Kuncin zuci
by @bintuuu
Washegari tun da sassafe Na'ima tayi waya dasu Hajiya da suka kamo hanya, Mami da tasan da zuwan nasu nan ta hau shirin tarbansu ita da masu aikinta da ta yo hayansu zasu mata aikin hidiman bikin, Naima ranan tareda Husna ta kwana a dakinta dan Nafisa na tareda Lauren, tun da gari ya waye take jin farin ciki na shiganta na zuwansu umman, abunda tayi ranan sai ya tuna mata da lokacin aurenta da Bilal a shekarun baya, ta yanda take ta leqa compound din akai akai tana jiran isowarsu, a leqawanta na karshe ne Mami ta fito daga kitchen ta ganta sai tayi murmushi tace "Sun kusa isowa Habibti" Na'ima ta sunquyar dakai tana dan dariya, sai Mami tace "maza je ki kintsa tukunna, su Nafisan sun fice ne" tace "Eh sunje kasuwa" da haka ta koma dakinta, zuwa hantsi event planner din tazo da ma'aikatan ta suka hau decorating compound din, while su Na'ima na daki Sharie na mata makeup, sai da suka gama aka shiryata tsaf cikin wani tsadadden lace dan ubansu sannan Al'ameen ya kirata tana dauka yace "Anty sun iso" da saurinta tace da Nafisa "sun iso" sai suka miqe gaba dayansu tareda 'yammatan dakin suka fice, jama'an falon sai fara'a suke suna yabon yanda tayi kyau, Kai a sunkuye ta rinqa gaishe da kowa har suka fice waje, Hajiya ce ta fara takowa gareta tana fadin "ma sha Allah daughter na ta fito a amaryarta" su Mami dake tsaya dasu faruk suna kallonsu while su Abu na taya su ciro tulin kayayyakin da suka taho dashi daga booth, bayan Hajiya ta saketa daga rungumar da ta mata sai ta nufi gurinsu Umma tana murmushi ta fara riqo kowannensu, iyalin kawunan ta ne sukayo mata hudu dantsam, hatta matan maqotan Ayuba sai da sukazo suma, zagayeta sukayi kowa na farin cikin ganinta, Na'ima ta miqa hannu zata karbi yaron Salame sai Umma tace karya bata mata kwalliya, Mami ce ta fara instructing dinsu Abu da sukai musu kayan cikin gidan, dan tun safe tasa aka sake gyara musu guestroom din gidan mai dauke da dakuna biyu acikinsa, nan kuma su Nafisa suka hau gaishesu har Nafisa na karban yaron Salamen da haka suka shiga cikin gidan....Ba'a tashi fara taron ba sai da akayi sallan la'asar, zuwa sannan sharie ta sake kintsa Na'iman dan aikinta ne wannan, fully aka biyata ta kula da kwalliya da kuma shirin Na'iman na wunin ranan, wani irin deco mai ban sha'awa akayi a compound din gidan mai cike da aji da alatu, kowanne table da kayan ciye ciye kala kala akai, iyalan gidan Baba sai la'asar din sukazo dan jama'a ne masu yawa sukazo daga fannin Mamma da Baban, su Mami sunsha laces da gwalagwalai ita dasu Hajiya, su Nafisa ba'a magana dan fitarsu ta musamman sukayi itada nata kawayen cikin fitted gown maroon color, ga make up da suka sha da dauri, sai da aka hallara tsaf a compound din sannan suka fito riqe da Na'ima da kanta ke lullube da veil me shara shara sanye take cikin wata gown da take Jan qasa white color, camera Man na gabansu yana aikinsa while suna tafe da Amaryan, nan guri ya hau guda, yan uwan Mami da na Mamma suka hau zuba guda, Hajiya da su larai ma suka miqe akayi dasu, wohoho jama'a Mc sai zuba kirari take agurin, A sannu aka kai Na'ima gurin zaman ta har sannan kanta a lullube, su Laila ne suka shigo compound din su uku itada Luba da wata qawarsu, dukansu sanye da baqaqen glasses daya kusa cinye rabin fuskansu kowacce na taunan cingam, Nafisa dake gurin Amarya ta duka kusada