Chapter 2
FREE PAGE2️⃣
Lokacin Da na fito Maryam na gani na, ta yi saurin rungume Haidar ta shiga masa wasu irin abubuwa waɗanda sam basu da ce ba.
Da sauri na ɗauke kaina ganin yadda suka fara fita hayyacin su, sauran kaɗan ya rabata da kayan jikin ta.
Dan tuni shima ya cire jallabiyar jikin sa daga shi sai ɗan gajeran wandan daya rage a jikin sa.
Ganin yanayin su yasa zuciyata bugawa da sauri-da sauri, addu'o'i kawai nake ja ko gabana ba na gani sosai.
Na ƙarasa inda Na'im ke yashe ya sha kukan shi ya ƙoshi, har muryar shi ta dashe bata fitowa sosai yayi lamo a kwance a ƙasan wajen.
Na ƙarasa na ɗauke shi, ban bari na ƙara kallon sashin da su ke ba, na zagaya ta bayan kujera Ina k'ok'arin fita.
Cikin rashin sa'a muka haɗa ido da
Maryam, ta kashe min ido tare da min gwalo.
Cikin sauri na bar farlon kamar zanci tuntuɓe,
ba na son na ƙara
ganin wani tashin hankalin.
Haidar kam hidimar gaban sa ya ke yama manta da wata halitta a cikin d'akin.
Dan babu wasa dama ya yi kewar abin,
sai kuma gashi ta kawo kan ta ta hanyar jan ra'ayinsa.
Ita kam dama tayi ne dan ta k'untatawa Salmah, kuma kwalliya ta biya kud'in sabulu, dan ta hango yadda wutar kishi ke cin Salmah lokacin da ta gansu.
Wani murmushin gefen baki tayi ganin fitar Salmar a rikice.
Nan ta shiga ƙoƙarin zame jikin ta, dan ita fa ta fara gajiya da wannan shegiyar jarabar ta Haidar, shi yasa yanzu take kulle ɗakin ta ta yi barcin ta ta barshi a farlo, haka zai ta bugawa ta share shi dan ta gaji da jarabàr shi,
tana biye masa ne
dan Nama da ta ke ƙara mata ƙarfin gwiwa,
da kuma tsoron kar yaje ya bi matan banza,
Tunda tasan yanayin
Kayanta,
duk da tasan tayi abin da koda yaje wajen.
Ba zai iya aikata komai ba.
Shigowar ta rayuwar shi bata shigo da wasa ba dan babu macen da za ta ƙara burgeshi, ta riga da ta gama da wannan babin ta masa abinda dole ita kaɗai ce zai yi sha'awa.
Ganin ta ture shi yasa shi kuma yace baisan zancen ba.
Cikin 'bacin ran da take danne wa
a daddafe ta biye mai anan inda suke.
suka yi komai.
Toilet yaso su wuce tare. amma tace
"Ni sai na huta tukun"
kan gadon ta nufa ta kwanta tare da miƙewa
ta shiga danna wayar ta hankali kwance.
Shikam wankan ya shige a gaggauce yana mai duba agogo,
dan yau yana da baƙi da su kai za su zo ƙarfe goma, akwai Meeting na musamman da za su gabatar kuma shi ne sai jagoranci komai,
gashi kuma har goma saura minti biyar.
Tana daga kwancen.
taji wayarta na ringing,
tsaki taja tare da ɗaukar kiran ranta a ɓace ta fara magana
"Haba Mama nace zan kiraki amma sai wani faman kirana kike"
Mama daga can ɓangaren cikin sassauta
Murya tace
"Haba Maryam naga
na jira kine shiru baki
kira ba, Kuma kinsan
ya kamata a kai kuɗin nan ko?"
Tsaki Maryam taja
tare da hararar wayar,
cikin gunguni tace
"Nace miki banda kuɗi
Mama, Ina kuɗin dana turo miki shekaran jiya?"
Daga can ɓangaren, Mama dake ƙara gyara
zaman ta kan yololuwar katifar ta tace
"Eh banda wannan kuɗin ai yace indai wannan aikin kike so kuma kina son ya tafi dai'dai tofa sai kin ƙaro kuɗi, bayan nan akwai buƙatar ki zo da kanki gaskiya"
Sai da taja tsaki tukun tace "Yanzu Mama dole sai nazo kinsan fa ni bason bin wannan hanyar nake ba, kullum mutum yaje a wahale ya ke dawowa"
Jin abinda Maryam ta faɗa tasan dole kuɗin za su fito duk rintsi,
tunda har tana batun ba zata je ba, ta ɗan nisa tace
"Ke dallah rufemin baki biyan buƙatar ai yafi dogon buri, ina ce sanadiyyar bin hanyar
da kike cewa wahalar ce kika kawo wannan matsayin da ki ke kai,
kin dai san Gamji baya magana biyu ki samu lokaci kizo muje kawai"
Jin motsin fitowar Haidar yasa cikin sauri
Maryam ta katse wayar.
Koda ya fito a cikin sauri
ya shiga shiryawa.
Maryam na kallon shi yaje ya buɗe wardrobe da ƙyar ya nemo wata shaddar shi itace dai kusan mai ɗan dama'dama, dan duk kayan nashi a hargitse suke da nata, duk da kuwa in ya gaji da ganinsu haka yakan tsince nasan ya kaiwa Salmah ta wanke ta goge masa ya dawo dasu fess, amma yana jerawa Maryam zata kuma watsa su, dan ita babu ruwanta da gyara kayan shi, kowa da ɓangaren kayan sa amma ta maidasu duk waje ɗaya, pant bra da rigunan barcin ta kwa dan ta saka babu ruwanta in ta cire sai ta danna wardrobe ɗin wankakkun kayan, in har ta zak'ulo su kam sai dai in tarasa na sawa haka kuma ya ke haƙuri,
har takai watarana in zai sa kayan sai dai ya ƙara gogewa da kanshi.
