Kuncin zuci
by @bintuuu
Jinginar da kansa Ahmad yayi a jikin seat tareda rufe idonsa yanajin komai baya masa dadi a duniyar ma, Adam ya juyo yana facing dinsa sannan yace "You need to cool down Ahmad, nutsuwarka muke buqata yanzu, nasani da ciwo kuma muma mana jin zafin hakan, but let's focus Dan Allah, let's talk this out mu samo solution, street dinnan baza'a rasa cctv ba, sai munsan meya faru bayan ta fitan sannan zamu kamo bakin zaren, muje mu nema before ma'aikatan nan su rigamu, kanada boys Ahmad, let them do their job, kasa Mazzy ya watsasu ko ina because time is ticking and we need to find her as soon as possible" Ahmad dake sauraronsa sai sannan ya bude idanunsa da sukayi jaa, sai wannan lokacin wasu abubuwan suke dawo masa cikin kansa, Mazzy, Smoke...sai ya juyo yana kallon Adam din ahankali yace "Where is my phone?" sai Adam ya fara waige waige yana duban cikin motan, nan suka ganta a wani nook na seat din sai kuma kiran Baba ya shigo wayan Adam din ya dauka, daga can Baba yace "Adam ku dawo yanzun nan tare dashi" Adam ya amsa da "toh in Sha Allah" da haka baba ya kashe wayan sannan Adam ya tada motan har sannan Ahmad na jingine da kansa ajikin seat din, motansu ce ta fara yin gaba sannan tasu Lamin da faruk sukabi bayansu suka dau hanyar komawa gidan, isarsu sai suka faka Dan nesa da gidan ganin mutane sunata fita wasu na nufar motansu wasu Kuma na takawa a kafa zasu bar layin, Ahmad ya qurawa jama'an Ido yana Jin zuciyarsa na karyewa kamar bashi ne cikin farin cikin a rana kafin wannan ba, kamar ba jiya suka gama farin ciki cikin taron jama'a ba shida Na'imarsa, sai ya rufe idonsa aransa yana Jin kamar muryarta na yawo akansa.. innalillahi wa inna ilaihi rajiun, sai yace "Ya Allah give me strength" Adam dake gefensa shima yaji hawaye na zuwa idonsa sai ya sake dafa kafadansa yace "We'll go through this together man, we'll find her aduk inda take da izinin Allah" Ahmad ya gyada kai sannan suka fita daga motan atare, A compound sukaga Anty Amnah dasu Fatima a tsaye da alamu su sukasa jama'an suka fita daga gidan, sai tayi saurin qarasawa ga Ahmad din ta dan riqosa tareda duqo da kansa a kafadanta tana hawaye take fadin "Take heart Ahmad, take heart" Ahmad ya gyada kai yanajin zuciyarsa na karyewa, Fatima ta matso tareda dafa bayansa tana share hawayen itama, sai Anty Amnah ta sakeshi tace "ku shiga su Baban na nemanku aciki" da haka ya sake gyada kai gaba dayansu suka shiga ciki su Lamin na bayansa, A falon suka sami Matan ne kadai dan Mazan suna part din Abba by then, nan ma su Ahmad sake nufan can sukayi su Mami na kallon sa da tausayawa, sun sami su Abban tareda Osagie da ya kasance commissioner of police nan zaune shima tareda wasu ma'aikatan guda biyu, zama su Ahmad din sukayi sai daya daga cikin ma'aikatan suka miqo masa laptop dake riqe hannunsu, karba yayi yana kallon content din ciki and his heart skip a beat for a moment ganin Na'ima na tafiya a street din tana kuka tareda share idonta, and there....right there wata baqar mota ta biyo bayanta aka bude wasu maza suka fito su biyu suka jata ciki tana fusge fusge, zuciyar Ahmad har rawa take yana kallon videon, so dagasken dauketa akayi, someone set this up, ransa ne yaji yana qara zafi, then who played this game with him..with his wife....
