KUNCIN ZUCI

Kuncin zuci

by @bintuuu

Bayan Nafisa tayi alwala tafito daga toilet idonta ne yakai gurin kwanciyan Na'ima, ganin bata nan sai ta qarasa gaban gadon ta dauki hulan aranta tana tunanin ko can dakinta Na'iman ta tafi yin  uzurinta a toilet dinta, ajiye hulan tayi ta nufi wardrobe ta dauko babban hijab sannan ta tada Husna dake bacci har sannan, Har sukayi sallahn Na'iman bata dawo ba sai Nafisa ta sake tsammanin ko tana gurin Mami ne dan duk safiya in sukayi sallah sai sun je gurinta a falo, Mamin ce ta shigo dakin sanye da hijab alamun bata dade da yin sallahn ba itama, tana tsaye a dakin ta kalli gadon itama, ganin bataga Na'iman ba ta juya gun Nafisa tace "ta tashi ko, ya jikin nata?" sai Nafisa ta miqe tace "Inaga tana dakina, bari na dubota" da haka ta fita sai Mami tabi bayanta zuwa can din, anan dakin Nafisan ma sukaga Lauren kadai kwance tana bacci sai Nafisa ta nufi kofan toilet ta kwankwasa nan ma shiru, sai Mami ta tura kofan ta shiga nan ma bata ganta sai da fito tace "dubo min guest room ko tana gurin su Hajiyan" sai Nafisa ta gyada kai ta fita, Falon Abba Mamin ta nufa shima dawowarsa kenan daga masjid yana zaune a falon hannunsa da Qur'ani, zama Mamin tayi nan kusa dashi amma kafin ta gaishesa sai ga Nafisa ta shigo falon tace "Mami batacan fa" dasauri Mami tadan miqe tace "Ha'a, maza dubo har part dinsu Faruk, barina duba dakina" Abba da ya tsayar da karatun sai ya rufe Qur'anin ya ajiye a stool gefensa sannan yace "Meya faru?" Mami tace "Na'ima muke nema, bamu ganta ba fa" sai shima ya miqe yace "kun duba ko Ina kuma" sai Mami ta girgiza kai ta nufi fita daga dakin, direct dakinta ta nufa sai ta samu nan ma cousins dinta ne guda biyu da dansu daya jariri suna sallah, fitowa tayi ta sake sauqa falon qasa sai taga Abba dasu faruk tsaye a falon, bata kulasu ba ta nufi kitchen nan ma babu Na'ima, bayan ta fito sai ga Nafisa ma ta shigo bayan ta gama zagaye gidan itama, adan firgice tace "bata nan fa Mami" sai Abba yace "when last kuka ganta" Nafisa tace "Dana tashi yin sallah ma tananan fa, har na shiga toilet tana kwance sai da na fito ne naga batanan sai hulanta kawai" Husna ce ta sauqo ta qaraso ta tsaya itama, sai Abba ya kalli 'yan mazan guda uku yace "Ku bi street yanzun nan ko za'a sameta, something is definitely wrong" Mami ta daga hannu aka tace "innalillahi wa inna ilaihi" sai kuma ta bi bayansu Abba ya riqota yace ta zauna yana zuwa, da haka ya fice shima, zuru sukayi a falon kowa da addu'an da yake fadawo arai, suna nan tsaye har zuwa 6:30 na safe su Abba basu dawo ba, zuwa sannan kowa na gidan ya hallara falo anyi zugum, asannan Mami dasu Nafisan harsu  Umma jummai sun fara kuka kuma, Jin qarar mota yasa Nafisan da Husna tashi da sauri suka fita zuwa compound din amma sai suka ga Baba ne dasu Mamma suka zo bayan kiran da Abba ya musu, a lokacin Abba ya shigo gidan su Faruk na bayansa bayan sun gama yawon bin streets na unguwar basuga ko alamun Na'iman ba, cikin sanyin jiki ya qarasa gurin Baban suna maganan, Nafisa na hawaye ta juya ta tafi dakin