KOWA YAƘI JI

Chapter 3

by @mamananalbarkace777


FREE PAGE3️⃣

Dawowa Salim yayi yana share hawaye, na daure na tashi na kalle shi cikin raunatacciyar  Murya nace
"Me yasa kaje kace ya kaimu asibitin Salim?
ba na kira kaba ka dawo?"
Na dakata kad'an da magana naja jikina na d'an jingina da jikin bango Ina sauke numfashi da k'yar, Saboda yadda  maganar kemin wahala  ga kaina da ke Sara min ji nake kamar zai rabe biyu.

Sunkuyar da kanshi yayi cike da ladabi yana matse k'walla.
Sai naji tausayin sa ya kamani nasan saboda ni yayi haka, amma naji zafin yadda Maryam ta masa da zagin da tayi,
duk da ba yau ta fara hakan ba, amma na yau yafi k'ona min rai.

Cikin hikima na shiga yi masa nasiha, akan kar ya sake zuwa ya tari Abban su yace ya mana wani abin, indai ba shi yayi mana da kansa ba, 
Hakan da yake Wata hanya ce ya ɗauko wadda nake Jin tsoron  kar raini ya  tsakanin su da Abban sa.
Tunda har ya fara yiwa Mahaifin nasa kallon Baya kyautawa, nan gaba ba iya haka zai tsaya ba, dan na fara hangon yadda wata wutar k'iyayyar mahaifin nasa ke ci a idanun sa,
bana fatan hakan ta kasance, ya fara fito-na fito da mahaifin sa abin  Allah ya kiyaye,

Cikin Ladabi ya jinjina  kai alamar ba zai ƙara ba, muryar shi na fita cikin kuka yace
"In Sha Allahu Ummanmu na daina"

Naji dad'in yadda yaji nasihar da na masa.
Haka na tattara yarana muka wuni a ɗaki.
Bayan nan  ban ƙara jin motsin su Haidar ba, 
tunda na ga bai fito ba da alama ya fasa fitar kenan duka.
Ina cikin tunanin me zamu ci da rana, tunda banda komai haka ko nera bana magani.

Cikin ikon Allah 
Sai ga aiken mama Uwani na Dambun zogale, wanda yaji kayan had'i cike da samira,
 Nana ce ta kawo min ita ce k'aramar Y'ar ta.

Cike da farin ciki na amsa tare da cewa ta mata godiya, haka na rarrabawa yaran zuciyata fal murna, duk irin yadda nake son dambu kaɗan naci na bar sauran saboda anjima kar Umar ya dame ni da batun yunwa. Tunda dai 
Alhamdulillahi yanzu sun ci sun k'oshi.

Zuwa dare zazzaɓin ya sake ni cikin ikon Allah
Kamar bani na wuni kwance ba,
Sauran dambun nan na bawa Umar ya cinye Yana lashe hannu Alamar bai k'oshi ba,
 ya kalle ni ya taɓe baki kamar wanda zai yi kuka cike da yarinta yace
"Ummanmu a k'aramin ban k'oshi ba"

Salim dake gefe ne ya taso ya k'wace kwanon, tare da dungure masa  kai yace
"Kai dai wallahi baka ƙoshi baka san komai ba sai dai a baka kaci,
to ya k'are sai kaci  babu"
Ya maida kwanon wajen bayan k'yaure inda nake ajiye kwanukan wanke-wanke. 
Ya Koma ya zauna 
Ya sunkuyar da kanshi.

Ai kuwa Umar yace bai san zance ba, ya ɓare baki ya shiga rusa kuka babu k'ak'k'autawa.

A hankali na ɗago na kalli Salim nace
"Me yasa ka masa haka um? kasan yaro ne ba hankalin sanin babu ya ke da shi ba"

"Kiyi hak'uri Ummanmu Allah haushi ya bani shi yasa"

Jawo Umar nayi na rungume shi, da  ƙyar na lallashe shi har yayi barci.

Shimfid'e shi nayi kusa da Na'im da tuni yayi Barcin sa, na kai kallo na ga Salim da har lokacin kansa a sunkuye ya ke,
Ya haɗe gwiwowin sa waje d'aya kamar wanda ya yi barci.

Tausayin sa ne ya kamani,  babu abin daya ci tun da rana dana raba na bashi dambun nan
rabon shi da sa wani Abu a bakin sa, ko yanzu naso ko loma ɗaya ya yi ko zaiji dama-dama amma yace a'a ya barwa Umar.
A zuciyata nace
_Inba dole ba yaro kamar Salim ɗan shekara goma, me ya sani in ba yaci ya ƙoshi ba yayi karatu, amma gashi rayuwa tasa har yasan shi ɗin babba ne ya barwa ƙanin sa abu shi ya hak'ura._

Ni kaina  yunwa ke sakud'ata kamar me,
dauriya ce kawai nake.
Ina ga yaro kuma wanda bai san wannan ba.

