Page-54
*FASAHA WRITER'S ASSOCIATION*
(*F.W.A)*©✍️
⭐⭐⭐
Ƙungiya masu aiki cikin salon hikima da fasaha gurin juya tunanin al-umma, kaifin alƙalumansu ya zarta takobi ©✍
___________________________________________________
بسم الله الرحمن الرحيم.
اللهم صلي وسلم على نبينا محمد.
❁ 𝐒𝐀𝐍𝐀𝐃𝐈𝐍 Ƙ𝐀𝐃𝐃𝐀𝐑𝐀𝐓𝐀 ❁
Free book📓
By: _*🌹𝑍𝑎ℎ𝑟𝑎-𝑡𝑢𝑙-𝑄𝑎𝑙𝑎𝑚🖋️*_
Page5️⃣4️⃣
Ayusha ta cika pam da kalaman Momy kausasa akanta, wai me yasa ba ta cin nasara akan Nuriyyah gaba ɗaya ne? Momy kuwa ɗaga kanta ta yi tana kallon sauran ta ce, "ku saurareni, ina son ku san cewa, Nur 'yata ba ta da wani alaƙa a game da rashin lafiyata, kuma ina son a nemomin ita".
Ta matsa kusa da Dady ta ce, "akan me za ka amince da Nur ce ta aikata? Kai kamar mahaifi ka ke a wurinta, taya har za ka bari zuciyarka ta yi na'am da wannan zancen da ba zai taɓa yiwuwa ba?" "Gaskiya ce, komin ɗacinta ba za a sauyata ba Rahama", share hawayen fiskarta ta yi cike da takaicin maganar Dady ta kuma faɗin, "ƙwarai gaskiya ce, kuma za ta fito!".
Abba ya ce, "Momy please ki kwantar da hankalin..." "ba na son jin muryarka!" Momy ta furta sai da kalmar ta girgiza kowa musamman wanda aka yiwa kalamar, "ansa maka ranar aure da ita, ya zama kai ne wanda za ta aura, amma tsawon lokacin da ka ɗauka da ita ka kasa ba ta yarda? Shin kasan yadda zuciyarta zai karye akan kalaman da ka jefeta da su?".
Kalmar da Momy ta faɗi sai da ya wuce kunnensa ya daki ƙirjinsa, ita ko ta kuma mayar da kanta gun Asma'u haɗi da takawa kusa da ita ta ce. "Ke kuma! Idan akwai wanda ya kamata ya ba da labarin halin Nuriyyah to ke ce, tare ku ke kwana, tare ku ke tashi tsawon shekaru, kun yi wasa tare, komai na ku tare ku ke yinsa, amma ki ka kasa sanin abun da za ta aikata da wanda ba za ta yi ba?".
"Momy yunƙurin kisan kai fah" Asma'u ta faɗi, cikin tsawa Momy ta ce, "ko da ace kisan kan ne sai a kasa bincike?! Kun san cewa yarinyar nan marainiya ce, ba ta da uwa kuma ba ta da uba, sai mu kaɗai, da mu ta dogara, ba ku yi tunanin abun da zai sameta bayan fitanta daga gidan nan ba? Kun san halin da ta ke ciki yanzu? Duk cikinku aka rasa wanda zai yi tunani kafin yanke hukunci? Zafin zuciya ya ɗebeku ku aikata kuskure? To wallahi idan har wani abu ya samu Nur ba zan taɓa yafewa kowa a cikinku ba!" Momy na kaiwa ƙarshe ta fice daga cikin falon tana kuka, da sauri Sadiya ta bi bayanta cikin tsananin damuwa.
Shiru ya gifta falon babu wanda ya ke ko ƙwaƙwƙwaran motsi, gaba ɗayansu babu wanda furucin bai dakarwa zuciya ba, taya zaune ta yanke hukuncin cikin rashin sani, me yasa za ta ƙi yarda?.
Momy na shiga ɗaki ta kuma fashewa da kuka, zuciyarta na yi mata zafi, Sadiya ta shigo tana rarrashinta itama tana hawaye, ta kalleta ta ce, "yata Sadiya, kema kin yarda Nur za ta iya kasheni?" Sadiya ta kasa amsawa nan take, zuciyarta ta ɗan tsaya kafin ta sami ƙarfin faɗin, "no Momy, ina tare da ke, na san Nuriyyah ba za ta aikata hakan ba, sai dai taya hakan ya faru?".
Momy ta rungumeta tana faɗin, "Ban san wani hali Nuriyyah ta ke ciki ba yanzu? Tana ina tsawon kwanankin nan? Ta ci abinci ko ba ta ci ba? Me ya ke faruwa da ita? Duk bamu sani ba Sadiya," ta yi maganar tana kuma fashewa da kuka.
NURIYYAH.
