9
*'KAFAR HAGU*
©️ Meenat A. 'Yandoma
Wattpad: Meenat_A_Yamdoma
Arewapen: @meenatyandoma
MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION
🅿️age 9
...Kukan Zinatu da Magajiya ta ji shi ya fito da ita rikice. Rauda kuwa ita mutuwar tsaye tayi, "ki fito mu tafi Rauda, baba ya aura miki Jatau" Ji, ganinta ɗaukewa suka yi na wurin gadi. Doguwar ajiyar zuciyar da ta saki sai gani suka yi ta yi baya luuu! Cikin tashin hankali Zinatu tayi saurin rikota. Girgiza ta ta hau yi zuwa can ta sauke ajiyar zuciya kafin hawaye su biyo baya. "Zinatu Jatau dai da na sani tsohon ɗan caca?" "Rauda shi fa, amma bazan taɓa bari ki aure shi ba sai inda karfina ya kare. Ki tashi mu je gidan Jatau domin ta kansa zan fara"
"Tsaya mana. Ban gane ta tashi ku tafi ba, da izinin wa za ki fita da ita" Magajiya ta karasa maganar ta na rirrike Rauda. "Kin ga ban kasa da ke ba Magajiya. Kada ki ce za ki shiga harkar da bata shafeki ba, ke kika haifa ta ne da za ki ce kar ta bini" Zinatu ta karasa maganar tare da bankawa Magajiya harara. "Wanda ya ajeta shi ya bani umurnin in kula da ita kada in bari taje ko kofar gida, don haka babu inda zata je." "To Magajiya wannan fita dai ta zama dole. In kuma kin ce ba haka ba don Allah ki dakatar da mu" ta karasa maganar tare da miƙar da Rauda ta fizgo mata gyalenta. Babu yadda Magajiya da iya tana ji tana gani haka suka fice a gaban idonta. Ta san wacece Zinatu karamin aikin ta ne su tarawa kansu jama'ar gari. Tamkar zasu tashi sama haka take sauri, Rauda kuwa jikinta ya yi sanyi. Tun kafin Gaga ya tafi jikinta ya gama bata akwai matsala.
"Kai! Shiga gidan nan ka ce a na sallama da Jatau" Maganar Zinatu ta dawo da Rauda daga duniyar tunanin da ta lula. Ba musu yaron ya fada cikin gidan, jim kaɗan sai ga shi ya fito. "An ce ga shi nan zuwa" "Ungo nan" Zinatu ta mika masa Naira ashirin. Alamun tafiyar da suka ji shi ya tabbatar masu da Jatau ne.
Watse haƙoransa da suka gama dafewa da goro yayi. "Zinatu ce da amaryata. Ai kamata yayi ku shigo daga ciki. Haka kawo muni ita aka yi?"
"Kai Jatau dakata! Zinatu ta fada a fusace" "ka ja ruɓaɓɓen bakinka ka rufe a wurin nan. Wace ce kake kira da amaryarka? Duk nan ka ga wadda ta yi kala da matsiyaci irinka?" Dariyar tsoffin 'yan duniya ya yi. "To mara mutumci wadda ta yi gadon rashin mutumci. In amaryta kika kawo min bani a bata ki wuce na gode ba sai kin shigar mini gida ba" ya karasa maganar ya na kokarin kamo hannun Rauda. Wata wuta ya gani tare da ganin duhu ya gifta masa. Sakamakon marin da Zinatu ta tsinkesa da shi. "A yanzu nasan za ka fi gane gargadin da na zo yi maka babu wasa a ciki. Ka gaggauta kwance wannan wulakantaccen auren da ku ka kulla, in ba haka ba kasan waye Gaga lahira zata yi bako" Gudumemiyar ashar Jatau ya ɗora. "Ni ki ka mara?" Ya karasa maganar tare da nuna ta da yatsa. "An mara ko zaka rama ne?" Ta karasa maganar ta na me cire ɗan figigin gyalen da ke kanta ta ɗauka shi a ƙugu. Cikin rufewar ido Jatau ya kawo mata mari, kafin ya ankara ta fizgoshi sun shiga dambatuwa. Rauda kan ta rikice wannan tashin hankali har ina, dama wannan halittar ce Baba ya aura mata? Hayaniyar dambe da suke yi ita ta fito da Matan Jatau. Ihu suka hau yi a kawo masu ɗauki, kafin a dauki dogon lokaci kofar gidan ta cika da mutane. Da ƙyar da jiɓin goshi aka kwaci Jatau, domin tsohon jini da baso ba ɗaya ba ne. "Kadan ka gani muddun ba zaka kwance auren nan ba" Zinatu ta fada ta na me kwance gyalen da ke kugunta. "Dan..." Ya danna mata zagi. "Bazan saki ba kuma yau zan sami ubanki a kawo mini mata ta a gaban idonki"
"Mai gida ban gane ba. Wa ka aura kuma ba dai wannan tsohuwar ƙaruwar ba." Hinde ta karasa maganar tare da nuna Zibatu. Garam! Kake ji. Zinatu ta make bakin Hinde har da jini. "Ki ga karuwa a gidan Uwarki. Tsoffin banza matan mashayi kuma ɗan caca." Firgita Hinde ta yi a rikice ta fada gida da gudu, domin ta kula In ta tsaya wannan bata da hankali. Uwar gidan Jatau ce ta lalle shi. "Jatau da gaske aure ka yi ba tare da ka sanar da mu ba?"