Cikin tausayawa na kalle shi nace
"Salim ka taso kazo ka kwanta kaji dare yayi."

Babu musu ya taso ya kwanta bayan Umar,
dan dama tsarin kwanciyar nice a farkon bakin ƙofa,
sai nasa Na'im a gabana sai Umar ya kwanta bayan Na'im Salim ne a ƙarshe dan ma tabarmar nada ɗan faɗi.

***
Da gari ya waye bisa dole na hana yara  zuwa makaranta, saboda bani da abin da zan basu suci  dole sai naje nayi aikin safe tukun za'a bamu kud'in abinci.
Dan haka da wuri na nufi Sashin Maryam.


Babu kowa a farlon alamar basu tashi ba kenan, dan haka kai tsaye na wuce kitchen na shiga gudanar da abincin karyawar kamar yadda nasan tsarin.

Ina gamawa na dawo farlon na gyare komai,
na jere abincin tsaf hakan yayi daidai da fitowar su.

Maryam ce a gaba,
sanye take da rigar barci iya gwiwa kanta babu ɗankwali hakan ya ƙara fito da munin ta, sai uban tumbin ta da rigar ta fallasa shi ya fito sosai kamar mai cikin wata biyar.

 Sai Haidar shi Kuma sanye yake da jallabiya fara tas, da alama ma daga wanka ya fito dan sai tashin ƙamshi ya ke,
Dan shi kullum da safe k'a'idar shi ce baya fitowa sai yayi wanka, haka tsarin sa ya ke tun muna tare.

Ganin hakan ya tabbatar min yau ba zai je ko'ina ba kenan, tunda har ya kai lokacin nan bai shirya ba.

Kai tsaye wajen cin abincin suka nufa, bayan sun zauna na ɗan matsa kaina sunkuye cike da ladabi nace
"Ina kwanan ku"

Ba tare da sun amsa ba
Maryam ta ɗaga min hannu alamar amsawa,  shi kam gogan dama ko gefen da nake bai kalla ba, sai  ƙoƙarin zuba sugar a shayin da ya ke.

Ganin haka yasa na ɗan koma gefe na tsaya,
a zuciyata ina Allah-Allah Haidar ya miƙo min kuɗin abincin mu, dan hankali na gaba ɗaya na wajen yarana.

Juyowa Maryam tayi ta kalle ni cike da wulaƙanci tace
"Tsaiwar me kike anan Kuma?  za ki iya tafiya anjima dai ki dawo da wuri saboda yau Baby yana gida"

Ji nayi kamar na juya na tafi, sai na tuna in na tafi me zan bawa yarana?.
Dan haka nayi k'undunbala na buɗe bakina cikin tsoron abin zai iya biyo bayan maganar tawa.
 Muryata na rawa idanuna a ƙasa nace
"Dama kud'in abincin mu nake jira"

Wani kallo ta jefomin cike da masifa tace
"Ank'i bayarwa tunda sai kin tambaya dama ake baki, ba za ki iya jira shi mai bayarwar ya baki ba sai kin roƙa? Dallah fice ki bawa mutane waje"

Duk maganar da muke Haidar na zaune.
Kamar Wanda bai ji komai ba, harkar gaban shi kawai ya ke.

Har na fara tafiya naji yayi magana cikin tattausar Murya yace
"Dawo ki amsa"

Na yi mamakin Jin hakan sai nayi zaton da Maryam ya ke magana, saboda da na juyo sai naga kamar bashi ne yayi maganar ba, dan ko inda nake bai kalla ba bare nace, dan haka na cigaba da tafiya jikina a sanyaye zuciyata na wani irin zafi.

Maryam da ta tsaya kallon Haidar jin abin da yace, ta k'ank'ance idanun ta cike da masifa kishin da ke cinta tace
"Dan zaka bata kud'in abinci sai kayi magana da ita a gabana dan cin mutumci?"

Bai ko kalle ta ba ya cigaba da cin abincin sa,
ganin Ina Shirin fita ya juyo ya kalle ni yace
"Ba za ki zo ki amsa ba?"

Cikin rawar jiki na dawo
zuciyata na wani irin bugawar tsoro,
Na tsugunna gefen su tare da miƙa hannu na da ke rawa.

Maryam ganin kuɗin da ya miƙo min cikin sauri ta fusge kafin na amsa.
Sai da ta harareni tare da cillo min dubu ɗaya, dama kuma dubu biyu ne ya miƙo har na fara murna Ina tunanin abin da zanyi da kud'in, sai naga ta rage wani baƙin ciki ya turnik'e ni na amsa a haka tare da furta "Nagode" na tashi a sanyaye na tafi Ina jin zuciyata duk babu dad'i.

