Chapter 5
FREE PAGE5️⃣
Ba karamin danbarwa suka sha da Maryam ba akan ita ya barta ta fita ta daki Salmah, shi kuma ya hana ta babu irin zage'zagen da ba ta yi ba akan ya barta.
Yayi burus ya k'yaleta ya rufe ƙofar farlon yasa key d'in a aljihun jallabiyar sa, ya koma kan kujera ya zauna dafe da kanshi daya ke ji kamar zai rabe biyu saboda tsananin ciwon da ya ke masa.
Haka tasa shi gaba sai tijira ta ke masa, ita sai ya bud'e k'ofa sannan yamata bayanin meye had'in shi da Salma da har zai bata izinin tafiya.
Ci kanki bai ce mata ba hayaniyarta ce kawai ta dame shi.
Ganin yaƙi kulata yasa ta nufi ɗakin ta tana zage'zage, Yana ganin ta shige ya yi saurin binta ya rufe ƙofar, da sauri ta juyo ta dawo bakin ƙofar tana faɗin
Ya zo ya buɗe ƙofar cikin ihu cike da tijara,
ita babban tashin hankalin ta zargin da ta ke lik'inta ne ke shirin 'ballewa, da kwa ta tagayyara ta shiga uku
In haka ta faru,
Shi kuwa ko kula ta bai yi ba ya bar wajen.
Ina shiga ɗaki na maza na nemi ruwa na kafa kai sai da na shanye kofi guda tas, tukun na nemi waje gefen tabarma na zauna ina ayyanawa a raina koma mene ne dole na nemi mafita ba zai yiwu in zauna acigaba da haka ba, kar watarana ta nakasta ni nasan koma ta kashe ni babu wanda zai bi ba'asi akan hakan, yo wama yasan dani bare ya damu dan an kashe ni, wa nake dashi da zai tsayamin gwara na nemawa kaina mafita tun wuri.
Ina nan zaune ina sauke numfashi sai ga su salim sun shigo a guje,
Salim ne a gaba Umar na biye da shi yana kukan ya bashi abin shi, shi kuma yaƙi tsayawa har sai da ya ƙaraso gabana.
Ya ɓoye hannun shi a baya yana faɗin "Wallahi bazan baka ba duk abinda za ka yi"
Duk da yadda nake ji ganin tak'addamar tasu taƙi ƙarewa yasa na tashi dak'yar nace
" Wai meye ka amsar masa ne Salim? kabashi abinshi ya wuce yayi wasan shi kasan dai halin shi inya fara wannan kukan nashi bai san yayi shiru ba bana son damuwa"
Salim da ke ƙara ɓoye hannun shi yace
"Umman mu wai fa kinga abinda ya je ya hak'o wajen shegen wasan shi a bayan famfo, shine nagani na ƙwace yake kuka sai kace wani mace wai zai yi wasa da shi, ai dai Umman mu babu k'yau kwaikwayon mata ko?"
Bin hannun shi daya nuna min abun na ke da kallo a tsorace ina jin jikina na wata iriyar karkarw, har wata zufa zufa nake ji na karyo min.
Wata yar baby ce ta roba da aka nannaɗe hannayen ta zuwa k'irjin ta da k'afafun ta da wasu irin zararruka daban'daban, fuskarta baƙaƙirin duk da kuwa jar k'asar data ɓata jikin ta, A tsorace na daka masa tsawa nace
"Dan ubanka kai ma yarda ta"
Jikin shi na rawa ya saketa cikin ikon Allah ta fad'o gabana, a hankali na tsugunna na ƙurawa y'ar tsanar ido, y'ar tsana ce dai irin ta yara normal,
Sai da na kula sosai naga harda wasu rubututtuka da akai da larabci a cikinta,
bandai fahimci abinda aka rubuta ba saboda yadda ƙasar ta rufe jikin yar tsanar,
Faɗa na fara musu sosai cikin wani irin k'arfin hali dana aro saboda nima na gama kaɗuwa.
Ganin yadda nake kallon ta a tsorace yasa jikin Salim fara rawa ya fara kuka yana faɗin
"Allah Ummanmu sai da nace ya yarda yaƙi"
yana y'arfa hannu yana ja baya a tsorace.
Salma saboda tsananin tashin hankalin da ta gani da tsorata da ta yi bata bi takan suba ta d'auko makwashin shara saida tayi addu'o'i da dama tukun tayi bismillah tasa tsintsiya ta d'auke y'ar tsanar, cikin ƙarfin hali ta fice da ita, ta kuma ce musu karsu biyota.
