Page-53
*FASAHA WRITER'S ASSOCIATION*
(*F.W.A)*©✍️
⭐⭐⭐
Ƙungiya masu aiki cikin salon hikima da fasaha gurin juya tunanin al-umma, kaifin alƙalumansu ya zarta takobi ©✍
___________________________________________________
بسم الله الرحمن الرحيم.
اللهم صلي وسلم على نبينا محمد.
❁ 𝐒𝐀𝐍𝐀𝐃𝐈𝐍 Ƙ𝐀𝐃𝐃𝐀𝐑𝐀𝐓𝐀 ❁
Free book📓
By: _*🌹𝑍𝑎ℎ𝑟𝑎-𝑡𝑢𝑙-𝑄𝑎𝑙𝑎𝑚🖋️*_
Page5️⃣3️⃣
ASIBITI.
Abba ne ya fito daga gurin Momy, jikinsa duk a sanyaye yana tafiya kamar ba tafiya ya ke yi ba. Su Sadiya da ke zaune har da su Dady da su Hajiya Kaka, duka su ka zo bayan jin labarin abun da ya sami Momyn. Ayusha ce kaɗai ba ta cikinsu wai ta je gaishe da mahaifiyarta Rumaisa. Gaba ɗayansu su ka miƙe zuciyoyinsu cike da fargaba suna kallon yanayin da Abban ke tafiya.
Gaba ɗaya zuciyarsu na ƙara da tsananin fargaba mara musaltuwa akan abun da su ke tsoron ya faru. Alokacin da ya iso gabansu ya tsaya kamar me tunanin ta yadda zai sanar musu da komai. Babu wanda bakinsa ya buɗu sai zubawa Abba ido da su ka yi.
A hankali ya fara cewa, "Momy... Momy!..." Dady kasa haƙuri ya yi saboda yadda zuciyarsa ya ke ta faman zillo ya ce, "Abba me ya sameta?!" "Dady, amma... Momy ta tashi, ta samu lafiya" ya ƙarashe cike da murna ya rungume Dady idonsa da ƙwallah, sai da Dady ya ja dogon numfashi sosai ya ƙame saboda jin daɗi, 'Allah kai ne abun godiya' ya faɗi cikin ransa. Sauran kuma su ka sauke ajiyar zuciya cike da murna.
Sadiya ta rungume Faruq da ke kusa da ita, Asma'u ta rungume Hajiya Kaka suna fitar da hawaye, su Uncle Usman ma cike da farin ciki. Ɗagowa Dady ya yi yana kallon Abba shima yana share hawaye, cikin rawar baki ya ce, "zan...zan iya ganinta yanzu?" Abba ya girgiza masa kai yana share idonsa.
NURIYYAH.
Ni dai ina kallon Haidar da ya kasa cewa komai sai tunanin da na ke ganin kamar ya shiga. Kafin na kuma masa magana ya ɗago yana kallona da cewa, "damar da na ke son ki bani ba komai ba ne sai... ki amince na yi Sanadin mantar da ke duk wata damuwarki, ko da ba duka ba ne kuwa, wannan shine abun da na ke buƙata ƙanwata". Murmushin jin daɗi na yi ko ba komai na samu wanda ya ke son mantar da ni ciwukan da su ke ƙunshe a zuciyata.
"Na ba ka dama yaya Haidar, sannan ina godiya da yadda ka ke ba ni kulawa" na faɗi ina share ɗan guntun ƙwallahna, Haidar ya ce, "na gode da ki ka bani wannan damar, kuma na yi miki alƙawari zan sa ki ki manta da wasu abubuwan, domin na san ba zan iya goge komai daga cikin tunaninki ba, amma zan rage wasu, wannan alƙawari ne".
Na yi matuƙar farin ciki da kalamansa sosai, ko a haka kawai ya barni ya gama min komai, khairat ce ta shigo da gudu ta faɗa jikinsa tana faɗin, "Pappa, chocola ka ba Anty Nuliya ne ta yi cilu?" Dariya mu ka yi ya ce da ita, "eh kema kina so ne?" Khairat ta giɗa masa kai, ya sake cewa, "to ki zauna da Anty Nuriyyah, ki yi mata hira sosai, ni kuma zan je inkawo miki chocolate ɗin kin ji?" ta giɗa masa kai da farin ciki, sannan ta koma kusa da ni.
ASIBITI.
Dukkansu su ka shiga ɗakin Momy bayan da Dady ya shiga, masu share hawaye na yi da masu murmushi, kowa ya shiga gaishe da Momy yayin da ita ta ke kallonsu kawai, Asma'u ta zo kusa da ita ta rungumeta tana murmushin farin ciki, itama Sadiya da ta jima ba ta sa mahaifiyarta a idonta ba, ta matso tana kallon Momy hawaye na sauka kan fiskarta.