Na'iman dan dubo wayanta ko yananan, aikuwa nan ta ganta kan bedside drawer, jikinta har rawa yake gurin dauka ta bude tana ganin miscalls din Ahmad da ya rinqayi tun asuba, da sauri ta bi bayan kiran bugu na farko ya dauka yace "Hello" muryan Nafisa na rawa tace "Yaya she's missing" daga daya bangaren sai Ahmad yayi stiff tukunna, ahankali ya miqe daga gadon da yake kwancen yace "Who?" ta amsa da "Na'ima, she's gone Yaya, bamusan me ya faru ba sai hulanta muka gani agadon" Ahmad ya bude baki zeyi magana sai yaji ya kasa, ya sake bude bakinsa nan ma ya kasa maganan, kawai sai ya kashe wayan ya juya kan gadon ya dauko white t-shirt dinsa ya saka akan dogon wandon dake jikinsa ya fita daga dakin, A falon ya wuce Lamin dake kwance ya nufi kofa, ya bude kenan Adam ya sako kai suka kusa cin karo, sai Adam yayi baya yace "meya faru" Ahmad bai amsa ba ya ratsa ta gefensa ya nufi fita daga corridor'n hotel din, biyo bayansa Adam yayi sai Lamin ma ya fito ya mara musu baya, shidai Ahmad tafiya kawai yake amma baisan Ina yake takawa ba har ya isa motarsa zai shiga, sai Adam yayi saurin riqosa yace "Man what happened?" sai sannan Ahmad yace "Bansani ba, gidan zanje" sai Adam ya shiga driver's seat sannan Ahmad din ya shiga shida Lamin suka bar hotel din, a  Lokacin da suka isa har kofar gidan cike yake da motoci bama cikin gidan ba, zuciyar Ahmad nan ta hau bugu da sauri sauri, shi ya rigasu fita daga motan ya nufi cikin gidan da saurinsa, jama'an da suka zo bikin ne a compound ana jimami while duk family na cikin falon gidan, Ahaka Ahmad ya wucesu ya shige su Adam na bin bayansa, shigansa Falon ya tadda kowa ya hallara wasunsu a tsaye wasu zaune, Mami na kusada Abba tana kuka bilhaqqi itada sauran mutanen falon, fadi take "Ina suka kaimin yarinyata, wallahi wani abu suka mata" Nafisa na ganinsa ta qaraso gurinsa tana kuka take fadin "tace wata mata ce, saida ta fada min jiya, wallahi ta fada Yaya, wata matace tasata rawan jikin" sai Mami tace "tun jiya ta nuna signs din bamu gane ba, innalillahi wa inna ilaihi rajiun" Baba dake waya da commissioner of police sai sannan ya gama ya ajiye wayan sannan yace "in sha Allah za'a ganta, Osagie is coming right now" sai ya juya gurin Ahmad dake tsaye har sannan yace "ka qaraso Ahmad za'a ganta in sha Allah" duqar da kai Ahmad yayi yanajin zuciyarsa na wani irin ciwo sai ya kasa cewa komai, Mamma da kejin kuka na taho mata tace "kanajin fa abunda suka fada, da nufi akayiwa yarinyar nan wani abun" Baba yace "Mu kyautata zato Amina" Mummy dake share hawaye tayi caraf tace "Haka akasan dan musulmi, mu kyautata zato, yarinyar nan ku tuna fa tun farko tasan yanda ake barin gida" sai murja tace "Mamma ance fa guduwa tayi daga gida fa tun farko" Tass akejin falon ya dauki sautin mari, ba wanda yaga zuwan Ahmad sai qaran marin da ya yiwa Murja, Anty Amnah tace "Ka qara mata Ahmaaad, qara mata nace" Murja na kuka dafe da fuska Mummy ta miqe daga zaunen a fusace tace "Wallahi badai a gabana ba Amnah, kaf falon nan babu wanda baida labarin guduwan da yarinyar tayi daga