Ta gama fahimtar komai ba aikin kowa bane face Maryam, godiya ta dinga wa Allah akan nuna mata gaskiya da yayi, ta dad'e tana addu'a akan Maryam Allah Ya tona asirin abinda ta ke.
Sai gashi yau yara sun bankaɗo sirrinta,
Duk da bata da tabbacin shi kenan amma tana fatan samun sauƙi akan lamarin.
Bayan tankin ruwa ta je wajen ciyayi ta ajiye yar tsanar tare da bismillah ta ƙyasta ashana akan ta aikuwa ta kama da wuta bal-bal, addu'o'i ta shiga jerowa ganin yadda wutar ke ruri kamar ana k'ara mata fetur.
Saida taga ta k'one k'urmus tukun ta juyo ta dawo d'akin, ta tsatstsaresu akan sai sun nuna mata inda suka ciro.
Haka ta sasu gaba sai da suka kai ta har wajen Wani ramin suka nuna mata, da sauri ta dakatar dasu tace su tsaya a baya, ta ƙarasa bakin ramin cikin tsoro zuciyarta na wata iriyar bugawa.
Sai dai bata ga komai cikin ramin ba,
ta juyo ta kama hannuwan su tace "Muje"
Harta juya za su bar wajen sai taga wani abu kamar ya lek'o daga ramin, duk da tsoron da zuciyar ta ke ciki ƙarfin addu'ar data ke ne kawai ke taimaka mata ta saki hannunsu tace
"Ku je ɗaki gani nan zuwa"
Ta koma ta tsugunna sai taga wani abune ya ɗan leƙo, wani ɗan icce tasa ta tono tana jawowa taga wani takalmi ne silifas yasha rubutu da ayoyin Allah a bayan shi, sai dai an tsinke katanar takalmin.
Wani tsoron Allah ne ya daɗa kamata ganin irin yadda aka wulak'anta ayoyin Allah akan neman duniya ta kuma san tabbas Maryam ce,
Lallai Maryam tayi nisa bata san abun nata yayi tsauri haka ba duk da tasan tana aikata asiri,
Lallai ya zama dole ta mik'e tsaye ta ƙara dagewa da addu'a tabbas rayuwar su na cikin had'ari ita da yaranta.
Rasa yadda za ta yi tayi kawai ta nemo wata leda da ta gani a gefe, ta sa a ramin tasa wuta kamar yadda tawa waccan,
abin mamaki wata iriyar k'ara wutar ta ke tana ruri kunnen ta sai ya dinga jiyo mata kamar maganganu ke fitowa ta cikin wutar,
Tsoron ta ya ƙara hauhawa ba tasan lokacin da hawaye ya fara zubawa a idon taba tana ƙara girmama Ubangijinta, tabbas tasan shine ya sota da har yasa hakan ta faru,
haka ta baro wajen jikin ta a sanyaye.
Dawowar ta ɗaki jigum tayi kawai ta rungume yaran ta na zubda hawaye, tana tunanin rayuwa da kuma irin halin rayuwar da suke ciki jinta take gaba ɗaya kamar ba ita ba.
Suna haka taga Haidar tsaye a bakin ƙofar kamar an jefo shi, hannayen sa d'auke da manya manyan kulolin da ta gama abincin ɗazu.
A hankali ya fara takowa ya shigo ɗakin, yaran na ganin shi suka k'ank'ame ni Umar kam har yafi Salim jin tsoron shi,
Dan Salim gefena kawai ya ke zaune.
Nima kaina binshi nake da kallo cikin tsananin mamaki ganin shi a ɗaki na a wannan lokacin, a yadda ya ke kallona da yanayin sa kamar ba shi ba, gaba ɗaya wani irin kallo ya ke bina da shi kamar yaga sabuwar halittar da bai taɓa gani ba, kallo ne da rabon da yamin irin shi tun ina Norryn Haidar, tun bai d'agowa kanshi batun ƙarin aurannan ba.
Lallai na yarda addu'a babu abinda bata magani inhar zaka jure tabbas watarana sai labari, ba wai ka dinga addu'a ba kana ganin Ubangiji bai amsawa kace bari ka dai na, ita addu'a muddin kayi ta bata fad'uwa ƙasa banza in kaga abinda ka roƙa baka samu ba, to hakan ba alkhairi bane gareka sai Allah ya musanya maka da wanda zai zamo alkhairin gareka ta hanyar dama baka taɓa tunani ba.