A hankali Momy ta buɗi baki ta ce, "ya isa, ya isa 'yata, ina lafiya ki daina kuka" Sadiya ta share hawayenta, "yaushe ku ka zo?" Momy ta yi mata tambayar, "yau ne Momy" Momy ta yi murmushi tana sake binsu da kallo gaba ɗaya, Abba da ya je yana duba wasu abubuwan ya shigo yanzu, daga ƙofa ya ke kallon Momy zuciyarsa na bugawa, Allah kaɗai ya san yadda ya ke ji yanzu, domin à baya ya gama sadaukarwa mahaifiyarsa ba za ta tashi ba, saboda ƙarfin gubar, amma dama Allah shine mai ikon yin yadda ya so.
Kafin Abba ya ƙaraso kusa da ita ya ji ta yi wani maganar da yasa shi dakatawa, "na ga kowa... dukkanku kun zo, amma banga 'yata Nur ba, tana ina?" Cewar Momy da ba ta ji ɗuriyar Nuriyyah a wurin ba, gaba ɗayansu su ka yi shiru ban da Sadiya da ba ta san me ya ke faruwa ba, sai a lokacin itama ta juya tana dubawa, tabbas ba Nuriyyah a cikinsu.
Kafin Sadiya ta yi wani magana Abba da ya iso da wuri yana faɗin, "Momyna da alamu dai yanzu kin ma fini ƙarfi" dariya mara sauti Momy ta yi tana lumshe idanuwanta da ya ke nuna tsananin jiyar da ta sha ta ce, "tabbas na fita ka ƙarfi. Tambaya na ke ina Nur?".
"Momy daga tashinki kin fara tambaye tambaye? Please calm down for now, za ki ga kowa daga baya" kafin ya ƙare maganar Momy ta fara ƙoƙarin tashi, da sauri Abba ya kamata ita ko tana faɗin ta samu lafiya za ta koma gida, Hajiya Kaka ta ba ta haƙuri ta bari nan da kwana uku ta ƙara samun lafiya, amma da ƙyar Momy ta haƙura zuwa gobe.
Washe gari da safe aka sallameta don ko zuwa rana ma ta ƙi haƙura akai, gaba ɗaya wani irin abu ta ke ji ba daidai ba a ranta, amma ta tambayesu shin komai lafiya? Ba wanda ya sanar da ita, to gwara ta koma gidan ta ganewa idonta komai, tun da Allah yasa ta samu lafiya, duk da a tunaninta zazzaɓi ne ba ma ta san ta shafe kwanaki a asibiti ba.
Bayan sun isa gida, suna zaune a falon Hajiya Kaka, Sadiya ce ta buɗi baki ta ce, "har yanzu ban ga Nuriyyah ba, tana ina ne wai? Ko dai tana ɗaki ne?" Shiru ba wanda ya amsa mata, "ko ba ta ji dawowarmu ba ne may be tana barci" cewar Momy.
Sadiya ta miƙe ta ce, "eh haka ne Momy ba ri na je na kirata" ta faɗi tana miƙewa za ta wuce, Asma'u ta dakatar da ita da faɗin, "Nuriyyah fa ba ta gidan nan Momy", sai da Abba ya yi ƙasa da kansa haɗi da rintse ido sosai, bai san ya Momy za ta ji da wannan zancen ba.
Momy da ba ta fahimci maganar Asma'u ba ta ce, "ba ta gidan nan? Ina ta je ko aikenta aka yi? Ina ji a jikina akwai abun da ku ke ɓoye min, Menene shi?" Sadiya ta dawo ta zauna tana jiran jin amsar Asma'u, "tabbas akwai, amma ba alkhairi ba ne jinsa, kawai ki manta da batun wannan yarinyar Nuriyyah" faɗin Mama tana kallonsu don ba ta son aji mutuwar sarki a bakinta.
Dady ne ya juya ya yiwa Abba alama da ido, hakan yasa Abba ya tashi ya je kusa da ita ya ce, "Momy ya kamata ki je ki ɗan kwanta, kina da buƙatar hutawa, har yanzu jikinki bai gama warwarewa ba, daga baya za ki ji komai kin ji?" Ya faɗi yana ƙoƙarin ɗagata, sauran ma su ka ce eh haka ne, ban da Ayusha da ta so komai ya fashe yanzu Momyn ta san komai, sai wani yamutsa fiska ta ke yi.
Momy ta ce, "ka ga dakata, ba inda za ni sai na ji me ya ke faruwa, Me ya faru? Mama ban fahimceki da na manta da Nur ba, akan wani dalili? Me ya samu 'yata ku faɗamin don Allah!" Ta faɗi da ƙarfi haɗi da miƙewa tana bin kowa da ido cike da fargaba, wannan karon Hajiya Kaka ta ce, "Rahama ki je ki kwanta, daga baya kyaji me ya faru... Ba ki da cikakken lafi...".