Gurin ƙarfe tara na safe Haidar ya ce da ni na shirya, da farko na ƙi yarda, sai da ya sake tunanimin da cewa kar na manta jiya na ce na ba shi dama, hakan yasa na amince. Musamman ya ƙi zuwa aiki saboda ni, su Ummee sun riga da sun san da maganar fitan na mu, bayan na shirya ni da khairat, na sanya ɗaya daga cikin kayan da shi da kansa Haidar ɗin ne ya saya min su kwanaki, dogon riga ne, na yi matuƙar kyau acikinsa duk da ban yi wani kwalliya ba, haka khairat ma gwanin burgewa.
A lokacin da mu ka fito kallonmu su Ummee ke yi suna murmusawa, Mu'azzam ya zo ya ɗauki Khairat da ta zunɓuro baki saboda ta shafa jan baki ya ce, "o'o'o, su Bobbina irin wannan jan baki haka? Wa ya sanya miki?" "Anty Nuliya ne, kuma a ce na yi kyau" murmushi mu ka yi sannan Ummee ta ce, "to rabu da ita su wuce".
Haka Mu'azzam ya sauke Khairat yana cewa shima sai ya bi mu, bai kamata ayi wannan fitar ba shi ba, Ummee ta ce babu inda zai je, muna dariya mu ka fita, haɗi da shiga motar Haidar ya ja mu ba tare da na san ina mu ka nufa ba. Ba wani tafiya mai nisa sosai mu ka yi ba.
Ya tsaida motar a daidai wani babban gate mai ƙayatarwa, tun kafin hankalina ya kai ga rubutun da ke nuna sunan wurin na ji muryar Haidar, "mu je ko?" Murmushi kawai na yi masa sannan na fara bin bayansa, yayin da ya ke riƙe da Khairat saboda ta nace wai ba za ta taka ƙasa ba takalminta zai ɓaci.
Sai da mu ka shiga na gane gurin shaƙatawa ne na wasa da nishaɗi, zuciyata ya cika da mamakin me yasa mu ka zo wannan wuri? Ko da ya ke ƙila saboda Khairat ne. Sai dai gurin da na tsinci kaina a yanzu na gane ba saboda khairat ba ne kawai, domin kuwa idanuwa ne su ka ci karo da wani fili mai cike da furannin masu kyau da ɗaukar hankali, masu launuka kalakala, fari, rawaya, shuɗi, suna shimfiɗe kamar tabarma a wurin gefe da gefe, ƙamshi na ta sh wanda zan iya cewa na furannin ne da kuma yadda ake kula da su sosai.
Na tsaya ina kallonsu sosai fiskata ya bayyanar da jin daɗi, na juyar da idona gun Haidar da ya saukar da Khairat, bai ce da ni komai ba sai fara'ar da ke wanzuwa kawai akan fiskarsa, ya min alama da hannu akan enjoy your happy. A hankali na maida kallona gun followers na fara takawa ina nufan gurin. Itama Khairat da gudu ta wuce tana ta dariya.
Ko da na isa ga furannin duƙawa na yi ina kai hannuna na fara shafasu cike da farin ciki, na lumshe idona na ɗan daɗe ina jin ƙamshin furannin, zuciyata cike da natsuwa, yayin da tunanina ya maida ni baya, ina kallon lokacin da Abba ya miƙo min furannin nan masu kyau da haske har cikin raina.
_"Nuriyyah i love you! Na yarda da tabbas na haukace akan sonki, ina ƙaunarki da duk wata tsoka ta zuciyata, ina son yin rayuwa da ke, Nuriyyah! Na yi miki alƙawari, zan kasance tare da ke har iya ƙarshen bugun numfashina, ba zan taɓa iya rabuwa da ke ba, ba zan iya jure nisantarki ba, please kada ki sake nisantani da ke kin ji?"_
Kalaman da Abba ya faɗa min ɗin nan sun ratsa zuciyata sosai a wancan lokacin, a yanzu fiskata ya bayyanar da murmushin da ban shirya masa ba bisa tuna lokacin da na yi.
Haidai ya ɗauke kansa daga kallon 'yarsa da ta ke ta shafa furanni, ya dawo da su kaina yana kallon yadda na ke yin kyau da farin ciki, ya tako ya matso kusa da ni shima ya duƙa yana kai hannunsa kansu, sannan ya tugi guda ɗaya a ciki ya tsaya yana kallonsa, nan tunaninsa ya koma baya shima.