Koda ya ɗaga shaddar zai sa sai da Salma ta faɗo mai a rai,
ya shiga tuna baya.
In da lokacin da suna zaman lafiya ne, Salmah da kanta take zaɓo masa kayan da zai sa, sannan ta zaɓi hular da zata shiga da kayan tukun ta ɗauko mai takalmi hatta da kayan kusan ita ke sa masa.
Hakaɓangaren takalmansa suke a jere a wanke tsaf, da kanta take aika almajirin su ya kaiwa me wankin takalman dake ƙarshen layin a wanko su fess ta jere Masa su bisa tsari.
Tuna hakan da yayi,
yaji wani abu na yawo a zuciyar sa mara daɗi, nan da nan kan shi ya fara sarawa, cikin sauri ya kautar da tunanin.
Ya nufi inda takalman sa suke a yanzu, ganin yadda suke a warwatse yasa yaji wani irin ɓacin rai na taso masa yayi ƙoƙarin wajen dannewa matuƙa.
Da ƙyar ya zak'ulo wani mai dan sauƙi, dan duk sunyi wata uwar ƙura,
ya shiga dashi toilet ya sa tsumma yasa ɗan ruwa ya goge sama sama saboda saurin da yake baya jin zai iya tsayawa ya bawa baiwar tashi ta goge masa.
Tunda ya auri Maryam Salmar ke masa wankin takalma, har abin wankin takalma ta siya da kuɗin ta ta wanke ta goge masa tsaf, ko wankin kayan sa yanzu ya daina kaiwa masu wankau Salmah ya ke ba,
a cewar Maryam kud'in ayi wani abu dasu.
Yana gama shiryawa
ya ƙarasa bakin gadon
yace
"Ni zan tafi"
Tana daga kwancen
da take tana danna waya, ba tare da ta ɗago ba tace
"Ok"
kawai babu a rakiya bare ayi batun addu'a ta maida kanta ta kwantar.
Har ya kusa kaiwa ƙofar fita ya juyo yace
"Kiyi ƙoƙarin ki tashi kiyi wankan" Dan shi mutum ne da baya son zama da najasa a rayuwar shi, haka baya son mutum mai ƙazanta.
Da ƙyar ta gyada kai saboda hankalin ta gaba ɗaya ya tafi ga chat ɗin da take.
Cikin hanzari ya fice yana duba agogon dake ɗaure a hannun sa.
Sai da yaje wajen parking tukun ya tuna motar da zai fita da itama babu wanki.
Cikin ɗan dafe kai yace
"Kash"
Ya juya cikin hanzari dan amsar makullin motar Maryam dan ba zai iya fita da tashi a haka ba.
Yana shiga ya tarda ta yadda ya barta bata tashi ba, ya girgiza kanshi yana takaicin halin ta yace
"Bani makullin motar ki ki amshi wannan, in waccan tazo ki bata ta wanke min kafin na dawo"
Yana maganar yana ƙara duba agogon hannun sa, ganin goma da rabi harda minti 9, gashi sai kiran wayar shi sakataren sa yake akan baƙin sun zo.
Tsaki Maryam taja ta tashi tana yatsine yatsine tace
"Ni kasan bana son fitar min da mota da kake haka kawai kana da taka bazaka hauba sai tawa, gaskiya bazan bayar ba"
Ganin tana neman ɓata masa lokaci yasa ya fara lallashinta, tare da
mata Alk'awarin kyauta mai tsoka idan ya dawo dan yasan abinda zata nema kenan.
Aikuwa sai gata harda dariya tana washe baki
kamar gonar auduga, babu kunya ta ɗaga gefen fillon da take kai ta miƙa masa mukullin.
Haka ya tafi Yana takaicin wannan hali irin na Maryam na shegen son abin duniya.
Babu damar yaƙi bata kuma. sai ta Hana shi ɗin kamar yadda tace,
dan ya fuskance ta sarai harka indai ba kuɗi to yanzu harkar zata watse.
**********
Tunda na koma ɗakina na tarda Salim ya gyara Umar wani daɗi ya ratsani, ganin yadda duk da yana ƙarami yasan ya kula da ƙanin sa, hakan ya tabbatar min koda bana nan zai iya kula da ƙannen sa.
Addu'a na shiga yi musu
akan Allah ya haɗe min kansu, ina mai ƙara tubarwa Allah akan nawa laifin da ya yafemin ya bawa waɗanda nayiwa ikon yafemin,
inda rabon zamu haɗu dasu kuma Allah ya haɗa mu cikin Aminci.
Wasan da Na'im ya ke yana ɓangala dariya shi ya zaftare rabin damuwar dana ke ciki.
Jin ƙarar horn alamar za'a fita da mota, yasa na tashi cikin sauri na ajiye Na'im na fito na nufi get dan bud'ewa.
Salim na biye dani
dan taimaka min,
duk girman get ɗin haka muka tura shi da ƙyar muka buɗe,
nayi zaton ma Maryam ce ganin Motar ta sai da motar tazo daidai in da muke tsaye sai naga Abban Salim ne.
Hakan yasa na ɗan matsa jikin motar
tare da sunkuyar da kaina na gaishe shi.
Bai ko kalle ni ba bare
Nasa ran zai amsa, na riga da na saba da hakan, ba tare da damuwa ba na matsa daga jikin motar ya wuce ni kamar bai ga kowa ba.