Husna tace "Meya kawosu kuma" Husna na kallonsu tace "daidai muke da kome sukazo yi ai", Kai a sama su Laila suka zauna a wani table suna kallon gurin da Amaryar take har sannan basu fasa taunan cingam din ba, Mummy daman tana cikin mutanen Mamma su murja kuma sun hade cikin su Fatima dasu Anty Amnah dake ta hidima agurin, nan kuma aka hau kashe hotuna iri iri da qawayen Na'iman, sannan da 'yan'uwa, su Umma dai na high table suna ganin abunda yafi karfin tunaninsu, wai haka kudin yake daman, basu gama shan mamaki ba sukaji ana maganan ango ya iso yin budan kai ga Amaryarsa, Jama'aa, Ahmad na hango bayansu Lamin, Adam, Faruk, Mus'ab da Jason sai wasu suma hausawa guda biyu, a tsakiyan su ya taho su Lamin na gaba, nan taron ya dauki murya kuma kowa na binsu da kallo, ahankali Laila ta cire glass dinta tana kallonsa ganin yanda ya sha fararren kaya sai gyara babbar rigansa yake kansa a qasa, a nutse suka qarasa gaban Amarya sai Anty Amnah ta nuna musu basket din da aka ajiye a wajen, Ahmad na murmushi ya miqa hannu gurin Faruk, sai ya miqo masa wata hadaddiyar jaka, nan ya budeta ya fara ciro bunches na kudi yana zubawa a basket, habawaaa sai guri ya sake rikicewa da guda Cameraman na daukan every bit of it, sai da Ahmad ya cika basket dinnan taf da kudi sannan Anty Fatima ta kawo wani basket din nan abokansa suka fara zuba nasu kudin suma, da haka Ahmad ya qarasa gaban Na'ima kowa na kallonsu, anutse yakai hannu ya fara daga veil din nata ahankali yana murmushi, sai da Laila taji numfashinta na rabuwa a lokacin tana ganin su, Na'ima da kanta ke duke tana murmushi har sannan bata dago ba, kama hannunta yayi sai ya miqar da ita ahankali nan ma Lamin ya sake miqo masa bunches din dollars sannan ya hau yi mata kari dasu.. guda, tafi da rawa duk aka hau yi agurin dan babu wanda hakan bai burgesa ba sai su o'o, su Nafisa ma duk da wayoyinsu a suna daukan komai, sai da Ahmad ya gama zuba mata kaf kudaden sannan Abokansa suka fara musu kari ataren, bayannan kuma sai kawayen Amarya da na angon suka jeru duka aka fara musu hotuna da videos, Abu dai yayi kyau san barka dan komai cikin Aji ya tafi, daga karshe kuma Ahmad na zaune a gefenta aka sake ajiye wasu baskets din, nan kuma Mc ta bada dama ga 'yan'uwa suyi nasu karin, Anty Amnah ce ta fara zazzaga nata bunches din daga jakanta sai su Fatima da sauran yan'uwan dake bayanta ajere suka rinqa zuba nasu, kowacce in ta iso sai ta duqa ta ciro daga jaka ta zuba a basket sannan ta bayanta ma tayi hakan, ranan Na'ima taga gata daga kan iyalan wadzani har zuwa nata 'yanuwan, dan har su Umma sai da suka mata kari, Hajiya daman da shirinta tazo ganin ba da qananan mutane suke alaqa ba, kudi ta zuba iya kudi itada kawayenta masu capacity, Abu da Al'ameen kam sai da suka matsar da basket din har gabansu Ahmad dake murmushi yana kallonsu, nan suka rinqa zubawa Abu na dan rawa shida Nafisa, kawayen Amarya nan suka hau rawa suma afilin, Lauren ta dulmiya cikinsu ta saje itama, Abokan Ango na zaune a nasu table din cike da aji wanda kana ganinsu kasan sunsan chanji, Lamin sai hararen Nafee yake ganin tana rawa, ita kuwa tana kallon idonsa tana masa dariya...Ahmad dake zaune gefen Na'ima har sannan kanta a duqe, anutse ya duqa gareta yace "You smell good Baby" sai Na'ima tadan dago tace "kafada jiya fa" sai yayi dariya qasa qasa yace "qamshin yanamin