_a hanyar dawowa daga wurin aikinsa ya sayi fure mai kyau musamman don matarsa Khairat, ko da ya iso gida knocking ya yi kamar baƙo kasancewar suprice ya ke son yi mata. A hankali ta iso bakin ƙofar ta buɗe à tunaninta baƙo ne, lokacin tana ɗauke da ciki wata na shida. Bayan ta buɗe ba ta ga kowa ba, ta tsaya tana mamaki tabbas ta ji knocking, amma ya aka yi ba kowa? Ashe bayan Haidar ya yi knocking ɓoyewa a gefe ya yi. Khairat ta juya za ta koma kenan ta ji an shafa mata wani abu a gefen wayanta. Cak ta tsaya tsoro ya fara ratsata, ta fara juyowa a hankali tana shirin fasa ƙara, kawai ta ga ashe mijinta ne farin cikinta. Wani nannauyar ajiyar zuciya ta sauke haɗi da turo masa baki niyyar shagwaɓa, dariya ya yi yana jan kumatunta cikin salon nishaɗi, sannan ya fito da furen da ke hannunsa ya miƙa mata da soyayya. Karɓa ta yi cike da murna sannan ta rungumeshi domin ta yi farin ciki sosai_
Share ƙwallan da ya zo masa ido Haidar ya yi kewan matarsa na dawo masa sabo, matarshi wacche bai taɓa son wata mace ba sai ita, amma sai ga shi bayan ta kawo masa 'yarsa duniya ita kuma ta koma.....
_"na tsaneki Nuriyyah! I hate you! Me yasa na sanki? Me yasa na so ki? Da ma duk hakan bai faru ba, da ma ban taɓa saninki ba... to ina so ki sani! Ba zan taɓa iya zama da ke ba! Ba zan aurenki ba! Kin rusa komai Nuriyyah! I can't live with you!"_
Kwatsam wa'yan nan furucin su ka faɗo min cikin rai babu tsammani kamar yadda su ka saba, farin cikin da ke raina ya shuɗe, murmushin ya ɓace daga fuskata, da sauri na buɗe idona da na lumshe ƙwalla lokaci guda ya ɗiga ƙasan idona, na janye hannuwana daga furannin a hankali, na mike zuciyata na ciwo, kalaman da na ke tsoron tunosu su ka hau dawo min.
_Me yasa za ki yi mana haka Nuriyyah?...... Rahama wacche ko da yaushe ba ta ganin laifinki Ita ki ke son kashewa..... Kasheta shine muradinki Nuriyyah? Kisa?..... karki taɓani!..... Ni dama na san lokacin nan yana nan zuwa.... Yayana kaima ka yarda? Ka amince ni zan iya wannan abun?...... Akan me zan yar da ke!?...... Na tsaneki Nuriyyah!...... Amma za ki iya bin maza ko?..... Ba za ta taɓa zama mahaifiyarki ba!..... Har abada ni ba 'yar uwarki ba ce!...... Babu amfanin zama da mai hali irin na ki!..... Ki fice mana daga gida Nuriyyah!..... Ki ɓace daga gidan nan na ce!...... I can't live with you!.... I hate you!....._
Hannayena duka biyu na ɗaga na kulle kunnuwana hawaye na ta zuba akan fiskata sosai, na kuma matse idona na hau giɗa kai kamar ina gabansu ina ce, "ba ni ba ce, ba zan iya kashe Momyna ba, ina sonta, ba zan aikata ba, bani ba ce", maganar da na ke ya dawo da hankalin Haidar kaina, da sauri ya tashi tare da matsowa kusa da ni yana kiran sunana, amma sai maimaita kalaman na ke yi ina hawaye.
Ganin kamar hankalina ba'a jikina ya ke ba yasa Haidar ɗaura hannunsa a kafaɗana, wanda yin hakan ya sanya dawowa cikin hayyacina, na buɗe ido cikin firgita ba tare da na sani ba na rungumeshi ina kuka, Haidar bai yi ƙoƙarin hanani ba, a hankali ya daura hannunsa akaina yana rarrashina, zuciyarsa cike da tausayina. Khairat ma da gudu ta iso tana kallona da damuwa.
Da hanzari na raba jikina da na Haidar bayan na gama dawowa hankalina, na yi gefe da kai ina share fiskata, "yaya Haidar don Allah mu koma gida" na samu damar faɗi domin ba na son na cigaba da kallon furannin.
Haidar ya fiskanci akwai abun da na tuna game da rayuwata, don haka ya ce, "ba mu daɗe da zuwa ba fa, mu canza guri to ƙanwata" ya faɗi domin ya san ba zan sanar da shi komai ba, kuma baya son ya ga ina hawaye, ya kawoni gurin ne don ya sani nishaɗi ba wai na kuma shiga matsala ba.
Daga nan ne ya ja hankalina ya kai mu sauran guraren wasan da ke cike da nishaɗi da annashuwa, kayan wasa masu ƙayatarwa, zagayen doki, motoci ƙanana, da wuraren ruwa masu ɗaukar ido, da fatan farin cikin da ya fara wanzuwa à gareni ɗazu ya dawo. Ai kuwa ya yi nasara, domin kuwa na yi na ji daɗi sosai wanda da daɗewa ban yi sa ba.
