AMRAH PART 24
AMRAH
<<PART 24>>
Sai da Amrah ta shafe sama da awa biyu tana tafiya da ƙafa kafin ta riski bakin babban titi. Lokacin da ta isa, ta gaji liƙis. Zaunawa ta yi a gefen titin, a ƙarƙashin wata bishiya, tana huce gajiyar da ta kwaso.
Rana ta yi ja, wanda hakan yake nuna alamar ta kusa faɗuwa. Duhun magriba ya fara sako kai. Da ƙyar ta yunƙura ta tashi, ta fara tarar mota. Duk da cewa ba ta iya bambance motar haya da motar gida, duk wacce ta zo sai ta ɗaga mata hannu. Amma babu wanda yake tsayawa. Wajen daji ne sosai, babu alamun gari a kusa.
Ita kanta Amrah, idan ka kalle ta, tana iya ba ka tsoro. Ta yi futu-futu, jikinta duk ya yi ƙura kamar mahaukaciya sabuwar kamu. Yanayin sanyi, ya sa fatar jikinta ta bushe kamar ba a taɓa saka mata ruwa ba.
Tun kafin rana ta gama faɗuwa Amrah take tare motoci, amma ba ta samu wacce ta tsaya ba, har duhun magriba ya mamaye ko'ina. Da ta ga haka, sai ta fara tafiya a gefen titin ita kaɗai.
Sai da ta sake shafe minti arba'in tana tafiya, amma ba ta sake ganin wata mota ta zo wucewa ba. Iya gajiya Amrah ta gaji. Ji take jiri yana niyyar kai ta ƙasa. Sake zaunawa ta yi a gefen titin, ta haɗa kai da gwiwa.
Wata sassanyar iska ce take kaɗawa, hakan ya sa ta ji wani irin sanyi yana shiga jikinta ta ko ina, takure jikinta ta yi waje ɗaya bakinta da ƙafafunta suna karkarwar sanyi. Amrah ta fara jin tsoro ya shige ta. Kaɗaicin wajen da tsananin duhun dare, suka fara cika mata zuciya da fargaba. Ta tuna cewa ba ta da ko sisi a jikinta, balle ta biya kuɗin mota idan ma ta samu. Ta fara tunanin kasancewar ta ita kaɗai, kuma ba ta san inda ta nufa ba. Kuka ya subuce mata a hankali, tana tuna yadda Inna ta yi mata wasiyyar cewa ta bar ƙauyen. In da ta san za ta sha wannan baƙar wahalar to babu abin da zai sa ta bar cikian ƙauyen Kiyawa.
Ta sake yunƙurawa ta tashi, ta koma bakin titi. 'Dole in bar wannan daji!' Ta faɗa a cikin ranta. Motoci biyu sun wuce ta da gudu, amma ko kallon inda take ba su yi ba.
Ta tsaya, ta jingina da bishiya, tana jin wata matsananciyar gajiya tana mamaye mata jiki. Sai ta ga wani haske daga can nesa yana matsowa inda take. Addu'a ta hau yi a cikin ranta. 'Ya Allah, ka sa wannan motar ta tsaya!'
Da hasken ya zo kusa da ita. Sai ta ga wata tsohuwar motar ɗaukar kaya ce ƙurƙura wacce ke fitar da hayaki mai yawa.
Motar ta wuce ta da gudu, amma sai ta tsaya a gaba kaɗan. Amrah ta ɗaga kai ta kalle ta da tsoro. Sai ta ga wani dattijo ya fito daga motar, yana sanye da riga da wando masu datti. Ya fara matsowa inda take. Amrah ta shiga cikin tsoro matuƙa, ta ji kamar ta kwasa a guje, amma sai ta dake har ya ƙaraso kusa da ita. Ya haske ta da fitila, sannan ya ce, "Ina ki ka nufa?" Cikin zumuɗi Amrah ta ce, "Birni zan je." Shiru ya ɗan yi na wani lokaci kafin ya ce, "Taho mu tafi ni ma can na nufa."
Duk da tsananin tsoron da Amrah take ji, kasancewar ta gaji liƙis, hakan ya ba ta ƙarfin halin yarda da dattijon. Wannan ita ce dama ta ƙarshe da za ta fita daga wannan daji. Dattijon ya juya da baya, ya nufi motarsa. Amrah ta ɗan dakata na ɗan lokaci, zuciyarta na bugawa da ƙarfi. Ta ga alamun dattijon yana da kirki a fuskarsa.
Ta tattara ragowar ƙarfin halinta, ta bi shi. Motar wata tsohuwar akori-kura ce wacce ta tsufa sosai, duk ta yi tsatsa. Dattijon ya buɗe gefen da fasinja ke zama. Amrah ta hau ciki da sauri. Warin gas da ƙura, ya mamaye cikin motar.
Dattijon ya koma ɓarin direba. Sai da ya yi ƙoƙari sau uku kafin motar ta tashi da wata ƙara mai ƙarfi wacce ta cika dajin, kamar ba za ta tafi ba.
"Sunana Mallam Bala," dattijon ya faɗa yana kallon titi. "Ke fa yaya sunanki?"
"Amrah," ta amsa a hankali, muryarta na rawa. Mallam Bala ya jinjina kai, bai ce komai ba. Ya tura gear da ƙarfi, sai motar ta fara tafiya a hankali. "Birni babban gari ne," Mallam Bala ya ci gaba da magana bayan sun fara tafiya. "Me za ki je yi a can?"
Amrah ta kasa bayyana masa cikakken dalilin tafiyarta. Sai dai ta tuna wasiyyar Inna cewa ta nemi danginta na asali. "Zan je neman wani abu ne," ta faɗa.
Malam Bala bai sake magana ba game da batun. Amma daga yanayin fuskarsa, Amrah ta gane cewa ya fahimci cewa tana guje wa wani abu ne. Ya kunna rediyo, a hankali wata waƙar Hausa mai daɗi ta fara tashi,sai ta rinƙa ragewa Amrah zafin kaɗaici.
Amrah ta jingina da kujerar da take zaune, tana kallon duhu ta taga. Ta ji wani irin sanyi mai daɗi ya fara shiga jikinta, kuma wani babban sanyi ya fara daskarar da zuciyarta. Ta san cewa yanzu babu damar komawa ƙauyensu Kiyawa, kuma Allah ne kaɗai ya san makomarta a birnin idan ta je...
Hussain Yusuf✍️