dadi ne wife" sai tayi murmushi ta dan juya kanta dan kamar ba acikin jama'a suke ba haka Ahmad ke maganansa hankali kwance..Laila dake kallonsu sai ta fara miqewa zata bar gurin taron ma gaba daya dasauri Luba ta riqota tace "kawata karki yi haka, dadi zasuji ai, karki badamu dan Allah" sai ta koma ta zauna tace "Luba bazan iya zama ba" Luba tace "Naki lokacin na zuwa kawata, yanda kika kallesu yanzu haka zata zauna ta kalleki a jikinsa" Laila ta sake juyawa gurinsu Ahmad dake magana qasa qasa a Na'iman ita kuma kanta a sunkuye tana murmushi, da sauri ta dauke kanta tana hadiyan wani abu kamar dutse da ya tsaya mata a wuya....Anci ansha sannan anyi rawa daidai misali agurin taron sai da taron yakai kusan maghrib sannan su Ahmad suka tafi shida abokanansa, sai sannan 'yan uwa suka fara sallama da Amarya, Na'iman na tsaye tareda su Nafisa kowa ya tashi tafiya zai iso gareta suyi sallama wasu har rungumota sukeyi kadan, Laila daman tuntuni ta kasa zaman ta tafi itada nata gayyan, wasu qannen Mamma ne suka zo sallama da Na'iman sai dayan da tafi kama da Ahmad ta dan rungumo Na'iman tana fadin "Allahumma Bareek Habibti, Allah ya baku zaman lafiya kinji" Na'ima na murmushi kanta a qasa sannan matar ta sake ta, kan Na'ima a duqe wata mata ta sake rungumota tana murmushi, ji tayi komai nata ya tsaya na wani dan lokaci ayanda matar ta dafo bayanta, sai matar ta cikata ta kuma riqo hannunta tana fadin "Allah ya baku zaman lafiya Amarya" kasa motsin kirki Na'iman tayi tana kallon matar kawai, jikinta ne taji yana wani irin sanyi da haka matar tabi bayan qannen Mamman suka nufi fita daga gidan, Na'ima na nan tsaye su Nafisan suka jata cikin gida, basu wuce ko ina da ita ba sai cikin dakinta, anan bakin gado Nafisa ta zaunar da ita har sannan batace komai tana jin kafanta na yin sanyi, sai Nafisa ta nufi wardrobe tafara nema mata kayan da zata saka mara nauyi haka, wasu cotton din kayan bacci riga mai dogon hannu da dogon wando masu bala'in laushi ta ciro ta miqawa Na'iman tace "ki cire kayan kiyi wanka tukunna" ahankali Na'ima ta amsa da "toh" sannan ta fara kiciniyar cire zip din kayanta, da haka Nafisan ta fita daga dakin, Na'ima na zaune tana faman zuge zip din sai taji hannunta ya fara rawa, barin abunda takeyin tayi sai ta dago hannayen nata tana kallon yanda suke karkarwa, can Nafisa ta sake shgowa dakin ganinta zaune har sannan sai tace "baki shiga wankan ba?" cikin rawan murya Na'ima tace "Nafisa kiga hannuna" da sauri Nafee ta qaraso tana kallon hannun nata tace "Meya faru, sanyi kikeji ne" Na'ima ta girgiza kai tace "wata mata ce....wata mata nagani..itace tamin" adan gigice Nafisa tace "ki nutsu Na'ima, wacece? Me ta miki" kawai sai ga hawaye a idonta, cikin sanyin murya tace "sanyi nakeji" da sauri Nafisan ta miqe tafara cire mata kayan jikinta ta dauko towel ta yafa mata sannan ta danna kira a line din Mami dake can falon qasa tareda mutane, tana dauka Nafisa tace "Mami something is wrong with Na'ima" da sauri Mami tace "Kuna dakinta ne?" Tace "Eh" sai Mamin ta kashe wayan, ba'a fi sakanni ba ta shigo dakin tana fadin "Meya faru da ita?" Na'ima dake karkarwa har sannan batace komai ba, sai Nafisa tace "she's shaking, kigani" zama Mamin tayi a gefen Na'iman tareda riqota tace "Habibiti meyake damunki" cikin rawan murya tace "Sanyi nakeji" sai Mami tace "Sannu, kwanta toh bari akira