Gaba kura 3
GABA KURA
AISHA HANWA
PAGE 3
BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM
Sai da ta tada biredin nan sannan ta ji hankalinta ya dawo jikinta, da dare aka aiko ta fito cin abinci ta ce "A ce ta koshi" ba suce komai ba. Shagargari aka kuma haka.
Tun daga nan ta fake da ƙin fitowa sai ta aiko da kwano a ɗiban mata ta zuba miya a sama ta ci. Cikin kwana bakwai ta fara dawowa haiyacinta, abun ka da gidan yawa nan da nan gulma ya fara tashi ana ƴan ƙus ƙus ɗin matar Munzali ba ta fitowa cin abinci.
Uwar mijinta da kanta ta binciki Munzali ya tabbatar mata da ko ƙarfanfana ba ya shigowa da shi hana ƙarya dai jiya ya dawo da rogo shima sha'awan shi ya ji ya dawo da shi, amma zai bincika ya ji inda aka haihu a ragaya.
Yana tambayar ta kuwa ta faɗa mishi har tana nuna mishi idan yana da buƙata, nan fa balli ya tashi yana faɗin gidansu sun raina mishi wayo, cikin masifa yake faɗin "Ke nan har kun yi arziƙin da za a aiko miki da abinci daga gida ko?, aikuwa dole ne na yi wa abun tubkar hanci".
Ba ƙaramin tashin hankali Mama ta shiga ba a dalilin wannan miya. Tun daga lokacin ba ta ƙara aika mata da komai ba sai dai idan ta zo taci.
Ana haka sai ga ciki me ɗan banzan laulayi da tsirfa kala kala. Nan ma suka sako ta a gaba babu damar ta ce ba ta son wani abun ace iya shege ne, duk ta bi ta lalace a haka cikin ya fara fitowa nan ma Mama ta ce ta je asibiti awo, tana faɗa ma Munzali ya daka tsalle ya ce bai san wannan ba, karshe Innarsa ta ji ta buɗe tijarar ana son kawo musu iyayi a cikin gida, cikin tutiya da alfahari take faɗin surukai takwas gare su babu wacce ta taɓa zuwa asibiti siyan ko fanado ballantana awo domin haka ba wacce ta isa da za ta zo jiya ta karya musu doka ta zauna lafiya ba.
Tana ji tana gani ta hakura da maganar asibiti ta kama rainon cikinta cikin azabar laulayi. Ana haka aka zo aka sakar mata girki wai sun gaji haka nan ta fito a dinga yi da ita; fad'ar wahalar da ta yi ma b'ata lokaci ne, ga wani ruwa da yake zuba mata kwana da kwanaki kad'an-kad'an ta ja bakinta ta rufe ba tare da ta fad'awa kowa ba.
Cikin daren da ta yi girki jiki yak'i dad'i tun tana yi ita kad'ai har Munzali ya dawo ya sameta a haka, da har ya fara sababin ba taso ya tab'ata ne shiyasa take langab'ewa sai da yaga da gaske ne sannan ya kirawo Mamansu. Da shigowarta tace "Yo Kai Munzali wannan ai haihuwa ce baka ji karnin ta ba?, Ya ce to "Wannan ai sai ku da kuka santa, amma ni tambaya ta shine dama ana haihuwa a wata bakwaini ne?, Cikin nan ko gama cika bakwai din da bai yi ba". "Ana yi mana amma ba sosai ba bari dai na jik'a mata hannu mu gani". Haka matan gidan suka taru a kanta wannan tace a bata wannan jik'o waccan ta ce abata kaza, wuni guda ana fama duk ta galaibata izuwa lokacin har an kira anguwar zoma ta zo amma duk da haka ba haihuwa ba labarinta. A takaice sai da ta kwana da wuni sannan ta haifi 'ya mace ba rai.