Nayi mamakin meya hana Maryam ta fito ta rakashi, dan in zai fita bata bari ya fita shi kaɗai ƙa'idar sai ta rakoshi har bakin get, bayan na buɗe sai ta tare ɓangaren da nake.
Nufinta shine karya ganni har sai ya fita tukun take kaucewa ta wuce ciki tana hararata.
Salim na ganin Abban nasu yana shirin tafiya.
Da sauri yabi motar da gudu dan har ya fara nisa ya shiga ɗaga masa hannu dan tsayar dashi.
Kamar ba zai tsaya ba sai naga ya tsaya,
Salim ya ƙarasa ya dafe gwiwar shi yana sauke numfarfashin gudun da yayi.
"Ya akai?" ya tambayi Salim kamar bai san abinda yaron ya ke wa gudu ba, haka ya ke kullum yasan da kuɗin abincinmu amma sai zai fita kullum ya ke bamu,
ba wai dan babu abincin gidan ba sai dan bamu isa in dafa abinci muci shi ba, kuma wannan tsarin Maryam ne a cewar ta bamu isa muci abinci iri ɗaya ba,
Kuma ita ta yanke nawa za'a na bamu.
Ganin kuɗin da Salim ya miƙo min yasa cikin murna na amsa,
Naga har dubu biyu muka samu yau, nan muka maida get ɗin muka rufe inajin wani farin ciki, yau wajen sati guda kenan yana bamu dubu ɗaya da ƙyar muke manejin ta mu sai dambu ko garin kwaki, yau ma ko abin karyawa bamu da shi guntun garin kwakin jiya da muka ci da dare na jiƙa musu na basu suka sha, haka duk da safiya ce ni sai hak'ura nayi.
Cikin sauri na farawa Salim lissafin abubuwan da zai siyomin, na duba inda nake ajiye gawayi naga inada ɗan saura, zai iya isarmu mu dafa taliya.
Na fito da ɗan murhun gawayin na bakin Ƙofar ɗakin na k'yasta ashana
na koma ɗakina na zauna Ina jiran dawowar Salim.
Umar ne ya farka ya kalle ni yace
" Umma yunwa nake ji"
Shafa kanshi nayi, cikin murmushin ƙarfin hali da son kwantar masa da hankali, na jawo shi jikina Ina shafa kanshi nace "Kayi haƙuri yanzu yaya zai siyo mana taliya mu dafa kaji Umaririna"
Cikin murna ya tashi yana tsallen murnar yana faɗin "Yeh za mu ci taliya yau"
sai kuma ya dakata da tsallen ya karkata kai ya kalleni cike da yarinta ya yace "Ummanmu da miya za ki mana ko da mai da yaji?"
Murmushi na masa nace
"Da mai da yaji zan yi"
Aikuwa ya cigaba da murna dan Umar akwai shi da son abinci da yaji, wajen shi na fara ganin yaro ƙarami mai son cin yaji, ina kallon shi Ina jin wani farin ciki ganin yadda ya ke walwala akan zamuci taliya kawai.
Sai naji wata ƙwallah ta cikomin idanuna,
Allah sarki rayuwa, wai akan taliya yarona ke murna kamar wanda yaji za'a dafa naman d'awisu.
"Astagfurullah Allah na tuba Allah ka yafemin kurakuraina"
Na furta hakan tare da
d'auke k'wallar data zubomin.
Ba'a jima ba sai ga Salim ya dawo ya siyomin
duk abubuwan da na aike shi.
Da yake wajen Wata mak'ociyar mu na aike shi siyan barkonon da manja. kuɗin da nace ta cire ta bani bashin wani.
Inna Uwani wata mata ce da ke sai da kayan miya
a bayan layin mu, da can muna mutumci da ita. har yaranta ma shigowa suna tayani aikace aikace, kafin wannan ƙaddarar ta faɗa min
kuma komai nasamu da ya ke abin duniya bai rufemin ido ba ina yawan yi musu kyauta, hakan yasa muke mutumci da ita sosai.
Amma sanadiyyar auren Maryam yasa duk wani wanda nake alaƙa dashi sai da Haidar ya hanashi shigowa gidan,
sai dai su shigo bayan ya fita.
Duk da haka sai da rashin mutumcin da Maryam ke musu yasa dole suka ɗauke min ƙafa, sai dai in aiko su akai kawo min wani abu
kuma hakan bai taɓa mutumcinmu dasu ba.
Dan sun san halin dana ke ciki. sai dai babu mai ƙarfin taimakamin,
Inna Uwani ce ma takan kawo min abinci watarana, kuma takan bani bashin kayan
miya da wainar da take saidawa, kuma duk lokacin dana samu na biya, haka duk ranar da suka yi tuwo ko dambu, takan aiko yarinyar ta a ɓoye ta wajen ƙaramar ƙofa ta kira Salim ya amso mana
*****
Ina cikin kasa mana taliyar da na dafa,
babu tsammani naga Maryam ta faɗo
ɗakin batare da sallama ba, daya ke banwani saki labule ba kasancewar garin akwai hadari ga kuma zafi.
Bin ƙafar ta na shiga
yi da kallo ko takalmi bata cire ba,
sanye ta ke da riga da sket wadanda suka matse ta, fuskarnan tasha kwalliya sai baza ƙamshin ta ke irin mai hawa kai ɗin nan.
Har yau Ina mamakin wanne irin turare Maryam ke amfani da shi, madadin ƙamshi ni ji nake yana min k'auri k'auri.
