KOWA YAƘI JI

Chapter 4

by @mamananalbarkace777

FREE PAGE4️⃣

Bayan doguwar tafiyar da suka sha, suka tsaida motar a bakin wani daji mai yawan bishiyu, anan suka bar motar a hankali suka fara kurdawa cikin dajin suna ratsa kwazazzaɓai da tsaunika. 
Sai da suka sha tafiya ba kaɗan ba sannan suka iso wani dogon tsauni a jigace, duk da irin hakin gajiyar da suke haka  suka nad'e k'afafu suka fara hawa tsaunin da k'yar suka haye shi.

Tafiya kaɗan sai gasu gaban wata bukka ita kad'ai k'wallin k'wal a tsakiyar dokar dajin.
Da shigar su  suka zube suka kwashi gaisuwa, cikin girmamawa Mama ta fara masa kirari, 
Ita kuwa Maryam sai faman toshe hanci ta ke tana harare harare saboda bala'in doyin da wajen keyi, shi kanshi bokan ba son had'a ido take da shi ba saboda muninsa.

Zaune ya ke a kan wani jan buzu, ba'ki ne d'an lukuti  sai uban tumbi  shirgege jikin sa babu kaya  sai wani d'an k'yalle kamar bante daya rufe gaban shi dashi, sai layu da guraye dake d'ad'd'aure a kowanne sassa na jikin shi  kan shi kam san babu kyan gani, cike ya ke da wani uban gashi daya cikurkud'e da gani kasan baya ganin ruwa.
fuskar nan a tur'bune bak'a k'irin sai jajayen hak'oran shi babu k'yan gani, Da idanun shi k'wala'k'wala abin tsoro.

Juyawa yayi ya watsa kallon shi kan Maryam da ke faman toshe hanci, cikin daka tsawa da muryar shi da babu dad'in sauraro yana dad'a zaro ido yace
 "Hattara gafalalliya ba'a toshe mana hanci anan, maza ki cire hannun ki ki mana bayanin abinda ke tafe da ke"
Ya d'aga wata sandar da ke gefen shi tare da bugata da ƙarfi,
Nan take wata ƙura ta tashi.

Bata san lokacin data cire hannun ba  jiki na rawa, cikin in'ina ta buɗe baki amma sam tsoro ya ta furta komai.

Cikin tsawa yace
"Fad'a min me kike so a ƙara mata bayan raba tsakanin su da aka yi?"

 Mama ce tayi ƙarfin halin magana ganin Maryam ta kasa cewa komai, ta sunkuyar da kanta tace
 "A mata gafara mai girma gamji"

Cikin ɗaga kai tare da bud'e ƙofofin wargajejen hancin shi yace
"Ina ji ta buɗe baki tayi bayani da kanta"

Dungurin ta Mama ta shiga yi cikin ƙasa da murya tace
"Ki masa bayani mana"

Cikin tsoro-tsoro ta fara magana
"Boka so nake a ƙara musu farraƙu a tsakanin su ya zamana baya son ko ganin ta, dan na fara ganin tausayin yaran a idon shi ina son a kauda wannan tausayin, ni inda halima asa ya koreta har yaran na daina ganin su baki d'aya dan ko kud'in abincin daya ke basu alamar yana tunawa dasu kenan.
Ina tsoron watarana ya dawo da hankalinsa gare su."
Ta ƙarasa faɗar tana wani sunkuyar da kai, dan har lokacin jikin ta rawa ya ke.

Ɓaɓɓakewa yayi da wata iriyar dariya ta rashin imani, can kuma sai ya had'e fuska murtik kamar bai ta'ba dariya ba, sai da yayi yan dube-duben sa ya shiga wasu sambatu tukun ya ɗago yace
"Abu ne mai wuyar faruwa kamar yadda nasha fad'a miki, saboda ƙarfin son da ya ke mata da kuma irin yadda bata wasa da ibada shi yasa aikin namu ya samu rauni. Amma yanzu zan iya miki aikin da zai ƙara tsanar ta, aiki ne mai zaman kanshi sai kin nemo gashin kanta da farcen ta na ƙafa da hannu da shi za'ai aikin"

Kallon kallo suka shiga jin abinda yace, Maryam ta daure tace
"Yanzu boka ina zan samu gashin ta da farcen ta? matar da kullum bana sanin tana kitso ma ko bata yi, rabona da ganin gashin kanta inaga tun ina Amarya, Gaskiya dai a canja dan farcen ma bansan inda zanne moshi ba, ita da kullum farcen ta tsaf ya ke a gyare"

Cikin sauri Mama ta   dungureta alamar ta yi shiru,  ta maida kallon ta ga Bokan cikin tsoro dan kar yace Maryam ta masa rashin kunya tace
 "Kayi hak'uri me girma Gamji za'a nemo su duka"

Cikin 'bata rai Maryam  ta ke kallon Mamar tana son tambayar ta tayaya za'a samo gashin da farcen?  amma babu halin magana dole ta yi shiru.