Dan gyaran murya Osagie yayi yace "cctv proof ya nuna mana daukanta akayi, but the real question is tayaya ta fitan, was this all a setup or not, dan muna zargin willingly ta fita" Ahmad ya girgiza kai da sauri yace "Ba fita tayi da kanta ba, i know her..Na'ima bazata gudu ba, bazata taba gudu na ba ku yarda dani" bawanda Ahmad bai bawa tausayi a falon ba sai su ka rinqa kallonsa cikin karyewan zuciya, Osagie na kallonsa yace "zamuyi iya kokarin bincikenmu na ganin anyi tracking dinsu, and in the process kuma zamu jira kiransu dan definitely zasu iya neman ransom" Abba yace "Amma wane irin jira zamuyi kuma, i need my daughter back as soon as possible" Osagie ya gyada kai cikin gamsuwa yace "zamu yi iya kokarinmu sosai, Ina baku assurance na zamu samota, but first sai mun kadaice da duk wanda ya kwana cikin gidan, sai mun yi namu tambayoyin, imam here will take care of that" ya qarasa maganan yana nuna yaronsa dake tsaye a agefe, Baba ya amsa da "Ba damuwa you can go ahead" Ahmad ji yayi ransa na baci, wai jira, jira like how, miqewa Adam yayi sai ya tabo Ahmad din akan su fita daga falon, a zafafe ya miqe ya fita, direct wajen gidan ya nufa yabar Adam gurinsu Mami dake zaune har sannan a main falon gidan, sai da ya isa ga motansa sannan ya ciro wayarsa daga aljihu ya fara neman numbern Smoke, aikuwa a bugu biyu ya dauka sai Ahmad yace "kana Nigeria?" daga daya bangaren Smoke yace "Yes" sanin ba fadan specific address dinsa zeyi ba yasa Ahmad cewa "Please ka fadamin inda kake yanzu haka" shiru smoke yayi sai kuma can yace "Abuja...ina hada maka papers din Saddam" rai abace Ahmad yace "Drop everything..some goons took my wife, I need you on this, I need you to find her as soon as possible, am sending you the clip" da dan sauri smoke yace "And we'll find those motherfuckers, they mess with me when they messed with you, I'll definitely find them Ahmad" sai sannan Ahmad ya fara Jin nutsuwa sannan yace "Do your best Smoke" da haka ya kashe wayan ganin Lamin na qarasowa garesa, ahankali Ahmad yace "I need that card" sai Lamin ya dago masa hannunsa riqe da card din cikin cctv, da haka ya bude motan Ahmad din ya fara duba laptop, anan cikin motan Lamin yayi extracting video clip din da Na'ima ke ciki ya turawa Ahmad din a wayansa, da Ahmad ya bude yana gani in ya qare sai ya sake rewinding, nan ma in ya sake qarewa sai ya sake rewinding, sai da yayi haka fin irge zuciyarsa na karyewa ganin kuka take tana tafiyan, Meya sata kukan? Me aka mata a gidan?, ganin yanda mazan suke janta tana fusgewa yasa ransa baci matuqa har wani daci yakeji a ransa, fita yayi daga videon ya kira Mazzy bugu na biyu ya dauka, a zafafe Ahmad yace "I'm in drow Man, some thugs took my wife...do something" sai da Mazzy yaji zuciyarsa ta tsinke shima a gigice yace "What dah f*ck?....u got the link?" Ahmad na dafa goshinsa yace "No man, am only sending u a clip right now, do what you must please, I need her back within hours if that's possible please" Mazzy yace "I got u Ahmad.. we'll do what it takes" da haka Ahmad ya kashe wayan sai da dafa kansa dake sara masa, da dan sauri Lamin ya riqosa sai Adam ya sake fitowa daga gidan da dan saurinsa ya qaraso gurin motan yace "Ahmad you're loosing your strength, let's go inside..banason zamanka a wajen nan, ban yarda da nutsuwarka a wajen nan ba" ahankali Ahmad ya dago yace "bazan iya zaman cikin ba, ji nake kamar bana making wani effort in ina guri dayan" Lamin yace "But you're loosing yourself Ahmad..muje ciki ka nutsu dan Allah, no matter what sai mun jira both the Boys and the Police" Ahmad ya duqar da kansa kawai baice komai ba, shi jiran ne bayaso, he wants her back right now, ji yaka kamar ya bude idonsa ya ganta agabansa ayanzun....