Jefomin makullin motar da ke hannun ta ta yi a fuska, yayi tsalle ya faɗa flet ɗin taliyar da na zubawa su salim,
ai kuwa abincin ya kife baki ɗaya.
Na ɗago na kalleta
sai faman girgiza ta ke.
Ganin bance komai ba,
yasa ta fara magana cikin isa
"Ki dauki makullinnan
kije ki wanke motar sweet, sauran ki tsaya shirmen banza har ya dawo baki gama ba"
ta karasa faɗar tare da gallamin harara ta fice.
Jin zuciyata nayi ta takure, Allah ya sani na gaji da wannan cin kashin da Maryam ta ke min, sunan kishiya take amsaawa amma juyani ta ke kamar wadda ta haifeni, yi take kamar ma ita ke aurena duk abinda tace nayi ban isa nace a'a ba,
shi kanshi Haidar ɗin jin tsoron ta ya ke bashi da ikon magana.
Ni kam dama ban isa na tanka mata ba, dan ko nayi magana wata wahalar zan faɗawa.
Bayan hakama tana tak'amar ƙarfi abu Kaɗan yanzu sai ta kai min duka, kuma ni ba iya ramawa zan ba dan marya ta fini ƙarfi ta ko'ina, yanayin jikin ma ba ɗaya bane,
tasha yimin duka in abu ya haɗa mu sai kace ƴar ta kuma a gaban Haidar baya cewa komai.
Tuna irin dukan da nake sha da irin wulak'anci Maryam yasa wasu hawaye suka cika idanuna.
Na fara tambayar kaina. yanzu haka zan cigaba da rayuwar nan a haka babu y'ancin kai?
wata zuciyar tace
"Ki gudu kawai"
Tunawa da yarana da nayi ya karyarmin zuciya da gwiwa, in na gudu yanzu ina zanje? wa nasani? ta ina zanfara?me zai sameni?
"Bansani" ba naba kaina amsa a fili
bayan haka ina zanje da yarannan duniyar nan data zama abar tsoron.
Bansan kuka nake ba sai da naji hannu na yawo a fuskata.
Umar ne ke share min hawayen fuskata
cikin muryar yarinta cike da tausayi yace
"Umman mu ki daina kuka inna girma nima na zama babba sai na zane Aunty Maryam tunda tana saki kuka"
Ji nayi tausayin sa ya kamani, ni kaina nasani yarana na tausayina.
Shi yasa bana son nayi kuka a gaban su,
saboda yadda suke shiga damuwa, amma wani abun bani da yadda zan yi bisa dole rauni na ke fitowa fili.
Salim dake zaune gefe ne ya taso ya ƙaraso kusa dani, cikin muryar tausayawa yace
"Umma kawo makullin naje nafara wanke motar sai ki kwanta ki huta"
Girgiza masa kai nayi
nace "Bazaka iya kai kaɗai ba Salim, bari dai
kuci abincin sai
Mu wanke tare"
yaso yayi min gardama, ganin kallon da na masa dole yayi shiru ya zauna kamar yadda na umarce shi, dan na hana su yin musu inhar nayi magana.
Salim Yaro ne mai hankali da tunani,
ga tausayi yana da zuciya mai kyau,
baya son hayaniya ko kaɗan, shiyasa zai yi wuya Maryam ta dake shi ko tasa a dake shi,
baya shiga harkar ta sam ko aiki ne tasa shi duk irin yadda take so ta zalunce shi bata taɓa sa'ar hakan, shiyasa bata cika shiga harkar shi ba.
Umar ne dai da baya ji ga ɓarna shi gaskiya ba'a daɗewa bata narkeshi ba, kuma bani da damar magana yanzu Abban su zai goyi bayan ta, yi ya ke kamar bashi ya haifi yaran ba, kwata kwata baya ɗaukar su a matsayin yaran daya haifa, sam baya nuna ko kaɗan akwai wata alaƙa tsakanin su.
Haka na rarraba muka ci muka ƙoshi, muka wuce dan fara wankin motar.
Har muka gama na dawo ɗaki ban daina tunanin maganar da Salim ya faɗa min ba,
lokacin muna cikin wankin motar ya kalle ni daidai lokacin da ya hango wasu hawaye kwance a idanuna,
Matsowa yayi kusa dani
tare da kama hannaye na cikin tausayawa yace
"Ummanmu ki daina kuka ki ɗauke mu kawai mu gudu wajen Umman ku mana, tunda nan Abba baya son mu kuma baya kulawa damu, kinga su za su kula damu sosai"
Ji nayi jikina yayi wani irin sanyi kamar an watsa min ruwan sanyi.
banyi zaton yaro kamar Salim zai yi tunani
irin wannan ba,
duk da na san watarana dole zasu tambayeni ina dangina, ko ba su ba na san mutanen da suka san halin dana ke ciki
zasu yi tunanin Ina dangina, nake zaune cikin wahala haka,sai dai ba zasu iya tambayata ba.
Ni yanzu jina nake kamar wadda bata da kowa, kamar marainiyar data rasa uwa da uba, duk da suna raye.
Nasan ni na jawa kaina komai, gashi yanzu bansan ina zanga Iyaye na da dangina ba.
Kasa bashi amsa nayi
na ƙwace hannuna kawai, na cigaba da aikin amma wuni nayi tunanin akan maganar da Salim ya min.
************
Haka rayuwar ta cigaba da tafiya yau daɗi gobe akasin sa.
Yau da wankin kayan Maryam da Abban Abban Salim na tashi,
tun da sassafe ina cikin wankin ruwan sama ya sakko, har zan ajiye na tafi ɗaki in yaso in ruwan ya ɗauke sai na ƙarasa.
