BAKAR RANA

9

by @alhunqawee

"Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un......." Da sauri na ɗago kaina domin ganin mugun abun da ake yi wa ta'awizi. Sai dai ban ci karo da kowa ba sai wasu samudawan mutane ma su kama da za su ci babu. Suna tsaye ƙiƙam a kaina tamkar an dasasu. Gefen da Hannatu ta ke na kai kallona inda na ganta durƙushe gaban wani farin mutum da ya sha ado da babbar riga kansa sakaye da hula saƙin yarabawa. Maganganun da yake furtawa Hannatu su suka yi wa kwakwalwata jagora wajen sanin ko wane ne. "Hannah, kin bani kunya kuma na yi tir da Allah wadai da wannan halin na ki. Abin da aka daɗe ana faɗa min ina ƙaryatawa ashe gaskiya ne. Hannah cin amanar aure...? Me ya sa Hannah? Me na rasa wanda wannan ƙazamin ya ke da shi?" Cikin hanzari na kai dubana gareshi ina ƙoƙarin miƙewa don na gama fahimtar inda zantukansa su ka nufa. "Yallaɓai idan kana da matsala da matarka bai kamata ka titsiyeta a cikin mutane irin haka ba, idan ka duba cikin makaranta mu ke yanzu idanu za su iya dawowa kanku." "Kai, kuna ji na da wanann mara kunyar yaron? Bayan nemar min mata da ya ke yi sannan kuma ya tsaya a gabana yana fasalta min abin da ya dace." Cikin ƙaraji da kaiwa ƙololuwa a fagen zuciya na ɗaga hannu da nufin yarfesa da kyakykyawan mari ko don ya farka daga mugun baccin da ya ɗaukesa har ya fara wannan mummunar mafarkin. Caraf! aka yi wa hannuna linzami daga sauka a lallausar fuskarsa. Ban ankara ba na ji an fara duka na ta ko ina. Tsawa ɗaya ya yi musu suka dakata daga jibgata da su ke yi. Abin da idanuwana suka zuƙo min yasa na gwammaci su ci gaba da dukana wataƙila zan iya farkawa daga mugun baccin da ya haddasa min mummunar mafarki. Hoton farko na bi da kallo, tabbas ni ne tare da Hannatu a ranar farko da na fara yi mata magana bayan ta kusa bugemu da mota. Sai dai a fasalin yadda aka ɗauki hoton babi wanda ya isa ya ƙaryata cewa babu wata alaƙa a tsakanin taswira biyu da ke zane a saman takardar. A hankali na kao duba zuwa ga hoto na biyu, idan ban manta a ranar da ta fara neman sulhu da ni a ka ɗauki hoton. Hoto na uku kuwa a bayan gidanmu aka ɗauke shi, ina tsaye a jikin motarta. Wani irin tsoro da razana suka yi min ƙawanya, na gagara motsa ko da ƙaramin yatsana har zuwa lokacin da hargagin mijin Hannatu ya ci gaba da amsa kuwwa a kunnuwana. "Ku rabu da shi, na bar shi da halinsa, ke kuma..." Ya juya ɓangaren Hannatu da ke zube a gabansa tana kuka tare da ƙoƙarin kare kanta sai dai ya hanata damar da za ta fanshi kanta. "Darajar ƴaƴanmu ba zan sa a kama ki ba, amma zan bar ki da hudowar rana da kuma faɗuwarta tare da sa almakashi in datse dukkan igiyoyin aurena da ke wuyanki, kar in ga waɗannan shanyayyun ƙafafuwan na ki a hanyar gidana balle idanuwana su yi tozali da wannan baƙar fuskar ta ki." Da hanzari na miƙe domin in wanke kaina sannan in ceci wannan baiwar Allah da ga halin da za ta tsinci kanta a ciki. Sai dai kafin in furta kalma guda tuni ya ja zugarsa sun bar wurin sai tarin ɗaliban jami'a da su ka taru domin kashe kwarkwatar idanunsu. Na hango irin kallon tuhumar da su ke jifana da shi a saman fuskokinsu, hakan kuwa ba ƙaramin ɗaga min hankali yayi ba. Cikin ɗaga murya na fara rero waƙen wanke kaina sai dai na makara domin tuni kunnuwana sun fara ɗauko min sautin zantukan da ɗaliban ke yi cikin hayaniya. "Da ganin kura ai an san za ta ci nama! Sai ƙaryar ustazanci ashe matar aure ya ke bi." "Dubi idanunshi kamar wani mai gaskiya dama Hausawa sunce 'Rana dubu ta ɓarawo, rana ɗaya jal ta mai kaya' "Yau dai dubu ta cika babu sauran cece kuce, dama ai mun faɗi aka ƙaryatamu" "Hasbunallahu wani'imal wakil!!! Wannan wace irin BAƘAR RANA CE?" Na furta hakan ina ƙara dafe kaina da hannuwa biyu, idanuwana sun yi min wani irin nauyi, ɗanɗanon saman harshena kuwa tuni ya kama gabanshi. Hasbunallahu na cigaba da maimaitawa biyo bayan maganganun da kunnuwana ke jiyo min daga bakin abokan karatuna har ma da waɗanda ba zan iya tantancesu ba. Nazifi na hango yana ƙarasowa, cikin azama na nufi inda yake domin na san a kafaɗarshi ne kawai zan iya kwantawa in yi kuka, sai dai tuni Naz ya ƙaryatani da irin maganganun da ya fara jifana da su ba tare da ya tsaya ya fahimce ni ba. "Habib, duk yadda ka kai da tsanar yarinyar nan ashe ba banza ba... Mu kake rainawa hankali, yanzu wa gari ya waya? Wace riba ka samu a neman matar aure? Ina hankalinka da tsantseninka su ka tafi? Wallahi ka bani kunya Habib." Hawaye ya fare sharewa jikinsa na rawa kamar mazari. A wannan lokacin tuni yawun bakina ya gama daskarewa, gaɓoɓin jikina kuwa sun gama saki, zaren tunanina ya gama tsinkewa ba tare da an yi rabin ƙullin ba. Gajiyayyun idanuwana na ɗago da launinsu tuni ya daɗe da canzawa, dandazon ɗaliban da su ka yi min ƙawanya na kalla ba tare da na ƙara yunƙurin furta komai ba, gangar jikina ta fara kokuwa da ƙafafauwana da ke neman yi mata turjiya wajen ci gaba da dakonta. Tamkar kazar da kwai ya fashewa a ciki ko Ɗan ruwan da ya sha ya yi tatul haka na fara jan ƙafafu ina haɗa hanya ba tare da ankara da mutanen da su ka cika wajen ba balle in ƙara waiwayar Hannatu da ke yashe a sume.