Haka suka masa sallama dan yace dole sai sun zo da abinda yace tukun zai musu aiki, bisa dole suka ajiye masa kuɗi kamar yadda ƙa'idar wajen take suka tafi.

A hanyar dawowar su Maryam d'in ke tambayar Mamar 
"Yanzu ya za'ai asamo gashin da farcen?"

Cikin nuna rashin damuwar ta tace 
"Kibar komai a hannu na, aike matsalar ki rashin tunani da dogon tsinkaye za ki ga amfanin tunani da kuma yadda ake cin mak'iyi da yaƙi cikin ruwan sanyi"

Cikin rashin damuwa ta Ta'be baki tare da d'age kafad'a,  ta kauda kanta daga kallon Mamar da ta ke ta maida hankalin ta kan tuk'in da take, a gajiye ta ke sosai yanzu kusan k'arfe  6:30pm shegen nisa ne da k'auyen.

Duk yadda Mama taso ta wuce gidan Maryam a cewar Mamar tana so tayi wanka ta huta,
Maryam tace bata isa ba  ta sauke ta a gidan ta ba, dole ta haƙura da ƙyar ta bata dubu biyu shima sai da ta roƙa tace kayan abincin ta ya ƙare taso ma ta bari ta sauka gidan nata ko abinci ne taci ta huce gajiya amma taƙi.

Dole Mamar ta sauka ta na binta da wani irin kallo, tare da sakin wani murmushi da ita kad'ai tasan ma'anar kayan ta.

Bayan ta sauke Mama ta kusa isa gida kira ya shigo wayar ta.
Ganin mai kiran cikin murmushi ta rage gudun motar, a hankali ɗaga kiran tare da kara wayar a kunnen ta tace
"Ya akai ne na wajena?"

Daga ɗayan ɓangaren mutumin yace
"Kina ina ne haka?"

"Ina hanyar komawa gida ne akwai wata matsala ne In zo?"

Cikin dariya yace
"Akwai matsala kam Mero kizo kawai yanzu"

Itama dariyar tayi tare da dukan sitiyarin motar tace "Karka damu zan zo dan na gaji ma, amma tunda kiran kane kaga ai ban isa na tsallake ba"

"To shikenan ina jiran ki"
Aka ce daga can.

Nan ta juya kan motar tare da nufar wata hanya, wani babban hotel ta tsaya tukun ta zaro wayar ta ta kira mutumin, nan yace mata yana zuwa zai fito yanzu.

Can sai ga wani Mutum ba'ki kakkaura ya fito
a k'alla zai kai shekara hamsin, sanye ya ke da riga da wando na shadda harda malun-malun.
Ya ƙaraso wajen ta yana murmushi, ita ma murmushin ta maida masa, ba tare da ɓata lokaci ba suka rungume junan su babu kunya duk irin yawan mutanen dake kai kawo a wajen,
Hannun ta yaja suka shige ciki suna manne da juna.

Basu fito ba sai wajen ƙarfe tara na dare, shi 
ya rakota har wajen motar ta sai da ta tafi shima ya shiga motar shi suka fice tare.

Koda ta dawo gida ta tarda haidar ya dawo yana zaune a farlo.

Ganin yadda ya ɓata rai, yasa ta fara zana masa ƙaryar sun biya gidan Mama ne kanta na ciwo.
Badan ya gamsu ba ya ƙyale ta.

Kai tsaye ta wuce ɗaki zuciyarta duk ba daɗi, dan tabbas aikin da akai akan Haidar yana daf da gama lalacewa.
Amma zata jira taga yadda Mama zata samo abinda aka ce su kawo.

*****
A kwana a tashi a wuya a wajen Allah.
 Yau wajen sati biyu kenan babu laifi Haidar ya d'an rage takura min da wasu ayyukan, har mamakin hakan nake.
Maryam kam babu abinda ya canja daga irin wulaƙancin da take min, sai ma abinda ya yi gaba.