Fad'a sosai Maryam ta rufe Haidar dashi,
akan me zai bawa Salmah har dubu biyu
 bayan ba haka ya saba bata ba.

Shi dai yana jinta bai ce mata ci kanki ba.
Har sai da ta gaji da banbamin fad'an tayi shiru dan kanta, dan ita ma tasan tunda yayi shirun ba kula ta zai yi ba.

Sai dai gaba ɗaya zuciyarta cike ta ke da tashin hankalin, ganin  canjawar Haidar ɗin lokaci guda, ta fuskanci tun jiya da Salim ya tare shi duk ya canja, ko magana bai cika mata ba tun lokacin haka duk irin yadda ya ke nuna zalama akan ta jiya har wasu abubuwa ta dinga masa dan taja hankalin sa amma a banza,
haka su kayi barcin zuciyar kowa ba dad'i.

Ko karyawar kasawa tayi ta tashi ta shige d'aki, cikin hanzari ta shiga kiran number Mama hankalinta a tashe'.

Tana d'agawa ko sallama ba tayi ba ta fara magana "Mama akwai matsala fa wallahi Ina ga aikinnan ya fara sanyi, dan yau Haidar ko shakkar idanuna bai ji ba ya yiwa Salmah magana"

Mama da ke kwance  K'ofar d'aki tana shan iska saboda zafi, jin abinda Maryam tace yasa ta miƙe  zaune cike da mamaki tace 
"Kina nufin Haidar har ya yiwa Salmah magana yau kuma ba faɗan nan da ya saba mata?"

Cikin jin haushin maganar Maman tace
"Wai taya zan miki ƙarya ne ? kawai ni ki fad'amin yadda za'ai"

Wani farin ciki ne ya ratsa zuciyar Mama ta cije baki tare da k'wafa tace 
"To ai dama duk laifin ki ne da ace tuntuni kin zo munje wajen Gamji kamar yadda yace da hakan bata faru ba"

Tsaki Maryam taja cike da jin haushin mamar tace  "Kinga Mama yaushe za ki zo muje,  danni gaskiya bana jin zan iya zuwa unguwar nan, Saboda kwatocin layin kunnan duk sai sun 'batawa mutum mota"

K'wafa Mama tayi jin irin rainin hankalin Maryam d'in sai kace ba a unguwar ta girma ba,
Tace "Ni sai nazo mu tafi daga nan tunda ba za ki iya zuwan ba"

Haka suka yi sallama madadin ta wuce ta karya d'in, sai ta kwanta kan gadon tare da danna wata number. ta canja muryar ta k'asa k'asa ta fara magana. 

****

Ina komawa na miƙawa Salim kud'in ganin har yanzu da sauran lokaci masu sai da abincin safe bai isa k'arewa ba,
Nace ya kaiwa baba mai koko kuɗin ta na jiya,
Ta bamu na ɗari biyu sai ya siyo mana waina wajen Inna Uwani yace mata Ina gaishe ta na kuma gode da wainar jiya na bashi samirar ta ya kai Mata.

Haka muka rarraba muka ci badan mun k'oshi ba, na adana sauran ɗari biyar ɗin ta 
da rana da ita zan sai mana gari koda kwata sai in sai sugar na ɗari muyi maneji har dare.

******

Nayi mamakin yadda Maryam tace na ɗora abincin rana tun da sauran safiya, dambu tace za ta ci dan haka da na ɗora, kasancewar Abban Salim na gida tace yace shi tuwon shinkafa ya ke so.
Cikin k'warewa na gama dambun zogalen da yaji kayan haɗi ga wani lafiyayyen k'amshi na musamman dake tashi.

Ganin basu fito ba kuma nasan ba ganewa zata yi ba kona ɗiba, sai na d'iba kaɗan a wani filet nasa mai dan tsoron karta zo ta ganni ko yaji ban sa ba na shiga turawa cikin gaggawa. 
Ina cinyewa na wanke filet d'in na maida shi wajen sa.

Shi kuma Abban Salim na ɗora mishi tuwon shinkafar data ce na masa daban, tace   miyar d'anyar ku'bewa zan yi masa,
Nan da nan na kammala na jere. 

Har na kama hanya zan tafi, tace na shiga ɗakin ta na gyara mata.
In har ban manta ba rabon ɗakin ta da gyara yafi sati ɗaya, saboda batama amfami dashi sosai, dan komanta ta tarkata ta maida shi ɗakin Abban Salim.

Ina daga cikin ɗakin ina gyaran naji yana cewa ya fasa cin tuwon tasa masa dambun, tana mita ta zuba masa akan yasan zai ci bai yi magana ba,  bai kulata ba ya hau kai loma.
 Ina jin yadda ya ke zuba  santi, tana jin ya fara ta haushi da faɗan yabo na yake son yi a fakaice shiyasa ya ke wani yabon girkin da nayi, da sauran su.