A hankali ya k'araso gabana ya ajiye kulolin hannun sa ya tsugunna yana kallon Na'im da ke kokawa da riga ta zai sha Nono.
Zubawa yaron ido ya yi cike da kallon sha'awa, a hankali ya tara hannu ya nawa yaron murmushi, ya jawo shi daga jikina ya d'auke shi.
Wani irin Abu ke yawo a zuciyata na rasa me na ke ji yau, farin ciki ya kamata nayi ko me?yau Haidar ne a haka a gabana, harda d'aukar Na'im, yaron da tunda yazo duniya bai san daɗin mahaifi ba, Inhar ban manta ba bai fi sau biyu ya ɗauke shi ba
tunda aka haife shi.
Gani nayi ya zauna a dandamalin sumuntin tare da ɗora Na'im a cinyar sa, Yaro kam yace bai san zance ba yasa kuka yana son sauka dan bai san shi ba bai saba da shi ba kwata kwata.
Ƙoƙarin kamo shi ya ke yana rarrafowa wajena cikin kuka yana gwaranci.
Sai naji Haidar ɗin ya bani tausayi ace ɗa na gudun ubanshi me ya kai wannan tashin hankali.
Rungume yaron nayi tare da ɗauke k'wallar da ta zubo min ina ƙara godewa Allah ganin hankalin sa ya dawo kan yaran.
Dan sai kiran su ya ke amma sunƙi zuwa wajen sa.
Ni dai a yanzu burina koda ace ba zai cigaba da zama da ni matsayin mata ba, to ya rik'emin yaran ya kalle su matsayin Mahaifi hakan zai faranta min kuma zan zauna da shi a kowanne hali har zuwa lokacin da Allah zai kawo ƙarshen wahalata,
In kuma babu rabon ganin hakan ina fatan Allah yasa kafin ƙasa ta rufe idanuna na nemi yafiyar waɗanda na ɓatawa.
******
*MARYAM*
Maryam kam nacan ta kusa haukacewa saboda yadda ta ke dukan ƙofar,
har ƙarfin ta ya ƙare ta koma a haukace ta rarumi wayar ta danna kiran wayar Mama,
ta kira babu adadi amma babu answer kiran ta ke kawai babu k'ak'k'autawa gashi ank'i dagawa daga can kuma sai aka ɗaga.
Cikin tashin hankali ta shiga rattabawa Mama bayanin abinda ya faru
Da ƙyar ta yi shiru jin Mamar tace
"Ga tanan zuwa"
Mun daɗe zaune ba um ba um'um tsakanin mu, da ya gaji da zaman ya tashi da kanshi ya nemo filet ya shiga zuzzuba abincin, hakan sai ya tunamin da wasu abubuwa da suka wuce da dama, sai naji dama na tariyo rayuwar mu ta baya da shi, da lokacin ne tare zamu zuba abincin yana in kawo Ina ni zan zuba.
Turo filet ɗaya daya zuba sakwarar guda biyu yayi gabana, ya kafeni da wani irin kallo mai k'unshe da tarin abubuwa idanun sa har wata ƙwalla ce kwance a hankali ya buɗe bakinsa yace
"Kici abincin kin ji."
Girgiza kai nayi alamar bazan ciba, saboda gaba ɗaya ni yanzu ba abinci bane a gabana kwata kwata na rasa me ke min daɗi a zuciyata.
Ganin yayi yayi naci nak'i, sai ya mik'awa yaran nasu da ya zuba,
Umar dai ganin abinci ya yarda ya je wajen sa babu ruwan shi ya wanke hannu ya fara ci, Salim kam ya dai saka abincin a gaba amma hankalin shi gaba ɗaya a kaina ya ke.
Gefe Haidar ya koma ya jingina da bango tare da dafe kanshi da hannu biyu, ji ya ke kamar kanshi zai rabe biyu dan tsabar ciwon da ya ke mishi har yanzu,
Sai dai idanun sa suna kaina duk motsin da zanyi har kasa ɗago kaina na yi saboda yadda kallon nashi ke dukan zuciyata.
Yafi awa ɗaya a ɗakin zaune ni da shi ba um ba um um, Can muka ji ana buga k'ofar get da ƙarfi kamar za a ɓalla ta.
Cikin mu babu wanda ya motsa sai Umar sarkin karambani da ya zabura ya mik'e ya doshi hanyar fita,
Janyo hannun shi nayi na maida shi cikin ƙasa da murya nace
"Koma ka zauna tukun"
Na ajiye Na'im na doshi hanyar fita dan naje na buɗe ƙofar.