 Cikin kazar'kazar d'ina nake aikin goge farlon dan bana son  doyar dana d'ora a wuta ta k'one,  yau sakwara gimbiyar gidan tace a mata  tunani na yadda zan daka sakwarar
dan ina jin jiki in nazo dakata, gashi yau ba wata cikakakkiyar lafiya na nake da ita ba, kuma nasan tana sane tace na mata dan mugunta da sanyin safiyar nan tace da ita zata karya.

Duk abinda nake hankali na kan yarana, dan nabarwa Salim Na'im ya kula da shi, Umar kam yana can wajen bakin get ya na wasan shi.

Bayan na gama goge gogen na wuce kitchen ɗin na duba doyar dana ɗ'ora, na tarda har ta dahu tayi luguf, ga doyar irin me garin nan ce sai tayi fara tas gwanin sha'awa. A rayuwata ina son doya  musamman in tana da gari, gashi  dama na kammala miyar alayyahu da agushi da taji bushashshen kifi, har na fara zuba doyar a turmi sai nayi sha'awar naci duk da bana taɓa musu abincin in nayi kamar yadda Maryam tasa doka, kuma shima me gidan ya jaddada amma sai na tsinci kaina yau da son in taɓa, da dama bawai bana jin sha'awar abincin dana ke bane kawai dokar suce tasa bana ta'bawa, inda nasan koda me aiki ka aje ba zai yiwu tayi abinci ba a hanata ci.
 Amma ni sai nayi wani lokacin k'amshin kawai shine rabona,  dan in y'an rashin mutumcin suna kanta tsaye min take a ka tace karna ta'ba gwara na safe ma watarana ina samun ɗibs.

Wani ɗan filet na ɗauka na zuba doyar da nufin nasa miya naci, sai kuma na yi tunanin kaiwa yara suma su ci doyar yau su canja bakin su.
Ɗibar mana doyar nayi a wata ƙaramar kula na aje, ina ji a zuciyata hakan shine dai-dai ai ubansu ne ya nemo dan na d'iba ba haramun bane. 

Ina gama daka sakwarar na  jere a Dining na koma kitchen da sauri na d'auko kular da nasa  doyar na maza na zuba miyar ko kifin ban ta'ba mata ba.
Sai da na leƙa farlon na  duba'naga babu kowa, cikin hanzari na  nufi hanyar fita daga farlon saura kad'an na fita naji muryar Maryam tace
"Keee ina za ki je min da kula a hannu?"

Ai bansan lokacin da na saki kular hannu na ba na juyo da sauri ina mai  kallon ta,
 tsaye take bakin ƙofar bedroom ɗin Abban Salim, sanye take da wata yar figigiyar rigar barci fara sam rigar bata da maraba da tsirara.
Da sauri nayi ƙasa da kaina zuciyata na bugawa.

 Cikin ɗaga Murya tace
"Sata kike min dama Salma?" Ta nufo inda nake ta cigaba da faɗin 
 "Shi yasa kullum kafin mu tashi kin tafi kenan? ashe dai kwasar min abinci ki ke saboda k'asurgumar 'barauniya ce ke ko?. to yau Allah ya toni asirin ki!"

A rayuwata na tsani cin mutumci da tozarci, shiyasa nake matuk'ar k'ok'ari wajen ganin na kaucewa duk wani abu da zai sa raina ya sosu.
 Ace bayan uwar wahalar dana ke sha harda cin mutumci, ai sai abin ya min yawa kalmar 'barauniya da ta jefeni da ita ita tafi komai 'batamin rai.

Bansan ta ƙaraso wajena ba, sai da naji saukar wani rikitaccen mari wanda sam banyi zaton saba.
A gigice na dafe kumatuna da nake jin kamar ba ajikina yake ba, zagina ta shiga yi cikin hayagaga
 "Dan uwarki ina miki magana za ki wani tsaya kina kallona, yau Allah ya toni asirin ki munafuka." ta shak'emin wuya ta gwarani da bango ta fara dukana, wai sai na faɗa mata tun yaushe nake satar musu abinci ina kaiwa shegun yarana.

Kasa k'watar kaina nayi a hannun ta, na dai sa hannu ina k'ok'ari wajen ganin na cire hannun ta a wuya na dan  muguwar shak'a tamin, abinka da wadda tafini jiki sannan k'arfin mu ba d'aya bane.

Da ace lokacin dana ke Salma tane nasan koda ban rama ba tofa zan k'waci kaina, hawaye ne kawai ke sintiri a fuskata bawai zafin shak'ar da ta min bane kawai, hards zafin kalmomin da ta ke jifana dasu suke sani kuka. 