 Fitowa ta daga ɗakin yasa tayi shiru tana bina da harara, ban dai san yadda suka ƙare ba na tafi ina tunanin halin ta.

Haka kwanaki fa akan wankin motar da na yi sai da suka yi faɗa, akan kawai yace yaji daɗin wankin motar da na yi saboda yadda ta wanku  na gogeta da kyau.
Naji yana faɗa mata ne, dan bama su san ina jiba saboda ina kitchen su kuma suna parlour, ina jinta tana masifar wai yabona ya ke son yi kawai a fakaice da yake wani cewa na iya wankin mota, ina ji yana bata haƙuri ni kam a zuciya ta nace  
_Wankin motar ma dan jarababben kishin ta dan yace na iya sai yazama masifa, to ta amsa tayi in kishin gasken ne sai dai fa tayi faɗan in taga nayi wani abun amma ita bata iyawa, haka fa bashi da ikon yin santin girki innayi duk da kuwa ita ɗin bata iyaba amma bai isa yana ciba ya nuna yaji daɗin abinci ba, duk da kuwa ita kanta ta tabbatar abincin nawa ya isa amai santi amma bata yi bata bari yayi bata qaunar duk wani abu nawa da zai ra'bi Abban Salim sam._

*************

Bayan kwana biyu da safe Ina gama aikin sashin Maryam, na koma na haɗo kayan wankin da na fara wankau yanzu saboda rayuwar sai a hankali, hakan  yasa Inna uwani tabani shawarar in fara wankau, ba dan naso ba na amshi shawarar ta yau ce rana ga farko da na fara, kayan wata mak'ociyar su Inna uwanin ce, ita ta amso min ma dan haka muka shiga wankin nida Salim  yana ɗebo min ruwa yana tayani ɗaurayewa, Umar na wasa da Na'im a gefe muka ji an ƙwank'wasa k'ofa, cikin sauri Umar da ya ke karambani yanzu in an bugo k'aramar ƙofa ya ke d'age da ƙyar ya ke buɗewa, yau ma sai ya tafi da gudu.

Har Salim ya bishi zai hana shi akan shi zai buɗe, na kira shi nace "Barshi ya buɗe mana yaya in  ya iya ai kaima ka huta ko?"

Dawowa ya yi muka cigaba da wankewar 

"Oyoyo Mama"
Da naji yasa na ɗago na kalli matar da ya kira da Mamar, haka kawai in na ganta sai naji gabana ya shiga faɗuwa, a hankali nasa hannu na ɗan dafe gefen k'irjina da ke bugawa.

 Mace ce Kakkaura tana da ɗan haske babu laifi duk da kamar tana ƙarawa da man kanti, 
Babu laifi tana da kyau gwargwado duk da ta ɗan manyanta, 
Sanye take da riga da sket na atamfa sai mayafi data yafa shima ba wani babba bane, 
akwai ta da yawan fara'a kullum in tazo haka ta ke cikin murmushi.

Juyowa nayi na bisu da kallo ganin yadda Umar ya ruk'unk'ume ta, yasa nace  "Umar ka dai barta ta huta ko daga zuwa ka mak'ale ta"
Na ajiye kayan da na matse na nufeta na ɗan rusuna na gaida ta, tana murmushin nan nata ta amsa tana mai bina da kallo kamar yadda ta saba. A da bana fahimtar kallo na ta ke in tana amsa gaisuwa ta, sai daga baya na fahimci hakan ya zama dabi'ar ta, hannu nasa na ɗan gyara wuyan doguwar rigar atamfar da ke jikina wadda wuyan ke faɗuwa saboda ramar da na yi, sannan rigar kanta tasha jiki dan atamfar kalar pink ce da ratsin baƙi, saboda wahala da yawan sawa duk ta fita a kamannin ta tayi wani fari'fari sai dai fes ta ke, saboda bana son ƙazanta.

Ganin ina gyara wuyan rigar yasa ta ɗauke kanta, tana mai murmushi tace
"Salma wanki ake sha haka?" tana mai ƙarewa kayan kallo.

Ina d'an sosa kai nace "Eh Mama"  danni gaskiya bana sakewa gabanta sam dan har ga Allah duk da bawani abun ta taɓa nuna min ba tunda take zuwa gidannan,  Amma sam zuciyata ta kasa yarda da ita duk da duk zuwan da za tai takan riƙo alewowi da biscuits da  kayan k'walama ta kawowa yarana,  tana  musu faran faran sai ma tazo ne suke cin albarka cinta suke samun shiga har farlon Maryam,  harma suci abincin shi yasa suke farin ciki da zuwan ta.

