KUNCIN ZUCI

Kuncin zuci

by @bintuuu

Bayan Ahmad ya gama saka mata takalmin sai Imam dake tare dasu agurin yace "Mu qarasa mota" Abba ya amsa masa sannan suka juya tareda nufan gurin da motocin nasu ke ajiye, dakyar Na'ima ke taka kafanta cikin sneakers din Ahmad da suka mata yawa, Ahmad din dake tafe a bayanta ji yake kaman ya kamota ganin yanda jikinta ke rawa har sannan amma sai beyi hakan ba, suna isa gaban motan sai kira ya shigo wayan Iman daga squad leader'n nasu yana dagawa yace masa "Rabi'u is coming now kuyi hanzarin maidasu gida, jejin nan is too risky for them" Imam ya amsa da "Yes sir" da haka suka hango Rabiun yana tahowa garesu da dan gudunsa, sai da Abba ya shiga seat din tsakiyan sannan  Ahmad ya taimakawa Na'iman ta shiga sai ya zauna a gefenta suka sata tsakiya, su faruk, Lamin da Adam ma cikin sauri suka shiga motan Imam ya tayar while Rabi'u ya zauna abayan riqe da bindiga ahannu, da haka suka sake daukan hanyan komawa Abuja awannan daren...Basu suka isa gida ba sai misalin 2 na dare, aikuwa su Mami na Jiyo shigowan mota gidan duk suka fito compound da sauri cikin tararradin me zau tarar, su Abu har da gudunsu suka fito daga side dinsu, anan compound Imam ya faka mota suka bude sai Ahmad ya kamo hannun Na'iman yana taimaka mata gurin saukowa daga motan, ganinta yasa Nafisa ta buga wani uban ihu tayi kanta tareda su Abu da Husna, group hug suka mata dukansa na kuka amma na Nafisa yafi tashi, Mami ma da saurinta ta qaraso ita dasu Hajiya, Anty Amnah, Fatima da Lauren, amma Mami bata jira sun sake Na'iman ba tayi joining group hug din tana hawaye itama, Na'ima ba bakin magana sai kuka har jikinta na jijjaga, Abba ya matso yace "mu qarasa ciki ta huta tukunna" sai sannan suka saketa amma Na'ima na ganin Mami ta sake fashewa da wani kukan me karfi tana nufan jikinta, Ahmad na tsaye har sannan a gefenta tare dasu faruk, Mamma na share hawaye ta matso ta dafa bayan Na'iman tana dan bubbugawa da zummar lallashi, ahaka Na'ima na kuka suka dunguma gaba daya zuwa cikin gidan, anan falon Mami ta zaunar da ita sai kowama yayi hakan, kowa sannu yake mata ganin jini a gefen bakinta gashi duk ta firgice na wuni daya, Nafisa da saurinta ta nufi stairs bata dade ba tadawo riqe da hula ahannunta ta cire mata jacket din da ke daure akanta, Mami ta hau gyara mata gashinta da yayi daddaya kwance har bayanta sannan Nafisa ta cusa mata hulan, kowa sannu yake mata afalon sai Baba yace "ku kaita daki tukunna, likita na hanya yanzu haka" dan yanda Na'iman ta firgice sai ta baka tausayi, Mamma sai kallonta suke da Anty Amnah da haka su Mamin suka sake riqeta suka kaita dakin Ahmad na binsu da kallo shima..Dakin Mamin suka kaita ita da kanta ta hada mata ruwan wanka a bath sannan Na'iman ta nufi toilet din tana dingisawa sai Nafisa ta kamota tace "muga kafan" nan ta zaunar da ita a bakin gadon suna dubawa tareda Anty Fatima da Anty Amnah, sai duk jikinsu ya qara sanyi ganin ciwukan da taji a tafin kafar ta ta, Mami tace "Allah zai saka miki kinji" ai kamar jira Na'ima take sai ta fara wani kukan kuma suna lallashinta, dan abune da ya firgita ta sosai kuma yazamo memoryn da bazata taba manta wa dashi a rayuwanta ba...Da likita yazo ya dubata tareda tambayan abunda ke damunta duk ta fada masa dan wani irin nauyi kanta yake mata kamar ya rabe gida biyu sakamakon abunda aka shaqa mata, haka ya mata allura tareda wanke ciwukan kafan nata sannan Mami tace Nafisan ta kawo mata tea tasha, da haka Mamin tace ta kwanta agurin ta su zasu qarasa kwanan a falo su dasu Hajiya dan Mamma tana falon Mamin ma a zaune tare dasu Umma jummai... su Abba dasu Ahmad