A lokacin da Mazzy ya bude video clip dinda Ahmad ya tura masa sai ya dan tsaya yana kallon content din da mamaki, can ya dago kai yana kallon yaronsa daya dake zaune a kujerar dake cikin babban falon nasu, adan firgice yace "Kai wane Gig su Tiyagah suka karba last two days?" Yaron me suna Bonu yace "I don't exactly know Boss, they said something about helding wata Amarya captive, wata mata is paying them huge money on it to take the girl to zamfara, amma basu fadamin details ba" A gigice Mazzy ya miqe wayar na faduwa daga hannunsa yace "Dah'F*ccckkk" a tsawace yace "Call them..call those motherfuckers duk inda suke su dawo da ita, That's Ahmad's Briiide.....Call them before he kills each and every one of them...Shiiitt" sai ya fara jeka dawo a falon, yaran nasa duk a gigice suka ciro suna dannawa da sauri ya kuma ya sake duqawa ya dauki wayansa dake qasan da qarfi ya sake fadin "Shiiiiiitttt" sai kuma be kira su Tiyagahn ba gudun kar numbernsa tayi appearing a wayarsu ma abun ya hado dashi, a firgice yace da daya yaronsa "Where is my burner phone, dauko min da wuriiiii" da sauri yaron nasa ya nufi stairs din falon, sai Mazzy ya ciji yatsa yana buga kafansa, lallai sai yaci uban Tiyagah, sai ya koya masa hankali ta yanda ko gaba in ya samu gig bazeyi gangancin karba batareda shawara ba.....
Wunin ranan asabar dinnan bayan jami'an sun koma station dan cigaba da gudanar da bincike haka wannan familyn suka wuni cikin zullumi da tararradin batan Na'ima, kowa kagansa kasan yana cikin damuwa, ko ruwa sun gagara sha, sallah ce ke tada kowannensu daga falon, Anty Amnah ta hana megadi budewa kowane baqo gate din gidan, dan mutanen da ke zuwa musu jajen ma qara tada musu hankali sukeyi more especially Mami da duk ta birkice itada Nafisa, ba abunda suke sai kuka da ajiyar zuci, Mazan sai zirga zirga suke zuwa police station da gidan radio da jarida dake cikin Abuja, Ahmad duk ya birkice dagashi sai yololuwar farar t-shirt suka rinqa yawon guraren cigiyar da sukasan zai iya linking dinsu ga samunta...zuwa sannan kowa ya yarda set up aka tsara na yanda za'a dauke Na'iman sai aka hado da aikin shaidanu dan ta samu ta fitan da kanta, amma wa yayi wannan aikin shine abun tambaya, dan duk wanda yaga video clip dinnan a kallo daya zai gane Na'ima ba a hayyacinta take ba kwata kwata, sannan duk amsan mutanen gidan daya ce "basu ga lokacin fitanta daga gidan ba" wanda hakan ba qaramin kulle kan polisawan yayi ba, sannan har cctv na main falon gidan ya nuna hakan, amma na street ya nuna wani aika aikan daban, su Mummy dake gidan har sannan ba su sake magana ba amma haka Mami ta rinqa harara da jefa magana, bini bini tace "Allah yafi qarfin kowa, Na'ima sai ta dawo ta tare dakin mijin ta kuma, ai Allah ba azzalumin bawansa bane, wahalar da yarinyar nan ta sha abaya ma kadai zai sa Allah ya kareta duk inda take" su Mummy ba bakin magana, daga qarshe ma da Abba ya aiko motocin da zasu koma da mutanen Yola sai ta miqe tabi bayansu itada murja akan zasu tafi, da harara Mami dasu Amnah suka rakasu Anty nabinsu da kallo, dan abunda su Mummy sukayi a falon nan kadai ya darsawa su Mamin zargin da sa hannunsu a batan Na'ima kuma, dan dama dai sun kwana da sanin Mummy na biye biyenta kawai