"Kwarai kuwa Asibi. A caca na ciyota ku shirya na yi auren huce haushi yarinya ɗanya shakaf! Salati da Sallallahu Asibi da sauran jama'ar wurin suka ɗauka a tare! "To munafukai kowa ya watse ai kunji abin da kuke son ji." Nan fa Jatau ya hau borin kunya ya na korar mutane. Hannun Rauda Zinatu ta kama suka nufi gida. A kofar gida Zinatu ta hango ƙwarta don haka Rauda gida ta shiga bakinta ɗauke da sallama. Gwoggo da ke duke tana wanke kafa jin sallamar Rauda ta yi har tsakiyar kanta. A rikice ta ɗago kai, ba shiri ta yi zaman daɓaso cikin ƙasa. "Innahu min sule... Na rantse da abin da zai kasheka babu hannuna a cikin auren da aka yi mata, laifin uwarta ne Baraka kina ina?" Wani fitsari me zafi ne ya wanke mata ƙafa. Ita dai Rauda mamaki ne ya kara kamata jin abin da Gwoggo ke fada. "Ai Gwoggo ba ki ga kome ba sai Allah ya yi wa Gaga dawowa. Ba dai kun kulla wannan auren ba?"
"Zinatu kuna nufin ba tare ku ke da Ghali ba?" Gwoggo ta karasa maganar tana kokarin miƙewa. "Ki saurari zuwansa, fitsarin da kika yi sharar fage ne. Idan kika ji saukar wuƙa a bisa wannan karkataccen wuyan naki a lokacin za ki gane Annabi Isa ba ɗan Allah bane"
"Aniyar moɗa ta bi randa. Tuf da baƙin yawu, Uwarki Zuwaira ki ke yi ma wannan fatan"
"Aa fa Gwoggo! Me nayi na ji ana luƙa mini zagi?" Zuwaira da ke kokarin fitowa daga ɗaki ta fada. " 'yar Kukar da kika haifa ce ta ja miki jifa." “au, sa munjaye ce wa za ki yi 'yar kukar da muka haifa da ɗanki"
"Zuwaira ni kike gayawa magana?" "Kyaleta Gwoggo! Ai duk ita ta karasa lalata Zinatu. Yanzu haka Jatau ne ya zo ya sanar da Ni irin rashin mutumcin da yarinyar nan ta iske shi har gida tayi masa. Jira ya ke a fito masa da matarsa"
"Wai Jatau ɗin kara biyo mu yayi har gida. Gaskiya ne zan nuna masa barikina ba irin ta shi ba ce."
"Kinga Zinatu ban ce ki fita a cikin sabgar nan. Ba?" Zuwaira ta fada rai a matukar a ɓace. "Tana jinin Mayu ta ina zata kyale min ɗiya ta yi zaman aure. Ina kyautata zaton duk yadda aka yi ku ɗin nan kun haɗa jini da Mayu" Baraka ta fada. "Baraka mu ne Mayu?" Zuwaira ta fada tare da nuna kanta da yatsa. "Akwai wata Zuwaira da Zinatu a gidan nan bayan ku?" Cewar Baraka.
"Ni fa kome za ki faɗa ki faɗa. Amma sai inda karfina ya ƙare wurin kwatowa 'yar uwarta 'yancinta" Zinatu ta karasa maganar tare da jan hannun Rauda. "Kinga irin Maitar ko? Ban raba ɗaya biyu ba ku dai annoba ce Malam ya kwaso mana."
"Baraka idan kika ƙara kiranmu mayu gaskiya za mu tuna baya a gidan nan." "Na fada na ƙara Mayu!" Cakumar wuyanta Zuwaira ta yi suka hau kokawa. Iliya kuwa mamaki bai wani kama shi ba domin inda sabo sun saba. Gwoggo ce ta ke fadar zata dauko mabugi in ba su tsaida faɗan da suke ba. Sai dai a banza domin ba su ma san me take fada ba. Cike da karfin gwuiwa ta ɗauki wata tsabga ta yi kansu. Bangaza ɗaya aka yi mata ta faɗa saman randar ruwa, rushewa tukunyar ta yi Gwoggo ta dira a saman ɓuraguzan tukunyar. "Innalillahi! Iliyasu gini ya faɗomin, ganina ya ɗauke na makance matanka sun kashe ni" a rikice ya yi kan Mahaifiyarsa. Wannan damar Zinatu ta samu ta figi wani rusheshen faskare ta yi waje. Zuwaira da Baraka da ke dambe. Tsayar da shi suka yi tare da mara mata baya a guje. Iliya kuwa bai san lokacin da ya kyale Gwoggo ya bi bayan Zinatu ba. Sai dai kafin ya taro ta tuni ta fice.
"Maye biyomu kayi? Ni na Fika bariki " Zinatu ta fada da ƙarfi. Ganin ta da yayi da Faskare a hannu ya saka Jatau ja da baya. "Ba tafiya za kayi ba tsayawa zaka yi ka amshi abinda ka zo amsa" ta karasa maganar tare da saukewa Jatau faskaren. Taga-taga JATAU ya yi kafin ya baje ƙasa tim!....
Saura page ɗaya free page ya kare. Ku saka 500 a wannan account din 8133562798 Palmpay Amina Abubakar
MEENAT A. 'YANDOMA
***