Har na ɗan gota Haidar kaɗan ba tare da zato ko tsammani ba naji ya riƙo hannu na, wani irin shokin muka ji ya jamu dukanmu mu biyun, cikin sauri ya saki hannun nawa nima da sauri na janye ina jan addu'o'i jin yadda naman jikina ke wata iriyar rawa kamar wadda wutar Nepa ke ja.
Idanun sa da suka yi wani irin jajawur ya d'ago ya watso min kallon da yasa babu shiri na d'auke nawa ganin daga gare shi, dan sam bazan iya kallon shiba jijiyoyin kannan kam duk sun tashi,
Sai faman yarfe hannun sa ya ke shima alamar dai Abu ɗaya muka ji.
Kallon hannunsa ya ke cikin mamakin abinda ya faru, me kenan? daga taɓa ni sai shokin sai kace wutar lantarki.
Nima a tsorace nake duka ina duba yadda hannuna yayi wani irin ja, ji nake ma kamar naji ciwo a hannun.
Kamar bazai bud'e bakin shi ba ya motsa la'b'ban shi cikin wata murya data matuk'ar shak'ewa kamar ta mai mura yace
"Koma ki zauna"
Ya lalla'ba ya tashi yana dafa bango y a hankali ya fita.
Wani tausayin sa naji ya dad'a kamani hak'ik'a yanzu na gano koma mene ne harda laifi na a ciki, tabbas koma wanne hali Haidar ya aikata na bada muhimmiyar gudun mawa ba kad'an ba, nice na bud'e koma wacce ƙofa ce, tabbas nayi sakaci kuma kaina na cuta Haidar mai kazar kazar Haidar shine ke tafiya yana bin bango, tabbas ba k'aramin abu ya ke ji ajikin sa ba.
Buɗe ƙofar ya yi, wadda ya gani tsaye yasa ya juyo ba tare da ya kalle taba ya bata hanya yayi gaba.
Tsaye tayi ta kasa shigowa rataye da jakarta ta saki baki da hanci da ido tana kallon ikon Allah.
Lallai kam gaskiyar Maryam komai ya canja, tabbas ga zahir ta gani, yau ita Haidar ya gani ba tare da ya gaida taba ya kalle ta ya wuce.
Ita sai taga kamar ma hararar ta yayi dan idanun shi ba k'aramin birkicewa suka yi ba kamar wani wanda yasha k'waya, yoh ko dai ƙwayar yasha shi yasa ya yiwa Maryam haka? dan dai ba haka kalar idanun shi suke ba.
Bata gama wannan tunanin ba taga ya doshi ɗakin da Salma ke ciki,
Tana ganin ya shige ai bata san lokacin data rufa mishi baya ba kamar taci tuntuɓe
Abinda ta gani ne yasa ta ja baya da sauri batare da tasaki labulen da ta bud'e ba, Haidar ne zaune ɗakin Salma zaman dirshan Salma na cikin ɗakin haka yaran da aka dasa mishi tsanar su suma na ciki zaune suna shan inuwa ɗaya, wani sabon tashin hankali ne ya rikito mata har bata san lokacin da ta fara magana a fili ba
"Ah lallai ba muga ta zama ba gaskiyar Maryam da ta kira ni a haukace lallai kam liƙi ya fara 'ballewa"
Bata san ma maganar da tayi ta fito fili ba sai da taga duk mun zuba mata ido muna kallon ta, Nan ta fara yan juye'juye da kame'kame cikin jin kunya ganin yadda ta rik'e min labule gam ta ke kallon mu tana sosa kai tace
"Ah Salma ina kwanan mu"
Ban iya amsawa ba saboda kaɗuwar jin kalaman ta sai ɗan ɗaga kaina da na yi, itama bata wahalar da kanta ba wajen k'ara magana ko kula su Salim kamar yadda ta saba ba,
Sai ta juya ta nufi Sashin Maryam a rikice da ɗan gudun ta ko nauyin jikin ta bata ji,
har tabar wajen kuma Abban Salim bai ɗago ko kanshi ba ya kalle ta.
Tana faɗawa farlon ta nufi nanyar ɗakin Maryam inda ta ke bugo ƙofar daga ciki tana ihu muryar ta har dashewa tayi saboda masifar da ke cinta.
Kara bakin ta ta yi a jikin ƙofar ta shiga mata magana tana kiran sunan ta, ai tana jin Muryar Mama ta fara ihun tace ta je wajen Haidar tasa yazo ya bud'e ta makulli na hannun shi.
