Kuncin zuci
by @bintuuu
Da Na'ima ta koma dakinta sai ta samu kanta da tsayawa gaban madubi tana kallon fuskanta..her lips in particular, wani irin kunya ne ya sake lullubeta sai ta damqe idanunta tana murmushi ita kadai, ji tayi duk jikinta na tashin qamshin Ahmad a lokacin, turarensa ya danne na humran dake fita a jikinta, sai ta samu kanta da jawo gyalenta takai hancinta tana dan murmushi, juyawa tayi ta nufi babban wardrobe dinta dake dakin ta fara rage kayan jikinta, bayan tayo wankan sai ga kiran Ahmad na shigowa kuwa, ji tayi kamar lokacin ne abun ya faru sai ta zauna abakin gadon tana kallon sunansa dake rubuce akan screen din wayan ringing din na tafiya daidai da zuciyarta, haka ya katse batare da ta dauki kiran ba, aikuwa nan take sai ga message dinsa ya shigo "I'm sorry kinji" murmushi me fadi Na'ima tayi idonta na kan wayan, ta kai hannu da nufin daukan wayan sai kiran Alhaji ya shigo, a ladabce ta gaishesa bayan ta dauka sai ya tambayeta batun aikin nata, nan ta fada masa yanda akayi sai yace mata "in kinada wani abunda kikeso kimin magana fa daughter" Na'ima ta amsa da "toh Abba" sai ya sake cewa "ki turamin account details dinki yanzu" nan ma ta amsa sai ya tambayeta ya iyalan gidan sannan sukayi sallama..da tazo kwanciya Mami ta kirata ta sameta a falonta, Mami na mita ta dauko wani abu a cup ta bata tace kuma ta shanye anan gabanta tunda batajin magana, ita Na'ima shaf ta manta da batun ma, da ta gama kuma nan Mami ta dauko wasu turarurrukan daban daban, ta hado da towel Na'iman ta saka, nan ta fara mulke matasu tun daga kanta tana sata tana gogawa lungu da saqo na jikinta..Na'ima ji tayi har wani sanyin qamshi na tashi daga jikinta bayan sun gama, bayannan Mami ta turarata sannan ta sallameta, da tazo kwanciya wani kiran Ahmad din. ne ya sake shigowa wayanta, dauka tayi a bugu na biyu sai kuma tayi shiru, anutse Ahmad yace "Na'eemah nah" ahankali tace "I'm sorry, something held me up earlier" ya amsa da "it's okay, bakiyi bacci ba" tace "Eh" da haka sukayi shiru, can Ahmad yace "yau kwanan mu hudu wife" sai tayi murmushi tace "Har yanzu kana counting" yana murmushin yace "Ranan saturday zan fara asalin counting din" sai ta rufe fuskanta dalilin tunawa da abun da ya faru tsakaninta su dazu, ahankali Ahmad yace "Your lips still lingers, it makes me want all of you Na'eemah" kasa magana tayi dalilin jin kamar tana narkewa acikin katifan da take kwance, Jin tayi shiru sai ya sake kwantar da murya yace "And i don't mind if i'll succumb to all of you" sai tayi shiru nan ma batace komai ba....sai da suka dauki mintuna babu wanda ya sake cewa qala cikinsu kawai suna sauraron numfashin juna, can Ahmad yace "Get some sleep kinji, I'll call in the morning" ahankali tace "Good night" da haka sukayi sallama ta kashe wayan tareda sake gyara kwanciya tanajin ranta na mata sanyi...