Sai na tuna kayan mu sunyi datti, nan tunani ya fadomin tunda dai ruwa ake gashi Abban Salim naga ko fita bai yi ba, zai yi wuya su fito yanzu dan in akai ruwa wani lokacin baya fita ranar,
ko masallaci naga yanzu ya daina zuwa, sa'banin da da muna zaman lafiya duk ruwan da akai indai har ba irin ruwannan ƙarfi bane babu abinda ke hana shi zuwa masallaci.
Amma yanzu sallar asubar ma wani lokacin sai naje na k'wank'wasa musu ƙofa ya ke yin ta.
Dama nice ke musu shara da wanke wanke da girki, komai dai nice keyi, kuma ko nayi iyakaci na kwashe musu na jere akan dining table amma bani da ikon taɓawa ko naci.
Kuma girkawa ya zama dole, wani lokacin inma naje haka zata taso shi su zauna suyi ta abubuwan da bai kamata ba a gabana, nasan duk dan in gani raina ya ɓaci ta ke yi, bana taɓa nuna hakan ko a fuskata, nakan ɗauke kaina na cigaba da aikina, duk da kuwa ran nawa na sosuwa.
Allah shine shaida son Haidar a cikin jinana yake, na kasa tsanar shi dukwaɗannan abubuwan da suke faruwa, duk da bana ganin nawa son daidai da k'wayar zarra a idon shi amma haka nake dannewa,
Duk ranar da na shiga na tarda basu tashi ba, cikin sauri nakeyin ayyuka na na gama karsu tarda ni, sai daga baya in Haidar ya tafi nake shiga nayi gyaran ɗakunan.
Haka na ɗauko kayan mu na shiga wankin,
duk da kuwa nasan illar da dukan ruwa zai min, dan yanzu zazzaɓi zai kama ni, amma haka nagama su na kai su can ta bayan tankunan ruwa na shanya dan karma Maryam ta gani.
Gwara Koda basu bushe ba, in dare yayi na kai d'aki na baza kafin safe sun bushe.
Dan akwai arzik'in fankar sama a d'akin. sa'banin cikin gidan da duk d'akunan su AC ce.
Ina kammalawa da sauri na shige ɗaki.
Saboda wani sanyi da ya fara ratsani.l,
haƙora na sun fara haɗuwa da juna suna kaf'kaf.
Har na kwanta na lullu'ba da wani tsoho zanin gadona. Na tuna sauran sabulun wankin da na bari a waje,
cikin dauriya na fito na ɗauka gudun kar ruwa ya narkar dashi,
dama in nayi musu wanki ne nake samun saura sabulun,dashi muke wanka babu batun man shafawa dama tuni mun rufe babin shafa shi a rayuwar mu.
Iyakaci muyi wankan dai, kasancewar mu farare dani da yaran duk sai muka dafe, duk da irin farin da nake dashi ada wahalar rayuwa duk ta maidani kamar bama farar ba.
Ina daga kwance jikina na wata iriyar rawa,
ga Na'im da ke min rigima zai ci abinci,
kuma bani da komai da zan bashi dan masu gidan basu ko fito ba tukun bare ya bamu kuɗin abincin.
Kasancewar su Salim sun tafi makarantar Islamiyya da suke zuwa ta nan gaban gidanmu, kullum ba fashi haka suke zuwa, bokon ce dai yanzu dole mun haƙura basa zuwa.
Saboda rashin wanda zai ɗauki nauyin su,
da Salim na zuwa Wata Tsadaddiyar Private school Abbansu na biyan da kanshi, ya sashi ne saboda kullum maganar shi bata wuce yana son yaran shi suyi ilimi mai kyau, dan su amfani Al,umma yadda za mu yi alfahari dasu zuwa gaba.
Ana shirin sa Umar ƙaddara ta kutso rayuwar mu, da farko bayan daina biyan kuɗin makarantar da Haidar yayi, ganin Salim baya zuwa ko'ina ga Umar ya Isa farawa, sai nayi ƙoƙarin sa su ata gwamnati.
Har sun Fara zuwa Maryam ta zuga Haidar, wai zan zubar masa da mutumci in a kaga yaran shi na zuwa makarantar gwamnati.
Haka ina ji ina gani ya hana su zuwa makarantar, ba tare da ya sasu a wata ba,
yanzu ta Islamiyya kaɗai suke zuwa,
Ita ma nina k'uk'uta na sasu, kud'in wata da ake kar'ba nera ɗari ne kawai, kuma kafin watan Ina ƙoƙarin ajiyewa.
Dafani Na'im yayi ya cigaba da jan zanin dana rufa yana kuka,
haka na tashi cikin tausayin yaron
na rungume shi, tare da sa masa nono a baki
duk da nasan ba wani ruwan kirki bane a ciki, Sanadiyyar banci komai ba yau,
Cikin sauri ya fara tsotsa wani zafi da raɗaɗi suka ratsa ni,
Na rintse idanuna Ina Jan numfashi da ƙyar.
Babban tashin hankalina yanzu aikin safen da ke gaba na, dan jikina gaba ɗaya babu kwari
bana jin zan iya ta'buka komai.
Gashi dole sai nayi aikin tukun zamu samu abin da zamu ci,
ga lokacin dawowar yaran ya kusa.
me zan basu nake tunani kawai,
Inhar banyi ba nasan ba zata bari a bamu kuɗin abincin yau ba.
Wasu hawaye zafafan ne naji sun gangaro min,
nasa gefen hannu na tare da share su.
