Chapter 16
by @aryaahriyad
Wasan sarƙaƙiya ( game of puzzle).
By Aryaah Riyad..
Book one 1…
Chapter 16…
Stars talented writers……
Palourn gidan ta shiga babu kowa a ciki sai kanshin turaren wuta dake tashi ko ina tsab tsab. Ga wani haduwa da palourn yayi komai ciki purple ne da red an zuba mishi kaya everything was so exaggerated.
Bata tsaya nanba ta wuce Elevator dake chan gefe a palorn tashiga ta danna button na third floor cikin minti daya ya kaita ta fita. Shima nan wani palor ne komai naciki purple ga animated characters an mammanna a bango da hotunan su Henry cavil, leonerdo decaprio da sauransu hollywood celebritys da anime characters.
Bin palorn tayi da kallo tana tuna rabon da tazo gidan yau wajen shekara daya kenan. Daga gefe wasu kofofi ne ta nufi gayan cikinsu ta bude ta shiga batareda tayi knocking bah yanda takeyi kamar gidanta take shiga.
Shimadakin purple ne da princess bed yahadu sosai saidai yafi kamada dakin yara akan na manya. Wata budurwar yarinya ce kwance akan princess bed ta kifa cikinta akan gadon ta dago kafafunta sama face dinta akan wani lallaisar pillow tana danna wayarta dake cikin purple case. Kunninta da headphones shima purple mai gashi gashi tana kada kai kana gani kasan tana cikin nishadi.
Dan tsayawa Alina tayi tana kallon yarinyar yanda take kada kai abunta batamasan an shigo dakin bah. Dan sallama tayi ciki ciki saidai ina bata jitaba tanachan duniyar waya.
Karasawa ciki tayi batareda ta tufe kofarba ta zagayo har gabanta ta zauna amma still bata lura da itaba. Hannu tasa ta janye headphones din daga kunninta a firgice yarinyar ta dago kai tana kallonta. Tunda suka hada ido Tahira ke kallon Yazrin kamar taga aljana. Ta waro manya manyan doll eyes dinta akan Alina cute pink lips dinta a sake alamardai bata taba tsammanin zataga Alina bah.
Ta dade a haka Alina ma bata dauke idanunta ba tana kallonta kafin Tawani zabura ta mike kamar wanda aka chakama allura tana sakin ihu. “ O.M.G Sis Alina.. nooo i can’t belieeeve this wallahi kece dama”. Tawani yi maganar a wata shagwababbiyar murya tanajan words din voice dinta so cute kamar na yara.
Dan smiling Alina tayi mata tana daga mata gira daya alaman yes itace. Wani fadowa tayi jikin Alina ta rungumeta gamgam kamar zata ballata. Alina ma rungumeta tayi kafin ta cireta daga jikinta jin tana nema taballa mata kasusuwa.
Sakinta Tahira tayi sannan ta koma ta zauna a gefenta tana cire Headphones din daga kanta gabadaya tareda wurgashi gefe akan bed din. Voice dinta cikeda farinciki da excitement tace “ OMG Sis Alina wallahi i missed you so much. Kin dena zuwa gurina tun last year fah baki kara zuwa gidannan bah, gashi konaje gidanku saidai ace mun kin fita kullun, jiya nakiraki ma wayarki bata shiga nace daddy yasa a kaini gurinki yace mun wai baisan inda kikeba”. Takarasa kamar zatayi kuka.
Murmushi ta sakin mata tanajin a ranta babu dadi ganin genuine farin cikin Tahira a yanzu, bataso tayi anfani da ita saidai tuna halin dasuke ciki yasata danne tunanin a zuciyanta.
Cikin tausasahiyar murya wanda inba Ummi bah babu wanda kesamun wannan murya daga gareta tace “ Tahira baby i miss you too. Kinsan yanda abubuwa suke a cikin masarauta so banida time sosai amma gashi yanzu nazo. Ya school?”.
Guada mata kai tayi face dinta cikeda annuri kafin ta tabe baki tana fadin “ Bayan kin tafi kin barni? Wai ya akayi aka yarda kika gama degree dinki a shekara biyu mukuma sai munyi hudu? Sannan kikaki ki rokan mun daddy nayi ko shekara uku ne kikayi graduation kika barni Allah banji dadi bah yanzu banida friends tunda kika tafi”.