Washegari Thursday tunda sassafe Mami ta fada musu zataje gidan Baba dan ganin lefen Na'iman saboda a ranan za'a kai Kano, tareda Nafisa da Al'ameen suka tafi aka bar Na'ima a gida tana kintsa part din Mami, acike suka samu gidan Baban da 'yan'uwa da abokan arziqi, 'yan'uwan Mamma ma sunanan zaune a falon, akwatuna ne sets har 6 making 36 kenan a tsakar falon da sauran wasu wrapped baskets kowanne cike da kaya, Anty Fatima na tsaye itada Salma suna budewa mutanen falon, Anty Amnah ma sai jeka da dawo suke na hidiman baqin itada su Husna da Ummi da twins yaran Anty, Mami na shiga suka fara mata lale Mummy na fadin "kaga uwar Amarya da kanta" murmushi Mami kawai tayi ta samu guri kusada Mamma ta zauna idonta na kan kayan, saida suka gaisa da jama'an falon sannan ta juya ga Mamma suka gaisa a mutunce, da Mami aka hau duban kayan and Alhamdulillah Anty Amnah tayi qoqari gurin ganin ta siyo duk abunda Mamin ta umarceta din, kaya sunyi kyau har sun gaji dan duk me kallo sai yayi mamakin kudin da aka saka wajen siyansu kamar ba neman kudin ake ba, dadin dadawa kayan ma na wadda ta taba aure, ana zaune kowa na yabawa sai wata daga cikin matan da ta kasance 'yar'uwar Anty tace "Akace fa ta taba aure ko, wannan kaya haka?" Kafin kowa yayi magana Mummy tace "A'a kinji ki da wani zanje, mutum na son matarsa ina zancen bazawara kuma, muyi fatan Allah ya basu zaman lafiya da'alla banda kawo wata magana daban" duk sai aka rinqa kallon Mummyn more especially su Nafisa da da Salma dasuke zaune, sai da Mami suka kai sha biyu agidan sannan suka miqe zasu tafi dan daga nan kuma gidan Ahmad din zasuje gani saboda duba abubuwan da zasu buqaci sakawa a part din Na'iman, gidan Ahmad na wata babbar unguwa dake other side of the city, wani irin area ne that only echo's luxury, ko ina ka juya luxurious Mansions na elites ne a estate din, the richness was different, gidan Ahmad ne na biyu cikin arean, wanda exterior dinsa akayi blending with glasses tun daga sama, kasancewan ya fada wa Mami pin na main door din gidan sai basu sha wahalan budewa ba, direct second floor suka wuce inda babban part din Na'iman yake wanda yake facing na Ahmad din, dan shima ya dawo da komansa part na second floor din gidan nasa daga third floor da yake living a da, Bayan sun gama duba babban falon Na'iman da kuma two bedrooms dake cikin side din nata sai Nafisa da Al'ameen suka fice suna touring gidan suka bar Mami nan dakin tana sake cross-checking saboda basu ga wani abunda za'a qara ba kuma, everything was more than okay, Alhaji yayi qoqarinsa matuqa gurin kayan dakin Na'ima, mutumin yayi exceeding tunaninsu sosai kuma hakan ya musu dadi sosai saboda ko ba komai hakan ya nuna Na'iman na da gatanta itama, saida sukayi sallah sannan suka bar gidan, isarsu gida suka samu har baqi sun fara taruwa agidan, da Nafisa ta gaishesu sai ta nufi dakin Na'iman, a zaune ta sameta tana waya dasu Umma jummai da suke can Kano gidan Alhaji, zama Nafisa tayi a gefenta ta jira Na'iman ta gama wayan sannan tace "Bobo munje munga lefenki da kuma gidanki, so so beautiful, yau zasu kai lefen ashe" murmushi Na'ima tayi kawai tace "Shine baki fadamin yau Lamin zai zo qasar ba" Nafisa tace "I'm sorry ai bamu nutsu bane yau din, sai dare zasu iso shida Lauren, they booked the same flight ashe" Na'ima ta gyada kai tareda kai hannu ta dauko flask din abincin da lantana ta kawo mata nan dakin, zubawa Nafisan tayi ta miqa mata sannan suka kama wata hiran daban kuma...Iyalan wadzani sun kai lefe lafiya kuma sun samu karbuwa ta mutunci gurin su Hajiya