yanzun basu da shedan hakan ne, saida Mummyn takai bakin kofa sannan ta juyo tace musu "zamu tafi, Allah ya rufa asiri kuma" Mamma ko kallonsu batayi ba dan ranta ba qaramin baci yayi dasu ba, Mami ce ta kallesu tace "Amin, mungode da Addu'an, ku gaida gida" da haka ta dauke kanta aranta tana fadin "Adduarmu kadai ta isheku" kuma adddu'a kam sun sha ta, isowar Alhaji dasu Ayuba daga kano shima ya kira Malamai biyu suka zo nan masallacin kofar gidan aka rinqa karatu da addu'o'i, sai da aka kai yamma babu labarin Na'ima daga gurin masu bincike, babu labari daga gurinsu Mazzy ko Smoke...A dawowansu gida na qarshen ne sun shigo falon sai Anty Amnah ta riqo Ahmad ganin yana layi shi kadai kamar zai fadi, tana kallonsu Lamin da suma duk sun firgice tace "He's not okay," da haka ta juya gurin likitan dake sawa Nafisa qarin ruwa tace "ka dubashi please" sai ta juya gurin Ahmad tana taba goshinsa tace "Gani fa jikinka zafi son" Mamma dake kallonsa tun shigowar sa sai sannan ta dauke kanta, Mami dake zaune kan sallaya ta miqe muryan ta na fita dakyar tace "Adam ku kaishi ya kwanta" sai sannan Ahmad ya bude baki a hankali yace "I'm fine" cikin karyewan zuciya Anty Fatima tace "Yaya you're not fine, you're breaking down" sai ya girgiza kai ya juya zai fita daga falon, nan kuwa yaji kafarsa na neman kasa daukansa, ganin haka da sauri Adam ya riqosa sai duk aka miqe a falon, likitan ya bar kan Nafisa ya nufesu, fashewa da kuka Mami tayi tace "Ya Allah..Adam ku riqeshi ku kaishi ya kwanta" Mamma dai har sannan kanta a duqe, Abu da Al'ameen sannan Husna dake miqe afalon suma sai kuka, Hajiya na share idonta tace "Allah gamu gareka, Allah ka kawo mana da sauqi" Umma jummai na kuka tana amsawa da Amin dan su kadai suka rage kuma...Ahmad na riqe da Faruk da Adam suka kaishi dayan part din gidan, anan kan kujera suka kwantar dashi sai ya rufe idanunsa kawai yana jin komai na duniyar na fita kansa, ji yake dama shi suka dauke madadinta, the pain he's going through now is unbearable, ji yake kamar ana qona masa zuciyarsa dan zafi, kawai sai cigaba da addu'an da yake tayi din azuciya tun safen, anan kwancen aka saka masa qarin ruwa har sannan idonsa a rufen bai bude ba, ko minti biyu ba'ayi da sakawa ba wayarsa tayi beep din shigowan saqon smoke, anan take sai ga kiran Mazzy ya shigo shima, dasauri Ahmad ya dauka kafin yace komai Mazy yace "Munyi tracking nasu sun bar Abuja yanzu haka, zan turo maka so digit dinsu and smoke will lead you to them" Ahmad ya miqe zaune yace "Ina suke yanzu haka?" Mazzy ya amsa da "Somewhere in Niger, sun samu matsala da motansu sunanan within Laiko forest, zanso muje tare amma kun sako masu kaki a harkan, it's messed up bro" Ahmad da bajin last statement din ma yayi ba kawai ya miqe tareda zare alluran jikinsa, Lamin yace "Ahmad ka fada masa yayi tipping su Osagie, we can't go alone" jikin Ahmad har rawa yace "They'll slow us down" Adam da ya miqe shima yace "taya zamuyi explaining kanmu ta inda muka samu tip up din, Ahmad ba wanda yasan alaqarka da su Mazzy fa, har kai jami'an nan zasu zarga" cikin hargagi Ahmad yace "F*ck them...maganar matata muke anan, I don't care about a thing they'll say, that forest is not safe, aduk wucewar daqiqa daya rayuwan