likita ya dubaki kinji" sai Na'ima ta gyada kai ta kwanta Mamin ta miqe tareda lulluba mata duvet, Hajiya ce ta shigo dakin tace "Maman Nafisa inata nemanki ashe kinanan, baqina ne zasu tafi zakuyi sallama" sai Mami tace "toh bari naje, fever ne ya rufe Na'ima yanzu" Hajiya ta isa gurin Na'iman tace "Subahanallahi, sannu Na'ima" sai ta gyada kai kawai tana sake shiga cikin duvet din, ji take zuciyarta na zafi a lokacin, ita kanta batasan me ke damunta ba, da haka suka fice daga dakin suka barta da Nafisa, zama tayi bakin gadon tace "sannu Bobo"...Bayan Isha sai ga Abba ya shigo dakin da doctor tareda su Faruk, zuwa sannan Husna da salame na zaune a dakin suma, Mami da ta biyo bayansu tareda dasu Hajiya da umma duk suka tsaya a tsakar dakin suma, Na'ima na kwance har sannan amma Nafisa ta saka mata kayan bacci da hula, dakyar Na'iman tayi sallolinta sannan ta koma kan gadon, idonta yayi ja gashi har sannan jikinta bai dena mata sanyi ba, doctor na tsaye kanta yace su dan basu guri mutum biyu ma sun isa, sai duk aka fice aka bar Mami da Abba a dakin, nan ya zauna ya fara duban Na'iman yana tambayanta abunda takeji, ahankali tace masa sanyi takeji sai ya gyada kai, sai da ya gama gwaje gwajensa yace dasu Abba stress ne dakuma jininta da ya hau kadan, sannan anxiety yana sa hakan a tarin lokuta, cike da fahimta su Abba suka gyada kai, sai yayi prescribing magungunan da za'a siyo mata, atake Abba ya kira faruk dake wajen dakin ya shigo sannan ya basa takardan...Na'ima na kwance har dare tanajin zuciyarta na azalzalarta duk da Mami ta bata maganin tasha, ranan adakinta Nafisa da Husna suka kwanta zasu kwana da ita, kiran Ahmad ne ya rinqa shigowa wayan Na'iman dake kan bedside drawer, Nafisa takai hannu ta dauka tareda sallama sannan tace "She's not okay ne Yaya" ta bangaren Ahmad dake zaune a falo cikin hotel ya gyara zama yace "Meya sameta" sai Nafisa tace "She's just shaking tun da aka gama taron" da dan sauri yace "Shaking like how? Me ya sameta ne, tell me everything" sai Nafisa tace "the doctor said, it was stress and all" Ahmad yace "Bata wayan" juyawa tayi tana kallon Na'iman dake kwance kamar me bacci sai tace "ta samu bacci ne yanzu" da haka Ahmad yace "Okay..call me when she wakes up" ta amsa da toh sannan sukayi sallama...Qarfe ukun dare Na'ima na bacci Mami ta sake shigowa dakin ta dubata, qarasowa tayi ta sake gyara mata duvet din tana kallonta sannan ta lullube su Nafisan dake gefenta suna bacci suma, da haka ta sake ficewa daga dakin sai Na'ima ta bude idonta ahankali, har sannan ji take kamar ana yanka mata fatarta, wani irin bala'in zafi take jin zuciyarta na mata, ahankali ta miqe zaune kawai ta fara kuka mara sauti, sai kuma ta koma ta kwanta tana cigaba da kukan, haka ta rinqa yinsa har asuba bata daina ba, tanajin anfara kiran sallah kuma nan wani zafin ya qara taso mata, Nafisa ce ta tashi a wannan lokacin ta nufi toilet idonta cike da bacci Na'iman na kallonta, sai da taji karatun liman anan masallacin dake kusa dasu sannan ta miqe a hankali ko hulanta bata dauka ba dake nan kan pillon kawai ta nufi fita daga dakin, tafiya kawai take tana hawaye gashinta ya sauqa bayanta da fuskanta ahaka ta fita compound din gidan ta nufi gate, sai akayi rashin sa'a megadin yabi su Abba masallaci shima, har ta bude ta fice daga ita sai kayan baccin babu wanda ya sani a gidan...