Murmushin gefen baki Alina tayi mata sannan tace “ Kinsan nima kawai dan Ummi tasa baki ne aka barni nayi shekara biyu. Kekuma bacewa kikayi bazaki dauki extra courses ba sunmiki yawa? Ni year one da year two a lokaci daya nayisu sannan level 3 da 4 shima a lokaci daya nayi kokin manta ne?”. Ganin an kamata yasa Tahira ta kara turo baki tana fadin itadai babu ruwanta wlh kawai dai anmata wayau ne fan ta wuce ta “ ai nima nanda 3 weeks zanyi graduating, dan haka na yafe miki”.
Abun dariya yaba Alina wai ta yafe mata. Kowa ya tambayi yafiyar ta oho halin Tahira sai ita. Duba agogon hannunta Alina tayi ganin yanzu time na masallaci yayi na sallar azhar kuma tasan lallai yanzu Daddy Tahira zai gita masallaci dake anan cikin gida yasa tajuya kan Tahira tace “ Tahira am hungry banci breakfast bah”.
Tsalle tayi ta dira daga kan bed din tana fadin “ am so sorrry my Alina. Murna ya hanani tuna manners dina bari nasa a kawo miki”. Wani iri Alina tayi da face dayasa Tahira yin saurin fadin “ sorry na mantaaa. Bakyacin abincin mutane muje dakaina zan dafa miki”.
Da ok Alina ta ansa sannan ta mike suka fita. Kasa first floor suka sauka Tahira tayi hanyar kitchen. Har tayi gaba kuma tajuyo tana kallon Alina data zauna a kan daya daga cikin luxurious red sofa dake palourn. “ Sis Alina bazakizo bah? Kinsan nifa ba iya girki nayiba, kuma bansan me zakiciba har yanzu banana pancakes ne favorite dink…”.
Bata bari ta karasa ba tace kawai ta hado mata tea mai honey shikenan. Da ok Tahira ta amsa sannan ta juya ta nufi kitchen din da sauri sauri gudu gudu.
Alina kuwa kalonta ta mayar zuwa elevator dan kujerar data zauna yana kallon elevator din directly, sannan ta daura kafa daya kan daya tana gyara zaman alkyabbarta tayi wani irin sexy yet casual zama mai daukar hankali.
Da biyu tayi hakan dan sotakeyi yana saukowa ya tarar da ita tana kara kallon time ganin lokacin tabbas yayi amma bataga saukowanshi bah. Tunani tafara Allah yasa bai riga ya tafibah datayi zuwan banza, saikuma ta tuna koda ya fita ai zai dawo, kawai dai zata kara bata lokacinta ne dan batayi niyyan zama sosai bah.
Tana cikin tunanin kuma taji karan elevator ya bude. Face dinta dayake ba yabo ba fallasa ta mayar kan wayarta dake hannunta data bari a bude tafara daddannawa.
Fitowa yayi daga elevator din a sannu yana sanye da Farar Kaftan. Dogo ne saidai ba chan sosai ba, kyakyawan arab man yana kama sosai da Rayyan da Tahira. Sumar kanshi dabai rufeta ba baki sidik bashida tsawo sosai an gyarashi baya.
Kanshi a kasa ya fito yana dan sauri haryayi nisa jin kanshin turaren wanda yasan mutun daya yasani dashi yasa ya dago kai zuwa inda yaji kanshin. Wani tsayawa yayi yana kallonta ganin yanda tawani kame.
Saida tadau lokaci sannan tadan dago kanta daga danna wayar datakeyi tsab Taji fitowanshi sarai da tsayawanshi.
Hada ido sukayi ta sakinmai wani sassanyar murmushi. Mayar mata da murmushin yayi sannan yace “ Alina yau kece a gidan namu? Ai nazata kin manta da kawar takine”.
Bata chanza fuskartaba still da smile din a face dinta tace “banida time ne kasan yanda abubuwa suke. Amma yanzu gani nazo. Tun last month nayi mata alkawarin zanyi finding time nazo”.
