamar wanda kwai ya fashewa a ciki haka na shiga cikin gida ina jan gajiyayyun ƙafafuwana. Maƙale a jikin ƙofar ɗakina ƙaramar takarda ce, cikin gaggawa hannuna ya sauka a kanta. 'Da sannu aikinka zai cika mizanin da mu ke buƙata. Nuna turjiya ko shigo da wani cikin wannan al'amarin daidai ya ke da tsayawar numfashin abin da ka fi ƙauna a garin Bauchi. Kar ka manta mun san wace ce Zainab.' Wani baƙin duhu ne ya kawowa idanuwana mamaya yayin da bakina yayi nauyi, da ƙyar kasalallun ƙafafuwana suka jefa gangar jikina cikin ɗaki. Kwakwalwata ta tsaya cak! Sunan Zainab kawai ke faman yi mini karakaina a ƙoƙon kaina. Ban ankara ba na shafe lokaci mai tsawo ba tare da na iya ɗaga ko da ɗan yatsana ba har zuwa lokacin da Ƙanina ya shigo domin duba dalilin barin ƙofata a buɗe bayan yasan hakan ba ɗabi'a ta bace. Duk yadda ɗan'uwana ya kai da son sanin damuwata abun ya gagara, hakanne yasa ya saci jiki ya je ya zo da Zainab da nufin idan ban faɗa masa damuwata ita zata iya tursasani in faɗa mata. "Habib, a tunanina babu abin da zaka ɓoye min sai ga shi ka ƙaryata zuciyata da yarda da amincinka suka zame ma ta tamkar abinci ga gangar jiki, ka da ka yi ƙoƙarin lulluɓawa kanka rigar zurfin ciki domin ko kaɗan ba zata dace da jikinka." Idanuwanta sun gama cikowa da ruwan hawaye, duk ƙoƙarinta na mayar da su bai hanani ganin saukowarsu zuwa dandamalin fuskarta ba. Tamkar an sokeni da mashi a ƙahon zuciyata haka na ji zafin ɗigar hawayen Zainab. Amma, ban san mene zai biyo baya ba idan na sanar da su cewa ana yi min albishir da mutuwa a rubuce da ma zahiri. Ban san mene zai samu Zainab ba idan har na bayyana mata wannan sirrin. "Zainab...! ungo ki share hawayen fuskarki in dai ba so ki ke ki zama silar da zan rasa wani ɓangare mai muhimmanci a jikina ba." Farin kyalle na ke miƙata mata wanda na ɗauko shi daga saman teburin karatuna. "Habib! Ba ka da sauran abin da zaka faɗa min in saurareka, yau ka tabbatar min da matsayina a wajenka, kuma ginin da zuciyata ke yi ka fara ƙoƙarin rusashi duk da ƙarfin ginin ba irin wanda zai rushe bane. Amma, Habib farfajiyar da ka dasa harsashin gininka ya fara zargin ka samu wani filin da ya fi shi ne ka dasa sabon gini shi ya sa ka bijiro da baƙin ɗabi'un da za su jijjige ginin sannan su gurɓata filin............! Dafe kaina na yi wanda da a ce a tsaye na ke babu abin da zai yiwa hajijiya shinge da sadani da ƙasa duba da yadda jikina ke rawa kamar ana kaɗa min gangi. Lura da halin da na shiga ya tilastawa Zainab yin shiru ta nufo inda na ke tana ƙare min kallo. "Habib! Habib!! Da kyar na ɗago rinannun idanuwana da tsananin tashin hankali da rashin natsuwa suka haddasa mu su sauya kala. "Zainab ki je gida kawai! Zan nemeki idan buƙatar hakan ta taso, amma yanzu dai ba zan iya furta komai ba. Kaina na shirin tarwatsewa. Kwakwalwata ba za ta jure waɗannan maganganun na ki ba." "Habib!" "Zainab ki tafi kawai zan nemeki" Na katseta ba tare da sauraron abin da ta ke son furtawa ba, ina nuna ma ta ƙofar fita. Ba ta tsaya musu ba kuwa ta bi hanyar fita daga ɗakin. Usman da ke laɓe yana sauraren duk abin da mu ke tattaunawa ya yi hanzarin shigowa a lokacin da tari ke neman sarƙeni.