Epi-2
TATSUNIYA.
By: _*🌹𝑍𝑎ℎ𝑟𝑎-𝑡𝑢𝑙-𝑄𝑎𝑙𝑎𝑚🖋️*_
WANI SON MAI WUTA❤️‍🔥
Episode two: murya a duhu soyayya Ă haske.
بسم الله الرŘمن الرŘŮŠŮ…
Malam Madu ya ƙara sauri hankali a tashe. Amma har yanzu ana binsa a baya. Sai ya juyar da fitilar da ke hannunsa baya, amma bai kuma ganin kowa ba. Shiru hanya ya ɗauke, ba takun mutane.
Ko wane shiru yana sa zuciyarsa ta buga da ƙarfi, ko wane mataki yana ɗauke da firgici.
"Me ya ke faruwa da ni?!"
Ya fada a tsorace yana nishi, sai kuma yasa gudu sosai numfashinsa na tsayawa.
A haka Malam Madu ya iso ƙofar gidansa, sannan ya tsaya yana waige. Har yanzu ba kowa, ya kai hannu na rawa zai buɗe ƙofa, zuciyarsa na ta bugu da sauri.
Kafin ya buÉ—e ya ji wata murya mai fitar iska. Aka sanar da shi wata magana, wanda yasa komai na Malam Madu ya tsaya.
Ya saki fitilar hannunsa ƙasa. Bai ga mai maganar ba, amma kalaman sun shiga ransa.
*washe gari*
Lokacin da safe ya yi… Malam Madu ya shirya kayansa da gaggawa. Yana tunanin cewa ba zai tsaya ba, dole ne ya bar ƙauyen.
Mutane sun tsaida shi, antambaya.
"Me yasa za ka bar ƙauyen Malam Madu? Kuma kai babba ne ka daɗe a ciki tun tarihi?".
Amma Malam Madu, ya furta.
"Jiya da dare, wani abu ya faru, ba zan tsaya ba".
“Me ya faru a daren jiya?"
Aka ƙara tambaya, amma Malam Madu bai amsa ba. Ya fara yin tafiya cikin razana da tsoro.
'Yan ƙauyen sun yi mamaki sosai, kowa yana kallonsa har ya yi nisa, sai sauri ya ke yi, yana waige kamar mai tsoron ganin wani abu.
A ƙarshe dai, Malam Madu ya bar ƙauyen.
*A gefe kuma*
Al'ameen da Aisha suna zaune suna hira. Aisha ta ce.
"Al'ameen, ka ji wani abu da ya faru yau a ƙauyen nan?".
"Eh, akan barin ƙauyen nan da wani Malam Madu ya yi ko?".
Aisha ta ce.
"Eh, kowa bai gane me yasa ba, mahaifina ya ce, Malam Madu bai taɓa tafiya mai nisa da ƙauyen ba, amma yanzu ya bar garin. Abun mamaki ne".
Al'ameen ya girgiza kai, da damuwa ya ce.
"Ba komai, ƙila hakan ba wani babban abu ba ne".
Su ka cigaba da hira, har da na soyayya sosai.
Suna anan Sabir É—an uwan Aisha ya zo, ya yi murna da ganinsu tare.
Su ka gaisa da Al'ameen shima ya zauna suna hira cikin farin ciki a tare.
Da Al'ameen ya koma gida, abokinsa ɗan ƙauyen mai suna, Halilu ya ce masa.
"Al'ameen ka yi sa'a, kaine ka samu soyayyan Aisha, amma na yi mamaki, yadda ta so ka da wuri".
Al'ameen ya yi murmushi ya ce.
"Babu abun da Allah baya yi. Cikin ikonsa n'a zo ƙauyen nan, na haɗu da ita".
*Da rana* Al’ameen da Aisha suna dariya da yaran gefensu, suna taimaka wa yara ɗebo ruwa da shirya wa wasu kayan wasa.
Soyayya ta su na ƙara girma a hankali, har mutanen ƙauyen su ka fara lura, saboda ba sa ɓoyewa.
Al’ameen yana kallon Aisha yayin da take taimakawa yara, idanuwansa na ɗauke da wani haske na musamman.
Aisha kuma tana kallon Al’ameen, zuciyarta na rawa, numfashinta na tsayi, ba komai ba ne shauƙin so ne.
Soyayyarsu ta zama haske, tana sa zuciyarsu cikin farin ciki sosai.
Wasu samari na baƙin ciki, baƙo ya zama musu cikas akan Aisha.
*Daren ranar*
Ya sake zama dare mai sabon al'amari, mamaki da kuma zargi.
Wasu maza guda biyu suna tafiya a dare. Su ka ji kamar ana binsu, irin yadda aka yiwa Malam Madu.
Sun tsorata, suna sauri suna gudu, amma lokaci É—aya takunsu ya tsaya.
Saboda murya da su ka ji mai iska, ta sanar da su wasu kalamai da yasa jikinsu yin rawa. Su ka cika da tsoro babu sassauci.
*Washe gari* suma su ka haɗa kayansu za su bar ƙauyen, yanayin razana sosai a tattare da su. Mai Gari ya dakatar da su, amma su ka ƙi.
Da an ambayesu me yasa za su bar ƙauyen sai dai su ce.
"Wani abu ya faru jiya, ba za mu tsaya ba!".
Suma su ka bar ƙauyen.
Haka Washe gari ma wata mata da mijinta, su ka yi shirin barin ƙauyen.
Tambaya, amsa É—aya su ke cewa.
"Wani abu ya faru jiya!".
Daga nan mutanen ƙauye su ka shiga tsoro, da tunanin wani abu na faruwa a ƙauyensu, wanda ba su san menene ba.
"Ko la'ana ce ta kama ƙauyenmu?"
Wasu su ke cewa.
_shin menene ke bin mutane a cikin dare? Sannan wani kalmai ake faÉ—a?_
_shin ƙauyen zai iya samun zaman lafiya?_
_ya ya Al’ameen da Aisha za su ci gaba da soyayya yayin da ruɗani ke kewaye da su?_
Like comment and share fisabilillahi.
_*🌹𝑍𝑎ℎ𝑟𝑎-𝑡𝑢𝑙-𝑄𝑎𝑙𝑎𝑚🖋️*_