_Ina ruwan yaro shi duk inda ake nuna mai soyayya nan ya ke._

Hankalina na kan Salim
da tunda ta shigo bai ko kalli inda ta ke ba, daga inda ya ke tsaye yana wankin ya ɗan rusuna ya gaishe ta, ya cigaba da wankin shi kamar ba shi ba.

Kallon shi tayi cikin  murmushi tace "Megida yau baka zuwa ka tarbi amaryar taka, sai k'aramin mijin ka bari  ya zo ko ka bar mai ne ka hak'ura da takarar kaci girma?"
Ta k'arasa fad'ar tana mai k'ara bin filin wajen da kallo.

Sai naji ban ji dad'in yadda Salim ɗin yayi banza da ita ba, 
da ya ke sun saba tana wasa da su sosai, tana cewa Salim babban mai gida shi kuma Umar k'aramin mai gida.

Bin Salim nayi da kallo  ganin ko motsawa bai ba, sai sai ma cigaba da wankin shi da ya yi.
Kamar na masa magana sai na fasa ganin ta
Sauke Umar daya kanannad'eta tare da mik'a mai ledar hannun ta tace "Ungo wannan ka shigar muku dashi ɗakivbari naje nayi bikon me gidana"
 Ta nufi inda Salim ya ke.

Duk sai naji kunya ta kamani.
Umar kam ledar ya buɗe  yana tsallen murnar alawowin da ya gani,
ya shiga gwadamin su Yana cewa
"Umma kin gani"

Salim na ganin ta ya tsugunna kawai tare da cewa "Ina wuni"
Kama kafaɗar shi tayi cikin murmushi tace
"Ba k'ara gaidani nace kayi ba nazo biko ne"
Sai naga ya sunkuyar da kai yaƙi kallon ta.

Duk yadda taso ta jashi a jikinta kamar yadda ta saba yi musu, sam Salim  bai bata haɗin kai ba sai ma kakkauda kai ya ke.

Na lura kamar ta  ji ba daɗi, tana yar dariya ta nufoni ta miƙo min ledar da ke ɗayan hannun ta tace
"Kinga ungo wannan garin kwaki ne na gani a hanya, Har zan wuce na tsaya na siya miki kwa samu ku sha ke
da yara"

Miƙa hannu nayi na amsa tare da cewa "Angode"
Cikin zuciyata Ina jinjina Hali irin na matar wai gari ta kawo min,
ko nace bazan amsa ba bani da hujja tunda dai bata taɓa nuna min wani abu na daban ba, kullum tazo tana mutumtani tana jan yarana a jiki.

Hausawa suka ce mai d'a wawa ne, duk da haka ni kaɗai nasan mai na ke ji a zuciyata akan ta,  har yau ina mamakin yadda Mama ke nuna tana sona da yarana, abin takaici kamar makauniya ko bata ganin meke faruwa a gidan ne oho?.

Maganar da tayi ita ta katse min tunani na.
"Mutanen gidan na nan kuwa?"

"Eh tana ciki."
Na amsa mata!.

"Ok ince dai kuna zaman lafiya da ƙanwar taki babu wata matsala ko.?"

 Nayi murmushin k'arfin Hali nace "Babu komai Mama."

"To to to masha Allah haka ake so Dan Allah in kinga tayi wani Abu da ba daidai ba, kece babba ki dinga bata shawara kinji"
 
Ban iya furta komai ba sai gyad'a mata kai da nayi, tace
"Allah ƙara haɗe kanku"
Tare da kama hannun Umar ta tsugunna ta tara hannu ta ɗauki Na'im da shima ke ta 'bangala mata dariya tana cewa "A'a ɗan auta kana nan a ra'be kenan? to taho Mu je ka ji.."

Sunan da ta ke kiran Na'im kenan Auta, inda bansan meyasa ta ke ce mai haka ba, wucewa ta yi da yaran ta nufi sashin Maryam. 

Miƙawa Salim ledar data bani nayi  nace "Maza ka miƙa d'aki ka ji ka zo mu ƙarasa wankin kar rana tayi"

Amsa yayi tare da 'bata fuska yace "Ummanmu nifa wannan Matar haushi ta ke bani, jifa wai gari ta kawo mana dan dai ta raina mu, bayan Aunty bata ci mu kaɗai ne ke cin gari a gidannan"

Rufe shi nayi da faɗan meyasa zai ce yana jin haushin ta me ta mai?  shiyasa kenan yaƙi zuwa wajen ta ya gaisheta,   na kuma ce masa karna ƙara gani ko jin irin kalaman da ya faɗa sun fito a bakin sa,  karya ƙara gwada mata wani abu tunda dai ita bata mana komai ba, ƙarshe na ƙarasa faɗan nawa da nasiha tare da lallashin sa, dan nasan kishin halin da muke ciki yasa shi faɗar hakan.