Na tuna rayuwata ta baya ada in Ina zazzaɓi haka Haidar ke rikicewa kamar zai yi kuka,
har sai munje asibitin anmin ƙarin ruwa da allurai banda magunguna da ya ke siyowa, shi dai burin sa na samu lafiya.
Gashi yanzu ko arzik'in paracetamol ban samu. haka nake ciwon har ya ci ya cinye ni ya barni.
Gani nayi gwara na daure naje nayi aikin
kawai gudun yin laifi,
Ajiye Na'im da yayi barci nayi na yunk'ura da niyar tashi, wata hajijiya ta kwasheni sai tsintar kaina nayi a ƙasa,
duk yadda naso na tashi kasawa nayi dole na kwanta nayi lamo akan tabarmar, nasan yau dai sai ta Allah duk tsorona jarabar su da zasu sauke min banda wulak'ancin da zan sha.
Ina kwance na rufe idanuna kamar mai barci naji sallamar su Salim sun dawo,
Ganin halin da nake ciki
Salim ya fahimci babu lafiya,
Ya ƙaraso kaina tare da tsugunnawa ya dafa ni,
Jin jikina da yayi zafi yasa muryar shi na rawa cike da nuna tausayawa yace
"Umman mu zazza'bi kike?"
Ɗan buɗe idanuna nayi da ƙyar na gyad'a masa kai a hankali. ji nake
bazan iya magana ba,
"Ummanmu ki tashi na shimfid'a Miki zani akan tabarmar Kar jikin ki yayi k'aik'ayi."
yace tare da kama hannuna kamar wanda zai iya ɗaga ni.
Duk yadda naso ya barni haka ƙi yayi.
Cikin tausayin na daure na tashi yana riƙe da hannuna dan kar yaga gazawata, ya gyara min tabarma Yace
"Umma ki koma kan tabarma"
Na koma na kwanta ina
kallon shi cikin tausayin sa, da ƙananan shekarun sa yasan ya nuna min kulawa haka,
nan da nan naji zuciyata tamin wani sanyi.
duk da irin ciwon da nake ji.
Ina daga kwance ya shiga tattara ɗakin,
ya hada kayan wanke'wanken mu da basu fi kwanuka Huɗu ba, dama shi ke wankewa dan ni bana samun damar wankewar, kasancewar ina zuwa can aiki har ya gama ina kallon shi Ina jinjina ƙoƙarin yaron.
Daidai lokacin Na'im ya farka da kukan yunwa.
Cikin sauri ya zo ya kama yaron ya kalle ni fuskar shi tayi kalar tausayi, tare da ɗaga rigar Na'im ɗin ya duba cikin sa yace
"Ummanmu yunwa yake ji fa"
Umar dama tunda suka shigo ya koma gefe ya zauna
Ya nutsu, dan ko kusa dani bai zo ba,
Yana Jin abinda Salim yace ya rakwakwkwa'be fuskar shi cikin muryar yarinta Yace
"Ummanmu nima yunwar nake ji"
Cikin tausayi na kalle shi Ina Jin wani irin abu a
zuciyata, nasan Umar bashi da jumurin yunwa ko kaɗan, shi haka ya ke ko Yaya in yaji yunwa yanzu zai rasa walwalar sa ko wasa baya yi,
shi yasa bana yarda na rasa ko garin kwaki ne a d'akin dan ko ba sugar na bashi yana shan abin shi shi dai cikin sa ya cika kawai.
Kallon Salim nayi nace
"Kaje gidan Baba Mai Koko, kace nace dan Allah ta bamu koko na naira ɗari In Sha Allahu zan haɗa da ɗarin ta ta da na kai mata"
Ɗan ɓata fuskar shi Salim yayi yace
"Ummanmu rannan ma da kika aike ni da ƙyar ta bani, haka ta dinga faɗa a cikin mutane wai bama biyan bashi a kan lokacishi yasa bata son sai da mana."
Cikin Jin ɗacin abin ya cigaba da magana:
"Wallahi kamar kar na amso na haƙura naji Ummanmu kawai dai saboda Na'im na amso"
Na riga nasan Salim yaro ne mai zuciya, baya son wulaƙanci ko kadan, sai dai akwai girmama na gaba dashi da ladabi. wulaƙanci ne kawai baya so.
Sanin bamu da yadda zamu yi in be amso mana ba, yasa na shiga lallashin sa har na samu ya tafi.
Yana dawowa ya juye a kofi kokon da bai fi shi ya shanye ba,
Ya miƙo min tare da fad'in
"Ummanmu gashi kisha ki bawa Umar da Na'im"
Duban shi nayi ina
mamakin karfin zuciya da dakiya irin tashi dukan shi bai fi shekara goma ba,
amma in yayi wani abin kamar wanda ya haura hakan.
Girgiza masa kai nayi cikin murmushi mai ciwo nace
"Ni ya kamata na bar muku Salim kasha ka bawa ƙanen ka ka ji"
Shima bai shaba duk yadda naso yasha ɗin la,
haka ya raba biyu ya bawa Umar rabin,
da kanshi ya tallafo Na'im ya shiga bashi a baki yaron ya kama kofin kamar ba zai cire bakin saba sai da ya shanye tas.
Jiƙa tsumma Salim yayi, ya gogewa Na'im fuskar sa data ɓaci wajen shan kokon, nan da nan Na'im ya fara ɓangala masa dariya saboda ya ƙoshi.