gidan iyayenta" rai a bace Ahmad yace "Mummy ki kama girmanki, she's my Wiife" a tsawace tace "Sai ka mareni nima Ahmad, ka mareni nace" Anty dake zaune sai ta dan tabe baki sai Mamma tace "Uwani koma menenen, wannan ba maganar da zaki fada bace" Mummy tace "Nafada Aisha a kulleni, tunda na tabo wankakke da sabulu, dama nasan inayin magana za'a ga baqina, wasu ma suyi zargina, itafa tsintacciyar mage bata mage" Mami tace "Wallahi Wallahi kinji nayi rantsuwa uwani, idan ki ka sake sunan ki ya fito cikin wa'inda suka salwantar min da 'ya, sai na miki dan banzan duka kafin na kulleku" nan falon ya kaure kuma matan suka hau cacar baki,  Abba yace "meye kukeyi haka ne" Baba sai fadi yake suyi shiru amma kowacce na hargagi, sai da yayi tsawa da qarfi sannan kowacce ta kama bakinta, Hajiya da gayyarta babu bakin magana sai kuka. Rai abace Baba yace "Meye hakan kukeyi kamar wasu qananan yara, mun wayi gari bamuga yarinyar mu ba madadin kuyi addu'a karta fada mugun hannu sai kurinqa abu kaman wasu yara, Haba..da wannan kukeson muji ne" nan Mami ta sake fashewa da wani kukan tana tuno sanda Na'iman take fada musu tana jin sanyi, Nafisa har jijjaga takeyi dan kuka itada Husna da Fatima, Abu da Lamin idonsu yayi ja, Sallama akayi a falon wani Babban mutum ya shigo bayansa da wasu maza uku sanye da suits Abba ya tafi garesu yana miqa wa shugaban hannu sukayi musabaha, Ahmad na ganin mutumin  ya gane Abokin Abbane DSS, kawai sai ya juya zai fita daga falon Mamma tace "Ahmad ina zakaje" kansa agaba ya fice su Baba na kiransa bai tsaya ba sai su Adam suka rufa masa baya, kamar dazun ma haka aka basa hanya ya wuce mutanen na qus qus din ga Angon, da sauri sauri ya qarasa gurin motarsa dake wajen ya shiga, Adam da su Lamin na kwala masa kira ya tada motan ya figeta a guje, shi Ina yake da lokacin amsa tambayoyin masu kaki ne, binciken da yasan sai sun kwana biyu har uku ana faman nemanta, kanshi ne yaji yana sara masa sai kuma sannan ya fara tunanin Ina zaije?, Ina ya nufa?, ta in zai fara nemanta? Ina taje da ta fitan? kawai sai ya faka motan a gefen titi ya dora kansa akan sitiyarin motan yanajin wani irin zafi a zuciyarsa, Adam dake tafe a bayansa ya faka tasa motan shima ya taho gurinsa, nan Adam ya hau kwankwasa glass din motan yana fadin "Open this door Ahmad, karka tada motan nan" ahankali ya dago kai sai Adam yace "Ka budemin, you can't drive like this, zaka kashe kanka" ahankali ya kai hannu ya bude motan sai Adam ya kamosa ya fito dashi yace "Ka nutsu Ahmad, za'a sameta" sai sannan hawaye suka kawo idon Ahmad ahankali yace "taya zan nutsu Adam, matata ce fa, mamata ta bata taya zan nutsu, bansan ina ta shiga ba, bansan ko tana cikin hankalinta ba, bansan me aka mata ba" ya duqar da kai hawayen na fita yace "God.....zuciyata na zafi" Adam ya riqosa yana bubbuga bayansa su Lamin da faruk ma sai lokacin suka qaraso, dasaurinsu sauka fito daga motan suka qaraso gurinsu suna bashi hakuri, sai Ahmad yakai tafin hannunsa fuska yanajin jikinsa na rawa, ahakan Adam ya sashi cikin motan sannan ya shiga....