Hak'uri ya bani ya amshi ledar ya kai d'aki kamar yadda nace, ya dawo  muka cigaba da wankin zuciyata cike da saƙe-saƙe.

Maryam da ke ɗaki jin sallamar Mama taji wani farin ciki ya mamayeta,
a guje ta fito tana cewa "Oyoyo Mam...." Bata k'arasa ba tayi  turus ta tsaya tare da  'bata rai sosai,  Tana bin hannun Mamar da kallo ganin ta d'auke da Na'im ga Umar dake gefen ta shima hannun Mamar cikin nashi, kasa jurewa tayi tace
"Haba Mama yaya za ki kwaso min wannan gayyar tsiyar ki kawo min su farlona, ke kullum kenan in ki ka zo  kamar dole sai sun biyo ki, Haba gaskiya ni fa nagaji da wannan abun" ta k'arasa fad'ar tare da  fincike Na'im,  Ta tangwarar dashi a ƙasa.

Ai kuwa yaro yace baisan zance ba ya tsanyare da Kuka.
Cikin fushi Mama tace
"Dallah matsa kin wani zo kin sa yaron mutane Kuka" ta tsugunna ta ɗauki Na'im d'in.

Nan Maryam ta shiga ƙoƙarin jawo Umar da Shima tsoron ta yasa ya ɓuya a bayan Mamar
 yana rirrik'eta, dan shi yama manta sam da ita saboda murnar ganin Mama, dan tun ranar da ta masa dukan nan bai ƙara takowa wajen ta ba.

Finciko shi take ƙoƙarin yi hakan yasa Mama kama hannun ta tace '
"Ke dakata bana son wannan rashin hankalin naki da gaggawar banza, matsa ki bani waje wadda bata iya bin komai a sannu ba kawai" 

Matsawa baya Maryam d'in tayi tana gunguni tana wani hararar Umar da ya gama tsorata da ita.

Murmushi Mama ta maye fuskar ta da shi ta kamo hannun Umar ɗin da ya ɓoye a bayan ta tace "Kaga angona ba za ta dake kaba" Tare da kamo shi ta zaunar kan kujera, ta laluba jakarta ta ɗauko wata alewa daban ta bashi tace "Maza sha abarka ka ji"

A tsorace ya amsa yana kallon gefen da Maryam ɗin ke tsaye, ta na hararar shi kamar idanun ta zasu faɗo.

Kama Na'im Mama tayi ta jingina shi jikin kujerar da Umar ɗin ke kai, tace  "Yawwa Umar yi wasa dashi maza kaba shi yasha alewar shi ma." 
Ta juya ta maida kallon ta ga Maryam tace
"Ke kuma muje ciki in kin gama tujarar" ta miƙe ta wuce ta ta nufi hanyar d'akin Maryam ɗin. 

Cikin sauri Maryam ta daka tsalle tasha gaban ta, tare da sa hannuwan ta ta tare bakin ƙofar da Mamar zata shiga babu kunya  tace
 "Gaskiya Mama muje can d'akin,  dan Mijina na ciki yana barci."

Sakato Mama tayi ta na mai Ƙurawa Maryam ido, cikin mamakin abinda tayi can ta nisa tace " Shine me dan Mijin ki na ciki? kika wani yi tsalle da sauri haka kika tare ƙofa inna shiga mene?"

 'Bata rai Maryam tayi ba tare da ta matsa ba, ta shiga Harare harare  tare da gunguni ta na turo baki tace "Nidai kawai muje can ɗin nace miki hankalina zai fi kwanciya, kinsan ai maganganun da za mu tattauna bai dace a nan ɗin ba? kuma bai kamata yaji abinda zamu fad'a ba"

Wani miskilin murmushi Mama tayi irin na manya tace "lallai Maryam" tare da k'wafa tace "Mu je can ɗin" Ta juya ta shiga juya shirgegen k'ugunta ta nufi ɗaya bedroom ɗin.

Bayan na ta Maryam ta shiga bi da kallo tana mai banka mata harara, ta ja tsaki ciki'ciki tabi bayan ta suka shige d'akin.

Ko Zama ba tayi ba ta kalli Mama tace
"Wai ke meyasa ki ke min hakane Mama tsakani da Allah, kin dai san ba ƙaunar ganin yaran nan na ke ba amma sai ki wani kwaso min su haba Mana" 

 "Duk jarabar ki dai Maryam kya bari na zauna ki kawo min ruwa nasha, kinga sai ki cigaba da tijarar taki yadda ki ke so ko?" Tace hakan tare da yakice   gyalen da ke kafaɗar ta, hakan yasa d'inkin jikin ta ya bayyana.
Sanye take da riga da sket na atamfa d'inkin ya matse ta kamar wata budurwa budurwar ma irin marasa ta idonnan. Kasancewar ta me jiki sai hakan ya ƙara fallasa sirrin halittar ta daga saman rigar ta matse hakan ya taimaka wajen fito war mamanta duka suka bayyana.
  Nufar bakin gadon tayi ta zauna ta na bin ɗakin da kallo.