"A ah Hajiya Kaka, yanzu na ke son jin komai, me ya samu Nur ɗina? Ku faɗa min idan kuna son lafiyata", Momy ta katse Hajiya Kaka da faɗin haka tana hawaye, saboda yanzu fargaba ta ke yi akan kar dai wani abun ne ya samu Nuriyyah su ke ɓoye mata.
Mama da ta fara jin haushi da kalaman Momy akan Nuriyyah ta kuma cewa, "lallai Rahama, to ina mai tabbatar miki idan ki ka ji abun da yarinyar nan ta yi miki ko? Sai kin dawwama kina tsine mata, domin ta cancanci hakan, tsintacciyar mage ce dama ba ta mage, kin yi renon 'yar kunama, a ƙarshe dai ta yi miki harbi mai matuƙar muni, kin ba ta kulawa kamar 'yarki, sai ga shi ta so kasheki Allah ya rufa asiri", fiskar Momy ya gama bayyanar da rashin fahimta, sai kallon Mama da ke wannan maganar ta ke yi, haka Sadiya da ba ta san me ya faru ba itama ta ke kallon Mamar babu abun da ta fahimta cikin kalamanta.
"Har yanzu babu zancen da na gane, ku fayyace min mana!" Cewar Momy. Ayusha ce ta gyara zama domin kuwa ta ga kamar kowa nuƙu-nuƙu ya ke yi baya son sanar da Momy lamarin nan, don haka ta ce, "Aunty, I will let you know everything, kin san kuwa kin shafe kusan two weeks kina kwance ba lafiya?" "sati biyu?!" Faɗin Momy da mamaki, Ayusha ta cigaba da cewa, "kuma wannan rashin lafiyar sakamakon poison ɗin da ki ka sha ne" "poison?!" Momy da Sadiya su ka haɗe baki gurin faɗi bayan sun fidda idanu waje.
"Eh poison Aunty Rahama, kuma ba a ko ina ki ka sha wannan poison ɗin ba sai a kunun da rannan Nuriyyah ta haɗa miki, wato dai Nuriyyah ce ta baki guban ki ka sha!" Zare idon da su ka yi yanzu daga Momy har Sadiya, ya ma fi na ɗazu da su ka yi.
"Wani irin magana ki ke cewa Ayusha? Kamar ya Nuriyyah ta sawa Momy guba a bun sha? Haba don Allah, ki yi maganar da hankali zai ɗauka mana", faɗin Sadiya da ɓacin rai, kau da kai gefe Ayusha ta yi da haushin Sadiya, wai ita ga ta ta yarda da Nuriyyah, ko da ya ke ma, Sadiyar ba za ta dameta ba indai Momy ta amince, don haka ta maida kallonta ga Momy tana ganin yadda ta ke sauke numfashi alamar zuciyarta na bugawa da sauri.
Asma'u ta matso kusa da Sadiya ta dafata ta ce, "gaskiyar kenan Anty Sadiya, abun da Nuriyyah ta aikata mana ne" kallonta kawai Sadiya ke yi ta kasa cewa komai, sai ta maida kanta ga mahaifiyarta, domin ta san wannan maganar ya fi girgizata sosai idan har hakan ya kasance da gaske impossible. Momy kuwa a hankali ta maida dubanta ga su Dady su Hajiya Kaka, domin neman ƙarin bayani a garesu akan wannan lamarin. Amma girgiza mata kan da su ka yi alamar tabbas hakan yasata yin zaman daɓas akan kujera, ƙirjinta na harbawa sosai, numfashinta ya fara sarƙewa, ko dai mafarki ta ke ne?.
Wani irin tari ne ya fara zuwar mata, da sauri Abba ya zuba mata ruwa ya miƙa mata, tasha sannan ya ajiye yana faɗin, "kin gani ko Momy? Please kina da buƙatar hutawa..." "ina son ƙarin bayanin abun da ya faru wancan ranar" faɗin Momy tana kallon Abba fiskarta a haɗe, Nusaiba 'yar Mama ce wannan karon ta faɗi duk abun da ya faru har yadda aka kori Nuriyyah, Aysuha sai murmushi ta ke yi, ba tare da kowa ya lura ba, aganinta komai ya ƙare a yau indai maganar Nuriyyah ne.
Hawayen da su ka cika à idonta ta matsesu ta hanyar rintse idonta, ƙarfin harbin zuciyarta ya ƙaru, hankalinta ya yi matuƙar tashi, Sadiya kuwa ta rasa ma me za ta ce sai hawayen da su ke ta zarya akan idonta. Abba dai shiru ya yi don sam bai so Momy ta san da hakan ba, domin har yanzu zuciyarsa ba ta huta daga tunanin komai ba, sannan ya san yadda Momy za ta ji. Su Dady ma shiru su ka yi cikin rashin daɗi.