matata yana sake shiga cikin hatsari ne" fusge wayan hannun nasa Adam yayi yace "You're not thinking straight, na maka uzuri amma wallahi sai an sanar da chief mun tafi tare dasu, tafiya tare dasu din is the safest way" da haka ya kira wayan Mazzy, faruk dai sai kallonsu yake dan bai gane inda maganan ta dosa bama, Mazy na dauka Adam yace masa ya tura tip din ga su Osagie dan su tafi tare dasu Ahmad yakai hannayensa fuska yana sauraronsu kawai, yana gama wayan Ahmad yace su tafi can station din dan bazai iya jiran isowar su Osagie ba, aikuwa nan Abba ya shigo falon yana fadin ga sunan zuwa suna tsammanin an samu inda su Na'iman suke, cike da jimami duk aka fito compound din gidan kowa ya tsaya ana jiran isowarsu, basu dade ba suka iso nan dan sanar dasu Abban halin da ake cikin, aikuwa nan Ahmad yace tare dashi za'a tafi Abba na cewa ya zauna amma sam yaqi sauraron Abba, da haka police squad su shida dinnan suka tafi dashi, Abba, Lamin, Adam Faruk sannan Alhaji...Hanya suka dauka cikin motoci guda biyu tareda zullumin abunda zasu tarar a jejin....
Na'ima...
A lokacin da Na'ima ta fita daga gidan cikin duhun asubancin nan itama kanta batasan inda ta dosa ba, tafiya take batareda tasan inda take takawa ba, wani irin abu takeji nan ingizata ta qara qarfin tafiyan nata bata bar kukan da takeyin ba, tana tafen motansu Tiyagah ta biyo bayanta dan daman jiran fitowan ta suke kamar yanda aka sanar dasu, Na'ima na kuka taji an kamota, adan tsorace ta juya sai taga wani qato ne ke janta zuwa ga motan, nan ta hau fisgewa da nufin su saketa amma haka suka hankadata cikin motan kanta na buguwa da seat, da haka dayan ya shiga suka ja motan tana kuka, tunda take bata taba jin tsoro irin na ranan ba, sai a wannan lokacin taji sunan Allah na zuwa bakin ta wanda rabonta da ta kira sunan Allah tun sallahn da tayi na isha a daren jiya, sai lokacin komai ya fara dawo mata, fitan da tayi daga gidan da kanta shi ya sake gigitata, sunayen Allah kawai ta hau kira tana fadin "Dan Allah ku kyaleni, wayyo Allah na" sai ta miqa kanta window da nufin tayi ihu kawai namijin dake gefenta ya jawota tareda dauketa da mari me karfi sai da bakinta ya fashe, Tiyagah da ke zaune a driver's seat dinne ya miqo wani hankie dayan yaron nasa ya karba tareda dannawa Na'iman a fuska tana ihun, nan kuma komai ya dauke mata ta fara ganin duhu, bata tashi farkawa ba sai da gari yayi duhu sai hasken farin wata kawai, dago kanta tayi daga kwancen sai taga hannunta a daure guri daya, dasauri takai bakinta ta fara warware kullin da suka mata a hannun sai Allah ya bata sa'a ya waru sannan fara waige waige ganin ita kadai a motan cikin jeji, nan ta hango samarin guda uku suna waje, biyu suna magana dayan kuma yana duba injin gaban motan tasu, ji tayi dayan na fadin "Wallahi bazan fada ramin nan tare dakai ba Tiyagah, kasan matarsa ce kasa muka karbi gig din nan, wallahi duk abunda ya biyo baya sai na rama linkinsa akanka" azafafe Tiyagah ya jefar da tabar bakinsa yace "Dan uwarka taya zan sani, kana ji dai tare dakai ya sanar da mu, sannan ba abunda zai faru na yarda da Mazzy" sai guy yace "ka yarda da Mazzy? yana tareda mai kudi irin wadzani kake tunanin zai bi bayanmu?" Shiru Tiyagah yayi sai guy din yayi