Tsaki Maryam taja saboda haushin wannan Halin na Mama tana kallon ta tace 
"Wai Mama har yanzu baki daina irin wannan shigar ba, Haba infa mutum ya girma yasan ya girma sam hakan bai dace da ke ba wallahi"
Ta k'arasa tare da kallon gefe ta na gunguni ciki-ciki.

Cikin d'an d'aga Murya Mama tace
"Maryam meye damuwar ki da shigar da nayi ne? To in za ki daina samin ido ki daina tun wuri,  dan in kinga na daina shigar nan numfashina ne ya yanke. Ni kinga  ki je ki kawo min abinda za ki kawo min muyi mu wuce rana na ƙara yi"

 Tsaki Maryam taja tace
"Ni dai gaskiya in za ki na zuwa gidana ki daina sako wad'annan kayan, haka kawai kiyi ta zubarwa da mutum mutumcin"  ta juya ta nufi Ƙofar fita.

"Dawowa za ki yi ki dake ni fitsararriya wadda bata san halacci da mutumci ba, Ni d'in ma halin kishin naki za ki nunamin na banza da wofi, wawuya mara wayo inba ni d'in ba aida yanzu wani labarin akeyi sha'shasha"

Ita dai Maryam na jinta ta na 'ba'batun fad'a ta wuce ta barta.

Dawowa tayi da d'an faranti wanda ke d'auke da lemon roba guda d'aya da ruwan roba d'aya, ta dire ta na mai bin bayan  Maman da kallo yadda ya fito a cikin sket d'in d'as, dan ta tarda ta tsaye a tsakar d'akin ne ta juya  ta na kallon d'akin.

Jin shigowar Maryam d'in yasa Mama ta juyo  ta na wani munafukin murmushi tace "Wato dai Maryam nan d'akin ya zama shi kaɗai ba kowa? baki mora ba kuma ba zaki bari na dawo ba tunda ba wani abu ake a cikinsa ba, d'akin ki daban na mijin ki daban sannan kinga ga kayan d'aki ga komai babu abinda babu amma kin hana ni in dawo nima na dinga jin dadin,  Kin barni a wancan mataccen gidan, sai kace  ba dani ake fafutukar ki ji daɗin ba.
I ba ke ba duk irin matsayina a wajen ki, ace ina can ina shan wahala babu ko wutar Nepa a gidan na, ke kuma kina cikin AC haba Maryam sai kace baki san halacci ba."

Nan-da nan Maryam ta  had'e rai, ta wani d'aga mata hannu tace  "Ni kinga  Mama nasha fad'a miki ba yau ba kibar maganar nan ba zai ma yiwu ba, So kike a zage mu bayan uban zagin da muke sha, Sannan ni kinsan bazan jurewa wannan halin naki ba, kuma ni gaskiya ba zaki zubar min da mutumci ba a idon Mijinaba, dan dama mutanen unguwar nan haushi na suke ji salon su k'ara samun abinda zasu aibatani, gwaramin kina can d'in dai ni Ina nan"

K'wafa Mama tayi ta karkata kai ta kalli Maryam d'in shek'ek'e tace 
"Har wani mutumci ne da ke dama Maryam?" Tabi flet d'in da ta aje mata da kallo tace "Kina nufin shine abinda kika kawo min kawai babu wani d'an abin ta'bawa, Hmm halin dai na nan har yanzu baki canja shi ba, Sai  shegiyar rowa da son abin duniya"

"Ni kinga Mama kefa matsalolin ki basa k'arewa, to me dafa abincin ma bata zoba tukun kuma nasan kema kin karya ki ka fito, bayan haka ma ai kinsan lokacin d'ora abincin rana baiyi ba duka fa yanzu k'arfe 10:30am sauran breakfast d'in mijina kawai ya rage,  in ya tashi zai ci kibari muje mu dawo in yaso kafinnan ta gama abincin kyaci"

"A she kuwa baki shirya mu tafi ba, dan nasan zan'zo nan ne nak'i tsayawa na sha kokon da Ladidi ta dama, Saboda nasan zan samu kyakykyawan kari a gidannan, Amma shegiyar rowa kina son yimin buk'ulu maza ki had'o min ko shayi ne ki soya min ko k'wai hud'u ne, nasan ba zaku rasa biredi ba ki kawo min"

"Cab Mama har k'wai hud'u gaskiya ni kinga bazan iya wani  soya  miki k'wai har huɗu ba, Dan ni na manta rabon da na shiga kitchen, bari na kira miki Salmah ta soya miki kuma gaskiya biyu za'a soya ina za ki kai k'wai har hud'u?" Ta k'arasa tare da nufi hanyar waje.