Zuwa almuru biki ya fara tashi abokan arziƙi duk an watse sai yan uwa na kusa kusa bayan an gama biko aka tattaramu zuwa ɗakin Baba dan mana nasiha, bai wani tsaya doguwar magana ba sai ma cewa da ya yi "Shi ba faɗan da zai mana sai gargaɗi duk yarinyar da ta sake ta zo mishi gida da sunan yaji sai ya ƙarya ƙafanta ya riga ya sallame su zai ji da ƙannen su.
Haka aka ja su aka miƙa kowa gidan mijinta, al'adar ɗan adam ne bin abu mai maiƙo wannan karan ma hakan ce ta kasance tsakanin su domin rabi da kwatan mutane gidan Jamila suka nufa aka bar wanda ya zama musu dole bin ayarin Munari.
Babban gida ne ko in kira shi gidan gandu sasan su Munari mata takwas ne kuma dukansu surukai ne idan aka cire uwar mijinsu yara ne ratata a gidan, babu laifi Munzali ya gyara ɗakin ya sha fentin farar kasa sai ƙamshi ɗakin ya ke yi.
Bayan kammala duk wani al'adar suka tattara aka watse, ita kaɗai tsuru a ɗaki a haka abokan ango suka rako shi bayan zantukan su cikin nishaɗi da annashuwa suka tafi suka bar su, ba tare da ɓata lokaci ba Munzali da duk ya ƙosa ya tafi garin maji daɗi ya isheta da tayin naman da suka shigo da shi ganin ta ƙi kula shi ya tasa abun shi ya lamushe ya bar ƴan kasusuwa da fiffike, ko sallah da ake yi na neman albarka bai samu damar yi ba ya bi takan ƴar mutane ba tausayi babu tausasawa, da taimakon Ladiyo matar wan shi da ya kirawo ta taimake shi ganin aika aika da ya yi, da ƴan dabarun su na karkara ta samu jikinta ya dawo daidai tun daga nan ya samu abin yi babu dare ba rana ita dai idan za'a sa mata wuƙa a wuya ba ta san mene ne daɗin abun ba amma hakanan take miƙa wuya domin bata da yadda za ta yi.
Tafiya ta fara miƙawa komawa na ta sauyawa amma banda ta wurin Munari ita ta na nan jiya iya ga wani baƙi da ta yi
Matsalar da ta fara cin karo da shi shine cin abincin haɗaka haka ma girki duk a tukunya ɗaya ake yi sai dai duk rana mutum biyu za su haɗu su yi tare, miyar nan haka za ki ji ta kamar an wanke kan Mahaukaciya ba ki isa azo kiranki cin abinci ki ce 'Kin ƙoshi ba' to sai a maida babbar magana ana faɗin "Me ki ka ci da zai ƙosar da ke?", Haka nan ta ke fitowa ta yi ta yafita har a ƙare cin abinci kafin kace me ta zauna ta zuge sai tayani muni fal fuska shi kuma gogan nata bai taɓa tambaryarta ko akwai abunda ke damun ta ne
Shi dai idan hakan ba zai kawo mishi cikas ana shi buƙatun ba to Falillahil Hamdu. Ranar da fara zuwa gida ta sha cece kuce a gurin mutanen gidan da masu yi har zuci da masu yi da ba'a. Duk kawaicin Mama sai da ta tambaye ta dalilin uwar ramar da ta yi. Amsar dai ɗaya ce babu komai sai Mama ta yi shiru a ranta ta fara tunanin wataƙila ciki ke gare ta.
Da zata tafi ta tambaye ta ko ta yi mata soyayyiyar miya ne idan tana so? da sauri tace "E" domin har ga Allah tana cutuwa anan ɓangaren. Hakan kuwa aka yi shagargari ta aiko mata da miyar cikin kwanon 26 tace ta riƙa ɗumama shi, har da guzurin katon biredin ta, ta hau biredi da gafza sai da ta yi rabin shi sannan ta haƙura.