daman anan falon suka zauna dan jiran isowar sauran squad din suje can police station din, har asuba suna nan zaune a main falon gidan dan ba wanda ya yi bacci kuma, su Ayuba da Nasir sai jajantawa suke while Abba na musu bayanin yanda lamarin ya kaya, bayan sunyi sallah a masallacin gefen gidan basu dawo ba sai da gari yayi haske, nan kuma Osagie yayi waya ya sanar dasu zuwansa da leader'n da ya jagoranci operation din...Na'ima tunda ta samu bacci itama bata tashi ba sai da kowa yayi sallah dan Mami hanawa tayi a tasheta saboda kan nata da yake ciwo, da suka idar da sallah gari ya fara haske Mamma tace zasu koma gida suma, Mami na godiya suka miqe gaba dayansu daga falon suka qarasa cikin dakin dan ganin halin da Na'iman take ciki, nan suka samu har sannan tana baccin, qirjinta sai hawa da sauqa yake alamun baccin me nauyi ne ya dauketa, Mamma na kallon ta cikin tausayawa tace "Allah ya qara kareki Na'ima" duk aka amsa da Amin sai Anty Amnah ta qarasa tana duba qafan nata, nan kuwa Na'iman ta motsa tareda bude idanunta da sukayi jaa, ganin mutane a dakin sai ta miqe ahankali tana duqar da kai Mami ta iso gareta tana mata sannu, sai da Mamma ta sake mata wasu addu'an sannan suka fita daga dakin ita dasu Fatiman, Mami ma ta miqe ta bi bayansu, A falon qasa suka tadda su Baban da matasan zazzaune tareda Osagie dasu Imam, tamabayansu Mamin sukayi yanda Na'iman take suka basu amsan ta tashi ma sannan suka fice daga falon Mami kuma ta wuce kitchen dan su hada breakfast itada lantana, Ahmad dai jefi jefi yake daga kai ya kalli stairs din, zuciyarsa na matuqar son ganinta, yana son ganin lafiyanta ko zai samu nutsuwa shima, he really wants to hold her ya lallasheta sosai, da tararradin ya kwana a zaune jiyan gani yake kaman ba abunda take buqata irin a lallashetan sosai...su Abu ne suka miqe suka tafi saman dan su dubo Na'iman, nan dakin suka sameta tana sallah su Nafisa na zazzaune a gefenta itada Husna da Lauren, akan stool din bakin mirror Abu ya zauna suka jira ta idar sannan suka gaisheta, ahankali Na'ima ta amsa sannan Al'ameen yace "Sannu Anty Na'ima, sun kama daya daga cikinsu ma yanzu haka yana hannunsu a station" Nafisa tace "Haba dai, sauran fa" Abu yace "Basu samesu ba amma an tura wasu nemansu" Na'ima kanta na qasa ta kasa cewa komai ma sai Mami ta shigo tace "ku barta ta huta mana" ta kalli Na'iman tace "Habibti hau gadon ki kwanta kinji" sai ta girgiza kai tace "Nan ma yayi, Ina kwana" Mami ta amsa sai su Al'ameen suka miqe suka fita daga dakin...
Da wuri Mami suka gama breakfast din sannan suka kai gurin kowa dake gidan, Ahmad dai kadan yaci nan zaune a part dinsu Faruk da suka koma, qara kiran wayan Na'iman yayi still yaji a kashe kamar yanda yayi taji tun dazun, Na'iman ma saida Mamin ta matsa  mata sannan taci abincin kadan sannan ta miqe ta saka babban hijabi ta fita gurin su Baban da suka aiko taje suna falon Abba, tareda dasu Nafisan sukaje nan suka samu duk an hallara ita dasu Mamin ake jira, ga Osagie na zaune shima da jami'an guda biyu, nan suka fara tambayan Na'iman cikin nutsuwa batun abunda ya farun, tana hawaye tafara musu bayani tun daga lokacin da su Tiyagahn suka kamata har zuwa sanda ta gudun, kowa sai kallonta yake cike da tausayawa jin  yanda Allah ya kubutar da ita, tana kukan Osagie ya sake tambayanta meyasa ta fitan, nan ta qara qarfin kukanta tana girgiza kai tace "Wallahi bansani ba, bansani ba nima" sai duk akayi shiru a falon Mami na dan bubbuga bayanta, yanda Na'ima ke kuka a falon sai ta bawa duk me kallonta tausayi dan har sannan bata gama dawowa hayyacin ba gashinan a bayyane daga yanayinta kadai za'a