Ya kama shi ya cire Masarigar jikin sa ya ɗauko wata tsohuwar rigar shi yasa masa,
dan dama ba wasu kayan kirki ya ke da suba, yawanci. kayan shi ne tun yana jinjiri, suma ba wasu bane waɗanda na tara ne na siya, lokacin komai bai gama lalacewa ba amma dama Abban sa bai sai masa ko ɗaya ba
Tunda ya k'yalla ido yaga na siya,
wajen shekara guda kenan haka nake saka masa.
Yadda ya gyaramin yaron sai naji daɗi,
ashe yana sa ido yana ganin yadda na ke yi, dan duk ranar da muka tashi bani da ruwan zafi a flarks kuma bani da sauran gawayi haka nake masa saboda sanyi.
Godiwa ga Allah nake kawai daya azurtani.
da yaro Mai hankali irin Salim. Allah yasa Sauran ma su zama tamkar shi. addu'a na shiga akan Allah ya shiryamin su akan tafarkin Islam.
*********
_*BANGAREN HAIDAR*_
Ba su tashi da wuri ba yau sun makara.
Saboda ruwan da aka yi,
ganin har tara saura yasa a gurguje Haidar yayi wanka tare da ɗauro alwala.
Tana zaune bakin gadon tana danne dannen waya bata da niyar yin wankan bare sallar ko a jikin ta.
Har ya tada Sallah ya idar ganin bata tashi ba, yasan hali in bai yi da gaske ba ba yin zata yi ba dan haka yace:l
"Ki hanzarta kiyi Sallar lokaci na ƙara ƙurewa"
Kamar ba za ta tashi ba,
sai can ta miƙe tare da nufar toilet ɗin
ba tare da ta daina danna wayar hannun taba.
Koda ta shiga waje ta nema tayi zaman ta.
Sai da ta 'bata lokaci tana harkokin ta da wayar tukun ta wanke iya fuskarta tayi brush.
tana gunguni ita kadai.
"Haka kawai mutum ya wani dame ni da batun sallah,Sai kace d'iyar liman, ai wallahi duk abin ka yau bazan yi ba"
Koda ta fito cikin sa'a ta tarar ya fice a ɗakin,
ba tare da damuwa da cire rigar barcin da ke jikin taba, ta nufi farlon dan wata iriyar shegiyar yunwa da ta ke ji..
Turus ta tsaya tana karewa farlon kallo.
Ganin yadda ya ke kaca'kaca. Babu alamar an taɓa komai a cikin sa a yau yasa ta shiga mamaki,
Tun jiya data yi baƙi suka 'bata farlon.
har ɗaya daga cikin su taso ta share, tace ta barshi tana da wadda zata gyara mata.
Haka suka barshi kamar wasu yara ƙanana ne suka yi wasa a cikin sa,
babu gyara dan tana da tabbaci tana da mai gyaran.
Ganin Haidar zaune a kan kujera dafe da kansa. yasa ta ƙarasa takowa cikin farlon,
ta kalle shi tare da cewa
"Baby kaga yau ba'ayi gyaran farlon"
maganar tace ta yanke bayan ta kai dubanta ta ga dining ta ga wayam babu komai sai flet ɗin abincin jiya da sauran burbud'in Indomen da suka zuzzubar a kai da robobin lemukan da suka sha tare da ledojin Biskit.
Shi kan sa Haidar ɗin yunwar ce ta fito dashi, Ya tarda komai babu shi yasa ya zauna nan yana tunanin me zai ci.
Magana ta sake masa ganin bai ɗago ba,
Murya a tsatstsaye dan ranta ya matuk'a ɓaci rashin zuwan Salmah tace
"Baby ya Ina magana ka k'i cewa komai,
Kuma kasan yunwa nake ji ko?"
Ɗagowa yayi da ƙyar dan har wani ciwo kansa ya ke masa,
Saboda jiya bai ci abincin dare ba ya kwanta,duk da Salmah tayi abincin amma ta bawa ƙawayen ta.
Kuma koda ya dawo
ce masa tayi baƙi kuma ta basu abincin sa.
Bisa dole ya hada shayi yasha ya kwanta haka,
Tunda dare ya yi bai san Ina zai samo abinci yaci ba.
"Ba ta zo bane Salmar?"
Ya tambaye ta.
Cikin zafin rai ta harare shi kamar shi ya mata laifin tace
"Inda ta zo ai ina ga za ka fini sani. tunda ka rigani fitowa"
Ta ƙarasa tare da jan wani dogon tsaki.
Shafa cikin sa da ya ke ji kamar babu ƴaƴan hanji ciki yayi haɗi da hamma yace
"To kije ki duba kiga ko lafiya, me ya hanata zuwa tabar mutane da yunwa haka"
Ya maida kanshi jikin kujerar ya kwantar tare da rufe idanun sa.
Cikin fushin rainin hankalin da Salmar ta musu ta rufe shi da faɗan haka kawai zai ce, tayi ƙwafa ta wuce ta fita farlon tana mita,
"Naga alamar raini ya fara shiga tsakani na da Salmah yanzu,
In ba raini ba tasan aikin ta ba za ta fito tayi ba, ta barmu da yunwa"
Tayi ƙwafa tana mitar har ta ƙarasa ɗakin.
Hayaniyar ta kawai ta ke a kaina akan na fito nayi aikin, amma na kasa ko ɗagowa na kalle ta saboda yadda nake jin kaina kamar zai rabe biyu saboda ciwo,
ganin na ƙi kula ta,
Haushin hakan tasa ƙafa ta kaimin hauri a cikina. Cata iriyar azaba data ratsani naji kamar zan shid'e. ta kuma sa kai ta fice tana faɗin
"Shi wanda ya isa da ke bari na kira shi.