Gyada kai yayi sannan yace bari yaje yayi sallah ya dawo. Da ok ta ansa mishi sannan ta dauke idonta daga kanshi takoma danna wayarta. Bai tafiba immediately saida yakusa 1 full minute yana kallonta sannan yafice daga palourn.
Tanajin fitarshi ta dago daga kallon wayar datakeyi tana sauke ajiyar zuciya. Daman tasan hakan zata faru dan ba karamin mutun bane dole zai gano da wani abu a kasa dukda bai nuna ba amma zuwanta gidan bayan wajen shekara daya rabonta dazuwa dole kobakayi dogon tunani ba kasan da wani abu.
Daga kafadunta tayi aranta tana fadin toh seme? Itadai tasan dole plan dinta yayi working, ko akan wane kuwa. Saita tozarta Hussain tamishi abunda bai taba tsammani ba. Bakuma wanda zai iya mata wannan sai Daddyn Tariha. Da alama kuma bazata sha wahala akan hakan ba dan kwallonta tariga tashiga raga.
Kuwait….
A bangaren Yazrin kuwa bacci ne ya kwashe ta saidai a wahale tayi baccin. Koda ta tashi still kata baibar ciwo ba infact karuwa yayi ga bayanta dake zugi kamar an saka mata shocking. Kamar tay kuka haka ta tashi daga kwanciyan datake tanajin jiri na dibanta.
Dakyar tasamu jirin ya lafa tafara tafiya zuwa toilet dan wanka takeson yi. Tuna tanada ciwo a baya ne yasa ta komawa ta dauki watarta sannan ta danna wa Dr. Katherine kira. Saida takusa tsinkewa sannan ta dauka.
Gaisawa sukayi sannan ta tambayeta zata iyayin wanka? Yes ta ansa mata saidai tace kartayi anfani da ruwan zafi sosai. Kashe wayar tayi batareda ta ansata ba ta shige wanka. Bata dadeba ta fito ta sa wata pure cotton night dress doguwa har kasa sannan ta fita daga dakin don yin exercise.
Waje ta fita kanta dake ba dankwali gashinta a sake ya barbazu dadan danshi a jikinshi bata tsaya tayi drying dinshi sosai bah.
First floor ta sauka sannan ta fice daga cikin mansion din gabadaya tayi left. Hanya ce sambal dake zagaye da flowers da short short trees babu security ko daya a gurin dan guri ne dasu kadai ke zuwa dantin trecking sudan motsa jiki.
A hankali take tafiyar tanajin jikinta na saki sabanin dazu dayawani rike. Takai wajen minti goma tana tafiyan tana tunanin wannan riddle din data karanta last, wani tunani ne yafado mata shin kodai ansar nacikin rubutun ne? Kokuma …. Tayi nisa cikin tunanin bata ankara ba kawai taji an bangaje mata kafada.
Wani juyowa tayi cikeda bacin rai tana kallon wanda tasan inba itaba babu wanda zai mata hakan a gidan. A harzuke tana tamke fuska kamar ba itaba tanuna Amrah tana fadin “ Amrah ni zaki buge? Duk girman gurinnan bai miki ki wuce ba saikin bigeni zaki wuce”. Tana fada tana nuna kanta.
Tsaki mai sauti Amrah tayi itama face dinta a tamke ba annuri ta ballama Yazrin harara cikin wannan voice din nata mai bakanta ma Yazrin tace “ Oh. Dukana zakiyi kike daga mun murya? Idan nace zanbi takanki nawuce akwai wanda ya isa ya hanani ne? Kokuwa kina ganin kin samu tsoho zaki aura wato yanzu kin girma ko? Har kun fara fadan kishi kamar mahaukata kinje ana dukanki a banza zakizo ki huce a kaina toh idan kin manta waye Amrah zan tuna miki yau basai gobeba ki bata mun rai kigani”.
Jin maganganun tayi suna wani sukanta batareda tayi wani tunani ba tafurta “ Kiyi abunda zakiyi Amrah. Duk rashin mutuncin dakike ji dashi ki rike shi inda kike karki kawoshi gurina ki kama girmanki”.
Kafin tarufe baki ji tayi kawai Amrah tayi wani ihu tareda zubewa a gurin……
For more information ga wattsapp number na ***.