"Kin gani ko Rahama? Wannan shine sakayyar da 'yar riƙonki ta yi miki, ta so kasheki ta wannan hanyar, ni so na yi da an kaita ga hukuma m..." Momy da ta buɗe ido lokaci ɗaya ta tsaida Mama da ga maganar da ta ke yi ta ce, "a ah! Ba gaskiya ba ne!" Kowa ya maida kallonsa ga Momy.
"Eh ban yarda ba! Ban yarda da cewa Nur za ta iya kashe wani ba bare ni, wannan ƙarya ce kawai", gaba ɗayansu sun yi mamakin wannan furucin na Momy, musamman Ayusha da sai da gabanta ya faɗi da jin maganar. Mama ta kuma cewa, "haba Rahama, me ki ke shirin cewa ne? Ki rasa wacce za ki yarda da ita sai wacche ta yi niyyar kasheki? Ita ki ke son cewa ba gaskiya ba ne duk abun da ta aikata miki? Ki buɗe idonki mana Rahama".
"Dakata Mama!" Cewar Momy fiska a haɗe, aikuwa Mama ta dakata ɗin tare da sake baki tana ganin Momy. "A cikinku akwai wanda ya ganta da ido ta sanya gubar? Eh? Ku faɗa min" shiru ba mai magana, Momy ta miƙe cike da ɓacin rai ta cigaba da faɗin, "to akan me za ku gasgata ta so kasheni? Sannan har ku koreta akan abun da ba ku da tabbacin ta aikata? Ina da cikakken yarda akan Nur fiye da kowa! Kuma na tabbata ko da ace ita makashiya ce ba za ta taɓa kasheni ba! ".
"Rahama, duk abun da ya faru ba ƙage ba ne, Nuriyyah ta aikata shi, wani irin yarda ki ke da shi akanta da har ji ke ganin ba za ta aikata ba? Kin ga, ki daina wannan kalaman don Allah ki je ki kwanta ki samu natsuwa" cewar Dady, girgiza kai Momy ta hau yi tana hawaye ta ƙara cewa, "in natsu? Taya zan samu natsuwa bayan 'yata ba ta tare da ni? Taya zan samu natsuwa bayan kun kora min 'yata, ai kun riga da kun raba ni da natsuwata, kuma tabbas, yardar da na ke da shi akan Nuriyyah ba na wasa ba ne, kuma ba zai karye akan wannan maganar da kunnena ba zai ɗauka ba".
"Aunty Rahama wallahi gaskiya ne, ya kamata ki fahimta, you don't know this girl well, Nuriyyah muguwace yadda ba kya zato, ba ta da hali mai kyau, she is a woman who loves herself, na ci karo da abubuwa da yawa akanta, amma sai na ke tsoron yin magana saboda ina ganin kamar ba za a yarda da ni ba, kuma sai ga shi har maza tana bi, ta so raba Asma'u da Sunu..." Ayusha ce ta ke yin maganar don tabbatarwa Momy zancen da aka faɗa, har da ƙara na ta akai, son ba ta ma son nan agaba à ambaci ko da sunan Nuriyyah a cikin gidan.
Sai dai, ba ta kaiga kaiwa ƙarshe ba Momy da ta cika da haushi haɗi da baƙin ciki akan maganar da ta ke faɗa, ta daka mata tsawa, sai da Ayusha ta razana da furucin, sauran ma su ka cigaba da kallon Momy cikin tsananin mamaki da abun da ke cewa. "rufa min baki!! Yaushe ki ka zauna da ita? Yaushe ki ka santa? Da har za ki iya ba da shaida akan halinta? Ki kiyayeni! Ba na son sake jin bakinki cikin wannan lamarin, sannan Idan ki ka sake yi min kwatan-kwancin wannan furucin akan Nur, to saina ɓata miki rai! Ba na wasa da ke".
Ayusha ta cika pam da kalaman Momy kausasa akanta, wai me yasa ba ta cin nasara akan Nuriyyah gaba ɗaya ne?.
Last page
___________________________________________________
Hmmm😌 mutanena na cikin alkahiri a wannan fannin dumu-dumu na sani😂
To mafari kenan, Momy ta tashi, sai dai mu ce masha Allah, gashi ta ƙi amincewa da abun da ya faru, kuna ganin za ta sauya à gaba?. Taya gaskiyar nan zai bayyana?.
Haidar ya yi alƙawarin mantar da Nuriyyah abubuwan da su ka faru, zai ci nasarar kuwa?.
_*🌹𝑍𝑎ℎ𝑟𝑎-𝑡𝑢𝑙-𝑄𝑎𝑙𝑎𝑚🖋️*_