Ai ni in kin raina ni shi ya isa da ke"
Salim da tun shigowar ta ya sunkuyar da kai,
ya Koma gefe yana jin ciwon cin mutumcin da ake min.
Ganin ta fita yasa ya ƙaraso gare ni cikin tausayawa Halin da nake ciki yace
"Sannu Ummanmu kinji ko dai naje wajen Mama Uwani na aro miki naira d'ari. Na siyo miki paracetamol ne kusha ke da Umar?"
Cikin dauriya na jinjina Masa kai, Ina Jin gwara
ya siyo mana ɗin dan duk muna buƙatar shan maganin ni da Umar, dan shima jikin sa yayi zafi. sakamakon raunin dake kansa da bai warke ba, nasamu sunyi barci shi da Na'im da ƙyar.
Haka Maryam ta sako Haidar a gaba
shima zuwan sa bai duba halin da nake ciki ba ya balbale ni da masifa akan k'in zuwan nawa sashin nasu,
ba tausayi ko kaɗan
duk da kuwa ya fuskanci bani da lafiya,
tunda yafi kowa sanin yanayin da nake shiga in ina ciwo ya ƙare maganar sa da jan kunnen, kar na sake ya dawo ban zo nayi aikin da na san Ina yi ba.
Ina jin fitar su yana cewa Maryam ɗin
"Sweet muje ki nema min koda Tea ne nasha zan fita"
Ina jin tana cewa:
"ita gskiya ta gaji ba zata iya haɗa wani shayi ba, kawai ya fita ya siyo musu abinda zasu karya"
Paracetamol ɗin da Salim ya siyo mana
Na amsa, harda wainar gero ta haɗo masa ta da ta haɗe ta da k'uli
ta dai ta ɗari biyu,
dan har sana'ar waina take haɗawa bayan kayan miyar da take siyarwa.
Wani daɗi ya ratsani, naji ƙaunar matar ta ƙara ratsani Allah sarki itama
tausayi ne kawai da karfin hal.
Ba wani jarin kirki gareta ba, dan ita ke kula da marayun ƴaƴan ta,
wani lokacin ma in sun cinye jarin ba tayi.
sai ɗan jarin kayan miyar shima ba wani ba,
Da ya sa naci na basu
sauran. ita ma dan zan sha magani ne da haƙura zanyi na bar musu.
Nan muka hadiyi maganin na kwanta dan in ɗan samu barci.
Sama-sama barci ya fara fuskata naji Haidar na ƙoƙarin fita da motar
shi.
Bani da halin zuwa in buɗe masa get yau, Salim kam ba iyawa zai yi shi kaɗai ba,
Muryar shi naji cikin tsawa Yana cewa
"Ke ke kee ki zo ki buɗe min get zan fita.
ko shima ba za ki iya ba?"
Ina jinshi nayi shiru baya faɗin sunana dama ban sani ba kodan tsanar daya min ne oho, sai dai yace ke.
ko baki ji ba,.
Salim ne yace "Ummanmu bari naje na buɗe masa"
Kafin nayi magana ya tashi ya fita
Ina kiran shi bai dawo ba,
Yana zuwa ya tsugunna gaban Haidar da ke tsaye yana sababi,
Cike da ladabi Salim yace
"Abba Ummanmu bata da lafiya tun da safe, Jikin Umar ma kuma yayi zafi sosai"
Ya ƙarasa maganar idanunan sa cike da k'wallah
Wani kallo yabi Salim da ke durk'ushe dashi,
Tare da jan tsaki ya juya zai tafi na tare da yace komai ba,
Cikin sauri Salim ɗin ya ruga da gudu ya riƙo ƙafar shi cikin kuka ya haɗe hannayen sa.
Muryar shi na fita da In'ina yace
"Abba ka taimaka ka kai Umman mu asibiti dan Allah ka ji"
Kamar zai haure yaron sai kuma ya tsaya,
Yayi jim yana kallon yaron da ke kama dashi sak kamar yayi kaki ya tofar, ji yayi kamar akwai abin da ya ke son tunawa amma ya kasa maganar da suka ji ta bayan su ita tasa su juyawa.
Maryam ce ke magana tana tahowa tare da tafa hannayen ta,
"Eyye kaga munafukin yaro da iya sanabe, au kai ma taya uwarka kishin ka ke kenan?,
yau ni Mero na shiga uku har kasan roko da munafurci haka"
Ta ƙaraso ta cakumo shi daga tsugunnon da ya ke tare da kwashe shi da mari.
Haidar na tsaye ya kasa cewa komai
Sai kauda kai da yayi
Kawai.
Salim da yaji zafin marin ya ratsa shi har kwakwalwar shi,
Ya zuba mata idanu da suke zubda hawaye.
Mari ta Kuma Kai masa
Cikin hargagi tace
"Dan uwar ka ba zaka daina kallona ba,
da shegen idanu kamar na mayu, daina kallo na dan uwarka kona cire idanun kowa ya huta,
Uwar ka Kuma ank'i kai ta asibitin, wuce ka bawa mutane waje" ta ƙarasa tare da hankaɗa shi ya fad'i gefe.
Hannun Haidar ta sak'alo wanda ya tsaya kamar mutum mutumi, babu um babu um'um.
Cikin narkakkiyar Murya tace:
" muje Dear in haɗa maka shayin kasha kawai" duk da ba haka tayi niya ba,
Amma ganin wannan ɗan iskan yaron ya tsare shi yasa ta fito.
Haka taja hannun Haidar ɗin kamar rak'umi da akala ya bi ta.
😍MAMAN 'DAN ALBARKA CE😍✍️✍️