Ta na fita ta tarda Haidar ya fito daga d'aki sanye da kayan shan Iska, da alamar daga wanka ya fito.

Cikin hanzari ta nufe shi ta na fad'in
 "A'a Baby ka tashi?" tare da shigewa jikin shi ta kwantar da kanta a k'irjin sa.
Hannayen sa yasa ya k'ara rungumota ya kai bakin sa daidai kunnen ta cikin magana k'asa k'asa yace
"Na tashi Baby, me Kika tanadar min ne?"

Wani farin ciki ne ya ratsa ta, ta k'ara shigewa jikin sa tana wani fari da ido tace
"Komai ma na tanadar maka Baby"
Dan ta riga data San kwanan zancen da abinda ya ke nufi.

Jin Yana k'ara jawota ta narke murya tace
"Baby muna da bak'i a gidan fa yau"

'Dan sakin ta yayi tare da juyo da fuskar ta daidai tashi yace
"Wace ta zo?"

"Mama ce ta zo"

Kafin ma ta rufe bakin ta Sai ga Mamar ta fito.
Tana ganin Haidar ta shiga gyara zaman rigar ta harda su canja tafiya, tun kafin shi ya gaishe ta tace
"Malam Haidar an fito kenan? Ina kwana"
Tayi kamar zata durk'usa masa.
  
Amsa wa yayi yana k'ok'arin raba jikin shi da na Maryam, Saboda kunyar ganin Mamar.
 Ita kuwa sai k'ara shige masa ta ke yi, duk da kuwa taga fitowar  Mamar.

Ta'be baki Mamar tayi ta d'auke kanta daga kansu, ta k'arasa inda su Umar ke zaune  suna wasansu, Ta zauna ta d'auki Na'im ta d'ora cinyar ta ta shiga musu wasa kamar ta manta su Maryam na farlon.

Cikin wani 'bacin rai Maryam ta saki Haidar,
Ganin rainin hankalin Mamar da ta zauna a farlon bayan tasan Mijin ta na nan ta fito a haka.

 Cikin ɓacin rai ta nufi Dining ɗin cike da jin haushi ta shiga zubawa Haidar soyayyen dankali da k'wai, sai stew da taji zallar hanta.

Yau da kanta taja masa kujerar zama ya zauna Yana ci cikin Jin dad'in kulawar da ta nuna masa, dan Haidar mutum ne shi mai son ya ga ana nuna masa kulawa a fili.

 Badan ta so ba ta zubowa Mama sauran a filet ko k'wan bata had'a mata dashi ba, Dan dai ta riga da ta gani ne da ba tayi niyar bata ba.
Haka ta kai ta dangwarar a gaban ta  tare da aje mata guntun biredin da ke leda ta galla Mata harara.

Cikin k'asa da murya Mamar  tace "Au da wai akwai abincin a gidan  ki ka hanani dan bak'ar rowa?"

Banza tayi da ita tare da shigewa d'aki don ta shirya su yi su yi subar gidan.

Cikin mintuna kad'an ta fito cikin shirin ta na doguwar riga da ta kamata  daga sama, daga k'asan kuma an sake ta sai wani d'an figigin  gyale da ta yafa akan kitson attachment  d'in kanta, sai baza k'amshin turaren da ta bulbula ta ke har wani hawa kai k'amshin ya ke.

Lokacin Haidar ya kammala cin abincin, yana zaune ya jingina da kujerar tebur d'in yana danna waya.

Ita ma Mamar ta gama yaran ma sun wuce abinsu, ta na zaune kamar an dasa ta sai kalle kalle take.

Cikin takun ta ta k'araso ga Haidar, ta tsaya a bayan kujerar da ya ke zaune ta zura hannayen ta a wuyan sa tare da kwantar da kanta a bayan sa tace
"Baby zamu d'an fita da Mama  yakamata kai ma ka fita, kasan ba na son barin ka gida kai kad'ai"

Cikin rashin damuwa yace 
"To sai kun dawo ni ba fita zan yi ba, Ina son zan d'an huta kinsan yau Weekend"

Cikin d'an 'bata rai tace
"A a gaskiya ka tashi ka fita ya ma za'ai na barka gida? Gidan dake cike da munafukai fal  ni dai ka tashi"

Tashi yayi yace
"Kin dai san  bata gabana ke kike damun kanki ki?"

Duk yadda yaso hutawa bata barshi ba har sai da taga ya rigasu fita tukun suka shirya suka fita ita da Mama a motar ta.


🥰MAMAN  ƊAN  ALBARKA CE 🥰 ✍️✍️