saurin laluba aljihun Tiyagahn yace "Ina wayanka, wallahi yanzu ma haka ban yarda baisa anyi tracking dinmu ba" Tiyagah yace "Meya haka ne, Mazzy bazai juya mana baya ba, sannan yace kudin nan zamu basa wani abu" dayan dake gyaran motan yace "Fada ba namu bane yanzu, kudin ma kunsani basu shigo duka ba sai mun qarasa komai, mu fara gyara motan tukunna muyi mu kaita can din mu karbi kudin mu ware, in yaso sai ta koma gidan da kanta, Oga baya juya baya a team dinsa kunsani" Na'ima na Jin hakan taji wani kukan na zuwa mata sai ta fara
qoqarin fita daga motan ahankali, dayan guy dinne ya sake cewa "Tii ina sake fada maka ka kashe wayanka" jikin Na'ima na rawa takai hannunta ahankali zata bude cap din motan nan taji basuyi locking ba ta sai ta tura ta sauqa a duqe dan kar su ganota, a duqe ta fara tafiya har sai da ta danyi nisa dayan ya hango yace "Kuut" da haka suka rufo da gudu, aikuwa nan Na'ima ta hau gudu itama dan Allah ya rufa mata asiri sai da tayi nisan suka hangota, gudu take tsakaninta da Allah a jejin har sannan babu takalmi balle dankwali, tana gudun tana ihu ko zata samu wasu su Jiyo ta...A lokacin da jami'an tsaron suka iso guraren jejin da tracker'n tayi leading dinsu sai suka fara ratsawa jejin amma basuyi nisa ba jami'an sukace dasu Ahmad dasu Abban su zauna a mota su zasu qarasa ciki dan basu san wane irin shiri ne dauke da kidnappers din ba, Ahmad dake tsayen tareda dasu Abban muryan sa na rawa yace "Ba zamu qara shiga cikin ba" squad leader'n yace "Nan ne limit din ku, imam will stay with you for your safety" da haka suka fara arming bindigunsu, basu kai da gama shirin ba suka fara jiyo ihun mace na ratsowa daga cikin jejin kasancewan ko ina tsit, da sauri Ahmad ya juya yace "Na'ima ce" Abba ma yace "ihun ta ne faaaa" sai Imam yayi saurin duba tracking device din hannunsa, ya dago dasauri ya kalli leader'n nasu yace "they're coming towards us" arude Faruk yace "Gatacan" duk suka juya suka hangota tana gudu tsakaninta da Allah tun daga nesan take fadin "Ku taimakeniii" ai Ahmad ya riga kowa fara nufan ta sai jami'an suka riqosa tare dasu Abban, suna fadin "kar kuje, bamusan meke tare da ita ba" squad leader'n ya fara daga bindiga sama yayi harbi duk da haka Na'ima bata daina nufo su ba tana ihu, Ahmad baisan lokacin da ya fusge hannunsa ya nufe ta da gudu ba yana fadin "Na'imaaa" tanajin haka ta fara fadin "Ahmaaad...Ahmaad" gudu yake jami'an na biye dashi a baya hannunsu riqe da bindugu suna harbin sama dan su firgita ko ma su waye biye da ita, ahaka Ahmad ya fara iddata ya rungumota da qarfi yana fadin "Na'imaaa" fashewa tayi da kuka a gigice tace "Zan mutu, wayyo Allah na" sake kamota yayi kamar zai maidata ciki yace "Bazaki mutu ba" Jami'an wucesu sukayi sukabi bayan su Tiyagah da suka juya a arce, su Abba dasu Adam ma sai sannan suka qaraso suna haki Abba yace "Na'ima" Jin muryan Abba yasa ta sake Ahmad ya ta nufesa tana fadin "Abbaaa" da sauri ya riqota yana fadin "it's Alright daughter, muje mota" sai Ahmad ya miqa hannu ya fara jan jacket din jikin Lamin danshi t-shirt ce kawai a jikinsa, da haka ya qaraso ya yafa mata akanta sai ya cire takalmansa ya duqa ya fara saka mata har sannan tana kuka a jikin su Abba da Alhaji...
Bintuuu ✍️📚