da nata jama'an, Larai dai sai Ido itama ba bakin maganan, dan abune wanda babu mai taba kawowa kansa zai kasance da Na'iman, kayane wanda ko auren budurwa za'ayi sai haka, kowa kiran Ma Sha Allah yake a falon, shafa ta cika gaban baqi da kayan ciye ciye, su Umma da matar kawu Nasiru na gefe dan har sannan Anty Amarya bata dawo ba, sun sha mamaki iya mamaki ganin wani gurin kudin da Na'iman zata kuma fadawa...Daren ranan Na'ima na dakin Nafisa tareda Lauren da Husna sannan Meerah data kawo musu kayansu, Nafisa ce ta shigo hannunta riqe da drinks ta ajiye anan kan gadon kusada Meerah dake magana da Na'iman akan event din goben da za'ayi, Nafisa da Husna sun gama magana da events planners da komai da za'a buqata agurin, Nafisa na zama gefensu Husna tace "Nafee kinaga Yaya zai zo ba" Nafisa tayi dariya tace "just watch and see, Yaya zai iya riga amaryan ma zuwa" duk sukayi dariya banda Na'ima data ke murmushi tana girgiza kai, Lauren da bata fahimci me akace ba tayi dariyan itama sannan tace "But what's funny?" nan suka sake kwashewa da wata dariyan ganin yanda Lauren din ke raba ido tana dariya itama, Na'ima ce ta fara mata bayani in English tace "ki rabu dasu Lau, tsokalan Meerah sukeyi".. Sai da suka tashi raka Meerah gurin motarta sannan Nafisa ke fadawa Na'iman cewa Lamin yana hanyan zuwa gidan zasu gaisa, Na'ima takai mata duka a kafada tace "Shine bamuyi preparing komai Nafisa, i thought ba yau zai zo ba fa shiyasa ban sake miki magana ba" Nafee ta gyada kafada tace "Toh yace wai daga goben zai zamo gidan da jama'a, a hotel ya sauka gurinsu su Yaya Ahmad" sai Na'ima tace "Yanzu yana hanya kenan" Nafisa ta gyada kai, Meera dake waya sai lokacin ta gama ta juyo garesu tace "Babes zan wuce sai gobe da safen zanzo" Nafisa tace "please remind sharie about the makeup, dan goben wani hidiman zai iya sawa na manta" Meerah ta amsa da "in sha Allah" sannan ta bude drivers seat na motan ta, har tayi reverse ta bar gidan suna tsaye, sai Na'ima tace "yanzu muje ki shirya Nafee, I'll deal with the refreshments" Nafisa na murmushi tace "Har sai nayi kwalliya ne, I'm just adding kimono on my dress" ta qarasa magana tana kallon knee length dress da jean din dake sanye a jikinta, hararanta Na'iman tayi sai ta kamota tafara janta suka koma cikin gidan, a falon suka tarar da Mami ta dawo gurin baqin nata, cousins dinta guda biyu da kuma kawayenta su biyu suma, kamar dazun da zasu fita haka ma yanzu Na'ima ta sake duqar da kai baqin na kallonsu, cousins din Mamin na tsokalan Nafisan wai itace next Amarya bada jimawa ba, suna murmushi suka hau stairs kowacce na dan dariya, sun samu Lauren har sannan kwance while Husna kuma tana toilet sai Na'ima ta nufi wardrobe din Nafisan ta fara binciko kayan da zata bata ta saka, zama nafisa tayi a bakin gadon tana danna waya sai ta dago tace "Bobo wai ya iso ma" da sauri Na'ima tace "Muje dakina ki yi wankan toh" Nafisa na dariya ta miqe sai Na'ima ta kwashi kayan da ta ciro din ta saka ta a gaba suka fice, anan dakin Na'iman ita Nafisan ta shirya cikin wani tsadadden atamfa da yasha beadworks, sai ta riqo gyalen a hannu suka fito while Na'ima na sanye da babban hijabinta, zuwa sannan Mami na falonta da wasu daga cikin baqin sai su Abu ne suka dawo nan main falon kasancewan Lamin din a side dinsu ya sauqa dan guestroom din akwai yan'uwan Mami aciki, Abu na kallonsu yace "Anty Nafee kinyi kyau" sai Na'ima tayi murmushi tace "Sosai ma" dan dariya Nafisan tayi sai tace da Na'iman "Mami fa, ban fada mata ba kuma gashi tana tare da baqi" Na'ima tace "kina wanka lokacin dinda na fada mata, yanzu kije zan kawo muku ruwan" sai Nafisa ta gyada kai tareda dora gyalen a kafada ta nufi fita daga falon, da haka Na'ima ta nufi kitchen, duk wani snacks da Mami ta sa akayi a gidan sai da ta debo su kala kala a babban plate ta hado da drinks kala kala sannan ta fita waje, motan Ahmad tagani a fake nan cikin parking space din sai tayi tunanin Lamin dinne yazo da ita, wucewa tayi side dinsu Faruk din ta shiga da sallama tana murmushi, Lamin dake zaune a gefen Nafisa ya dago kai yana murmushin shima yace "Amaryarmu" cikin sanyin murya Nafisa tace "Yaya ya hana a kirata da haka fa" sai Na'iman da Lamin sukayi dariya atare, nan kan babban glass table din ta ajiye tray din hannunta sannan ta zauna ta gaishesa, amsawa yayi yana fara'a sannan yace "kinganni sai yau ko" Na'ima tace "Da zamu ci taron ka ai, amma yanzu ka wanke kanka" yana dariya qasa qasa ya kalli Nafisa yace "Shiyasa yau sai na tabbatar ta huce sannan zan tafi" Nafisa ta juya kai tana murmushi batace komai ba, Na'ima sai kallonsu take admiringly dan ba qaramin dacewa sukayi a idonta ba, what a match, sama sama suka taba hira sannan ta miqe tace "toh Yaya sai anjima" sai Lamin yace "kar ki bari yaji Yayan nan abakinki" tana dan dariya ta nufi kofan falon, da haka ta fice compound din zata tafi main building din kawai taji qaran bude cab din mota daga parking space, juyawa tayi sukayi Ido hudu da Ahmad da ya fito yana kallonta, sai ta dan tsaya itama tana kallonsa da dan mamakin dama tare yazo da Lamin din, jingina yayi da motan bai bar kallonta ba yana murmushi ya ware mata hannunsa alamun tazo garesa, dan dariya tayi sai ta maqe kafada tana kallonsa, hannu yakai aljihunsa yaciro wayansa tareda dialing line dinta duk tana kallonsa yakai kunne, sai da ta jira taga ya dago wayan daga kunnensa yana kallo alamun kiran ya shiga sannan ta ware hannunta tana dariya akan yagani bata tareda wayan, maida wayan yayi aljihu sai ya sake miqa mata hannunsa alamun tazo, nan ma ta girgiza kai duk tana tsayen har sannan, dan langabar da kansa yayi yana kallonta sai ta fara takawa a hankali zuwa garesa, tana isa ya kamo hannunta ya jata other side of the car inda babu haske sai ya jinginata da motan ya mata rumfa yana kallonta, dan waige waige tafara ahankali tace "People will see us" anutse yace "Let them see" sai ya kamo waist dinta ahankali yace "shine kika dade a wajensu, magana kike tayi da Lamin din" duqar da kai tayi tace "Gaisawa mukayi fa" sai taji yayi shiru bai sake cewa komai ba, dan dagowa tayi sai taga kallonta yake baya ko kifta ido, ahankali ya matso da fuskansa gareta har tana jiyo numfashinsa sai ta rufe idonta da sauri Jin ya sake hade bakinsu guri daya, Ahankali yake kissing dinta tanajin every movement din yana sending shivers ga duk jikinta, a sannu takai hannu bayansa batareda tasan tayi hakan ba, Ahmad dake riqe da waist dinta har sannan sai ya sake matso da ita zuwa jikinsa while deepening the kiss in a tentative motion, brain din Na'ima ne ya hau banging a wannan lokacin sai ta sake sa da saurinta ta fara kokarin kwacewa tanajin kunyan kanta kuma, murmushi Ahmad yayi yana kallonta bai saketa ba, cikin rada yace "You smell good Baby" sai ta fara matsawa tace "Mami ta sani aiki aciki" yana murmushi yace "Wayo zakimin" ta girgiza kai tana danne dariyan da ya taho mata tace "Uhm Uhm" bai bar murmushin ba ya saketa dan yasan in ya cigaba da riqeta a gurin nan din bai san mezai biyo baya ba, yana saketa kuwa tayi saurin barin gurin ta nufi cikin gidan yana kallonta...