fahimta, Osagie ya sauke numfashi yace "Ku dan bamu guri da ita" Abba yace "Baku yarda bane? Yarinyar nan is telling you nothing but the truth Osagie, I know my daughter" Alhaji ya amsa da "Tun Na'ima na yarinya har zuwa yanzu bawanda zai ce maka cikin halayenta akwai qarya" Ayuba ya jinjina kai "Wannan gaskiya ne" Hajiya tace "wallahi hakane Alhaji sai ma a zalunce tayi shirun ba dai tayiwa wani ba" Mami tace "Kuma fitan da tayin duk yana daga cikin zaluncin da aka mata, officer baka taba coming across sihiri bako?" Osagie yace "Ma'am hakan baya daga cikin aikin mu ne" tace "Amma ai baza kace min kaf shekarunka na aiki har zuwa yanzu baka taba samun case irin wannan ba" ya amsa da "har fiye da wannan ma muna samu, but right now i want to be sure of everything ne" sai Abba yace "Then saboda zargin ko wanin mu na buqatar sanin ko da hannunta ne aciki ai zakuyi hakan ko? Toh mu mun amince babu hannunta aciki, yarinyar muce, mu mukafi kowa sanin halinta, buqatar mu a yanzu a nemo mana marasa imanin da sukasa  aka kaita wannan jejin" sai Osagie ya sake sauqe numfashi ganin Abba bai bashi qofar dazai sake ja dashi ba, sai kawai yace "shikenan, we'll see to that as soon as possible" da haka Abba ya gyada kai kawai sai jami'an suka miqe tareda nufan kofa, nan Mami ta sake dago Na'ima tareda kama hannunta suka fita daga dakin tana hawaye Ahmad na bin ta da kallo...Da misalin qarfe sha daya na ranan sai ga su Mummy sun dawo gidan zuwa taya murnan bayyanan Na'iman, suna zaune a  main falon gidan a lokacin suka shigo cikin hijabansu itada murya da Ummi sai Laila dake biye dasu cikin matsattsun kayanta itama, Na'ima dai kallonsu kawai tayi amma bawai ta kawo komai a ranta ba, time din su Ahmad ma sun koma hotel tareda dasu Adam, Mami ce ta sauqo nan falon ganinsu sai ta dan daure fuska ta qaraso, Su murjan ne suka fara gaisheta ta amsa sama sama dan Nafisa kan ma dauke kanta tayi tareda miqewa ta nufi kitchen, bayan sun gaisa sai Mummy tace "Sannu Na'ima, Allah ya qara kiyaye na gaba kuma" ahankali Na'ima tace "Ina wuni" sai Mummyn bata amsa ba ta kalli Mamin tace "su Hajiya Amina sun koma kenan" itama Mamin bata kula ba saida taja iska tukunna tace "Eh, dazu da safe" Laila na zaune tana facing din Na'ima sai kallonta take ita kuwa idonta a qasa ma dan itadai tun zuwan cikin familynnan taqi jinin shiga sabgan iyalan Daddy, sai lokacin Laila tace da Mami "Ina wuni" sai Mamin ta dauke kai tace da Lauren ta bi Nafisa kitchen su kawo musu ruwa, sallama akayi a falon su Ummi suka shigo tareda duk sauran qannen Ahmad din both siblings da step ones din, nan falon suka zauna Mami na musu sannanu da zuwa sai Fatima ta miqo flask din hannunta a Mamin tace "Mami gashi Mamma tace akawo mata" da fara'a Mamin ta karbi flask din tana fadin angode sannan aka gaggaisa, anan zaune falon Mami tayi serving din Na'ima hot pepper soup din tace taci tana ganinta, su Laila sai ido ganin yanda iyalan baba ke nan nan da Na'iman kowa na mata sannu, Salma ce kawai me shiru acikinsu tana binsu da kallo itama, Mummy ce ta daure tace da Mamin "Ma Sha Allah ai da lafiyanta ma sai hamdala" sai Mami tace "Alhamdulillah, ai gobe ma in Allah ya kaimu zata tare a dakinta bi'iznillah" Mummy ta gyada kai tana fadin "Ma sha Allah, dafatan dai ankama wa'inda sukayi laifin" tace "Suna station ma yanzu haka ai" sai Mummy tace "Ayya, Allah ya kara karewa" duk aka amsa da Amin sannan ta miqe tareda su murjan sukace zasu tafi, cike da sanyin jiki Laila ta miqe itama tace "sai anjima Mami" sai sannan Mami ta amsa mata da "toh sai anjima" sannan suka fice daga falon tana kallonsu, duniya abun tsoro....