INNA JUMMAI.
Tun bayan rasuwar Halima Inna ta dawo kamar kurma, ba ta cika magana da ta zauna sai damuwa, kuka, ƙunci, da zurfin tunani duk sun zama abokan zamanta, har gwara na baya akan yanzu, wai fa shikenan ta rasa 'yarta ɗaya tilo, wacche ta ke matuƙar ƙauna fiye da kanta.
Hajiya Luba ce mai taimakonta baiwar Allah mai tausayi, ranar da ta zo duba Halima da fatan mahaifiyarta ta yafe mata, kawai ta ji labarin mutuwarta, abun ya ɗan taɓata, daga baya da ta zo ta gaishe da Innar ta kawo mata kayan abinci wanda za ta buƙata daidai ƙarfinta, wannan taimako ne ya taimaki Inna, da ba don haka ba da yanzu ƙila itama ta bi 'yarta don yunwa, ko da ya je wani yunwan ma wuri ya ke samu.
Kalaman Halima sun mannewa Inna a rai sosai, a duk lokacin da ta zauna sai su taso mata a zuciya, suna buɗe ƙofofin abubuwan da su ka wuce, wanda ta daɗe da gudu daga tunaninsu.
Yauma kamar kullum, tana zaune a gefen ɗakinta saman tsohuwar tabarma, tarihi ya sake dawar mata, tun ranar da mahaifinsu Nuriyyah malam Abbas ya aureta, irin wahalar da ta ganawa 'ya'yansa. Aiken da ta yiwa ƙaramin yaro kasuwa, ba tare da duba ƙan-ƙantarsa ba, ko kuma tunanin inda ta aikesa da abun da zai iya biyowa baya.
Wanda hakan yasa mota ya bugesa kuma ya rasu a ranar, babu abun da ta ji à ranar na rashin daɗi ko daidai don Annur ya rasu. Ba ta saduda ba ta cigaba da yiwa Nuriyyah abubuwan wahala na rashin tausayi, har izuwa lokacin da Allah ya nufa rasuwar mahaifinsu, sannan daga baya ta korata babu imani babu tsoron Allah, bare wani tunanin yadda rayuwar Nuriyyah zai kasance a matsayinta na mace kuma ƙarama.
"Inna lillahi wa'inna ilaihi raju'un, inna lillahi wa'inna ilaihi raju'un" abun da Inna ta ke nanatawa kenan tana hawaye, "Allah na tuba, Allah na tuba, Allah ka yafe min" haka yauma ta rinƙa faɗi tana kuka, tabbas ta gane kuskurenta, haƙiƙa zuciyarta ya cika da nadama.
"Ni ce SANADIN ƘADDARATA da kaina, na gallazawa yara a ganina su ba nawa ba ne, ba ni na haifesu ba don haka kome zai samesu ba ni da matsala akai, na yi sanadin mutuwar ɗaya ba tare da hakan ya dameni ko kaɗan ba, sannan na kori ɗaya marainiyar Allah wacche ta ke da buƙatar ja a jiki da kuma kulawa. Na ɗaura 'yata cikin tarbiyyar da aganina shine daidai, sa ga shi yau SANADIN tarbiyyar ne Halima ta rasu. ƘADDARATA ya zama haka ne domin ni ce na saƙa shi da kaina". Ta faɗi tana fitar da numfashi da tsanin nadama.
"Na yi dana sani a rayuwata, ya Allah ka yafe min, ka bani damar haɗuwa da Nuriyyah kafin nima na bar duniya, ya Allah kasa tana cikin ƙoshin lafiya, ya Allah ka cika min wannan fata nawa, insamu damar sanar da ita kalma ɗaya tak... ki yafe min! Ya Allah karka karbi raina alhalin ba ta yafe min ba".
Sai kuma ta yi shiru, numfashinta na nauyi, sannan ta ƙara da cewa da murya cikin rauni, "ya ubagijina kada ka barni da wannan nauyin a zuciyata" ta faɗi tana sa kuka mai ban tausayi, tana à haka ta fara jin hayaniya a ƙofar gida na mutane ana rafka sallama, sai da gaban Inna ya faɗi ta dakata da kukan da ta ke ta share hawaye sannan ta miƙe tana amsawa ta ɗauki himar ta yi waje
Last page
___________________________________________________
Tom kuna ganin kalaman Momy bai yi tsauri ba kuwa?.
Ga Nuriyyah da Haidar kuma, me za ku ce game da su?.
Inna ma ta yi nadama fa, to a tunaninku me ya kawo mutanen nan? Kun ji tausayinta?.
_*🌹𝑍𝑎ℎ𝑟𝑎-𝑡𝑢𝑙-𝑄𝑎𝑙𝑎𝑚🖋️*_