_Wai akan abincin da nima ina da hak'k'i akan shi take cemin 'barauniya?_


Cikin barcin da ya ke ya ji kamar an doka mishi guduma akan shi, a zabure ya tashi zaune tare da kai kallon shi d'akin da idanun shi da ke ganin dishi'dishi, ga  kanshi da ke masa wani azabar ciwo kamar zai rabe gida biyu, hannayen sa yasa ya dafe kan tare da rintse ido ko zai ji sauk'i, amma ina sai ma ji da ya ke kamar ana ƙara buga masa guduma akan.

A hankali ya kasa kunne yaji kamar hayaniya a farlo, muryar Maryam ke tashi cikin masifa tana zage'zage.

Da ƙyar ya yink'ura ya tashi saura kad'an ya faɗi ya dafe gefen gadon, ya kai kallon shi kan gadon daya ke kamar bola duk kaya ne barbaje, neman jallabiyar daya cire ya ke ganin bai ganta ba yasa ya juya ya fara duba ƙasa, can ya tsintota bayan gado fasa d'aukar ta yayi jin hayaniyar na k'ara yawa. Cikin layi ya nufi wardrobe ya d'auko wata jallabiyar ya d'ora akan boxes d'in dake jikin sa, ya shiga bin bango ya nufo hanyar farlon.

Marina kawai take tana  kaimin duka ta ko'ina tana aibata ni da kalmomi munana, ni kam har zuwa lokacin hawaye ne ke sintiri a fuskata, ina dana sanin ta'ba doyar dan bana son tashin hankali ko kad'an.

Jin muryar Abban Salim mu ka yi, hakan yasa ta dakatar da dukana da take ta muka juya tare muna kallon shi.

Cikin wata murya wadda tayi laushi lu'bus kamar wanda ya tashi daga jinya yace 
"Meke faruwa ne  nake jin hayaniya Maryam meye haka kika shak'eta?"

Jin sunan ta a bakin shi ya bata mamaki, amma sai ta ƙara had'ani da bango ta shiga girgizani tare da fara rattabo masa bayanin abinda ya faru.

Ga mamakina sai naji yace
 "Sake ta mana haka"

Na yi zaton shima zai zazzagenin ne ya aibatani kamar yadda ya saba, sai naga sa'banin haka.
 ita kuwa jin kalmar ta sake ni da yace tasa cikin masifar da ke cinta tace bazata sake ni ba, na riga na gama saddak'awar kawai kashe ni zata yi yau.

"Ki sake ta nace ko" ya fad'a da d'an fad'a'fad'a duk da kuwa muryar tashi har lokacin a ciki'ciki take.

Sakin baki da hanci tayi tana kallon shi ganin yadda ya;ke fad'a akan ta sake ni.

Ni kaina mamakin nake, ganin ta sake nin batareda tasan tama sakenin ba, saboda kaɗuwa.

Sakin baki tayi tana kallon shi kawai, yana tsaye jikin kujera ya dafe gefen kujerar hannun shi d'aya dafe da kansa har zuwa lokacin jin ciwon kan ya ke ga jiri da ke d'ibar shi.

Ai ina samun dama da ta sake ni na nufi hanyar barin parlourn ko gani ba nayi sosai 

Cikin wata tausashashshiyar murya naji ya kira sunana wanda rabon dana ji sunana a bakin'sa nama manta.

"Salma dawo ki d'ibar muku abincin da zai ishe ku kije kuci keda yara kin ji" 

Ban ko juyo na lalle shi ba, burina shine kawai nakai d'aki na nemi ruwa nasha dan mak'ogwarona a bushe nake jinshi sannan na nemi waje na kwanta.

 Cigaba nayi da tafiya 

Cikin tsawa'tsawa yace 
"Ki dawo nace ki d'ibar muku abincin ko" 

Hakan yasa ni juyowa da sauri dan jin tsawar nayi har tsakiyar kaina.
Maryam ce tayi tsalle ta tare ƙofar tace
"Wallahi wallahi kayi kaɗan ka wulak'anta ni ni, ni za ka kawowa rainin wayo, ta shigo ta d'iba bayan satar da ta min wallahi baka isa ba,
nan tafara zazzaga ruwan bala'i dan ita mamaki ta ke yau Haidar ke dakatar da ita akan Salmah meke faruwa kenan ?

Ganin yadda tayo kaina yasa cikin sauri na fice na nufi d'akina ina ƙara shafa wuyana da ke min wani irin rad'ad'i.


🥰MAMAN 'DAN ALBARKA CE🥰✍️✍️