Aikuwa ta juya da sauri ta nufi ɗakin Salmar.
Shigowa ta ƙara yi wannan karon har cikin ɗakin, ko kallon inda muke bata yi ba kamar ba Mamar nan ba mai fara'faran dani da yara na, ni dai kallon ta nake bata wani bani Mamaki sosai ba dan dama na riga dana san ba qaunar mu take tsakanin ta da Allah ba, dan babu masoyin ka da zai ganka kana cikin halin wahala sannan ya nuna kamar bai gani ba, inba yaudarar kaina nayi ba ta ya zance sona ta ke bayan y'ar ta na cutar dani sannan tana gani wani lokacin ma gaban ta bata taɓa nuna min wata alama ba ko guda ta tausayi ko wani abu ma da zai nuna min tana yi dani ba ko kaɗan.
Gaban Haidar taje ta tsaya kamar wata budurwa ta kama ƙugu ta mik'a mai hannu tare da cewa
"Bani makulli inje in bud'e y'ata da ka rufe min ita a d'aki kamar wata dabba" ta k'are tare da galla mai harara.
Nikam idanuna biyu dan har yanzu banajin zan iya sakin jiki na dan komai ya riga da fice min a rai bana damun kaina sam.
Hayaniyar da ta ke mai ne yasa ya ɗago ba tare da yace mata komai ba, ya mik'e ko kallon inda take bai yi ba ya kalle ni yace
"Taso"
Gani nayi kamar ba dani ya ke magana ba sai da ya tsugunna har lokacin layi ya ke kamar zai faɗi, ya ɗauki Na'im da tuni yayi barci ya saɓa a kafaɗa tukun yaja hannun Umar.
Ya kalli Salim da ke kusa dani zaune ko alamar motsawa bai yi ba yace
"Ku taso mana mu je"
Ganin bamu tashi ba ga Mama nata hayaniya yasa ya ja Umar da ke da ke ƙara manne masa a jikin sa suka fice.
Juyowa Mama tayi ta kalle ni a wulaƙance tare da galla min wata harara ta ja tsaki tace
"Ki ƙarawa Bokan ki kuɗi kin shiga kin fita kin raba Soyayya shegiya mai baƙin hali"
Tasa kai ta fice tana muskuta mazaunan ta da suka cika doguwar rigar jikin ta.
Koda ya fita tafiya yayi kaɗan ya nufi wani part da ke bayan na Maryam,
Wajena da aka daɗe ba'a buɗe ba, koda ya buɗe wajen cike yake da ƙura sai dai kujerun farlon an lullu'be su da leda,
a hankali ya yaye ledar da aka lullu'be kujerun babu abinda ya same su sabbin kujeru ne dal,
Nan ya kwantar da Na'im ya ɗora Umar a ɗayar kujerar.
Ya zauna ya jingina da kujerar yana sauke numfashi a hankali,
Yana bin farlon da kallo yana tuna abubuwa da yawa da suka wuce, ya kalli ƙofar kitchen ɗin su sai yaga kamar lokacin suke rayuwa da Salmar shi cikin soyayya da k'aunar juna,
tashi yayi ya nufi ƙofar farlon dan ya rufe,
yana jin yadda Mama take hayaniya a sashin Maryam da har lokacin sai buge buge ta ke a zo a buɗe ta.
Kara ƙofar yayi tare da dawo ya zauna yana kallon Umar da sai tsalle tsallen sa ya ke.
A hankali ya zame ya kwanta gefen Na'im yayi lamo ya rasa abinda ya ke masa dad'i.
Bugun k'ofar da Mama ta dawo tana yi ne yasa ya tashi bisa dole ya fita, bai kulata ba ya wuce ta ya nufi sashin Maryam ɗinya buɗe ƙofar ɗakin Maryam ɗin ya juya ya bar ta tsaye.
Maryam tana ganin an buɗe ta a haukace ta fito kallo ɗaya zaka mata kasan tabbas ta fara fita a hayyacin ta, dan gaba ɗaya a birkice ta ke kannan a hargitse
dama ɗan attachments ɗin ke rufawa kan asiri, sai gashi yau ta tuje shi kan dama ba wani gashi arzik'i ba duk ya cukurkud'e.
Da gudu ta runtuma tayi hanyar waje tana ik'irarin yau sai ta kashe Salmah yau sai taga bayan ta,
Mama na k'ok'arin rik'e ta ta fincike ta fice a guje.
*_🥰MAMAN ƊAN ALBARKA CE🥰✍️✍️_*